Sashe 57
Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"innahlillahi wa innah ilaihi rajiun,likita kace ba matsala bace bayan jini ne ke zuba a jikinta?"jinjinawa yaseer kai yayi yace "Tou bincike ya nuna mana matarka na dauke da ciki na sati hudu"yaseer ya zaro ido wasu hawaye suka zubo masa a idonsa ya kasa magana tsananin mamaki momy ta kalli ummah hadiza tacev"ciki?kardai Aljanin nan yayiwa husnah ciki yaushe husnah ta tare?"hajiya saudece daga kofar shigowa tace "ciki na yaseer ne ki kwantar da hankalinki"yaseer ya sunkuyar da kai cike da kunya damuwa cunkushe kasam zuciyarsa ya dago dakyar ya motsa bakinsa yace "likita yanzun ya zaayi? gashi kace jinin na zuba har yanzun kar cikin ya zube"
"nima mamakin daya kasheni Kenan yadda jini ke zuba idan cikin ya zube zamugani a gwaje gwaje da scanning kuma munyi iya kokarinmu wajen ganin jinin ya tsaya yaki"momy ya girgiza kai ta kauda fuskarta gefe ta share hawayenta momy tace "Tou ni yanzun likita a rubuta mana sallama mana muje gida matsalarta bata asibiti bace"
ya ciro takardu ya kallesu yace "amm muneeba fa?"kallon kallo sukayi yaseer ya hadiyi wani miyau yace "likita ina kasan muneeba?tazo nan ne?"ya gyada masa kai yace "sunzo ina dubata akacemun ga wata patients din to naga banma gansu ba kila sun tafi ne"hajiya saude tace "au itama?tou Allah ya kyauta yaseer kaga ta kanka mata biyu duka ba lafiya duk ga ciki koda yake waccen cikin ya tsufa"likita ya rubuta sallama yace "muje tana dakin Hutu"suka fito a tare,
Abraham na tsaye cikin dakin dik yadda yaso shiga jikinta ya kasa cikin fushi yake mai tsanani cikin jikinta yakeson fitarwa ya kasa a tare suka shigo dakin nusrah da yusrah suna zaune gefenta sunyi zugum zugum likitan ya kalleta ya girgiza kai ya dafa goshinta yaji sanyi kalau yace "bismillah ammafa bazata iya tafiya ba"yaseer ya mikawa nusrah wayarsa ya dauketa cak jikinta duk jini yasata a kafada suka fito a tare sukayi mota dukkansu cikin alhini da tausayin husnah suke babu meyiwa wani magana haka suka shiga motar nu yusrah a napep suka bisu motar tayi musu kadan.....
*****
hajiya rabi zaune a daki muneeba nata jujjuya abinci ta kasaci sukajiyo muryar daddy ya dawo ta mike ta fito da sauri bata gansa tace "ah ah naji kamar muryar alhaji"fitowa yayi daga sashensa da gorar Zobo a hannunsa yanasha yace "ah ah ai naji gidan shiru nadauka babu kowa ne,ina zainab?"tambayar da yayi mata kenan gabanta ya yanke ya fadi yace "yadai naganki wani iri ina zainab?"bakinta na rawa tace "am umm sun fita nima bansan inda sukajeba nadai gansu umm"daddy ya kafeta da ido yace "kince baki gantaba kuma kince kin gansu a ina kika gansu?"sai ta fashe da kukan takaici daddy ya tsareta da ido cike da mamaki yace "kukan me kikeyi rabi?meyafaru?"
"yanzun ace Alhaji yaseer muneeba ba matarsa bace ya tashi da safe saboda ya kwana a wajen husnah yarso yar gaban goshi ace ya kasa zuwa dubata har yanzun batada lafiya asibiti ma nice nakaita yanzun nadawo daga kaita asibiti gashi ance cikin dake jikinta baa gansa ba"gaban daddy ya yanke ya fadi yace "what?baaga cikin muneeba ba?"Yaseer ne ya shigo sab'e da husnah a kafadarsa hajiya saudece ke fadin "ni banso muka shigo nan ba aida sashenta mukaje tunda ga malam din yazo"daddy cikin rawar jiki ya nufi yaserr ya jefar da gorar zobon dake hannunsa gumi ke karyo masa dikda sanyin dake cikin zobon yace "lafiya yaseer?meke faruwa ya naga husnah a hannunka da jini a jikinta?"hajiya zainab kuka takeyi ummah hadiza ta rukota cikin sigar lallashi take fadin "ki kwantar da hankalinki kindaisan halin da kike ciki ko?ki duba kigani kema cikin nan gareki haihuwa yau ko gobe"
cikin kuka momy tace "dik halin da husnah ta shiga nice sila nina jefata ciki sakamakon sakacin da nayi da ita da adduoi da rayuwarta gaba daya"shiru sukayi mamaki ne ya kashe ummah hadiza ganin daddy ya karaso ya ruko hannun momy cikin kulawa da tausayawa "zainab me kike fada haka?kaddara ce baki imani da itaba?ko me kikeso kice banason jin wadanan maganganun marasa amfani wanda Allah ya rigada ya aiko dashi"yasa gefen rigarsa ya share mata hawaye yace "muje babban parlorna ko?ina muneeba itama ta fito tunda gashi mahaifiyarta tace wai baaga cikinta ba"
"baaga cikinta ba?"suka hada baki tsuttt wajen yayi hajiya rabi mutuwar tsaye tayi tana bin daddy da kallo yadda yake rawar jiki akan husnah da zainab wani gumi ne ya karyo mata tsaye take ta kasa koda motsawa saida daddy ya sakeyi mata magana a daburce ta amsa suka shiga cikin dakin.....
husnah kwance kamar gawa malam ya karanto adduoi sosai ya tofa mata a mararta da aka dan bude mata yace "Yaseer kaine mijinta shafe mata marar tata"yaserr yayi yadda akace daddy na tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa idonsa nakan husnah tsananin tausayinta yakeyi minti minti yake girgiza kansa hajiya rabi kuwa dik motsin dady a idonta yakeyi malam ya nisa "cikin yakeso ya fitar matq"
Anty sadiya da hajiya rabi suka kalli juna jin an ambaci ciki sadiya tayi gyatsine tace "ciki kuma?har yaushe akayi daren balle gari ya waye?inace jiya husnah ta tare a jiyan ne harta samu ciki?"hajiya rabi da zuciyarta kamat ta fasa kirjinta ta fito tace "ganemin hanya ko kuma cikin aljanin ne,alhaji naga yaushe husnah ta tare ake zancen ciki?"
daddy cikin rashin fahimta yake kallon yaseer ya sunkuyar da kansa ummah hadiza tace "ciki na yaseer ne tunda mijinta ne kuma akwai aure ko bata tare gidansa ba zata iyayin ciki ai"
hajiya rabi ta karbe zancen "kenan zagayewa yakeyi yanacin amanar muneeba Kenan batare da saninta ba ko?shiyasa har kwana yakeyi saboda ansan abinda aka kulla to asirinku ya tonu"....wata tsawa daddy yayi saida hajiya rabi ta girgiza yace "ke wani irin iskancin magana kukeyi haka ko ince kikeyi?wanan malamin ba bako bane kuma ba namiji bane bazaki iyajin kunyarsa ba?"zaro ido hajiya rabi tayi tace "Alhaji tsawa kakeyimun fa kuma kana ganin munada gaskiya dan dai kawai mubamu da me tsaya mana dan anga mahaifinta ya rasu?"ta rushe da kuka ta rike hannun muneeba ta dagota "muje tashi muje muneeba zan kaiki inda zaayimun maganin matsalarki'ta rukota dakyar take daga kafa yaseer yabi muneeba da kallo itama kallonsa takeyi idanuwanta sunyi jajir,dikda yanajin haushin abinda tayi masa amma tabashi tausayi ganin yadda gaba daya ta sauya....
malam na rike da kan husnah yanata addua yana fesa mata cikin ikon Allah ta bude idonta hajiya saude tayo tozali da husnah tace "Alhamdulillah husnah ta tashi"da sauri daddy ya taho ya karaso ya tsugunna ya tsurawa yarsa ido itama kallonsa takeyi da tsananin mamaki dakyar ta bude baki tace "ina yaya yaseer?macijim ne saresa bako?"take tambaya hawaye na zubowa a idonta dukkansu tabasu tausayi malam yace "Alhamdulillah ta tashi kuma jinin ma zai tsaya ga magani zan baku a bata Insha Allah zata haifi abinta cikin yakeso ys zubar tunda beyi nasarar raba auren nasu ba kuma sai kun tayasu da addua dan a yanzun komi aljanin nan zai iyayi"ajiyar zuciya ummah hadiza tayi tace "kaidai malam mungode sosai Allah yayi maka sakamako da Aljanna shi kuma wanan aljanin Insha Allahu zamuga bayansa"tsaki sukaji anyi suka shiga kallon kallo malam yayi musu sallama yaseer ya taimakawa husnah suka rukota da ummah hadiza suka nufi sashenta....
******
muneeba na rungume jikin Anty sadiya yaseeer yayi sallama a sanyaye fuskarsa a daure ya shigo a dakile ya gaida hajiya rabi ta kallesa itama ta watsar kamar bazatayi maganaba tace "ai nadauka ka sallamata ne yaseer tunanin yadda zaayi in dauke yata nakeyi saidai kuma ina auren ubanku"yaseer ya dago jajayen idonsa ya kalleta zaginsa fa tayi a fakaice wato tana auren ubansu yau da badan ita din surukarsa bace da taga rashin mutunci ya tsugunna gefen muneeba da idonta ke kallonsa tace"yaseer kenan yanzun kasan dani inda na mutu fa?"ta fada jikinsa ta fashe da kuka hajiya rabi da sadiya suka fice yadan janyeta daga jikinsa wani irin karni takeyi yana dan daddaga hanci ta kalli yadda yakeyi da hancinsa tace "ko wari nakeyi?"girgixa kai yayi "umm umm bahaka bane naji karni ne kamar kifi am ya jikin naki?"ta share hawayenta tace "da sauki"ta sunkuyar da kai yace "yanzun menene abunyi?gashi ance cimin baaganiba gashi ya girma"jikinta a sanyaye tace "ehh baa ganiba amma likitan ya tabbatar mana da wasu sunayi. hakan baby ke boyewa"ya jinjina kai yace "Allah ya kara sauki"Allah Allah yakeyi zai fita ta tsaidashi "ummhmm mai kikeso kina bukatar wani abune?"ta girgiza kai tace "kayi hakuri da abinda nayi jiya kishi ne bazan iya jure ganinka da wata maceba ina tsananin kaunarka mijina ina tsananin kishinka zuciyata kamar zata fasa kirjina ta fito nakeji"tausayinta ya kamasa yayi ajiyar zucuya hmm tayi hankali kenan tasan ita tai masa laifi ko?ya zauna yana fuskantarta yace "karki sakeyimun irin abinda kikaimun inayi Miki warning da kakkausar murya idan ba hakaba tamu dani dake bazatayimana kyauba "ta jinjina kai hawaye ke gudu a fuskarta ya kalli yadda lokaci daya ta rame tayi baki gashin kanta a hargitse yake yace "oya tashi kije kiyi wanka zan fita daku anjima keda husnah"ta jinjina kai tace "ba sai naje ko inaba"ta mike da kyar tayi daki ya makale kafadarsa Alamar ko a jikinsa ya fito cikin sauri yayi hanyar waje tsaye tayi ta window din bedroom dinta take kallonsa ya fice ta durkushe a kasa cike da takaici da kunar rai....