← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 68

Sashe 10

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

******
mahaifiyar yaseer shiru tayi tana fuskantarsa kannensa yan biyu guda biyu mata suna gefe ta nisa tace "yaseer ka tabbatar da maganar da kake fadamun gaskiya ne?idan itadin ba yar Alhaji badamasi bace meyasa gwajin jini ya nuna haka?"yaseer ya dago jajayen idonsa cike da damuwa yace "momy nifa ina zargin yarinyar nan aljana ce kawai ba mutum ba sanan babban abunda kedamuna yadda ake hadani da ita wai ni mijinta ne tayaya na zama mijinta ai nafadawa momy idan mani mijinta ne nasaketa"

tsawa momynsa ta daka masa tace "kai yaseer kana hauka ne?to baka isaba idan ma kasaketa dole ka maidata idan kuma baka maidata ba to dama babu idda akanta tunda baka kwanta da itaba amma iname gargadinka karkazo kanamun kuka"gumi ya karyowa yaseer ganin yadda momy ta hakikance yace "momy kukan me zanyi miki nida bansanta ba"momy ta girgiza kai mamakinda al'ajabin yaseer ya cikata tace "yaseer anya kanka daya kuwa anya kana cikin hayyacinka idan ban mantaba ranan aurenka da muneeba kuka kazo kanayi akan kar a aura maka muneeba kanajina jikinka husnarka zata dawo yanzun kazomin da wani zancen banza kana nunamin kamar bakasan husnah ba?"ya kauda kansa gefe ta tsura masa ido sai gumi yakeyi yana tura kai gefe ta jinjina kai tace "tashi katafi zanje wajen malam ya bincikamun idan aljanu gareka su sakeka tin wuri amma kasani Ka tafka babban kuskure tashi kabani waje yau din nan bazaa kwanaba idan nayi sallahr magriba zansa driver ya kaini gidan malam inji inda matsalar take shashasha tashi kabani waje kuma zanzo gidan inga husnar inyi magana da zainab"yaseer ya mike yau mahaifiyarsa dake mugun sonsa itace ta koresa akan husnah?ya Kai kofa ya juyo harara momy ta watsa masa ya fice....

******
ana kiraye kirayen sallahr magriba husnah da Abraham suka fito da siyayya niki Niki wanda ya mugun kashe mata kudi hafeez na ganinsu ya kwantar da kai a mota kada yaseer ya gansa Abraham kuwa kada kai yayi ya bude boot yasa kaya husnah ta shiga yaja motar,

Allah Allah yakeyi yaje ya ajiyeta ya tafi duniyarsu neman narjisu suna isa ya rike kayan suka jera suka Shiga ciki momy tayi alwala tace "yanzun nake cewa shiru"husnah sai faraa takeyi wucewa tayi da kayan dakinta Abraham yace "bari inje inyi sallah momy"ta gyada masa kai ta bishi da kallo ya fito ta window muneeba taga giftawarsa tacewa ummahnta "ummah yaseer ya dawo bari inje"ta mike cike da zumudi"ta fice Abraham na fita ya bace,

yaseer ne yayi parking motarsa a waje daidai nan hafeez ya karaso da sauri yayi parking ko makulli bai cireba ya sha gabansa yaseer ya hada rai yana kallon hafeez,
tuntsirewa da dariya hafeez yayi yana kallonsa ran yaseer yayi mugun baci yace "lafiya ni mahaukaci ne kakemun dariya ko haukar budurwarka ta soma shafarka ne?"

"aikam budurwarmu zakace yaseer ashe dama son husna kakeyi yasa kakemun barazana akanta har kake ikirarin in fita daga rayuwarka?na shaida hakan tinda yau na ganku ido da ido kaida husnah kunje shopping kuna tafe kuna soyayya cike da nishadi"dammm gaban yaseer ya Fadi kallon hafeez yakeyi galala ganin hafeez babu wasa a idanuwansa yasa yace"ni kuma ta yaya ta ina?nidin kagani badai niba kadaiji labarin daddy yabani kudi in kaita shopping ka fito ka fadi haka ba kace ka ganmu tare ba don ni ban fita da ita ba"

"karya kakeyi yaseer niba makaho bane tare na ganku da ita kasani rungumar husnah ko fita da ita shopping bashi zaisa indaina kaunarta ba dan soyayyarta a jinin jikina take kuma kasani haramun kakeyi dan ba aure a tsakaninku"hafeez ya gifta ta gefensa ya wuce cikin gida yabar yaseer baki bude yana bin hafeez da kallo cike da takaici da bakin ciki ya nufi gida cikin sashen su yayi karo da muneeba tana haduwa dashi ta fadada murmushinta shima murmushin yayi mata suka jera tace "yanzun naganka ai a dakin momy ta window injidai ka ajiyeta inda bazata dawo mana ba ko?"dammm gabansa ya fadi shi kuma?ta cigaba da magana "kayi shiru ai naga fitarku nayi hamdala nagodewa Allah mun rabu da Allah kakai"taji yayi shiru tana kokarin bude kofa yasa kai ya shiga ya zauna jagwab a kujera tacev"yadai ya naga kayi shiru meyafaru ni baxan fadawa kowa plan dinmu ba saboda taimakon momy da daddy kayi"girgiza kai yayi yace "muneeba ni banje ko ina da husnah ba hasalima na Dade ina jiranta a waje batazo ba nagaji na buga motata natafi gidan momy"zaro ido tayi tana masa wani kallo "lallai yaseer karka maidani wata mara wayau da hankaki mana ko kuma baa hayyacina nake ba?da idona naganka da wanan kayan fa?"tana nuna yaseer wanda yayi tsuru tsuru cike da tsoro yana kallon muneeba dake kunfar baki ya kasa magana sai kawai ta fashe masa da kuka tace "shikenan sonta kakeyi kaki kafito kafadamun gashi ka fita da ita ka kasa batar da ita kamar yadda kayimun alkawari?"tagumi yayi jikinsa a mace ya kasa motsawa shashekar kukanta yasa ya zabura ya bita bedroom....

*****husnah na zaune gefen gado tana bubbude kaya momy ta shiga tana bun kayan da kallo tace"yanzun sai akai laces da atamfofi dinki ko husnah?"husnah ta jinjina mata kai momy ta girgiza kai cike da kaunar yarta ta ruko hannunta tace "muje ki gaida yayanki hafeez yaya hafeez"husna ta maimaita "hafeez "a bakinta taji sunan ya Mata dadi hafeez na zaune yana daddana waya a parlor husnah ta daga labule ta tsaya tana kallonsa a hankali tace "ina yini yaya hafeez"da sauri ya dago yana kallonta cike da shauki ya kasa boye farin cikinsa husnah ta kirasa da yaya ya mika hannu ya yafitota yace "taho nan".....ummah ce ta kira wayarsa nan da nan ya bata rai shikenan yasan nemansa takeyi be dauki wayar ba yace "ya kike!"ta jinjina kai tace "Alhamdulillah "tana zaune a d'arare momy ta wucesu ta shige dakinta ta tada sallah yacev"husnah ki saki jikinki dani kinji?ni yayanki ne ko?"ya yyada masa kai hade da ajiyar zucuya take taji ya kwanta mata a rai zata rinka magana dashi yana tambayarta tana amsawa har momy ta fito ta samesu yayi sallama da momy ya tafi,

momy na zaune tana jiran shigowar daddy har goma na dare bai shigo ba taga wucewarsa sashen hajiya rabi ta tabbatar yana can ta jinjina kai kawai can kasan zuciyarta nayi mata zafi....

*****
karfe dayan dare husnah ta juya daga gado taji tanajin fitsari da sauri ta mike dakin tana yana juya mata ta murza idanuwanta taga yadda dakin keyi tsoro ya cikata Taja da baya inuwa tagani ta gefenta ta wanan gefen alamar mutum ne a gefenta da sauri ta waiga tace "Abraham...."shiru tayi tozali tayi da mace da bakaken kaya gashi ya rufe mata ido ta sunkuyar da kai wani mugun miyau ta hadiye bakibta na rawa tace "wace....ce"dago kai tayi gashin ya baje a bayanta ta xaro mata idanuwa suka firfito waje ta bude bakinta wasu hakora ta gani masu tsayi sun canja Kala sak horo ta daga hannuwanta taga wasu kumbuna zako zako farare masu ban tsoro dakin na juya mata wata iska na kadawa,

cikin wata irin murya tace "narjisu....narjisu ce husnah nadawo gareki"husnah bakinta na rawa kamar mai jin sanyi tace "narjisu.......narj"sai kawai taga ta malkwaye ta rikida ta koma narjisun data sani haske ya bayyana cikin dakin ta harde hannuwanta a kirjinta tace "kin tabbatar da nidin narjisu ce?"jikin husnah na karkarwa ta kasa magana,

"ki rabu da mijina Abraham idan kinaso ki zauna lafiya idan kuma ba haka ba saina hanaki zaman lafiya sai rayuwarki ta zame Miki DUHU bakin kirin Wanda zaki kasa ganin haske"gumi ne yake zubowa husnah cikin tsoro take narjisu ta rikida ta koma yadda tazo mata dakin ya shiga juya mata winduna suna budewa suna rufewa nan da nan husnah ta shiga waige waige ganin komi na dakin na sauyawa ta Dafe kanta ta runtse idanuwanta ta kwalla kara

zabura momy tayi daga kwanciyar da tayi tace "husnah!!!!"ta nufi dakin husnah aguje......

*LITTAFIN DUHU NA KUDI NE KI BIYA DARI UKU300 KI KARANTA IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN ALLAH YA ISA*

GA MAI BUKATAR BIYA YA TURA 300 TA WANAN ACCOUNT DIN

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYAN KUDI TA WANAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN TA NUMBER

*SLIMZY*✍🏻
Chapter 10 · 0% Book details