← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 68

Sashe 60

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin wata irin kasalalliyar murya mai cike da wahala da tsananin jin ciwo Abraham yace "husnah.....husnah nabarki husnah ina sonki nafada miki mutuwa ce zata rabamu yau gashi an konani sanadinki sanadin cika miki alkawarin da nayi bazan iya barinki ba"yana gama magana sukaga hayakin dake tashi a dakin a hankali yana bacewa cikin ikon Allah ko minti goma baayiba suka Nema hayakin suka rasa husnah ta kalli yaseer yadda yake a jigace sakamakon rukon da yayiwa aljanu ta rungumesa ta fashe da kuka shima kukan yakeyi yace "Alhamdulillah husnah yau kin rabu da wanan aljanin yanzun zamuyi rayuwa tare cikin kwanciyar hankali"ya dago fuskarta yana kallon yadda take zubar hawaye yace "menene yasa kike wanan kuka?"girgiza masa kai tayi ta kara rungumesa tace "ya bani tausayi yasaka kansa a soyayyar da ba jinsinmu daya ba babu yadda zaayi mu rayu tare a baya da nayi masa alkawarin rayuwa tare nayine a rashin sanin bansan banbancin mutim da Aljani ba banso aka konasa ba saboda kaunar da yakeyimun"yaseer ya shafa kanta yace "ki kwantar da hankalinki husnah idan baa konasa ba bazai taba daina bibiyarmu ba ko kadan kinga konasa shine maslaha"ta jinjina kai ya zare jikinsa daga nata yace "ashhhh wayyoo kafadata"cikin jim ciwo ya sauko daga gadon ya kalli nusrah dake zaune gefe yace "taimaka mata ku gyara dakin tayi wanka bari nasamu malam"ya fito dakyar yake takawa yasamu malam zaune a parlor ya zauna akan gwiwarsa yace "malam mungode bamu da bakin da zamuyi maka godiya"malam ya jinjina kai yace "kaima kayi kokari kai namijin duniya ne inba namijiba babu wanda zai damki aljani cikin suffar kumurcin maciji"yaseer ya sunkuyar da kai malam ya cigaba da magana yace "be mutu ba amma inada tabbacin zai mutu din saidai kasan aljanu sunada hadin kai sosai mu kuma bil'adama munada sakaci musamman da addua karkuga husnah tasamu lafiya sun rabu kuyi tunanin angama yakin ku shagala kar gidanta ya kasance babu karatun alkurani maana kullum ya zama cikin saka karatu koda bacci zaku kwanta banda yawan kallace kallace a ragesu sanan maganin da akace amininka ya bada tabbas shima ya bada gudunmawa kaso tamanin cikin dari wajen samun warakartq yanzun babu wani aljani da zai iya kusantar husnah da sunan zama a jikinta saidai tsoratarwa da abinda baa rasa ba"yaserr ya gamsu da maganganun malam sosai ya bashi wani hayaki yace "karbi wanan kuyi kaida ita inshaaa Allah angama da wanan matsalar"ya karba cike da girmamawa yayiwa malam godiya ya rakashi....

*****
"ummah anya wanan matar batasamu bokan dayafi nakiba kuwa?kina ganin yadda daddy yakeyi miki magana yana amsaki kamar bayaso abin nan ya bani tsoro ummah"hajiya rabi taja numfashi ta sauke cike da damuwa idanuwanta jajir ta dubi muneeba dake zaune ta mummuke kafafuwa tace "al'amarin akwai daure kai sosai muneeba saidai ninasan ta inda zan bullo musu yanzun ba gashi tana nakuda zata haihu ba bazan taba barinta da wanan d'an ba muneeba ke saina kashe dan tunda bansamu na kashesa a cikiba kuma Alhaji badamasi koda ya dawo hayyacinsa dolene ya zauna dani"cikin sauri sadiya ta shigo dakin tana numfarfashi ta rufe kofa dik sun tsorata kallonta sukeyi sun Kasa tambayarta dafe kirjinta tayi tana sauke numfashi tace "tou wallahi hajiya zainab ta haihu naji anacewa yan biyu maza ta haifa sanan naji kanwar yaseer ta shigo cikin gidan nan cikin farin ciki tana fadawa mahaifiyarta an kona aljanin husnah"

"mai kikace sadiya?kinsan me kike fada kuwa?"a haukace hajiya rabi ke magabar jikinta na kyarma dakyar kafafuwanta suka dauketa saboda yadda taji maganar kamar saukar aradu cewar Zainab ta haihu kuma har yara biyu kuma duka maza,baya baya tayi ta zauna dabas akan gado muneeba bataji nauyin cikin dake jikinta ba ta yunkura ta mike tsaye tana kallon sadiya biyu biyu dakyar ta saita natsuwarta ta hadiye wani miyau mai kauri na tsananin bakin ciki tace "kina nufin husnah ta dawo hayyacinta?husnah ta dawo sak mutum kenan ta rabu da aljanin mijinta?"girgiza kai tayi kamar mai aljanu tace "ah ah bazan taba yarda da abinda kike fadaba bazan taba amincewa yanzun zamuyi zaman kishi da husnah ba husnah fa? sanan cikin dake jikinta tana zubar da jini bai fita ba?"sadiya ta jinjina kai tace "tabbas bai fitaba kuma likita ya tabbatar da tanada ciki"a zabure muneeba ta ruko mahaifiyarta kamar mahaukaciya cike da bakin ciki idonta ya rufe tana girgiza hajiya rabi tace 'ummah baxan yarda ba bazan taba Amincewa ba ummah dole zan rabu da cikin nan na jikina cikin da bana yaseer bane ina bukatar cikin yaseer cikin da zai zama nima inaso agansa kamar yadda akaga cikin husnah"ta girgixa ummahntq tana kuka mai cike da damuwa da tashin hankali"ummah kiyi wani abu ummah ki tashi kiyi wani abu dole mu koma wajen boka ya ciremun wanan cikin dayasamun ina bukatar cikin yaseee"

sadiya ta ruko muneeba "ke haukar meye kikeyi haka?kishi ya rufe miki ido kinata zayyano maganganu idan wani ya labe ya jimu fa?"cikin daga murya cike da tsiwa muneeba tace "ya jimu"da sauri hajiya rabi ta ruko muneeba cikin tashin hankalin ganin yadda muneeba ke neman haukacewa ta riketa sosai sauke numfashi kawai takeyi gumi na tsattsafo mata tare da sakin wani irin kuka mai ban tausayi rungumeta tayi sosai tace "ki kwantar da hankalinki gobe zamuje wajen boka nasan koma menene yanada mafita idan ma haihuwa zakiyi zakiyi ki haifowa yaseer dansa kin manta yace dan dake cikinki na yaseer ne? aljani yasa ya dauko kwan yaseer ya shiga jikisa yasa miki?"kallon ummahnta takeyi kamar zararra sam bata yarda da abinda take fadaba cike da damuwa tace "ummah nidai muje gidan bokan yanzun?"sadiya da hajiya rabi suka kalli juna hajiya rabi bazata iyawa muneeba musuba itama tana bukatar boka yanzun yadda komi ya jagule mata tace "kije ki shirya"ta saki mahaifiyarta ta kwashi wayoyinta....
******
cikin dajin babu aljanin da babushi a wajen kallon yadda jikin Abraham ke zagwanyewa fuskarsa gaba daya ta koma kamar gawayi murnushewa takeyi kamar rushin dayayi toka kiran sunan husnah yakeyi a wahalce, zuhraliyya cikin kuka tace "waye yayi maka wanan abun?"narjisu dake gefe tace "shine yakai kansa tsabar taurin kai irin nasa yau bil'adama sun nuba maka halayyarsu na rashin sanin halacci dikda kaine ka kai kanka"tace tana hararar zuhraliyya zabariyya zubewa tayi akansa tana kuka mahaifinsa kuwa dik yadda akayi yayi magana a wajen ya gagarayi yana tsaye dogare da sanda jikinsa a sanyaye cikin tausayawa ya kallesu yadda suka zagayesa yace "ku matsa ku bashi wuri Abraham bazaiyi ba mutuwa zaiyi domin ya konu dayawa"ganin babu wasa a tattare dashi yasa kowa yake kaucewa kafafuwansu basa taba kasa yawo sukeyi akan iska haka suka bace hannunsa dafe da kirjinsa gefen zuciyarsa wani irin abu ke fitowa daga hakoransa da suka kakare waje daya a haka yake motsasu Yana kiran husnah idanuwansa na kallon sama yayinda yake iya hango showing dinsu itada yaseer tana dannawa yaseeer jikinsa haka Abraham ya soma wata shakuwa mai warin hayaki haka kansa ya langwabe cikin wani irin yanayi yace husss....nnh be karasaba ya daina numfashi,

husnah na cikin dannawa yaseer jiki taji kirjinta ya buga haka kawai taji jikinta yayi sanyi Abraham ne ya fado mata kwalla ta cicciko a idonta Yaseer jin shiru ya daga kai tana ruke da karamin towel yaga tana hawaye ya ruko hannunta yace "yadai? lafiya?"girgixa masa kai tayi ta share hawayenta tana matsa masa jiki haka suke jiyo bugun kofa suka saurara da kyau nusrah ce tana numfarfashi tana fadin "yaya yaya yaseerr Anty husnah momy ta haihu yan biyu maza"yadda towel din husnah tayi suka kalli juna da yaseer tuni ya yunkura ya mike ya rungumeta a jikinsa cike da farin ciki tare suka karasa wankan suka fito suka shirya a hanyarsu ta shiga gidan sun jero yayi kicibis da muneeba idonta dik sun kumbura sakin hannun husnah yayi ya karasa "yadai munee ina zakuje da yamman nan?"yatsina fuska tayi kamar bazata kulashiba ganin husnah ta tsaya ta tsaresu da ido yasa cike da kissa ta shagwabe masa tana kokarin rukosa yace "menene ko jikin naki ne?"ya kalli cikin ta shafa cikinta tace "umm umm bakomi zamuje asibiti ne da ummah likita yace mu koma"

jimm kadan yayi ta katse masa tunani "kaci abinci?"ya kalli husnah data dauke kai cike da kishi ya gyada mata kai ta shafa gefen fuskarsa tace "ka kulamun da kanka sai na dawo"

"da naso na kaiku ne"da sauri ta katsesa "ina zaka kana tare da amarya na yafe maka mijina"tayi masa murmushi yabita da kallo dakyar take daga kafa muneeba ta watsawa husnah wani kallo mai cike da tsana irin zamu gamu din nan suka fice driver na jiransu.....

*****
daddy natw rantsuwa suka Shiga "nifa bansan lokacin dana auri rabi ba dan haka babu wani aure a tsakanina da ita mema ya hau kaina da har zan auri rabi saboda cin amana suna tare da zainab?"yaseer turus yayi yanajin furucin daddy suna shiga innah tayi musu nuni da suyi shiru yara sun shigo cikin faraa ummah hadiza ta ruko husnah tace "barka barka husnah Masha Allah aimu nan muka taho muka barku da dan shegiyar can aljan ni malam din ma daga baya mayi masa godiya"husnah ta zauna ta kalli sashen da mahaifiyarta ke zaune ta kalli yaran tayi murmushi take taji wani son yaran ya shigeta ta dauko dayan yaseer ya shigo ya dauka,daddy kuwa ficewa yayi a fusace ya nufi sashen hajiya rabi be sameta ba ya koma dakinsa ya shiga sintiri don me innah zatace bazai rabu da itaba?....

*****
dukkansu dake tsaye akan dutsen cikin tsananin tashin hankali suke ganin babu ko kayan boka a wajen sai fulani dake wajen wani dake saida kwarya a wajen ne ya shaida musu boka ya mutu.....muneeba duhu ta soma gani ko ganin gabanta batayi cikin tashin hankali ta kalli cikin dake jikinta ta kalli ummahnta tace "bo....bokkkka ya mutu ya barni da cikinsa?"ta dora hannu akai tayi baya zata Fadi ummah da Anty sadiya suka tarbota ta saki wata gigitacciyar kara....

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BANYAFEBA*

07042277401
08036953516

*SLIMZY*🥱😒ina boka yaje ni Amina?
Chapter 60 · 0% Book details