← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 68

Sashe 15

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

cikin tashin hankali momy na sintiri cikin parlor take kara kiran wayar daddy innah tace "kadauka mana ana kiranka a waya ko shedaniyar ke kiranka ta kitsa maka wata maganar"ya girgiza kai a dakile yace "zainab ce"innah tace "saika dauka kaji uzurinta"ta tsaresa da ido badan yaso ba ya fito da wayar daga aljihunsa yasa a kunne momy cikin sassarfa da tashin hankali tace "daddyn yara husnah ce banganta ba na duba dakinta ko ina a cikin gidan nan bangantaba shine nace bari in kiraka inji"daddy yace "what?to ina taje ina ta tafi kuma?"innah cikin kosawa take daga hannu tana masa nuni da lafiya?ya cigaba da waya yace "gani nan zuwa gidan"ya kashe wayar ya mike yana kokarin sa takalmi innah ta rike kwankwaso da hannu daya tace "kai badamasi ina zaka?lafiya naganka cikin tashin hankali?"dakyar ya hadiyi miyau idanuwansa jajir yace "husnah ce baa ganiba wai aljani ya dauketa"...
cikin daga murya innah tace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ni hajara nashiga uku yanzun biyota yayi ya dauketa kuma? badamasi abinda nake fada maka kenan"daddy na kokarin fita ta tsaidashi "ai tare zamu tafi gidan bamuga ta zama ba ina zuwa bari in kira hadiza mu dunguma mutafi can gidan ohh ni yasu "daddy gumi kawai yakeyi yana tsaye ji yakeyi kamar jiri zai daukesa idan har baaga husnah a karo na biyu ba zai sassabawa zainab dan itace tabarta ta fice innah ta fito gyalenta a hannu da yar jakarta ummah hadiza kanwar daddy dake zama a gidan da d'anta sakamakon mijinta ya rasu cikin tashin hankali take kuka "shikenan yanzun ana murna yarinyar nan ta dawo amma shine yanzun zaace an nemeta an rasa kardai aljanun nan sun sake saceta ko kuma hajiya rabi ta dauketa tunda taji zatayi zaman kishi da Yarta ba"daddy tafiya yake kawai daga cikin gida besan inda yake saka kafarsa ba hajiya innah kuwa kokarin kiran hajiya saude takeyi ta mikawa ummah hadiza waya "lalubomin number hajiya saude"ummah hadiza ta karba tana kokarin shiga mota innah ta shige daddy gaba daya ya fita hayyacinsa ya kasa ko ganin gabansa

******
blue din jeans yaseer yasa da bakar riga da hula picap yayi matukar kyau muneeba ta daga kai ta kalleshi tana sanye da riga abaya baka mai stones farare tayi rolling da d'ankwalin rigar tayi daurin acuci maza tayi kyau suna tsaye gaban madubi ya rike kwankwasonta ta kallesa ta cikin madubi sanan ta d'ago kai ta shafa sajensa tace"kayi kyau har naji kishi ya kamani kamar kada na fita dakai kai wata ta ganemin kai gashi cikin gidan nan ana neman ayimun fashinka"ya kama kumatunta tace "ausshhh da zafi"ya rungumota jikinsa yace "wanan ai kinsan bazai yuwuba matar aljan fa?wanan husnar ita kanta aljanar kanta ce jin momyna kawai nakeyi da tace wai sai an maida aurenmu gaskiya bazan aureta ba wanda ya tattagota sai ya aureta"tayi yar dariya yace "zo muje banaso muyi lattin fita yanzun haka momy kirana takeyi naki daukar wayarta idan naje zan fada mata a yanzun bazai yuwuba don akwai d'ana a cikinki"ya shafi cikinta ya ruko hannunta yayi kissing dinta wani yarrrr taji soyayyar yaseer na kara mamaye mata zuciya tasani aikin boka ne yake aiki a jikinsa sanan tana shirin gobe tayi amfani da damar zuwa asibiti wajen karayin wani aikin akansa tayi shiru yace "yadai akwai wani abu ne?"ta girgiza masa kai ya rukota sai kamshi suke zubawa yana rike da jakarta ya fito ta tsaya ya rufe sashensu a harabar motoci har zasu shiga yace "mu shiga ciki muyiwa su momy sallama"ta tura jakarta mota tana makale dashi hannunta cikin nasa kamar zata shige jikinsa tana zuba masa shagwaba suka shiga tin daga kofar shiga sashensu yake jiyo sautin kukan momy hankalinsa yad'an tashi yace "kamar momy ke kuka"cikin sauri yaja muneeba da gaba daya ranta ya baci suna shiga sukai kicibis da hajiya rabi tadau wanka ta washe baki "ah ah sai ina?"yaseer yace "ummsh kamar kukan momy meyake faruwa?"hajiya rabi ta tabe baki tace "can musu itada aljanar yarta Allah yasa ma Kar aganta wai ta fito bata ganta ba bata cikin gidan shine take rusa kuka take kiraye kirayen waya"

waya yajiyo momy cikin kuka tana fadin"hafeez dai ya fita nasan yana hanya yace akwai malamin dake bada taimako akan aljanu dik inda yake ya kusa gashi husnar bata gidan"jin muryar yaseer ta katse wayar ta fito tana shirin masa magana yace "momy kidaina kukan nan godewa Allah zakiyi baa ganta ba ni yanzun fita zamuyi da muneeba tanaso taci shawarma tasha ice cream masu ciki abinda sukeso ake musu"hajiya rabi ta kannewa muneeba ido sukai murmushi a idon momy cikin tsananin mamaki momy ke kallon yaseer ya kada kansa ya ja hannun muneeba ummah tace "Allah ya tsare kuna nan tarw harabada dik dan bakin ciki saidai ya mutu "momy hawaye shabe shabe take kallon hajiya rabi ta tafi tana wakoki da adduar kar aga husnah,

a mota yaseer yacewa muneeba"ni Allah yasa ma kar aganta shikenan an Raba gardama ance wanan munafukin ya tafi wajen nemo malami"yayi tsaki ya tada mota muneeba ta kwantar da kai jikinsa suna barin wajen motar daddy tayo kwanar Layin daga nesa daddy ya hangi motar yaseer ta fice a bayansu hajiya saude ce cikin tashin hankali driver yajawosu da kannen yaseer biyu a tare sukayi parking a kofar gidan....
*****
addua sosai hafeez keyi cikin tashin hankali idanuwansa a rufe ji yakeyi bugun zuciyarsa ya tsananta saboda tsananin furgici ji yaje tartssssssseeee akan gilashin motarsa cikin dimaucewa ya bude ido yana bude idanuwansa yaga yadda gajimare yake yawo a sararin samaniya Yana sauya kala ya kalli gilashin motarsa yanda yayi watsa watsa ko Ina har ta cikin motar gani yayi katuwar dabba mai kamada ayu tayo kansa kakarta baka Kirin ya kara runtse ido zaiyi addua ya Kasa gumi kawai yake keto masa ya tsaida motarsa a tsakiyar titi horn motoci keyi masa suna zagayewa suna wucewa bin motar da kallo akeyi yanda glass din ya tarwatse mutane suna cewa kila hatsari yayi a wani wajen,
shi kuwa hafeez duhu yake gani ya mamayesa yadda garin ke juyawa kamar zaa kifasa jiri ke daukarsa dakyar bakinsa ke furta kalmar Allah!!Allah....ya sake bude idanuwansa a karo na biyu shiru yaji sai wata k'ugiya dake kuka ya d'aga kansa yaga katon tsuntsu na yawo bakinkirin a saman motarsa tsuntsun na wurgo wani abu kamar wuta a bakinsa saidai daya doso motar sai ya tarwatse sakamakon adduar da hafeez keyi a hankali ya bude motar ya fado daga ciki ya kuma kansa a titi nan da nan jini ya balle,

mutane sukai masa caaa "dama munce mai motar nan badai lafiya ba tayaya zakazo tsakiyar hanya ka Parker mota kuma ga yadda motar daga gani hatsari yayi a wani waje"cikin mutanen dake tsaye tsaye a wajen husnah na gefe can da Abraham yace "la kamar hatsari akayi jirani a nan wajen inzo "yace ta gyada masa kai tana kallon wajen ya tsallaka titi babu mai ganinsa ya rikide ya koma sak kamannin hafeez ya shiga cikin wadanda suka taru hafeez ne ya dago a galabaice jini na zuba yayi ido hudu da Abraham da kamanninsa sak ya Nuna masa gefen hanya da yatsa hafeez ya hangi husnah tsaye tana kalle kallen motoci tacu Ado baki sake Abraham ya tsugunna a gaban hafeez yace "dik abinda yake faruwa dakai nine kasheka nasoyi saboda Naga kana nema kayimun katsalandan akan husnah dik wanda yayi yunkurin shiga tsakanina da husnah rabashi da duniyar zanyi "Abraham ya daga hannu sama ya watsa yatsunsa saiga mulmulen dutsen da yayo kansa Yana yawo a Sama batare da an rikesa ba iska mai karfi na kad'a dutse yacev"da wanan dutsen nayi niyyar fasa kwakwalwarka,saidai kaci saa d'aya da Allah a bakinka ka tsallake wanan sirad'in saura na gaba idan kaki ka juya ka koma gida ko a aikawa da iyayenka da gawarka"dutsen ya bace Abraham ya mike idanuwansa suka canja gudan idonsa ya koma baki ya tsallaka titi Yana hangensa ya nemesa ya rasa sai husnah ya gani tana murmushi ita kadai alamar Abraham ya isa gareta bakinsa na rawa jini na zuba a goshinsa yake nuna titi"jama...aaa ku...ku tai..makeni gata can husnah ce aljani zai gudu da ita"da sauri mutanen wajen suka juya inda yake nunawa tuni sunbar wajen da husnah nan jamaa suka dare wani yace"gaskiya wanan mahaukaci ne anya ba shaye shaye yayo ba sanadin soyayya?"hawaye kw zuba a idon hafeez ya kalli motarsa yadda tayi ga wayarsa na cikin mota balle ya kira momy ya fada mata halin da ake ciki yaga husnah....
Chapter 15 · 0% Book details