← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 68

Sashe 62

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"umm"kawai ya iya cewa yana jinjina kai shima ya zauna gefenta ya fuzgota jikinsa yana rungumeta ywce"cikin damuwa nake amma tarbar da kikaimun ta furgitani"tadan sakesa cike da kulawa tace "damuwa kuma?wace irin damuwa fadamun inji?"shafa kansa yayi yana tunanin yadda zai fada mata damuwar muneeba yake ciki yasan zataji haushi ta sake tambayarsa nan ya kwashe komi abinda ya faru ya fada mata ta cije lebenta tana matukar kishi da muneeba amma furucin ummah hadiza ta tuna"karki kuskura kibari mijinki ya gano lagonki na kishi ko kishiyarki rainaki zatayi zai rinka amfani da hakan wajen musguna miki gara ko ranki ya baci ki danne ki koyi hakuri shima yanasa mace martaba da kima a idon mijinta wani abun shakkar yi miki zai rinkayi"tayi ajiyar zuciya tace"ka kwantar da hankalinka addua zamuyi mata kuma ka kwantar mata da hankali ka lallasheta karka kyamaceta ko ka gujeta saboda abinda ke jikinta,yanzun kaci abinci sai muyi sallah mujeko?"yayi kuri da ido yana kallon husnah ta mike ta fice daga hannunsa yayi sama yana godewa Allah he cant believe husnah ce ta koma normal mutum....

******
sukur sukur hajiyq rabi taji a dakinta ta kasa shiga gabanta na faduwa ta tsaya daga wajen sadiya tace"kamar sukur sukur"ta jinjina kai bude kofar akayi sukaga daddy tsaye da kwaryar da hajiya rabi ke magani a hannunsa, Gaban hajiya rabi ya yanke ya fadi sadiya ta wucesu itama jikinta sai kyarma yakeyi "am Alhaji ina kasamo wanan kwaryar?daga ina kuma?"wani kallo yayi mata data kama bakinta,

"rabi yanzun dama abinda kikeyi kenan?wadanan surkullen da kulle kulle kikeyi rabi?ashe asiri kikaimun na aureki bansaniba?"damm gabanta ya fadi gumi ya karyo mata cikin daga murya yake maganar innah da hajiya saude sun shigo daga waje suna magana suka tsaya "lafiya badamasi? meyake faruwa?"ya nunata da yatsa da kwaryar hannunsa yace"a dakinta nagani wanan ga wasu can dana binciko asirin da tayimun nida zainab"hajiya rabi ta sunkuyar da kai sai hawaye ta dago kai ta soma rantsuwa "wallahi wallahi banyi maka asiri...."bata karasaba daddy ya dauketa da mari zai kuma innah ta ruko hannunsa "banda duka badamasi abi komi a hankali yanzun ni dik ba wanan ba babbar damuwa shine halin da muneeba take ciki"daddy yayi saurin yadda kwaryar hannunsa yace "wani hali muneeba ke ciki?wani hali kikasamun yata?"

"ka tsaya mana ba ita tasata ba zata iya yuwuwa ciwo daga Allah tunda matsalace data shafi cikin dake jikinta"dammm gaban Hajiya rabi ya yanke ya Fadi jikinta sai makyarkyata takeyi gumi na karyo Mata ji tayi kamar ta saki fitsari innah ta fadawa daddy halin da ake ciki ya kalli hajiyq rabi yana nunata da yatsa "ki fadamun meye silar faruwar hakan baxaki rasa saniba ko mugun abun da kikayi ne ya koma cikinta?"ya daka mata tsawa cikin in ina tace "ah ah ahah aljanu aljanune"daddy yace "aljanu sukai me?su suka dauke d'an"tayi saurin jijjiga masa kai "eh ehh sune"ya girgiza kai yace "dare yayi innah gobe in Allah ya kaimu zamu dauketa muje asibiti idan be yuwuba mu kira mai magani"

"saidai mu Kira mai magani Alhaji bana asibiti bane wanan"a sanyaye hajiys saude tayi maganar sukace "mu zamu tafi sai gobe"suka bar wajen daddy ya wuce masallaci.....

hajiya zainab na zaune a daki tana rike da jinjirinta daya take jiyo ihun hajiya rabi ta zabura harta ajiye dan ta dawo tadau Daya tasa a bayanta ta dauko dayan a hannu ta jiyo ihunta a sashen daddy tana shiga taga hajiya rabi tayi zaman yan bori tana rusa kuka "badamasi kada ka sakeni karkamun haka"wani kallo yayi mata "ni zaki zubowa magani a abinci kikawomin saboda ke shedaniya ce?yanzun nan fa na fito da abubuwa daga dakinki shine zakice bari ki zubamun wadda zaki rufemun baki ko to na sakeki saki uku rabi dama auren bansan dashi ba....turus momy tayi tana kallonsu daddy ya karaso ya tarbeta ya karbi dan dake hannunta yace"muje sashenki"

husnah rike da hannun juna suka nufo sashen muneeba surutan da takeyi ya furgitasu suka kasa shiga yadda take jifa da kaya yaseer ji yayi kansa kamar zai rabe biyu jikinsa ne ya hau rawa jiri na neman kadashi......

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTA MUN BANYAFEBA*

07042277401
08036953516

*SLIMZY*✍🏻🥱

49
zama daddy yayi a gefen gadon hajiya zainab yana rungume da jariri guda daya kallo Daya zakai masa kasan yayi kololuwa cikin bacin rai da tashin hankali dikda yadda hajiya zainab ke jawa daddy aji wanan karon zama tayi gefensa ta ruko hannunsa yayi saurin kallonta ya janyota jikinsa da hannu daya ya rungume yana sauke ajiyar zuciya sunajin kururuwar hajiya rabi a daki ta dauki wanan ta fasa ta dau wancen ta jefar tamkar zararra girgiza kai momy tayi tace "Alhaji meyasa ka dauki mataki cikin bacin rai?da baka saki wanan matar ba da ka barta"hararar da daddy ya wurgo mata yasa ta kama bakinta jikinsa na rawa yace "ke zainab banason shashanci kwata kwata ke kinsan ban taba raayin auren wata maceba sanan in rasa wadda zan aurama sai rabi matar kanina ?"cikin bacin rai yake maganar cikin tattausan lafazi da sigar lallashi momy ta ce "kayi hakuri tunda dai ka rigada ka saketa shikenan yanzun dik be kamata kayi wanan bacin ran ba Alhaji kamata yayi yanzun aji da muneeba dake cikin wani yanayi na ban tausayi yarinyar na bani tausayi sosai koba komi muneeba yarka ce kuma matar yaseer dan amininka"jinjina mata kai yayi yasa hannu ya shafa mata kai yace "Allah yayi Miki albarka"ta jinjina masa kai jijjiga kofar dakin hajiya rabi keyi a fusace daddy ya dire jinjirin dake hannunsa ya fita hajiya zainab ta mara masa baya yana bude kofar ta zube a gabansa "daddy daddy Dan Allah ka maidani kada ka sakeni idan ka rabu dani ina zani ina matukar kaunarka inaso inzama matarka shiyasa dik na aikata abinda nayi"mari daddy ya shararawa hajiya rabi yasa kafa ya hankadera gefe yana nunasa da yatsa "ke mahaukaciyar inace?kinsan abinda kike fada kuwa idan baki gacemun daga gidaba wallahi rabi sainayi mummunan saba miki shashasha kawai jahila"ya maida kofa ya rufe nan hajiya rabi kamar zararriya take magana "Baka isa ka sakeniba ban sakuba kayi kadan Alhaji badamasi koka sakeni ban saku ba haka kawai ina matarka kace ka sakeni tayaya ma zaka sakeni bayan boka ya fadamun cewar dani kadai zaka zauna dole karabu da zainab"ta hada kai da gwiwa tana rusa kuka "wallahi bazanbar gidan nan ba"take fadi tare da mikewa tabar wajen tana maganganu kamar mai tabin hankali.....

a hankali husnah ta ruko muneeba da ta daga cup Zata wurga gefenta na dama tana zaune dakin yayi kaca kaca da ruwan daketa zuba ta gabanta juyowa tayi shabe shabe da hawaye tana kallonsu tsura musu ido tayi dukkansu yaseer idanuwansa sunyi jajir tsananin tausayin muneeba kalaman da takeyi ke yawo a kwakwalwar kansa ya rasa Inda maganganunta suka dosa tana ganinsa ta yinkura zata mike yayi saurin karasowa ta fada jikinsa tana fadin "yaya yaseer kaga yadda Allah yayi dani ko? kagani ko ummahna batasona taki kaini a rabani da abinda ke cikina yaya yaseer inaso in rabu dashi kada na mutu banaso na mutu yaya yaseer ancefa ba d'a bane a cikina"ta rushe da kuka yaseer ya rungumeta tsamm hushah dake tsaye ta tsura musu ido tana hango tsantsar kaunat da muneeba keyiwa yaseer a kwayar idonta shima tana hango tausayin muneeba a idonsa yana shafa bayanta yace "ki kwantar da hankalinki banason kukanki muneeba idan kina kuka kara tadawa kanki hankali zakiyi damu kanmu ga abinda ke cikinki kisawa kanki hawan jini"tq kafesa da ido wasu zafafan hawaye ke zubo mata husnah kuwa karnin da takeji yasa amai ya Shiga yunkuro mata ta daure ta cije harshenta ta kallesu cikin dakewa tace "Bari na gyara mata cikin dakin ko?ko ina yayi kaca kaca gashi ta fasa wadanan kofunan kada taji ciwo dasu"ra nufi kitchen yaseer yayi saurin rukota Yana kallon yadda tayi da fuska yasan dauriya takeyi akwai abinda ke damunta "kibari nayi kawai karki damu ki koma gida "langabe kanta tayi gefe guda ta makale kafada cikin shagwabarta mai daukar hankali tace "kabari kawai inyi insamu ladan yar uwata koba komi ai abokiyar zamana ce inaso insamu lada"muneeba ta saki baki tana kallon husnah mamakine da al'ajabi ya kasheta tabbas husnah ta warke rayuwa kenan yauga husnah ta warke ita kuma ga halin data tsinci kanta ta kwantar da kanta a kafadar yaseer tana hawaye yaseer na bubbuga bayanta cikin sigar lallashi husnah nata gyaran wajen momy da daddy suka turo kofar dakin suka shigo daddy ya kalli momy ganin yaseer da husnah tare da muneeba husnah na gyaran wajen momy ta jinjina kai cike da farin ciki taji dadin ganinsu tare da muneeba,
Chapter 62 · 0% Book details