← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 68

Sashe 63

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

muneeba na ganin momy ta fashe da kuka tace "momy ke ki taimakamun in rabu da abinda ke cikina kinji?mahaifiyatace ta cutar dani"damm gaban momy ya fadi ta kalli yaseer ya kalli momy tare sukace "ta cutar dake?metayi ta cutar dake muneeba ki fadamun karki boyemun komi"ta kalli yaseer cike da takaici da tsananin son da takeyi masa da tausayi daya bata ta kasa magana sai hawaye da yake zuba a idonta kamar famfo daddy yace "muneeba ki fada mana meyafaru kinsan damuwarki dama?"girgiza kai tayi ta cije baki ta kalli yaseer daya kafeta da ido tayaya zata kalli tsabar idon yaseer ta sanar dashi cewar cikin dake dauke a jikinta ba nasa bane cikin boka ne?tayaya zata dubi tsabar idon daddy dayake matsayin mahaifinta da mijinta ta sanar musu da tayi zina da boka?ta fashe da wani irin kuka mai ciwo ta gagara magana mikewa tayi kawai ta shige bedroom dinta tana kuka mai ban tausayi yaseer ya mike yana fad'in"ki dawo ki sanar mana da abinda kike boyewa muneeba"dakatar dashi daddy yayi "yaseer ba haka akeyiba ka bita a hankali tunda tayi wanan furucin ka kwantar da hankalinka nesa tazo kusa zata fada maka sauran ma inaga mubarta ta kwanta dare yayi ko?"yaseer zaiyi magana take jiyo yunkurin Aman husnah a kitchen momy ta ruko hannun daddy jin husnah na amai "muje ko?mutafi mubar yaran nan suma zasuje su kwanta ne"ta jinjina mata kai kamar wani karamin yaro yasa kai ya fice tabi bayansa tana jinjina kalamai da maganganu da muneeba ta fada,

yaseer kuwa ruko hannun husnah yayi suka rufewa muneeba kofa suka wuce tsaye muneeba tayi a jikin window tana kallon yaseer rungume da husnah yana tarairayarta,ta gefen idonsa ya hango kamar mutum a windown muneeba ya juya da sauri ta saki labulen ya ganta ya girgiza kai cike da tausayawa da alhinin maganganunta da suke barazanar tarwatsa masa kwakwalwa haka suka shiga sashensu shiru sai karatun alkurani parlorn ma sun kashe wutar alamu sun nuna sun kwanta har sun wuce suka jiyo muryar ummah hadiza nayi musu magana "ya jikin na muneeba?ya kuka sameta"

yaseer yasa hannu ya kunna fitilar dakin haske ya gauraye cikin damuwa ya zayyanewa ummah hadiza komi dangane da muneeba da maganganun da take furtawq ta jinjina kai tace "tabdijan wanan abu akwai lauje cikin nad'i yaseer anya munafukar matar nan mai kama da shedanu batasa yarinyar nan gaba ta aikata wani abu da yazo yanzun yakeson zame musu masifa ba?"ajiyar zuciya da numfashi yaja ya sauke yace "yadda take maganganu ummah hadiza nafara ko kwanto akan wanan cikin nata"ummah hadiza ta jinjina Kai "gobe zaa zo da malam insha Allahu idan aljanune zai fada koma menene yana ganintw zai fada ka kwantar da hankakinka kaje ku kwanta rike matarka wanan laulayi nabata wahala kuje asibiti idan kun natsa saida safe"ta juya ta shige daki ya kalli husnah tadan zumburo baki tace "banason ganinka cikin wanan yanayin ina shiga damuwa nima banason damuwarka"murmushi yayi mata ya ruko hannunta suka shiga daki ya taimaka mata tayi wanka ya gasa mata jiki da ruwan zafi ya daukota ya koma yayi wanka yazo yasa jallabiyarsa ya gyara mata kwanciya ya tofeta da addua ganin tayi bacci yasa shima ya kwanta gefenta ya daga kansa yana kallon ceiling zuciyarsa cunkushe da tunani kala kala kunnuwansa har yanzun maganganun muneebw yakeji....ya mike ya shiga zarya cikin dakin yana kaiwa da komowa husnah ta motsa ganinsa yasa tadan tsorata ta kunna fitilar gefen gado "meya hanaka bacci?"tambayarta tasa yayi saurin juyowa ya hayo gadon yw rungumeta yana bubbuga bayanta "nakasa bacci ne maganganun muneeba ke barazana da kunnuwana da zuciyata cikin tattausan lafazi take lallashinnsa hade da kissa da har tajw raayinsa suka kwanta rungume da juna...

******
da sassafe hajiya rabi ta nufi sashen muneeba tana tafiya kamar akan iska ko ganin inda takesa kafarta batayi a kitchen ta jiyo motsinta da sallamarta can kasan makoshi tace "muneeba ya jikin naki?"jin muryar mahaifiyarta yasa taki juyowa tadai amsa amma ba a sake ba "muneeba fushi kikeyi dani muneeba?ni mahaifiyarki ko?wato wanan bakar dagar matar ta shiga ta fita tasa alhaji ya sakeni yanzun ke kuma kina gaba dani dubi yadda kika koma muneeba dik kin rame kin fige?"muneeba ta juyo a fusace ta kalli mahaifiyarta tace 'au kin damu da ganina cikin wanan halin ne ummah?bayan koma menene ya sameni kece sila?waye silar shiga tashin hankalina da rashin lafiyata?duba kiga yadda dakina yake karni da wari duba kiga yadda yseer da husnah suke shan soyayyarsu ni kuwa fa babu dama dik waye ya jawomin?"tana maganar muryarta na rawa idonta cike da hawaye ummahnta ta kalli cikin yayi kasa kasa can sosai dik ya rairaye kamar baa jikinta ba muneeba ta cigaba da magana "ummah saki kuma da daddy yayi mike kece sila ninayi nadamar binki da nayi muka sabawa Allah nayi nadamar biye miki da nayi kika jefani a rijiyar gaba dubu"ta fashe da kuka,

"ki kwantar da hankalinki ki shirya yanzun zamuje wajen wanda zai bamu magani yanzun kisamu lafiya ga kawata nan zuwa akwai wani boka tace idan mukaje bazamu dawoba batare da ya cire miki abinda ke jikinki ba"

ummah hadiza ne da hajiya saude suka nufo sashen muneeba da taxo da sassafe akan maganar zuwan malam kicibis sukayi da daddy da hajiya zainab zasuje ganin jikin nata suka rankaya,

muneeba cike da tsana take kallon mahaifiyarta tace "to bari kiji bazani ba koda zan mutu da cikin nan yanzun nan da kike ganina tuba nakeyi ina rokon Allah gafarar zina da kikasani na aikata da boka yasamun abinda ke cikina"cakkk daddy da su hajiya saude sukayi suna kokarin shiga ko wannensu cikin tashin hankali yake jin furucin muneeba na karshe ta cigaba da magana "tabbas kuma zan sanarwa dasu daddy cewar kece kikai silar samuwar wanan cutar a jikina ta hanyar saka boka yayi zina dani yasamun ciki in haihu shine yasamun ciwo"waigawa hajiya rabi tayi jin motsi a kofar kitchen din tsautsaye taga su momy hajiya saude da daddy da ummah hadiza....

cikin sauri yaseer ya shiga gidan tare da malam ya nufi cikin gida ya shiga bega kowaba sai sadiya dake fito da akwatunanta dana hajiya rabi yace "inasu momy?"a sanyaye tace"suna sashen muneeba"har yaser ya wuce ta tsaidashi "Dan Allah yaseer ka rokarmun alfarma daddy ya rikeni kaji?wallahi zan zauna dasu da amana"yaseer jin abun yayi banbarakwai ta zauna dasu dama korarsu akayi?ya kalli akwatunan bece komuba yace "malam muje sashen mara lafiyar dik suna can"malam yabi bayansu....

To mutanena masuso muyi savin number juna suyimun magana sanan akwai documents hudu nawa na zafafan labarai akan 1k meso tamun magana....

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI KARANTA IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BANYAFEBA*

08036953516
07042277401

*SLIMZY*🥱

50
muneeba hawaye ke gudu a idonta bugun zucuyarta ne ya tsananta ganinsu daddy a tsaye dukkansu sun zuba musu ido hajiya rabi ja da baya tayi kafafuwanta sun kasa daukarta ta durkushe a kasa jagwab daddy ya kasa magana gumi ne kawai yake karyo masa kawai ya fashe da kuka yana nuna hajiya rabi jikinsa na karkarwa "Allah ya isa tsakanina dake rabi?yanzun dama shirkarki da rashin tsoron Allahnki har ya kai kisa yar cikinki da kika haifa tayi zina?rabi zina fa kikasa muneeba tayi da boka"yaseer wata juwa ce ta fuzgesa jin furucun daddy yana kokarin shigowa ganinsa sukai kamar an jefosa malam yayi sallama cike da natsuwa mazurai da idanuwa yaseer keyi idanuwansa sunyi jajir yana kallon muneeba ko kifta idonsa bayayi tamkar an dasashi yake tsaye itama shi take kallo cikin kuka ta sunkuyar da kanta kasa cike da nadama da tsananin tashin hankali ta durkushe akan gwiwoyinta cikinta ya zauna akan cinyoyinta tace "yaseer ka gafarceni na aikata babban laifi na aikata mummunan laifin da nasan bazaka taba yafemunba,dikda zuciyata da gan gan jikina basason aikata hakan amma zuga da kururuwa da busar iblis hade da wanan da nake kira mahaifiyata suka hadu sukai tasiri wajen karfafamun gwiwa na aikata zina da aurena na aikata mummunan aiki da boka matsafi, yaseer am sorry to say cikin jikina ba naka bane cikin boka ne wanda a yanzun haka bokan ya mutu ya mutu ya barni da cikinsa a jikina wanda banida tabbacin shin mutum ne ko aljan ko kuwa wata cuta ce?"tuni hawaye sun balle a idon yaseer dikda dauriya irinta yaseer da jarumta kuka yaseer ya balle dashi yana ja da baya hafeez ya rukosa cikin tattausan lafazi yace"comr on my friend bansanka da raunin zucuyaba kai jarumi ne wanan mummunar kaddara ce ta sauka a gareku wanda muneeba koba yar uwarka bace ta cancanci taimako da afuwa"
Chapter 63 · 0% Book details