← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 68

Sashe 16

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

wani park suka isa Abraham ya zaunar da husnah ya tsaya gabanta yace "Mai zan kawo miki?ko yar kullum?"ta gyada masa kai tana dariya cike da shaukin soyayya Abraham yayi kissing kumatun husnah ta shafa wajen shock yaser yayi shida muneeba da sukai parking a wajen yaseer ya kalli muneeba ta kallesa ta gagara magana yana nunasu suna dariya yace "wancen ba hafeez bane da husnah?inace cewa momy yayi ya tafi karbowa husnah magani ya tafi nemo malami mai rukiyya".... Abraham yace mata tana dariya"ko insake kissing dinki ne?"ta gyada masa kai yakai bakinsa bakinta yaseer ya saita wayarsa ya kashe musu hoto muneeba dadi ya kasheta tace "ya kawota ne dama dan ya rinka fita da ita yana iskanci da ita dama ba wata husnah sai karya yazo ya ajiye mana Ita gara da kayi musu hoto maganin karya hallara"yaseer cikin bacin rai da takaici yace"bazan bari ya ganni ba mu canja wuri dadina daya da nayi musu hoto Wanda shi zan nuna a gida prove in nunawa momy cewar ba husnah bace wanan karuwar hafeez ce"muneeba tace "kwarai dagaske gara da Allah yasa kai ka gansu yanzun da nice da cewa zaayi nafada ne dan kar ka maida aurenka da husnah ka tabbatar babu wasu aljanu sai karya?"yace "gani ya kori ji"ya karya motarsa ya juya ya fice Abraham yayi murmushi dik yaji abinda suka fada yana sane yati hakan ya kalli husnah a Ransa yace "ke tawa ce nikadai babu mai rabani dake,kallonsa tayi yayi shiru a wajen tace "lafiya?"yace "bari in Siyo miki" park ne dik ga Yan mata da samari nan suna zazzaune a kujeru narjisu ce ta dira a wajen tana shawagi a kan iska tana kallon husnah tayi wata dariya "hahahaha"da sauri husnah ta juya tana waige waige bataga mai dariyar ba takalli tables din dake gefe da gefenta dik yan mata da samari ne saidai tanajin wata karar iska a kunnenta narjisu tace"bazan taba barinku ku zauna lafiya ba husnah kina bil'adama ki rabani da Abraham mijina jinn da nake tsananin kauna".... Abraham na tsaye wajen masu siyayya hankalinsa ya tashi gashi a suffar mutum narjisu tazo wajen yasan abinda tazoyi babu yadda zaayi yayi yunkurin wani abu dan zasu tsorata jamaar wajen gumi kawai yaji yana karyo masa cikin tsananin damuwa waigawa yayi yaga husnah tanata runtse ido ya kalli narjisu dake tsaye ta kere kowa tsawo wata irin dariya takeyiwa Abraham husnah ta juya tana kallon mutanen gefenta tagansu da wata iriyar fuska mai ban tsoro bakinkirin da hakora a waje ta kalli na gefen damanta taga sune ta zabura ta mike tana bin wajen da kallo cike da furgici take kirab "Abraham"cikin sauri Abraham ya taho da hollandia a hannunsa da cups mutanen wajen kallonta sukeyi yadda take runtse ido tana nunasu bakinta na rawa tace "do ...dodo wayyoo Allah na nashiga uku"sai kowa ya fara kallon kowa suna kallonta cikin wata fuska take ganinsu dik kawunansu da kahonni ta zuba aguje zata fita Taku daya biyu Abraham yayi yakai gate ya cafkota dikda irin nisan dake tsakaninsu da wajen ya rungumeta tana fuzgewa tana ruko hannunsa "ni kazo mu gudu kazo mutafi gida"Abraham yana kokarin rada mata a kunne narjisu ce inaaa ta rude jamaar wajen a guje suke fita cike da tsananin tsoro ganin sunayo kansu da wanan bakar fuskar da hakora ta kara fuzgewa zata zunduma da gudu ya fuzgota....

*****
hajiya saude ce ta rafka tagumi tana kiran yaseer dakyar ya dauka tacev"dik inda kake kazo gida yanzun kataho gida halan bakasan baaga husna ba"
"momy can naga husnah da hafeez a wani"ya bata labarin wajen cikin bacin rai yake magana ya d'ora da "dama hafeez ya kawota gidan mu ne dan ya rinka fita da ita Yana rungume rungume da ita"momy ta daka nasa tsawa tace"karyane ba hafeez bane hafeez din dayavtafi tahowa da malamin da zai mata rukiyya hafeez bazaiyi haka ba wanan sharein jinnu ne"ran yaseer ya bacu yasan momy bazata yarda ba amma zasu yarda idan ya kawo hoton husnah da hafeez,yana rike da hannun muneeba sun fito shopping ya kashe mata kudi zucuyarta fari tass tace"muje gidan kada ran momy ya baci banason bacin ranta kaga uwace bacun ranta zai shafeka"cikin kissa tayi maganar don yaji dadi murnushi yayi suka shiga mota suka nufi gida,

hafeez dakyar yana nan zaune yasamu wani ya taimakesa yayi masa kwatancen gidansu akan ya kaisa gida dakyar ya sauraresa ya daukesa a mota suka nufi gida
*****
kuka sosai momyn husnah keyi tana rungume a jikin innah wadda keta kwantar mata da hankali hajiya rabi na jifanta da harara cike da kishi momyn yaseer tacev"akwai magani a jakata dik abinda ke jikin yaseer yanashan maganin nan ya karye zanga ta iskancinsa kuma wallahi saiya auri husnah ko bayaso"hankalin hajiya rabi yayi kololuwar tashi ganin momy ta fito da wata gorar swan ta ajiye gefenta kallom gorar takeyi cike da zullumin yadda zata sauya ruwan ciki daddy ya buga tagumi sallamar Abraham data husnah sukaji murya biyu amma husnah sukaga ta shigo a hargitse zabura sukayi momyn yaseer ta rukota ta fuzge husnah ta kalli Abraham tace "kaga suna rikeni ni kace su sakeni"kallon kallo sukayi wata murya sukaji a parlor "tinda bata bukatar rayuwa daku ku kyaleta ku sakarwa matata mara tayi fitsari nine na fita da ita munje mundawo tunda baku barinmu muyi soyayya a gida"ya rike hannun husnah sukaga hannunta yadan daga alamar rike ake da hannunta dukkansu sun shiga furgici da tsananin tsoro yaseer na shigowa da muneeba ys ciro wayarsa yace "bari in nuna muku ku tabbatar can naga hafeez da husnah suna rungumar juna harda kiss"ba wanda ya kulasa ya ciro wayarsa ya lalubo hoton yana nuna musu abun mamaki husnah ce kadai a jikin hoton babu hafeez momy tayi masa wani kallo tace"toba hafeez kaganiba aljani kagani yaseer dan yanzun yayi magana dim excuse din da zaka kawo saidai ka kawo karbi wanan ka shanye"ta tsugunna ta mika masa gorar ruwa kallon gorar yakeyi yana kallonta ta daka masa tsawa tace"karbi ka shanye yanzun kafin in sassaba maka"yaseer ya karba yana budewa muneeba ta kalli ummahnta Suka hada ido ummahn muneeba gumi ne kawai yake karyo mata

husnah kuwa cikin daki Abraham ya taimaka mata ta cire rigar jikinta daga ita sai under wear skirt babu ko bra shima ya cire rigarsa ya janyota yace zokimum wasa.....

*WANAN LITTAFIN NA DUHU NA KUDI NE 300 DIK WADDA TA KARANTAMUN BATA BIYABA ALLAH YA ISA*

*GA MAI BUKATAR BIYAN KUDI GA LAMBAR ASUSUN BANKI*

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYA TA WANAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN....

UWAR GIDA KO KINSAN ANTYN AFFAN NA KAWO KAYAYYAKI A KUDI KALILAN DA RAHUSA?INA MASU BUKATAR SIYAN KAYAYYAKIN ANKO? SUNA KO HADA KAYAN AKWATI CIKIN RAHUSA?TO GA DAMA TASAMU KI TUN TUBI
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*Auntyn~Affan collection*
Dealer in all kinds of material,shadda,atampa,
Laces,and alot more.......
*07045216749*

20

A kofar gidansu hafeez meenahl ta sauka a keke napep cikin sauri tagaji jakar ma wani irin ruko tayi mata Allah Allah takeyi ta shiga cikin gida tayi magana da ummah akan yadda tabar su hafeez da yaseer dan tasan ummah ta koreta ne kartaji suna fada tana kokarin bude gate ta Shiga horn yasa ta juya da sauri mai gadi ya leko da kai motar hafeez ce tagani raga Raga ta d'ora hannu akai ta fashe da kuk"nashiga uku ya hafeez meyasamu motarka haka innahlillahi wa innahilaihi rajiun ya hafeez yayi Accident"

ummah na zaune a parlor da sister dinta sunzo da yaransu kanwar ummahn tace "kamar muryar meenahl nakeji tana rusa kuka"ummah ta zabura jikinta na rawa ko takalmi batasa ba dukkansu aguje suka fice daga parlorn suna rige rigen fita suga wanene hafeez suka gani an rukosa Wanda ya rok'a ne ya kawoshi gida ummah ta fashe da kuka "lafiya hafeez meyafaru naganka cikin wanan yanayin accident kayi?a ina kayi hatsari kaiba barin gari kayiba"

"in Banda Abinki ummahn hafeez ai ko a kofar gida kana iya hatsari tsautsayi kuma ai baa kauce masa"kuka ummah ta fashe dashi suka rurrukeshi aka shiga dashi ciki sayyeed cousin dinsa ya karbi wayoyinsa da makullin mota wajen wanda ya kawosa yayi masa godiya ya karbi number wayarsa suka shiga ciki meenal itadai kuka takeyi aka shimfide hafeez akan gado fuskarsa dik jirwayen jini na ciwon dayaji ummah ta kasa hakuri tambayarsa takeyi"hafeez meyasameka a ina wanan abun ya faru da kai"rufe idanuwansa yayi mulmulelen dutsen dayake yawo a sararin samaniya yake gani lokaci guda ya tuna da yadda abun yafaru ya bude idanuwansa ya kasa magana yana kallonsu daya bayan daya Abraham ya gani a suffarsa lokacin dayazo cikin mutane yanayi masa wani wani miyau ya hadiye daga bisani ya gyara kwanciyarsa tunanin yadda zai yiwa ummahrsa bayani yakeyi ya tabbatar idan har ya fad'a mata abinda ya samesa cikakke to yasan zata dauki hukunci akansa dakyar cikin yanayi na ciwo da jikinsa keyi kamar an d'ora masa dutse yace"ahhh washhh"
Chapter 16 · 0% Book details