← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 68

Sashe 58

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
hajiya zainab na bedroom dinta ta idar da sallah tana adduoi taji takun shigowar mutum har yanzun kuka takeyi gaba daya bata cikin sukuni daddy ne ya tsaya daga kofa a darare yana kallonta sam ya kasa gane kansa ya kasa gane meke faruwa tsakaninsa da ita dik yadda yakeson shiga harkarta taki bashi fuska yace "zainab har yanzun baki daina kukan ba ko?baki duba abinda ke gabanki zaki cutar dashi"ta dago jajayen idonta ta wurga masa harara ya tako ya shigo dakin jiki a sanyaye ya zauna gefen gado tace "zaman yayana nakeyi a gidanka zaman in haihu nakeyi dana haihu zan kama gabana"gaban daddy ya yanke ya fadi gumi ne ya karyo masa dakyar ya hadiyi wani abu daya tsaya masa a wuya yace "kamar yaya?"tanasane tabbas daddy ya dawo hankalinsa dik abun nan da yakeyi tamkar wani mai bataccen tunani tace "kaida kace in tattara inbar maka gidanka in nemi uban dan da girmana nayi cikin shege?kaida matarka kuka taru akaina"daddy ya girgixa kai yace "matata kuma?nidin mukai miki haka wace matar tawa?"dago ido tayi ta kallesa ta kauda kanta kawai batare da tace wani abuba ya tako zai karaso ta dakatar dashi gababta na tsananin faduwa tanason mijinta sosai tasan yadda badamasi ke tsananin sonta ta kara tabbatar da baya cikin hayyacinsa amma wanen abun dayasha ya dawo da kaso tamanin cikin dari na hankalinsa tace "nidai bana bukatar wata magana dakai kawai kabarni inji da matsalar da yata ke ciki"

"yarkice ke kadai?"ya watso mata tambaya a sanyaye batace komiba ta mike ta gifta ta gabansa ta fice abinta ya dade ya kasa motsi sanan ya fita daga sashenta sashensa ya nufa cike da damuwa da tunani kala kala....
******
"jinin ya tsaya?"tambayar da yaseer yayiwa husnah kenan tad'anyi farrr da ido ta jinjina masa kai "ehh gaskiya niban gansaba dai ya tafi"a yangace tayi maganar ya saki baki yana kallonta mamaki take basa yace "Mai kikeso na siyo miki?"tayi shiru tayi jimm kadan tace "banaso ka wahalar da kanka"yace cikin shauki da kauna "Allah ko?"gyaran murya ummah hadiza tayi musu kunyq ce ta lullube husnah ta rufe fiska yaseeer ya fice yana dariya,

ummah hadiza ta gyara zama tace "ke bude idonki ki kalleni"husnah ta bude ido cike da kunya ta sunkuyar da kai tace "karkiji kunyar mijinki ko kadan kinaji na mace a gidanta yar iska take zama idan kinki waccen karuwar kishiyar taki zata kwace mikishi"tadan bude ido ummah hadiza ta jinjina mata kai tace "kwarai dagaske dan idonta yafi naki budewa amma nima dikda ba yar zamani bace zan budar miki da naki idon zan koya miki yadda zaki karbi mijinki a hannunki kafin wata ta karbe mikishi"husnah tayi ajiyar zucuya ta maida hankakihta gaba daya kan ummah hadiza kamar ance ta waiga taga kamar gilmawar abu tayi saurin kallon wajen ummah hadiza ta kalli inda husnah ta kalla tace "yadai?"tace "wani abu nagani ummah naga wani Abu dogo ta nan"yinkurawa ummah hadiza tayi tace "nusrah ruga ki kiramun yaseer maza ya dawo wanan shedanin yazo"nusrah ta fita jiki na rawa ummah hadiza kitchen ta shiga ta dauko tabarya aguje zaninta na kwancewa yaseer turus yayi ganin ummah hadiza da tabarya yace "lafiya meyafaru?"ya kalli husnah jikinta nata rawa tace "kamar abinda nagani a mota"yaseer idonsa suka firfito yace "yau koni koshi a gidan nan"muryarsa sukaji "ka isa kayimun wani abu kana bil'adama ina aljan karka manta da nidin Zan iya sauya halitta daban daban in kuma yi dik abinda nagadama dan haka bazan taba barin abinda ke ciki. husnah ba"ya fito dankareren maciji ya zagaye gadon yayi mugun girma yusrah da akabari gidan ita tayi saurin turawq momy message ta wayarta Yaseer ji yayi gaba daya wani karfi da kwarin gwiwa yazo masa husnah kuwa cikin tashin hankali take jikinta na rawa yaseer cikin sassarfa yake fadin"karkiji tsoro ki kwantar da hankalinki babu abinda zaiyi miki ina tare dake"girgiza macijin yayi kansa ya rikida ya koma mutum sai sheki yakeyi bakin kirin ummah hadiza jikinta sai rawa yakeyi ta kasa motsa tabaryar dake hannunta yaseer yayi addua ya murza hannunsa ya kaiwa Abraham cafka.....

"momy in zakuzo kuzo da malam kawai ga yaya yaseer nan aljanin nan ya fito masa zasuyi fada karya kashe mana yaya momy"cikin kuka yusrah ke labe tana wayar ummah hadiza sakin tabarya tayi zaninta ya kwance taja da baya zata afka musu sukaji an rukota ta Baya momy ce suka dawo dama basuyi nisaba tafiyarsu da malam yaseer na rike da Abraham ruko sosai yayi masa dikda irin nauyi da yadda iska ke wujijjigasa bai sakesa ba addua kawai yakeyi da karfi gumi kawai ke karyo masa.....

*WANAM LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANRAMUN BANYAFEBA*

07042277401

*SLIMZY*✍🏻
46
momyn husnah na tsaye cikin kitchen ta gama had'a miya taji gabanta na tsananin faduwa ta rasa dalili kashe wutar gas din tayi ta fito da sauri zucuyarta kamar ta fasa kirjinta ta fito yadda gabanta ke fas fas kicibis sukayi da daddy ya fito da makullin motarsa a hannunsa cikin sauri ya rukota yadda yaga tanayi "ke lafiya?meyafaru ko jikin ne?"girgixa kai tayi tace "bugun zucuyata ya tsananta husnah nake tunani tamkar wani abu na samunta hankalina ya kasa kwanciya"tayi maganar fuskarta a daure daddy ya shiga damuwar yadda hajiya zainab keyi masa yana kokarin yin magana ta fizge hannunta ta dauki hijab dinta dake jikin kujera cikin sassarfa ta fito hajiya rabi ma ta fito zata sashen muneeba "ah ah Alhaji lafiya ya naganku haka?meyafaru kuma? halan cikin ne ya zube na husnah"wani kallo daddy yayi mata yace "fatan da kikeyi kenan banason iskanci da rashin mutunci rabi wace irin magana ce kikeyi kamar kinci Kashi?"mamakine ya kasheta "alhaji ni kake cewa wai ina magana kamar kashi"tsaki yayi mata ya fice cikin sauri ta bishi da kallo daddy cikin tashin hankali yake gidan innah zashi ya sanar mata da halin dayake ciki dangane da zainab....

momy na shiga jikinta ya kama rawa jin muryoyin mutane cikin gidan dakyar take d'aga kafa tana shiga su momy da malam suka shigo wuceta sukayi yadda suke cikin sassarfa tace"ah ah meyake faruwa"malam be jira me zataceba ya shiga da sallamarsa yaseer ya matukar jigata yadda yake rike da Abraham yana wujijjigasa saida momynsa ta girgiza ta kira sunan Yaseer da karfi "yaseer "rukota ummah hadiza tayi "ki kwantar da hankalinki saude ga malam yazo na tabbatar zaasamu maslaha wanan aljanin daya addabi rayuwar yarinyar nan"malam bece komiba ya sauke jakarsa ya curu turaruka masu karfi yayi addua dik ya watsa cikin dakin nan da nan katangar dakin ta zamewa Abraham kamar wuta babu yadda zaayi ya fita malam ya kalli yadda yaseer yake a jigace yace "ka sakeshi na dauresa babu inda zashi"yaseer a wahale yace "na sakesa?kana ganin yadda yake a suffar maciji zai iya cutar da husnah"gimi kawai husnah keyi ta sharbe da hawaye kasa motsin kirki tayi malam yace "ai ninace ka sakesa ko?"cikin wani irin azama yaseer ya sakesa ya fadi kasa yadda ya jigata ko motsi yaseer ya kasayi ji yakeyi tamkar ya dauki dutse,
cikin wata irin murya Abraham yace "malam kasakeni in tafi bazan sake dawowa ba karku kasheni kauna da soyayyar husnah ke dawainiya dani wanda na rayu dashi shekara da shekaru"tsumu tsumu su ummah hadiza sukayi momy tace "ikon Allah yau gamu ga aljani bamu gudu ba lallai in bala'i yayi bala'i dolema ka hakura"
gyaran murya malam yayi yace"inaso ka fadamun labarinka kaida wanan baiwar Allahr da yadda akayi ka sarku da ita kuke rayuwa shekara da shekaru harka saceta".....rikida Abraham yayi ya rage girma fuskarsa ta fito karara a jikin maciji wasu hawaye ne ke zubowa yace"wanan itace silar shakuwata da yarta"ya nuna momy dake tsaye jingine a jikin kofa dukkansu suka juya cikin mamaki,

lokacin da ta haihu bayan kwana bakwai ....takan ajiye yarinyar a daki ita kadai babu kowa ta fito tayita sabgar gabanta ni kuma cikin gidansu wajen wucewata ne akwai wata rana nazo wucewa na rinka jin kukan jinjira a daki cikin iska da guguwa na taho ta cikin gidan mahaifiyarta nata aiki a kitchen tana fadin "kiyita kukanki husnah bazan ajiye aikin da nakeyi inzo mu zaunaba inada abunyi"tausayin jinjirar ya kamani na wuce ta cikin dakin na Shiga ina shiga na sauya kamannina na koma mutum sak amma ba babba ba na dauketa na rinkayi mata wasa har tayi shiru jin motsin maman nayi saurin ajiyeta sai naji tana cewa "ah tou waya fada miki barno gabas take gashi ai kinyi shiru"tazo ta dauketa ta bata nono anata kiraye kirayen sallahr magriba ta sake akiyeta har natafi nayi nisa a cikin iska nasake jiyo kukanta nadawo na kula da ita a hakan na saba da ita sosai mahaifiyarta bata taba ajiyeta tayi mata addua a inda ta ajiyeta a nan take barinta tabbas nasha zuwa wajen husnah inga wasu jinnu masu cutarwa wadanda suke sata kuka na koresu a haka husnah ta saba dani sosai tasanni dik kukan da takeyi idan nazo ta ganni tanayin shiru,wani lokaci ma bana zuwa inda zani tare muke wuni da ita tunda koda yaushe uwarta ajiyeta takeyi tayi sabgoginta har tayi wayau sosai bata taba lura da cewae idan ta ajiyeta a daki ita kadai zatajita tana wasa tana dariya ita kadaiba tasha shigowa daukar abu ko yin wani abun ta ganta zaune ita kadai tana wasa nine nake wasa da ita har dauketa nakeyi inyi yawo da ita muyi shawagi in dawo da ita sakamakon mahaifiyarta bata damu da kulawa da itaba,

hawaye ya wanke fuskar momy dukkansu cikin tashin hankali suke da gumi ke karyo musu,wanan dan uwan nata sau dayawa shi yake daukarta yayi wasa da ita shi yake renonta idan yatafi makaranta nakanzo a suffarsa sakk inyi wasa da ita batare da mahaifiyarta ta gane cewar bashi bane akwai wata rana husnah nacin abinci ta zuzzubar a wajen tazo tayita mata fada tayita kuka sai gani nazo tana ganina tace "abokina"tana kallon wani sashe na cikin dakin,
Chapter 58 · 0% Book details