Sashe 35
Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"momy Anty husnah tace taci abinci wai yusrah ta kawo mata sunci tare"zaro ido yusrah tayi tana kallon nusrah tana kallon momy tace"ni yaushe?"husnah ta yatsina fuska tace "ah ah yanzun fa kika kawo abinci bayan fitarki yayanku ya shigo"kasa magana yusrah tayi cikin dimuwa ta fice daga dakin nusrah ta juya da plate din momy tace "taso muje parlor mu zauna tare banaso kina zama ke kadai, nusrah kai tray din kitchen kuje parlor da Antynki asa tashar karatun kurani"nusrah ta jinjina kai suka fito tare jiki a sanyaye husnah ta fito tamkar wadda aka zarewa lakar jiki to ya akayi yusrah zatace basuci abinci ba alamu sun nuna cikin dimuwa ta fita waye zai kawo mata abinci bayan yusrah?.....nusrah ta fito daga kitchen suka jera suka nufi babban parlorn gidan...
yusrah na zaune tayi tagumi momy ta shiga girgiza kai momy tayi tace"ki kwantar da hankalinki na fahimcu komi na fahimci cewar bake kika kai mata abinci ba jinnu ne"yusrah ta zabura tace "shine sukai shigata?"ta dafe kirji momy ta jinjina kai tace "kwarai kuwa dagaske zasuyi abinda yafi haka ki daina damuwa nakira malam dazun xaizo bayan sallahr isha'i yace,tashi kije kisamesu a parlor "tsoro nakeji"momy tace "ba abinda zai sameki ki kwantar da hankalinki "tayi ajiyar zuciya ta fita,
husnah zama tayi a kasan carpet a d'arare tana bin ko ina da kallo nusrah ta dauki remote din tv bayan ta kunna Abraham ne ya shigo ya shige jikin husnah yana kallon remote din hannun nusrah remote din ya fad'i kasa,tayi tsaki ta tsugunna ta dauka ta canja tasha ta ajiye ya kalli inda remote din yake take taga alamar ana danna remote kuma babu kowa a wajen tashasho sukaga suna fitowa nusrah jikinta ya kama rawa yusrah ta shigo tana kallon yadda tashoshi ke canjawa tace "dallah meye haka ki tsaya mana wajen Tasha daya kin tsaya sai canja tashoshi kikeyi"nusrah bakinta na rawa tace "ba....bani ba nibace yusrah kinga remote din can"ta nuna mata da yatsa sukaga husnah ta kafe tv da ido ko kiftawa batayi a hankali suka juya suka zare jiki sukabar parlorn...suna fita husnah ta mike Abraham yayi dariya a jikinta ya shiga zagaye parlorn yaje ta gefen tv zai taba momy ta fito da karatun mp3 a hannunta suratul bak'ara tace "husnah lalala karki taba menene haka?"da sauri ya dago kai a jikin husnah jin sautin karatun kurani yasa ya sheke da dariya ya yanke jiki ya fadi ya fice daga jikinta momy ta kalli nusrah tace "dama ba ita bace"suka jinjina kai cike da damuwa
******
narjisu ce ta shigo dakin muneeba ta jikin bango Abraham yana zaune kan dadduma kansa nad'e da bandeji bai gantaba batazo masa a yadda zai ganta ba ta dade tsaye tana tinanin yadda zata fito masa ta juya ta Shiga kitchen taga muneeba tsaye tana yanka albasa kamshin girki ya cika kitchen din tayi murmushi tace "wanan abincin saidai ku bil'adama"muneeba ta juyo da sauri taji kamar anyi magana bataga kowa ba tayi tsaki tace "kunnena nayimun gizo"ta cigaba da aiki kamannin muneeba sak narjisu ta koma ta dauko tray da jug din da ta ajiye na zobo ta fito dashi daidai yaseer ya shafa addua ya fito ta dire masa ya kalleta ya jinnina kai yace "sannu da aiki"ta gyada masa kai ta juya baya ta dawo da dubanta garesa tace "ba matarka bace"ya tsura mata ido kawai yaga fuskarta ta canja ta koma wanan budurwar da yake gani gyara zama yayi cikin sassarfa yace"ina kika Shiga?"murmushi tayi masa tace"ina nan ina gefe ne kawai yau nakawo maka agaji da taimakon Allah da yanzun anyi jana'ixarka"ya jinjina kai take ya tuno da yadda trailer ta bugi motarsa cikin seconds yaga tana komawa da baya da baya kamar ana turata kan iska yace "wanan aikin nayi tunanin naki ne dama,Dan Allah wacece Ke?"
"ni matar Abraham ce"tace a takaice take ya gane ya gano cewar wato Abraham na kokarin rabasa da husnah tana kokarin gyara lamarin gudun karta rasa mijinta batare da sanin taimakonsu takeyi ba,"kana ganin taimakonku nakeyi ko?"ya jinjina mata kai tace"tabbas da ba taimako nakeyi ba amma yanzun taimakon nakeyi dikda ina tsananin kishi da husnah yadda mijina ke tsananin sonta"muneeba ce ta shigo dakin daidai yaseer ya bude baki zaiyi magana tace "ah ah kai kadai kake magana kuma?"ya wayance yace "kiranki dama zanyi"tayi turus tana kallonsa yana kallon yadda gashinta ke lilo a bayanta ya burgesa tace "yaushe zobom nan yazo nan?"ta nuna masa ya kalli inda narjisu ke zaune bai ganta ba ransa yad'an baci zuwan muneeba yasa tabar wajen yace"kece kika kawomin halan kim manta ne?"ta dafe goshi tayi shiru tace"na manta kam"ya kalli cikinta da yad'an turo yace"duba kigani cikinki ya fara fitowa"murmushi tayi cikin jin dadi tace "ehh mana ai nadauka kadaina son d'an naka ne zumudin husnah"ta hararesa yace "jeki soyomom kwai please bakina babu dadi inaso inci kwai"ta jinjina kai cike da jin dadi tad'an samu samu sakin fuska wajensa harta fita ta juyo tayi kiasing dinsa ya shafa wajen yayi yak'e ta fice ya mike da sauri yana kalle kalle "ina kike? Dan Allah ki fito"ya wawwaiga bai ganta ba yayi tsaki ya zauna ya dafe kai haushin muneeba ya kama yaseer mema ya kawota?mtswww tsaki yayi yana kaiwa da komowa cikin dakin dan motsi yaji a bayansa ya juya ya dauka itace baiga kowa ba ya zauna ya dafe kansa meyasa ta tafi suna magana?kansa ya dau zafi Yana mamakin yadda sanadin husnah yau shike magana da aljana,muneeba ta fito dauke da plate ta soyo kwai sai zuba kanshi yakeyi ta dire masa a centre table taga ya mike "ina kuma zakaje?bayan kace in soyo maka kwai ko zakaji dadin bakinka gashi na kawo maka yanzun zaka fita"kan yaseer ya dau zafi yasani tunda ya ganta yasan akwai wata matsala dan haka yasa kai ya fice muneeba tabi sa da kallo baki bude ta jinjina kai tabbas tasan saita mike tsaye yadda Anty sadiya ta fada mata dazun ta zauna dirshab tsakar daki,
momy na kokarin kai abinci bakinta ya shigo dakin tace"ah ah yaseer ya naganka haka kamar an koroka?"ya kalli kayan dake gefen kujera yace "momy wad'anan kayan husnah ne?"ta jinjina masa kai tace"kayanta ne kayana ta diba ta tafi dasu taki daukar wad'anan wai wanan aljanin ne ya sai mata"ya kalli kayan yayi tsaki yacev"momy kamar akwai wani abu dake faruwa fa bari inje"momy tad'an tsorata tace"abu kuma?"ya jinjina kai yace "ehh momy kawai tunda naga narjisu"momy tayi saurin kallonsa tacw "narjisu kuma?kaima yanzun ka koma husnah ne aljanun kake gani?"bece komiba zai fita ta tarbesa "Babu inda zakaje da wanan raunin akanka kaji nafada maka ka koma ka kwanta ka huta kabari gobe sai kaje gidan "ransa beso ba ya fice kawai momy ta girgiza kai yanaso ya fita da ita ya siya mata kayayyakin gyara da kwalliya itama ta fito kamar mutim inso samune har makaranta zai sakata kicibis yayi da daddy ya shigo yace "barka dai daddy"d'aga masa hannu daddy yayi yace "barka"yasa kai ya wuce yaseer jikinsa yayi sanyi ya tabbatar daddy fushi yakeyi ya rasa meyasa daddy ke fushi akan maida aurensa da husnah ya dade tsaye ya koma sashen muneeba tana nan zaune ta tasa plate hannunta tana ganinsa tayi ajiyar zuciya tana magana ya wuceta ya nufi daki shi kawai koma ya zaayi sai yaje gidan momy yau,dabara ce ta fado masa yana shiga daki yasan idan yace asibiti zashi babu mai hanasa canja kaya yayi yasa kananun kaya sun karbi jikinsa matashi dan shekara talatin da daya yana fitowa muneeba tace "ina zuwa Kuma?"yayi dan tsaki yace"asibiti zani kaina nad'snyimun ciwo"ta kafesa da ido tanaso ta gano gaskiyar zancen yacev"meye kike kallona?"ta girgiza kai kawai ya fita beko bi ta kanta ba,
*******
husnah ta fito wanka daure da towel ta wanke kanta sosai ya fita fes d'akinta da karatun kurani ta zauna gefen madubi tana kallon kanta gado ta kalla ta girgiza kai tayi murmushi ganin kayan nusrah kan gadonta ta shafa mai data gani da turare mai mugun kamshi momy ta ajiye matashi,ta bude kayan fited gown ce ta tsurawa rigar ido yadda zatasa rigar take tunani yusrah ta shigo tace "har kin fito?"ta jinjina mata kai ta kalli sashen mp3 din yanayi ta rufe kofa ta fita,ta zura rigar sosai ta karbi jikinta ta taje kanta sosai ta dauki ribbom ta maida gashi kam Allah ya horewa husnah tayi mugun kyau orange din atamfa ce da kwalliyar ganye kore jiki shiru tayi tana kallon kanta yadda rigar tabi jikinta kunya ce tayi mugun kamata tana tsaye tana kallon kanta ta nemi waje ta zauna ta tsare mp3 din dake karatun kurani da ido,