Sashe 52
Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A hankali yaseer ya tura kofar gate dinn cikin gidan yana bin ko ina da kallo hannunsa dauke da rushin wutar da ummah hadiza tasa aka bashi tsaye yayi jin kamar ana binsa a baya ya waiga bega kowa ba cikin rashin tsoro da dakewar zucuya yace "waye?"wata murya yaji mai ban tsoro ana magana ko ina na cikin gidan na amsawa "waye kake tambaya?mai gidan ne a cikin gidan ai kasan ko waye kuma kake tambaya"yaseer yayi shiru yana kalle kalle shiru babu kowa bega kowa ba tabbas yasan ko waye jikinsa nadan tsuma ya tattaro natsuwarsa ya ajiye yace "au ka fito ne mukara?ko kazo makasarka ne?"dariya Abraham ya sheke da ita yaseer ya hadiyi wani miyau da dauri ya dire rushin wutar kasa ya mike tsaye yana laluben cikin aljihunsa yana kokarin ciro magani yaga kaskon rushin wutar na yawo a gabansa kamar a hannun wani yake amma baya ganin kowa haka yake shawagi cikin gidan yaseer sakin baki yayi yana kallon siddabarun da akeyi masa ta bayansa yaji mutim yayi saurin juyawa bega kowa ba nan take yaji wata dariyar saidai ba muryar da yaji bace ta dazun wata muryace ko tantama babu ta macece yaji tana fadin "bil'adama akwai tsoro da karfin hali yafaji tsoro yaya"kyalkyalkyal yaji anyi dariya gumi ne ya karyo masa ya soma karanto ayatul kursiyyu da karfi yana kallon ko wani bangare na gidan yana karantawa gidan ya soma juya masa kici kicin kwace turaren maganin dake hannunsa akeyi cikin azama ya kwace hannunsa ya tofawa sashen dayaji an rike hannunsa ayatul kursiyyu da sauri aka saki had'e da tsaki idanuwansa jajir ya nufi kofar shiga sashenta da sauri yaja da baya ganin kayan da suka baro a gidan momy ajiye a wajen ya leka cikin ledar kirjinsa na harbawa yaga tabbas kayan ne daga bayansa yaji ance "kayan da kuka bari can ne natahowa da matata shi babu wanda ya isa ya rabani da matata"yaseer ya jinjina kai cike da jarumta ya shiga parlorn komi ya tsaru a cikin gidan sosai dakin yayi masa kyau karatun kurani yaji yasa yayi ajiyar zuciya kila dalilin dayasa baa shiga da kayan ba kenan ya mike kawai ya fito kicibis yayi da mutum agabansa ya daga ido Abraham ya gani tsaye a gabansa cikin suffar daya saba ganinsa saidai jikinsa a kokkone yaseer ya hadiyi wani miyau mai kauri yaceb"mekazoyi nan?kunar taka harta warke kazo ka kara samun wata?"jinjina masa kai yayi yace "bata warke ba kuma bazan bari ta warke ba bazan taba iya nisantar husnah ba"yaseer bece masa komiba ya gifta kamar zai wuce ya karanto adduoi ya tofa masa take ya bace ya rufo gidan ganin kaskon turaren a gefe ya fadi ya fashe ya rufo gidan ya fito da sauri ya nufi cikin gida,
tana zaune cikin mutane ana hira ya shigo "yaserr ina kaskon kasamu saka turaren kuwa?"ya girgiza kai "ah ah bansamuba saidai na tarar da kayan da muka baro gidan Momy an kawo sanan wanan aljanin ya fitomin yanzun haka munyi artabu dashi kamar ma yanzun bashi kadai bane"cikin damuwa yakeyin magana momy tace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ni saude wace irin masifa ce wanan?daga wanan sai wanan aljanu kamar ibilisai?"ta dafe kanta ummah hadiza ta yunkura ta mike "bani maganin"tace cikin dakewa,ya mika mata maganin a sanyaye tace "Bari naje nasaka yanzun zan dawo"yusrah da nusrah sukai tsuru tsuru cike da tsoro ummah hadiza ta fice momyn husnah kuwa dafe kai kawai tayi cike da damuwa ta dago a zabure tace "husnah ina maganin dana baki kisha yanzun?"yaserr ya kalli momy wato dai sun dage sai husnah tasha maganin nan?husnah ta dauki kofin a sanyaye "gashi nan"ta nunawa momy ta kallu yaseer taga ransa a bace kasa sha tayi batason bacin ransa musamman yadda ya kafeta da ido hajiya saude ta saci kallom yaseer ta taso Kamar zata fita ta ruko husnah ta karbi kofin "oya shanyeshi maza maza kafin ranki ya baci wato bazakisha ba saboda mijinki ko?"haka husnah ta kwalkwale ruwan maganin sauran momy ta zuba a hannunta ta shafe fuskarta dashi aiko husnah na gamasha wani jiri ya soma daukarta dakin taga yana juyawa ta mike tsaye ta dafe kanta tana binsu da kallo tayi kasa ta yanke jiki zata fadi momy ta rukota da sauri yaseer jikinsa har rawa yakeyi "kingani ko momy kingani ko shiyasa banaso Tasha maganin nan ko kadam yanzun kinga abinda ya faru bakusan maganin menene ba ko maganin da zai kasheta ne ma oho"momy ta kalli yaseer a fusace "rufemun baki dalla can kishi ya rufe maka ido na tabbatar wanan maganin aiki zaiyi tunda har ta soma ganin jiri"hajiya hafsat kawai momyn husnah suka kama husnah a hankali suka shiga ciki da ita aka kwantar da ita momy ta bubbude windows din cikin dakin,
momy ta zauna gefen gado innah dake sallah,Allah Allah takeyi ta idar cike da jaraba tace "dom meyasa mijinta bayaso zaku bata magani?bakusan a hausance idan mijin mutum bayason Abu aka bashi sai wani abu ya samesa ba?yanzun gashi nan ai yarinya ta yanke jiki ta fadi "hajiya saude tadan canja fuska "haba innah don meyasa zakice haka?dan Allah kada ku camfi wanan maganin zata samu sauki"innah tace "tabbas wani abu yasamu jikata kabiru xan fadawa bazan yarda ba"ta koma gefe ta tankwashe kafa yaseer kuwa ya kawo wuya cikin tsananin bacin rai yake zuciyarsa ke ingizashi yaje yasamu hafeez yaji maganin menene wanan ya bada?ficewa yayi momy na kiransa be saurareta ba ya fice daga gidan,kicibis yayi da Anty sadiya "dama kai zanzo in sama Nace ko zaa kai muneeba asibiti jikin nata yaki gata can a daki amai kawai takeyi tacemun ko gani batayi saboda yadda kanta keyi mata ciwo"shock yaseer yayi a tsaye daidai nan ummah hadiza ta shigo da kaskon wutar tace "lafiya naganku tsaye a nan?"
"ummah muniba ce batada lafiya wai tana ciki amai takeyi da ciwon kai ko gani batayi"tabe baki ummah hadiza tayi tace"kissa dai"yasa kai ya nufi sashen muniba sadiya tayi dariyar mugunta tace "kissa ai bakuga komiba ma sai ya kasa angwancewa da matar aljan tukunna"tasa kai ta nufi sashen hajiya rabi...
ummah hadiza na shiga dukkansu suka zuba mata ido cike da mamaki kallonta sukeyi daga sama har kasa kowa na mamakin yadda taje ta dawo momy tace "hadiza kinsamu saka turaren kuwa?"jinjina kai tayi tace "nasamu sakawa mana naje inajin surutai a dakin amma haka nasaka,ina hanyar dawowa naga sadiya da yaseer"ta labarta musu abinda taji babu wanda yayi magana,
hajiya hafsat na tallabe da husnah idanuwanta a rufe ruff duhu take gani cikin sanyin jiki hajiya hafsat ke shafa kan husnah tace "husnah bude idonki kifadamun ya kikeji yanxun"ta bude idonta tangaras bata ganin komi ta dago fararen idonta tace "banajin komi"ta yunkura ta mike Abraham na cikin dakin yana tsaye gabanta ya kasa karasawa Kusa da ita gaba daya ta canja masa dik yadda yaso ta gansa bata ganinsa tsaye yayi yace "husnah yanzun kin zabi rabuwa dani akan ki zauna da wani kin karya alkawarin da kikamun kenan?"hannu tasa ta toshe kunnuwanta jin sautin wata murya a kunnenta hajiya saude ta shigo "yadai husnah"cikin tsoro da wani yanayi tace "momy wata murya nakeji wai na karya masa alkawari momy kuma ni bansanshiba"
"baki sanniba husnah?nine mijinki Abraham ni din ne baki sanniba?"ta zabura tana waige waige cikin tashin hankali tace "momy kinji Yana cewa wai bansanshiba shi mijina kinjifa nifa bansan wayeba momy tsoro nakeji ina yaya yaseer?"ta jefowa momy tambaya hannu momy ta daga sama tace "Alhamdulillah "suka kallu juna da hajiya hafsat sukai murmushi alamu sun nuna husnah bata ganin Abraham sabanin da sanan yadda take cikin damuwa ya tabbatar musu da maganin datasha ya batar mata dashi daga tunaninta tasamu mantuwa,
ummah hadiza tace "ku fito kuyi haramar rakamu nida diyata amarya da husnah kunga Garin yana had'a hadari kar ruwa ya tsareku,husnah tashi ga gyalenki"ta mika mata babu musu ta karba"Abraham yana tsaye wasu hawaye ke zuba a idanuwansa husnah bata ganinsa? muryarsa kawai takeji dik soyayyar da husnah keyi masa yanzun shikenan bata ganinsa jinsa takeyi shima ta mance dashi?ya bace daga dakin momy suna fita tayi sujadar godiyar Allah yanzun shikenan husnah yau zata tare da yaseer?abinda suka dade suna jira?ta shige dakinta suna kokarin fita hajiya rabi ta shigo gidan harajan majaran kamar an korota suna rike da ita suna adduoi aka shiga da ita....