← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 68

Sashe 27

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"da sauki Daddy naji sauki zan koma sashena ne"ta fice babu karfi jikinta ta fito momy da husnah ne a kan dadduma ta tasa husnah gaba tayi sallah ta mike ta cire hijab ta nufi kitchen da sauri waige waige takeyi cikin saa taga ruwan zafi a kan gas an kashe ta diba ta fito Abraham tagani tsaye "mai kakeyi a nan"ruko kwankwasonta yayi yace "naga kuna addua ne kinga in kina adduar nan babu yadda zaayi in shigo "tayi jimm kadan tace"zan rama maka abinda wancen yayi maka ne"ta kalli jajayen idonsa yaseer ta hanga yana kokarin shigowa gate din gidan cikin sauri ta karasa momy ganin husnah ta fita tabi bayanta yaseer na juyowa tana antaya masa ruwa a kafadarsa wani azaba da radadi yaji yana ratsasa ya daga kai yaga waye husnah ya gani tsaye tace "bansoba fuskarka naso in watsawa yadda ka konawa Abraham dina fuska"Abraham na tsaye tana juyowa taga yana mata tafi murmushi yayi ya fuzgota jikinsa yace "ai ban koneba koda na Kone ni zan warke amma shi bazai warkeba"kici kicin kwacewa daga jikinsa takeyi momy ganin haka kawai ta juya tabarsu anan cikin tashin hankaki ta nufi cikin gida husnah ta kona yaseer a jikinsa da ruwan zafi? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ta wuce ciki
.tsamm ya riketa yana addua Yana tofa mata tana kokarin kwacewa "ni ni kadaina watsamun miyau"Abraham ya dumfari yaseer gadan gadan ganin wuta na fita a bakin yaserr ya koma baya yana huci tabbas yasan bazai taba sukuni da husnah ba tunda wanan na gidan wata dabara ta fadowa Abraham cikin fushi yabar wajen yana fita ya rikida ya koma yaseer sak ya nufi gidan momyn yaseer cike da kwarin gwiwa kawai zaije yasameta husnah ta dawo gidanta yadda zai samu damar soyewa da husnarsa batare da kowa ya Gane bashi bane,

cikin karfin hali ta funcike ta barsa nan tana hararsa "karka sake tabani"dariya tabashi ma yasan kila ba ita bace ya taba kafadarsa dake masa zugi ya nufi sashensa yau ma kamar jiya ya ganta a gaban sashen sa tayi masa murmushi wanan karon yaseer ya mayar mata batare da wani tsoro ba yace "narjisu ko?"ta jinjina masa kai tacev"katafi gidan mahaifiyarka yanzun nan kasameta dikda nasan Abraham ya rigaka zuwa"ta bace hankakinsa ya tashi mai aljanin nan yajeyi gidan mahaifiyarsa?shiru yayi tsaye ya laluba aljihun rigarsa yaji makulli kawai ya juya a hanyar fita yaci karo da hafeez da mahaifinsa da kuma kanin mahaifinsa daddy ya fito daga gida cikin faraa ya tarbesu

mari momy ta zabgawa husnah tana shiga ta fincikota husnah hankalinta ya tashi take taji wani yarrr tsoron mahaifiyarta ya shigeta taga bacin ranta karara a kwayar idonta tabbas tasan abinda tayi yasa momy ke fushi da ita dole zataje tabawa yaseer hakuri momy gani tayi husnah ta zube a kasa "momy kiyi hakuri bazan sake ba"cikin bacin rai momy tayi mata wani kallo ta barta nan ta dauko mp ta kunna karatun alkurani a
dakin ta nemi waje ta zauna husnah cikin sanyin jiki ta mike ta shige daki ta fashe da kuka......

*WANAN LITTAFIN NA DUHU NA KUDI NE GA MAI BUKATA YA BIYAV300 KACAL YA MALLAKI NASA WADDA TA KARANTA BATA BIYABA BANYAFEBA*

07042277401
08036953516

*SLIMZY*✍🏻

26
ta jikin window kanwar yaseer taji shigowar mota gate din gidan tad'an leka lokacin hajiya saude na zaune tana lalubar number a wayarta ta d'ago kai tace "yusrah banason gulma karar mota ne baki taba ji ba ko yaya?"yusrah ta koma ta zauna cikin damuwa tace "momy yayah yaseer ne yazo fa?"da sauri momy ta kalleta tace"yaseer kuma?menene yazo dashi nan gidan bayan yanzun muka baro gidan toko wata matsala ta faru tsakaninsa da husnah ne ko jikin nata ne?"cikin faduwar gaba momy ta gimtse maganarta tozali da tayi da yaseer wani yarrr taji ganin tsayuwar da yayi tana binsa da kallo yaseer baya wanan tsayuwar Abraham ganin kallon da momy keyi masa karta gane ba yaseer bane yasa ya Tako cikin dakin tabi kafarsa da kallo takalmi mai rufi ne yasa tabbas kayan dake jikinsa ne amma kamar ba yaseer ba ya zauna ya dafe kai cikin yanayi na damuwa Momy tace "yadai yaseer naganka a yamutse a hargitse Kamar ba kai ba ni jinakeyi ma kamar kaima aljanun na neman shafarka"Abraham ya shafa kansa ya saita natsuwarsa da zuciyarsa dake tafarfasa yace"momy ba dole ki ganni cikin wanan yanayin ba?kina gani fa abinda ke faruwa yanzun husnah ta konani da ruwan zafi"momy tw zaro ido tace"ruwan zafi fa kace?"ya jiniina mata kai ya nuna masa kafadarsa daidai inda husnah ta kona yaseer rigar a jike momy tace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"Abraham yayi murmushi ya hade rai yace"ni momy gaskiya so nakeyi husnah ta dawo gidan nan da zama kawai inaga zaifi idan yaso zan rinka zuwa nan ina jan raayinta har insamu ta dawo hayyacinta tunda kinga gashi zaa maida aurenmu kuma can momy bata wani kula da ita"hajiya saude ta jinjina kai cike da gamsuwa tace "tabbas munyi wanan maganar da ita ban sanar maka bane tukunna sai gobe munyi shawara dasu innah akan maganar amma tunda haka ne ni zan daukota in dawo da ita nan inga ta inda aljanin nan zai rinka shigowa dan kwana zatayi da karatu. kurani"Abraham ya cije lebe ya kalli yusrah data tsura masa ido tun shigowarsa take kallon yanayinsa gabanta na faduwa suna hada ido ta sadda kanta kasa yaji alamun kamar ta fahimci ba yaseer bane ganin kallon da yayi mata ta shagwabe masa "yaya yaseer ni tunda ka shigo ma baka wani kulamu ba nida nusrah"Ajiyar zuciya ya sauke "bana cikin hayyacina ne shiyasa gaba daya cikin damuwa nake yanzun zan tashi in koma"momy ta jinjina kai tace"ya mai jikin?"yana kokarin mikewa yace"da sauki nabarota zataci Abinci zanbkoma Dan Allah momy ki taimakeni ki dawomin da husnah nan"ya marairaice momy tayi dariya tace"mara kunya kawai"ya dagawa nusrah hannu tana daddana waya yace"saida safe Antyn waya"murnushi tayi masa ya daga musu hannu momy ta sauke ajiyar zucuya tace"ni dama nayi tunanin hakan sam ban son zaman husnah can gara ta dawo nan,

yaseer kuwa motarsa ce ta tsaya yana kokarin gyarawa cikin rud'ani yake da tsananin tsoro yana kaiwa da komowa a bakin titi babu kowa ga gari ya soma duhu ya ciro wayarsa yayi dialling wayar momy yaji ko lafiya akace masa yaje gidan momy yana tsaye irin motarsa sak tayi parking a gabansa yabi motar da kallo yana sauraren yaga waye da irin motarsa yazo har inda yaje Abraham ne ya fito da irin kayan jikinsa sak kamanninsa sak wani furgici yaseer ya shiga yana kallonsa cikin duhu ido waje cikin tsananin tsoro yace"kai wannene?"wata dariya Abraham yayi yace "badai bakajin magana ba zakaja dani ko? to mu zuba mu cigaba da fafatawa naje na aiwatar da nufi na, wanan motar da kake gani dama ka barta a nan dan bazata gyaru ba kwata kwata"ya kyalkyale da dariya yana nuna yaseer da tuni gumi ya jikasa "Mai mai kaje ka aikata karka kashemun iyaye karka kuskura zan kasheka"Abraham yana dariya yana nuna yaseer dake karamar hauka ya bace tare da motar tasa yaseer ya bugi jikin motar gumi ya karyo masa ya rasa inda zaisa kansa kaiwa da komowa kawai yakeyi yana juyowa yaganta a gabansa suna hada ido kafin yayi magana batace komiba ta wuce inda ya bude murfin motar tana kallon motar cikin duhu wani haske blue na fitowa daga idanuwanta narjisu ta dubesa tace"zaka iya shiga katafi dikda kayi latti"ta bace yace "narji....."kafin yayi magana ta bace ya dafe kansa meyasa bata tsayawa saurarensa tana tsaye a gabansa murmushi tayi ta harde hannuwanta ganin yana kokarin fadawa kogin tunani ga tsananin tsoro a tare dashi yasa tayi gyaran murya take ya dawo hayyacinsa yana waige waige ya rufe murfin motar ya shiga cikin ikon Allah yana tada motar ta tashi ajiyar zuciya yayi yadau hanya dikda akwai nisa tsakanin su amma ko ganin gabansa bayayi....

******
cikin kissa hajiya rabi ta hada tray da drinks bayan daddy ya shigarda magabatan hafeez cikin babban parlonsa na baki Abraham ne ya shiga yana binsu da kallo ya harde hannuwansa a kirjinsa hafeez ya daga kai kenan yayi tozali da inuwar mutum a gabansa ya juya ya kalli mahaifinsa yaga alamar basu ganiba ya jinjina kai ya maida dubansa garesa wato aljanin husnah ne yazo ya bata masa show kenan?daddy ya shigo da tray hajiya rabi sanye da gyale ta dire na hannunta tace"ina yininku"cikin kulawa daddyn hafeez ya amsa ta fice daddy yace"sannunku nabarku zaman jira ko?kuyi hakuri ga ruwan sanyi kusha Na kira makocina Alhaji sidi gashi nan shigowa "yana rufe baki amininsa kuma makocinsa Alhaji sidi ya shigo da sallamarsa ya mika musu hannuwa suka gaisa yace"barkanku da zuwa"ya zauna gefen daddy,shima daddyn zama yayi yace"Bismillah kusha ruwa"hafeez gabansa ya tsananta faduwa yana kallin Abraham cikin inuwarsa ya gegi jikin daddy ya zauna wani miyau ya hadiye makwat uncle dinsa Na lura da yanayinsa yace"yadai Hafeez?"girgiza kai hafeez yayi daddy yace"tou Mashaa Allah ya kamata mufara gabatar da abinda mukazoyi hafeez ina takardar sakin da yaseer ya rubuta kace zaka kawo ka tsinta a gidan nan?"damm gaban yaseer ya yanke ya fadi yana kallon daddy ya sunkuyar da kansa yace"Daddy wallahi na duba takardar nan ban gantaba saidai inada tabbaci akan ya rubuta ina zargin ta shiga cikin takardun office dina"daddy yayi jimm ya jinjina kai yace"nima inada tabbacin hakan dan hajiya rabi ta fadamun"

"Tou Alhamdulillah Alhaji badamasi kadai san abinda ya kawo mu ko?munzo ne akan neman izinin Auren yarka husnah ma yaronmu hafeez gashi yace ka bada damar muzo dan yanzun haka da sadakin mu ma mukazo idan har ka amince ka yanke zamu biya"cewar kawun hafeez
Chapter 27 · 0% Book details