← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 68

Sashe 5

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alhaji badamasi ne ya shiga dakin momy bai ganta ba ya fito ya dudduba bai ganta ba kitchen ya laika mai aikice keta faman had'a abincin rana tana ganinsa ta tsugunna "Barka da war haka Alhaji"

"barka,ina zainab take?kota shiga sashensu yaseer ne na duba dakinta bansameta ba gashi nan ma babu ita"jimm kadan tayi tace "tare suka fita da yaseer bata dan jin dadi ne kamar sunje asibiti"

muneeba ce ta shigo cikin sauri ko ganin gabanta batayi tana ganin daddy ta kirkiro murmushi ya washe baki yace "munee kece da rana tsaka"

"ehh daddy na shigo ne can din shiru"jin motsi ya fito da hajiya rabi taba ganin Alhaji badamasi ta natsu ta kirkiro kunya ta tsugunna ta gaisheshi yacev"yanzun nake tambayar inda zainab take ashe ta fita"ummahn tace "hmmm ai bata fadamunba da zata fita"yayi jimmm bata fada ba?yace "mai aikinta tacemun taje asibiti batada lafiya"a ran hajiya rabi tace bakin ciki zai kasheta saima an daura aurenmu gobe nida kai alhaji badamasi katse mata tunani ringin wayarsa tayi ta kalli muneeba wadda keta gumi ta kosa daddy ya kauce ta labartawa momy tashin hankalin daya duso ta daddy yace"gashi tana kirana "

"hello zainab yanzun nadawo gida da rana ina tambayar inda kike kina ina ne?"momy ta share hawayenta tace "Alhamdulillah gamunan dawowa"daddy gabansa ya fadi jin muryarta a dishe alamar tana kuka yace"lafiya kike kuka ko har yanzun baki hakura akan maganar Aurena ba?"ta girgiza kai kamar Yana ganinta tace"yau shekara goma sha takwas rabonmu da husnah yau Allah ya had'a fuskokinmu nida yata can na tsinceta "ta fada masa wajen wani shock yayi yacev"what?husnah fa kikace kin tabbatar husnah kika gani zainab?"zaro ido hajiya rabi tayi ta dafe kirji ta Kasa boye mamakinta da tsoronta a fili tacev"husnah kuma wace husnah data mutu kodai taga yar mutane tanaso ta daukota ta laqaba maka alhaji"dagawa hajiya rabi hannu yayi yacev"gani nan zan sameku a wajen bari inzo"ya kashe wayar jikinsa na rawa anga husnah idan yaje wajen ya tabbatar zaigani in husnah ce iidan ba ita bace ficewa yayi cikin sauri yabar hularsa a parlor,

muneeba ta rushe da kuka "ummah nashiga uku husnah fa husnah ta dawo husnar da akwai auren yaseer akanta shikenan munzama mu biyu kedashi"ummahnta ta rungumeta cikin tsananin bakin ciki da hassada tace "husnah bazata taba zama mallakin yaseer ba indai ina raye husnah da mahaifiyarta bazasu taba farin ciki a cikin wanan gidan ba harabada ki share hawayenki"ta share mata hawaye Anry sadiya kanwar hajiya rabi ce ta shigo cikin parlorn tacev"meye na kuka keda yaseer ke hannunki ko babu boka babu malam kissa kadaib ta isheki ki kwace miji kuma kinadani"ta bugi kirji muneeba gaba daya a rikice take.....

******
ganin taron jamaa yasa daddy ya parker motarsa daga nesa ya fito yana taka kafafuwansa ya shiga turmitsitsin mutane tun daga nesa idonsa ya sauka akan husna wadda kanta babu dankwali ya kalli goshinta ya haska masa fuska tabbas wanan yarsa ce husnah yana tura mutane ya shiga hajiya zainab ta fashe da kuka ya kamo hannun husnah ba musu ta mike ta rikesa Abraham na rike da dayan hannunta ta juya tana magana daddy sakin baki yayi Yana kallonta yadda take magana kamar zararriya tacev"tare zamuyi rayuwa ko mijina?nasan bazaka barni ba kaji nifa bansan wadanan mutanen ba amma zan bisu tunda kace tare zamuyi rayuwa"

"innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"daddy yacev tabbas Aljanu ne suka sace masa yarsa ya ruko hannunta cikin bakin ciki ya waiga Yana neman yaseer ta hangensa gefe yaseer na mamakin yadda daddy ya biyewa momy zasu dauki wanan yarinyar mara hankali yace "yaseer zo nan mu riketa mukaita mota"hannunta ya sumbule a jikin na Abraham ta turje yaseer ba yadda zaiyi cikin bakin ciki ya fuzgeta yayi mota da ita hafeez yayi ajiyar zuciya burinsa ya cika muradinsa ya ganta yanzun yasan Inda zai ganta ashema ta gida ce yau zai labartawa ummahnsa labari mai dadi kasan zucuyarsa mugun haushin yaseer yakeyi ya jefata a mota ya rufe daddy ya zauna a gaban mota yaseer ya karbi key ya tada motar hafeez da momy mota daya suka shiga,

Abraham mikewa yayi yana yawo a sararin samaniya a sama yana kallon yadda motarsu husnah ke tafiya dole zai koma duniyarsu zaije yayi bankwana da jinsunsu zaije ya azabtar da narjisu kafin daga bisani yazo su shimfida rayuwa sabuwa shida matarsa husnah.....

narjisu ce cikin jinsinsu tana numfarfashi jin kugiya na ihu tasan Abraham na hanya ta dubi hajiya babba tacev"Abraham ya zama nawa tunda aka dauramun aure dashi saidai nasan bazai yafemun ba zai azabtar dani amma rabbas tsugunu bata kareba dan baxansa idon ganinsa Yana rayuwa da jinsun bil'adama ba"zuhraliyya hawayen rashin husnah takeyi ta saba da ita sosai yanxun ya zaayi ta ziyarci husnah?ya zaayi taje ta sanar da ita shirin narjisu?dibbbb Abraham ya sauka a cikinsu yayi kan narjisu......

******
fitowa da husnah sukayi momy da hafeez yaseer kuwa sashensu ya nufa muneeba na ganin haka ta nufi sashenta ko kallon inda husnah take batayiba tsananin kishi daya rufe mata ido burinta kawai ta shiga ta shiryawa yaseer maganganu tayi masa kuka,

daddy gefe ya koma gidan iyayensa ya kira ya sanar musu da ganin husnah da yan uwansa maza da mata ya shiga kiran waya yana fada musu ganin husnah....

kalle kalle husnah keyi a cikin gidan sam hankalinta yaki kwanciya gefe da gefe take kallo ko zatagansa daddy yace "husnah"ta waigo tana kallonsa yace "menene?"ya ruko hannunta tace "mijina nake nema"murmushi yayi yace "ga mijinki can ya shiga sashensa wajen yar uwarki mijinki yaseer"tana kallonsa wani iri tace "sunan mijina Abraham ba yaseer ba dan jinsin jinn"gaban daddy ya fadi hajiya rabi kuwa ji tayi tamkar ta fashe kissa kawai zatayi amfani dashi wajen ribatar zucuyar daddy akan husnah kar ya taba yarda yarsa ce....

yaseer na Shiga muneeba ta shigo ta fada jikinsa ya cire mata rigar jikinta kamshin turarenta ya baibaiyeshi yaja numfashi ya sauke ta fashe da kuka yana bin kayan jikinta da wani irin kallo idanuwansa sun kankance tsananin damuwar da yake ciki wanda besan daliliba gabaki daya hankalinsa da tunaninsa sun gushe tunda yayi tozali da husnah muneeba ta dago fuskarta hawaye na zuba tacev"ya yaseer yanzun shikenan wanan ta zama husnah bakuyi bincike ba bakuyi komiba kun daukota kun kawota?sanan idan wanan ta kasance husnah shikenan fa mun zama mu biyu matanka"ya rungumeta sosai "cikin bacin rai nake sam ganin yarinyar nan ya gusar mun da tunani nashiga matsananciyar damuwa,muneeba bansanta ba bansan daga inda ta fitoba amma daddy da momy suna lakabamun ita a matsayin matata yarinyar da gabaki daya mahaukaciya ce alamu sun nuna matar aljan ce tayaya zasu lakabamun ita?tou wallahi akwai matsala dan zan samu daddy akan hakan kar hankalinsa ya gushe a kan wanan yarinyar renom Aljanu"wani farin ciki ne ya lullube muneeba ta share hawayenta ta Shiga shafa fuskarsa a hankaki ya runtse idanuwansa fuskar husnah yake gani dazun ji yayi ta hade bakinsa da nata tana sauke numfashi tana tsotson lebensa yana shafa kanta a zahiri yana tare da ita amma a bad'ini hankalinsa ya gushe gaba daya daga jikinsa.......

*LITTAFINA NA KUDI NE KI BIYA KI KARANTA IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTA ZAKI BIYANI HAKKINA A INDA BABU DAN BAN YAFE BA*
*NAIRA 300 KACAL ZAKI BIYA DAN MALLAKAR WANAN LITTAFI*

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYA 08038953516 KO KATIN MTN TA WANAN NUMBER

DOMIN KARIN BAYANI KI TUNTUBI MARUBUCUYAR TA WANAN LAYI 07042277401

*SLIMZY*✍🏻

13

Daddy ne ya shigo fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "ina yarinyar take?"ya tsaya daga bakin kofa momy batare da ta kallesa ba tace "tana ciki ta d'an kwanta ne yaseer ne ya shiga wajenta Yana ciki"

"Yaseer kuma?"momy ta ansa da "ehh"kawai ta mike tana kokarin barin wajen muneeba ta tsugunna ta gefen kofar da daddy ke tsaye tace "daddy barka da yamma "

"barkadai muneeba kin shigo,kema kinzo ganin husnar da akace ta dawo ne? tana ciki mai gidanki ma Yana wajenta"rasss Gaban muneeba ya fadi ji tayi kafafuwanta sun sage ta kasa mikewa daga tsuggon da tayi hajiya rabi ta karaso tana faraa ta kashewa muneeba ido tace "ki shiga mana ba kince kinzo ganin husnah bane ki shiga"muneeba murmushin karfin hali tayi daddy ya matsa yace ki shiga"

hajiya rabi tace "daddy dama angwama maka farfesun ne nace akawo maka ga dambun shinkafa nayi nasan zakaso abincin gargajiya"daddy ya washe baki yace"mashaaaa Allah ki zubo ki kawomin nan"hajiya rabi ta mike suka hada ido da momy ta kashe mata ido hade da gwalo tana yar dariya wani bakin ciki ne ya lullube momy ta Kasa magana muneeba kasa shiga ciki tayi ta zauna a kujera lallai yaseer wato zuwa yayi wajen husnah?she cant believe yaseer yaje wajen husnah me yajeyi?tambayar da tayiwa kanta batada amsa kenan kishi ya turnuke mata makoshi idanuwanta sun kad'a sunyi jajir saboda takaici kamar ta fashe da kuka takeji,
Chapter 5 · 0% Book details