Sashe 64
Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin kuka muneeba tace "ban cancanci afuwa da gafarar yaserr ba abinda yafi cancantata shine karbar hukunci daga garesa ko wani iri ne,dikda tsananin son da nakeyiwa yaseer ya zama dole in hakura dashi saboda Bai kamaceniba bai dace dani ba nidin ba macen data cancanci a zauna da ita bane,dik abinda ya sameni mahaifiyata itace sila ita ta jefa rayuwata cikin DUHU daga haske ta jefani cikin mummunan had'arin da na gwammaci mutuwa da Rayuwa"da sauri hajiya saude ta rike muneeba ta toshe mata baki tana kuka itama kukan takeyi "dik wadanan maganganun basu bane muneeba kidainayinsu ko a kalaman da mukazo muka tarar dake munsan cewar ba yin kanki bane uwace bakiyi dacen da ta gariba,tirrr da halinki rabi Allah ya wadaran halinki kin cucemu kinci amanarmu kuma sai Allah ya saka mana sanan kisan da sanin dik inda kike zamu nemoki mu mikaki hannun hukuma akan dik abinda yasamu muneeba kece "cikin kakkausar lafazi hajiya saude ta karasa maganar ummah hadiza tuni zucuya ta kawo mata wuya tana bude baki zatayi magana ta kasa kallonsu kawai tayi tw zare hijabin jikinta cikin fakon idonsu momy dake kuka a tsaitsaye sukaga ummah hadiza ta rufarwa hajiya rabi da wani irin duka ta hankada kanta jikin bango ji kake kummmm "matsiyaciya wallahi bazakicu bulus ba kafin kibar gidan nan kibar zuriar mu sai na canja miki kama"nushin hajiya rabi ummah hadiza keyi ta cukwikuye kanta cikin hijabinta ta danneta ihu hajiya rabi keyi cikin azaba "hadiza karki kasheni kada ki kasheni numfashina ki kyaleni ki rabu dani zainab kuyi mata magana kuna gani zata kasheni?"momy tana kokarin mikawa innah jinjiri daddy ya rukota "badai karbarta zakiyi ba ko?ai abinda ya kamaceta kenan dan idan nine wallahi na kamata kasheta zanyi har lahira kubarta ta canja mata kamanni kafin yan sanda suyi gaba da ita suyi mata nasu"cikin wani irin yanayi momy ta share hawayenta tana kallon yadda ummah hadiza ke kirbar hajiya rabi kamar Allah ya aikota tace"ummah hadiza ya isa haka dukan bashi bane maslaha"hafeez ya kama yaseer yana kuka ya fita dashi muneeba tabi yaseer da kallo tausayinsa ya lullubeta take taji wata tsanar kanta da tsangwamar kanta ta dira a zuciyarta cikin gyaran murya malam yayi wanda shi yasa ummah hadiza tana cafke da wuyan hajiya rabi ta dakata yace "dukan da koke koken bashi bane maslaha ki rabu da ita dukan bashi zai bawa yarinyar nan lafiya ba bashi zai goge bakin fyantin da uwarta tayi mataba dan haka kyaleta shine maslaha yanzun asan abinyi"...hankadeta ummah hadiza tayi bakin hajiya rabi ya tashi yayi zundundum yayi jajir idonta daya ya kumbura suntum fatar idon tayi baki goshinta kuwa jini ne kawai yake tsattsafowa fuskarta dikta kuje da jikin bango ummah hadiza wani bakin ciki ne ya tokare mata wuya ta fashe da kuka tace "fitar mana a gida zoki fita idan ina ganinki kasheki kawai zanyi"tsoro ne ya cika hajiya rabi dakyar ta yunkura ta mike jikinta da kafadarta dik ya sage muneeba tabi mahaifiyarta da kallo fuskarta jajir hajiya saude tace"yanzun mal muje cikin gida baban parlor ko?"malam ya jinjina kai ya fice hajiya rabi na hada hanya ta fito sadiya nayin tozali da ita ta fuzgi akwatunta ta baza aguje tayi gate cikin sassarfa itama tabi bayanta a waje suka hade "Anty lafiya?meyafaru kinga yadda fuskarki tayi kamar kinyi hatsari"cikin tsoro sadiya ke maganar tana waige waige "nidai mubar gidan nam kafin su fito su cinmana a nan natabbatar sunji abinda yasamu muneeba ko?"gumi ne ya karyowa hajiya rabi cike da nadama a karo na farko tace "na cuci rayuwar yata ma cuci rayuwata sadiya yanzun ina zamu gashi Alhaji badamasi yace idan har muneeba wani abu ya sameta sai ya daureni"jim haka sadiya taja akwatinta tayi gaba hajiya rabi na biye da ita hannu akai take rusa kuka tana waigen tamfatsetaem gidan tana fadin "nashiga uku na lalace na shiga uku shikenan ni rabi yanzun ina zani"....
****
shiru sukai dukkansu daga yaseer hafeez da husnah dake parlorn sautin kukan yaseer ne ya karade cikin parlorn tsananin bakin ciki yasa yake kuka husnah cikin tattausan lafazi tazo gabansa ta durkusa ya dago idanuwansa shabe shabe da hawaye Yana kallonta yadda yake kallonta taji wani abu ya karya mata zucuya ta fashe da kuka yayi saurin zamowa daga kujera ya tsugunna gabanta "husnah kukan mai kikeyi husbah?meyasa kike kuka?kina zargin na dauko cuta daga jikin muneeba nasa miki ko?wallahi"be karasa ba ta rufe masa baki ta kwantar da kanta a kafadarsa tace "haba yaya yaseer wanan kukan da kakeyi bakasan shi kadai tadamun da hankali zaiyi ba?bakasan bazanso ganinka cikin wanan yanayin ba?shin muneeba kake ganin laifi ko laifin ummah?"yayi saurin kallonta yana nazarinta ta girgiza kai ta share hawayenta da bayan hannunta tace"muneeba batada laifu hasalima yanzun itadin abar tausayi ce dan baasan menene a jikinta ba batada laifi ba ita tasa kanta ba idanuwan mahaifiyarta ne suka makance har tasata ta aikata abinda ta aikata Dan Allah ka tausaya mata yaya yaseer ko zakai wani hukunci kabari tasamu lafiya tukunna"zucuyarsa tamkar zata tarwatse yakeyi daya tuna furucin daddy na karshe dayaji akan muneeba ta aikata zina da boka,sanan furucin muneeba na daga masa hankali cewar cikin dake jikinta ba nasa bane cikin boka ne kuma ya mutu, yaseer ya cije bakinsa saida lebensa ya fashe jini na zuba a bakinsa yace "muneeba ta cuceni ta cutardani da danginmu ta bata mana suna da ace zanyi ido hudu da wanan bokan da saina rabashi da ransa"hafeez ya jinjina kai yace"ko baka rabasa da Ransa ba Allah kadai yasan Azabar dayake ciki tunda ya mutu yanzun yaseer dik wanan bashi bane a gabanmu ka duba furucin matarka"ya nuna husnah da tayi tsumu jiki a sanyaye tayi saman rakuma a jikin yaseer hafeez ya cigaba da magana "maganarta abun dubawa ce yanzun abinda zaayi shine tashi zakayi muje cikin gidan tunda kaga malam na ciki musan abinda ake ciki"kin magana yaseer yayi zucuyarsa cunkushe take da tsananin bakin ciki miyaun bakinsa har d'aci yakeyi masa ya kallesu kawai ya mike ya nufi hanyar bedroom dinsa saida yakai tsakiya yace "kuje amma bazan iya shigaba bazan taba iya kallon fuskar muneeba a halin yanzunba domin bakinkirin nake ganinta bazan taba jurar ganinta ba zan yanke hukunci a lokacin da be kamata ba dam haka kuje kawai"yana gama magana ta nufi bedroom dinsa da besan kalarsaba yaune ranar farko daya Shiga Yana shiga yasawa dakin key ya zube a jikin kofar ya dafe kansa wasu sababbin hawayen bakin ciki yakeyi yanaji husnah na bubbuga kofar dakin ta baya take fadin "haba masoyina haba mijina ka bude kofar nan ka saurareni nicefa matarka husnah kayimun alkawarin farantamun rai akan dik abinda nakeso"cikin sassanyar murya take maganar da tattausan lafazi zucuyarsa na azalzalarsa ya bude amma bazai iya budewa ba kasa magana yayi ya mike ya zare rigar jikinsa yana zuwa ya fada gadonsa ya kifa ciki husnah jin bayi da niyyar budewa ranta a bace ta shiga dakinta ta gyara fuskarta ta sako hijab ta fito ta samu hafeez tayi tagumi a parlor yana ganinta yace"yaki budewa ko?"ta jinjina kai tace "muje can gidansu momyn nasan yayi fushi ne zai bude zan lallashesa"hafeez ya saci kallon husnah tayi kyau ta koma normal mutum kamar ba husnahr Abraham ba tare suka fice.....
hajiya saude na rungume da muneeba malam yana rike da kofi ya juye ruwan zamzam husnah da hafeez suka Shiga daddy na ganinsu yace"ina yaserr din?ina kuka barosa?"husnah ta sunkuyar da kai batace komiba suna hada ido da muneeba wani tausayinta ya lullube ta ta fashe da kuka tana kallon muneeba itama muneebar ita take kallo tayi murmushin karfin hali ta mika mata hannuwanta ta taho ta rukota ta durkusa a gabanta "yaya yaserr ya tsaneni ko husnah?nasan bazai sake marmarin rayuwa dani ko zama daniba na tabbatar yanzun hakan ya sakeni"shhhhhh husnah tace "be sakekiba kuma bazan taba bari ya rabu dakeba idan har zai rabu dake to tabbas saidai ya rabu damu tare saboda kedin yar uwata ce"sosai sukaba mutanen cikib parlorn tausayi muneeba ta gyara zama sosai jikin hajiya saude tana sanye da hijab amma gumi ya gama jika wuyan hijabin gyaran murya malam yayi sukayi shiru "kun tabbatar kun amince akan ayi Mata addua ta haife abinda ke cikinta ko mutum ne koba mutum ba?"dukkansu a tare suka hada baki "mun amince"malam ya jinjina kai yace"wanan addua ce nayi a ruwan zam zam gashi Wanda mafi akasari masu nakuda akeyiwa su haifi abinda ke cikinsu dan wasu ma idan sukasha lokacin haihuwa beyiba zasu haihu a lokacin da izinin Allah dan haka gashi tasha ta shafe cikinta sai musa ido mu zubawa sarautar Allah ido"momy ta girgiza kai ta kalli muneeba rike sa kofin tana kokarin sha tausayin yarinyar ya lullubeta ta kauda kanta gefe ta fashe da kuka muneeba tashanye adduar husnah ta taimaka mata suka hude cikinta aka shafe cikin da adduar
"Tou Alhamdulillah yanzun ni zan tafi tunda bamusan lokacin da nakudar zata tashiba ko?saidai kar a barta ita kadai asamu wani yq zauna tare da ita"hajiya saude tayi ajiyar zuciya tace "mungode malam Allah ne kawai zai biyaka abinda kayi mana Allah ya saka maka da alheri"suka hada baki tare suka amsa da "Ameen"malam ya tashi hafeez yabi bayansa yacewa su momy "Bari in kaisa gida zan dawo zuwa yamma"suka fita tare da malam daddy ma ficewa yayi sakamakon kiransa da akayi a waya....
husnah ta yunkura ta mike muneeba ta rukota tayi saurin juyowa tace"ina zakije?"murmushi husnah tayi tace"zanje ne nidasu nusrah muyi aikin abinci duka gidan nasan yanzun bazaa samu sukunin dafa wani abuba yanzun zanje in dawo kinji?"ta jinjina mata kai shaawa sukabasu dukkansu tasa kai ta fice suka bita da kallo,
suna nan zaune ko minti goma sha biyar husnah batayiba da fita muneeba ta fara jin ciwo motsawa tayi dakyar ta ruko kasan mararta da yayi mata nauyin gaske tace"ciwo nakeji momy"tana kallon hajiya saude jikin hajiya saude ya mutu nan da nan gumi ya soma karyowa muneeba ta soma murkususu a kasa mararta na ciwo addua takeyi tana yarfa hannu tana kiran sunan Allah tana kiran sunan yaseer,