← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 68

Sashe 25

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"ah ah zainab ya naganki a burkice haka?meyake faruwa"kuka momy ta fashewa da hajiya saude tace "wanan yarinyar ce aka kawo malami dazu"ta kwashe abinda ya faru tafadawa hajiya saude mamaki da al'ajabi ya kasheta ta nemi waje ta zauna ta cire gyale tace "tabdijan akwai babbar matsala"momy hankalinta tashe ta bude dakin husnah tana Shiga ta kalli kan gadon a burkice alamar ba ita kadai bace ta bude wardrobe saiga jarkar maganin wata ajiyar zuciya ta sauke ta dauka ta fito dashi hajiya saude tace "ni yanzun abinda ya kawoni akan matsalar yaseer ne yasameni dazun Alhamdulillah yaseer ya dawo hankalinsa tinda ya tuno da husnah"momy ta zauna ta jingina da kujera tana sauke numfashi dakyar tace "tou ai ya rubuta takardar saki saidai nida idona banga takardar ba "hajiya saude ta kad'a kai tace "ya fadamun nima inaso asan inda takardar sakin take yadda zai yagata batare da kowa yasani ba"daddy ne ya shigo yace "aiko karya kukeyi naji tattaunawarku ashe gaskiya ne maganar da hajiya rabi ta fada saboda kinjini da mummunan kama kukace karya ne to tafadamun takardar sakin na hannun hafeez kuma na umarceshi da yazo da ita tare da magabatansa"gaban hajiya saude ya fadi ta ciro waya cikin sauri ta kira layin yaseer,

yana rungume da muneeba doctor ya tabbatar masa da tana dauke da ciki yana cikin farin ciki saidai dayan bangaren zuciyarsa bayaso ya rasa zukekiyar yarinyar nan gashi babban damuwansa yanda akayi idan yazo baya ganinta saidai yaga alamar tana wajen ana magana da ita, "hello momy"...yace cikin kosawa da rudewa tace"kazo kasameni a sashin momy"

"ok ok ganinan zuwa"ya gyara mata kwanciya ta ruko hannunsa cikin shagwaba zatayi magana yace "momy ce tazo take kirana"ta jinjina masa kai ya shafa gefen fuskarta ya fice yana fita muneeba ta mike ta zabura ta zauna ta leka ta window taga tafiyarsa cikin sauri jakarta ta bude ta ciro kwarya da maganin da boka ya bata akan ta fasa ta farraka tsakaninsa da husnah ta jinjina kai tace"idan kunsan wata bakusan wataba zan farraka tsakanin yaseer da husnah harabada saidai ta cigaba da rayuwa da wanan aljanin amma badai yaseer ba"cikin kishibta sa yadda boka yace ta shiga kitchen ta dauko tabarya bata ganiba tana shiga cikin store taga tabaryar ta fito mamaki ne ya kasheta ganin yadda maganin ya zube batare da antaba ba ta kalli cikin dakin bataga kowa ba waye ya kwance maganin a ledar ya zubar a kasa?tambayarr da tayiwa kanta kenan ta zauna gefen gado tana rike da tabarya kanta ya dau zafi ta dafe kanta wata dabara zatayi ta aiwatar da wanan abun?ajiyar zuciya ta sauke ummahnta zata kira suyi shawara ta jefar da tabaryar ta nufi parlor inda tasa wayarta a carji....

da baya da baya take tafiya cikin damuwa take yayi karo da ita gabansa ya fadi ya gabta tabbas itace amma meyasa dazun dayaje be ganta ba?cikin wata irin murya yace "husnah"damm gabanta ya fadi ta tsaya cakk jin muryar da aka kirata ta kasa juyowa shima ya kasa takawa ya tafi kusan seconda talatin sannan ta juyo sukai ido hudu wani Abu taji ya caki zuciyarta tayi saurin ja da baya ganin shine saidai ta kasa dauke idanuwanta daga garesa ya yafitota yace "zo nan"kasa musa masa tayi a hankaki take takowa yana kallon surar jikinta da Saida ya hadiyi wani miyau makwat ta karaso yace "ina zaki naganki a nan?me kikeyi zo muje cikin gida"ji yayi daga bayansa ance "ina ruwanka da wanda take tare dashi?nine nan take tare dani inace ka saketa?to meyafi saura?"juyawan da zaiyi yayi kicibis da hafeez wanda ba hafeez bane Abraham ne Abraham kallonsa yakeyi da mamakin yadda akayi ya iya ganin husnah a yanzun bayan abinda yasa mata a jikinta na bazai kara ganinta ba ya kalli fuskarsa take ya hango wani abu wanda ya tabbatar da narjisu ce itace ta karya masa wanan abin ya ciro takardar dayabi hafeez ya dauko ya nuna masa "gashi nan shedar saki dan haka ba sauran aure a tare da kai da ita"yaseer ya karanto ayatul kursiyyu cikin zafin nama ya tofa a fuskar hafeez wanda tuni ysseer ya gano ko waye yayi kara ya runtse idanuwansa ya saki takardar ya bace,

ajiyar zuciya yaseer yayi ya duka ya dauki takardar cike da tsananin farin ciki yasa hannu ya yayyagata husnah kuwa tsoro ne ya kamata dan tasan Abraham ne wanan ita baa hafeez take ganinsa ba tace "meye ka tofa masa a ido kagani yatafi ka kashe masa ido ko?"ya girgiza mata kai yace "ban kashe masa ido ba kinji zo muje"ya ruko hannunta suna tafiya a tare yana juyowa yana kallonta itama juyowa tayi taga ita yake kallo ta sunkuyar da kanta kasa narjisu ce ta shige jikinta suka Shiga a tare Turus daddy yayi ganinsu Tare da husnah sum shigo kallom juna momy da hajiya zainab sukayi cikin farin ciki daddy yace 'ke husnah ina kikaje daga ina kike?"ta kalli yaseer tayi murmushi tace "muna tare da yaya yaseer ne tun dazun daddy"mamaki ne ya kashe yaseer jikinsa na rawa yace "eh eh muna tare daddy naganta a wajene shine muke magana na shigo da ita"hajiya saude tace "da kyau dama abinda ya kawoni shine in sanar dakai innah daga gidanta nake akan maganar yaseer da husnah cewae ranan jumaa zaa maida aurensu"murmushi yaseer yayi cikin tsananin farin ciki ya kalli husnah ta sakar masa murmushi dik abin nan da akeyi momy na kallon kwayar idanuwan husnah tasan ba ita bace ba haka kwayar idonta take ba saidai bazatayi magana ba dan tanaso ko hajiya rabi zata mutu a maida aurensu,ta daddy cikin fushi yace "Tou yw zanyi da mutanen hafeez da nace su turo sanan nace hafeez ya tahomin da takardar sakin inga hand writing din yaseer in tabbatar da hakan saboda gaskiya bazan amince da hakan ba dan hajiya rabi ta sanarmun muneeba na dauke da ciki haka?"daddy ya tambayi yaseer ya fadada murmushi ya sunkuyar da kansa yace "haka ne daddy na kira doctor ma dazun ya dubata yanzun haka na barota tadan kwanta ne"daddy farin ciki ya cikasa hajiya saude murmushi tayi ta kauda kai tace "Allah ya inganta"husnah ta wuce su ta shige daki yaseer ya bita da kallo yana kokarin mata magana daddy yace "ka koma kaje ka kula da matarka tunda batada lafiya yanzun dai gobe ko jibi zanga hafeez zan tabbatar da hakan ingaskiya ne"yaseer ya jinjina kai daddy na fita ya zauna kujera ya dafe kai momy tace "yadai yaseer?"ya kada kai ya basu labarin yadda sukayi da husnah da aljaninta a waje momy tace "da kyau gara da kayi hakan kada ka kuskura ka rinkajin tsoronsa"yaseer yace"wata aljana dazun tazomin wai narjisu"hajiya saude ta dafe kirji tace "nashiga uku gida ya zama na aljanu kai kuma? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun "yaseer yayi murmushin karfin hali yace "ki kwantar da hankakinki"ya kwshe komi ya fada musu cikin alajabi dik sukai shiru suna mamakin wanan masifa,

******
husnah zama tayi a kasa warwas tana mamakin yaushe ta shigo dakin ta ina?waye ya kawota tambayar da tayiwa kanta kenan Abraham ya bullo ta jikin bango tana ganin idanuwansa da fatar idonsa ta tsorata yadda idanuwansa ya sale ta mike jikinta sai rawa yakeyi ta kasa magana yace "kinga abinda dan uwanki yayimun ko?yana shirin kwaceko daga wajena ko?hmmm yana shirin haka rami ya birne kansa da kansa Kenan "cikin rashin fahimta take kallonsa tausayinsa ya kamata wata tsanar yaseer taji ya dira a zuciyarta tace"yaseer ne yayi maka haka ko?ka kwantar da hankalinka nima zan rama maka saina konasa da hannuna"cikin fushi take maganar Abraham yayi murmushin jin dadi yace "kin tabbatar da hakan?"ta gyada masa kai tana ruko hannunsa suka kwanta kan gado tana kallon fuskarsa tana shafawa a hankali a hankali ya runtse idanuwansa ta shafa cikinsa tace"kana jin yunwa ko?"ya bude ido sa da sukai jajir tsabar azaba yace"idan ina tare dake banajin yunwa bana jin kishin ruwa"yana kokarin janyota ya rungumeta tace"bari in zubo mana abinci inajin yunwa"ya zauna yace "karkije nine zani in zubo idan kika fita bazaa barki ki shigo daki ke kadai ba"ta jinjina masa kai tana murmushi ya mike ya fito ya wuce su momy a parlor yana shiga kitchen ya tarar da hajiya rabi tana barbada magani a abinci harde hannuwansa yayi yana kallonta lallai wanan bil'adamar yace a ransa amma zanyi maganinta rikida yayi ya koma lafcecen kadangare jangwalagwada kansa har sheki yakeyi......

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 NE KACAL MAI BUKATA YA TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN....

07042277401
08036953516

DIK WADDA TA KARANTAMUN LITTAFI BATA BIYABA ALLAH YA ISA!!!!

*SLIMZY*✍🏻

25
Chapter 25 · 0% Book details