Sashe 21
Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
daddy ne ya shigo dakin cikin shirin fita sai kamshi yake zabgawa momy kallo daya tayi masa ta kauda kanta cike da takaici shima haushinta yakeji yace "ina takardar da yaseer ya baki jiya?"shiru momy yayi cikin zuciyarta tace takarda?tabbas taga lokacin da yaseer yaba daddy takarda amma ita be bataba tace "wace takarda kuma?"hajiya rabi tana kokarin shigowa tace "takardar sakin husnah daya rubuta mana ai biyu ya rubuta yaba daddy nasa ya baki dayake bakiso arabashi da ita yasa kika boye naki na daddyn ma kika dauke"daddy ya dubi hajiya rabi ya jinjina kai yace"da kyau yaseer ya saki husnah ko?dama ai bai dora mata idda ba tunda ko tarewa batayi ba batamasan da auren ba yanzun ta mijinta aljani takeyi dan haka nasan yanzun yaseer yaje aiki zan kirasa a waya aida ransa inji sanan ya rubutomin sabuwa saboda hafeez inbashi aurenta suje su karata dama shi ya tattagota ninafara ko kwanto ma akanta dikda ban tabbatar ba"yana gama magana yasa kai ya fice bai jira ta bakin momy ba,gaban momy kuwa dukan uku uku yakeyi wato yaseer takardar sakin husnah ya rubuto?hajiya rabi ta katse mata tunani tace "tunanin me kikeyi zainab?"ta sheke da dariya tace "husnah itada yaseer saidai ido dan tuni nasa yaserr ya rubuta takardar saki uku zaa damkawa yarki idan ma kinga takardar kin boyene to karyarki Tasha karya idan kinga yaserr be sawakewa husnah ba to niko shi wani ya mutu ne"momy ta watsa mata kallo mai cike da tsana tacev"tirre da halinki rabi dik kutungwilar da kike kullawa wallahi ta Allah bataki ba burinki bazai taba cika ba kuma yaseer da husnah babu Wanda ya isa ya rabasu dan tun husnah na cikin yaseer ke dawainiya da ita dan haka sihirin da kukayima yana gab da karyewa dan yanzun haka yaseer na cikin dakin husnah yana ciyar da ita"shekeke hajiya rabi ke kallon momy ta sheke da dariya tace "mafarkin da kikayi jiya ko tabadai ciki tare da mijinta aljani yana kwanciya da ita"tasa kai ta wuce tana dariya momy tayi kwafa maganar hajiya rabi na karshe yayi mata matukar zafi hajiya rabi kuwa ranta ya sosu cewan da tayi yaseer na tare da husnah a daki dan haka yasa ta nemi waje ta labe,
momy kuwa tsaye tayi jikin labulen dakin tana iya hango yaseer yana rike da plate din yake taku sautin takalminsa a tiles yasa tayi saurin juyowa tanayin ido hudu dashi ta mike fuskarsa ce ta shiga canja mata ta koma yaseer ta rikide ta komata Abraham tsoro ya kamata tadan ja da baya cike da fargaba take kallonsa tana ganin yadda yake rikida,ganin tanaja da baya yasa yaseer dan furgita ta zauna gefen gado bakinsa dakyar yasamu damar fusta addua ayatul kursiyyu yayi Abraham na tunkarosa ya koma da saurin jin zafi da hucin wuta a tattare da yaseer rikidewa yayi ya shige jikin husnah wani abu daga idon husnah ya fito zirrrrr kamar walkiya ko shocking Yana wuta ya shiga bakinsa ji yayi harshensa ya daure jikinsa sai tsuma yakeyi bugun zucuyarsa ya tsananta yana zama a gabanta Yana kallonta ita kuma a Abraham take kallonsa shi kuma tuni fuskarta ta rikide masa ta koma abun tsoro fuskarta ta koma baka kirin irin yadda yagani jiya take hakoranta suka zazzago masu tsayi guda biyu idanuwanta a warwaje gadhin kanta kamar kaya yaseer ya runtse ido dakyar ya kira sunan Allah kamanninsa suka koma nasa sak tace "meyasa kake canjawa kana komamun Abraham yanzun naga ka rikide ka koma mutumin nan daya rungumeni jiya"a sanyaye tayi maganar idanuwansa a rufe ruff baya kallonta daya bude ido kamanninta ke sauyawa haka ya dibo abincin a hankali yace bude bakinki "ta bude bakinta batare da tayi masa musu ba ya bata ta kara karba a haka yake bata har sau biyar daga bisani yaji wata iska mai karfin gaske ta mamaye dakin windows din cikin dakin ke kadawa fanka ta fara zazzagowa kamar zata fado ya juya yaga wardeobe dinta na buguwa yanayo kansa da karfin gaske aka fincike plate din abincin aka wurgar gefe ji kake tasssssss tasa hannu ta toshe kunnuwanta aka angije yaseer daga gefen gadon ya fadi kasa wata murya yakeji tana magana sam naya fahimtar me ake fadi ya mike cike da tsoro saidai ya kasa gudu ya kuma kasa kallon inda take ganin drwer nayo kansu yasa hannu ya fuzgota ta suka Fadi kasa ta fada kirjinsa kamar kugiya aka dauketa aguje momy ganin wanan dramer ta shigo dakin ganin yaseer warwas a kasa tace "an tureka ko yaseer tashi tashi"tana kokarin rukosa yayi murnushi yace "zan iya tashi"ya mike ya juya ya kalleta rabe a gefen gado sai gumi takeyi ta bishi da kallo ya fice yana fitowa a idon hajiya rabi ya fito ta zaro idanuwa waje tana kallon yaseer cike da tsananin mamaki tasa hannu ta murza idanuwanta tabbas shine a hankali ta taka ta koma sashenta dakyar take taka kafarta saboda yadda jikinta yayi nauyi jiri na nenan daukarta....
ko ganin gabansa yaseer bayayi ya fito kicibis sukayi da muneeba ta zuro hijab tana sauri da slippers a kafafuwanta turus tayi ta kallu agogon wayarta tana kallonsa cikin tuhuma tace "yadai har yanzun baka wuce aiki ba?me kakeyi a sashensu momy naga kamar daga nan ka fito"nannauyar ajiyar zucuya ya sauke tana kallon yadda kwayar idanuwansa suka kada cikin tuhuma take kallonsa gabanta ya tsananta faduwa ruko hannunta yayi ya shafa cikinta yace "babu komi mun dan tattauna da daddy ne yanzun ma sauri nakeyi zan fita in tafi"ta waiga bataga motar daddy ba tace "ai daddy ya dade da fita naga fitarsa ta window"gabansa ya fadi bayaso ranta ya baci sam yarasa meya shiga jikinsa yakejin yana damuwa da wanan yarinyar sam yar da ko ganinta bayasonyi bayi rasa nasaba da kamannin da yake gani da wata yarinya dayasani a baya kwalla taji ta cuko a idanuwanta ganin ya rasa me zaice masa kawai ta gifta ta gefensa ta wuce juyawa yayi yana kiranta "muneeba muneeba"ta juyo yadda idanuwanta suka kada yasa yaji ya damu saidai sauri yakeyi yayi latti dole ma ya wuce yasan idan ya dawo akwai daru ya kada kai ya wuce cikin damuwa da tsananin faduwar gaba ya bude mota ya shige yaja ya fice,
cikin kuka ra fad'a dakin ummahnta wadda ke tsaye tana kaiwa da komowa tana sakawa tana kwance yadda zatayi da wanan lamarin da yake shirin bullowa muneeba ta fada kan gado ta fashe da kuka tace "ummah nashiga uku yaseer zai dawo hankalinsa akan husnah yarinyar da tuni muka dauke masa hankali akanta idan ya dawo hayyacinsa na tabbatar tawa ta kare a gidan nan gaba daya tarewa zaiyi wajenta dikda dai nasashi ya rubuta mata takardar saki"ummsh ta karaso tace "mummunan tashin hankalin da nake ciki kenan takardar saki kuma yabawa daddy saidai daddy ya yar da takardar yanzun haka baa ganta ba"zabura muneeba tayi tace "shikenan tawa ta kare nashiga uku ummah kiyi wani abu ya zamuyi mutafi wajen boka gashi karyar ciki nayi masa sam banaso hankalinsa ya koma kan waccen matar aljan din"ta Dora hannu akai kuka takeyi hawaye na zuba ummah ta dafata tana kasa da murya tace "ki kwantar da hankalinki inada tabbas akan boka nakan tudu matsafi ne na gasken gaske na tabbatar sai yasa husnah tabar gidan nan dan haka na yanke shawarar mu shirya yau muje wajensa inaso yanxun ki kwantar da hankalinki yarinyar da rainon aljanu ce me zaayi da ita? itama durkusar da ita zamuyi yarda ko sallah kin taba ganin tunda ta dawo tayi?dan haka kara burkitar da ita zamuyi nida zanga aljanin ma zance ya sake saceta tashi maza kije ki shirya"muneeba ta share hawaye cikin kidimewa tace "karyar cikin da nayi fa?"hajiya rabi tace "zamuje wajen boka akan hakan inta kama a sama miki ciki dik zaayi kedai tashi maza kije ki shirya"ta mike cikin sauri a kidime tasa hijab din gaba a baya ta fito kicibis sukai da kanwar momy mahaifuyar husnah kallon kallo sukayi ko gaisheta batayi ba tsaki taja mata ta watsa mata harara ta wuce,