← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 68

Sashe 53

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
muneeba ta makalkale yaseer cikin kissa da shagwaba kukan shagwaba take zuba masa dik yadda yaso ya zare jikinsa ya tafi taki barinsa satar kallonsa tayi ta kalli lemon data hada masa da kwayar da sukasa ciki "tin dazun nake cewa gashi kasha kaki ko dan yau amarya zata tare?"ta kwanta a kirjinsa gashin kanta ya hargitse tamkar mara lafiyar gaske "ba haka bane muneeba itama wadda kike maganar batada lafiya gatacan kwance kuma nazo wajenki kinamun korafi umm?yanzun kisha magani ko na kaiki asibiti"ta faki idonsa cike da shagwaba ta fizgo kansa ta hade bakinsu waje daya ransa ya baci sosai mutumin da beda lafiya yake wanan abubuwan ga halin da husnah ke ciki ya janye ta fashe da kuka hawaye biyu biyu ya kalleta yadda ya rame ves ce jikinta cikinta ya fito haihuwa kamar kanka fita yadda cikin yayi girma ya shiga share mata hawaye "ya isa ki daina kuka ina sonki banason abinda zai sameki ko kadan kinji?"ya gyada mata kai tasa hannu ta dauko glass cup din tayi narai narai da ido "yanzun ko abu na baka ma baka karba yaushe rabon da kaci wani abu nawa bayan da aljani naketa rayuwa bansaniba"yayi ajiyar zucuya yace "shikenan bari yanzun zansha kawo banason rigima inace idan nasha dai shikenan?"ta gyada masa kai ya karba yasha murmushin mugunta tayi ya shanye tas ya dire cup din ya tsareta da ido tadan muskuta zata Tashi cikin yanayi na ciwo tace "washhh cikina"tana yarfa hannu "menene kuma cikin ne ko muje asibiti?"wani Abu yaserr yaji yana fuzgarsa kansa na juyawa biyu biyu yake gani nan da nan idanuwansa sukai jajir idonsa har rufewa yakeyi tsananin yadda yake ganin jiri da bacci ya koma yw zauna yaraf,
ta dan gyara zama cike da kulawa tace "yadai?"yace "bacci nakeji sosai gashi na baro husnah"yana hamma yayi maganar ta miko masa pillow "akwai mutane a tare da ita ina ganin kadam kwanta kafin su watse"ya jinjina kai ya karbi pillow yasa ta bayansa ya kwanta ko minti biyu beyiba bacci yeyi gaba dashi tayi murmushi ta mike tana kallomsa ta cije baki "badai rawar jiki kakeyi ba?zakaje ka angwance da matar aljani wadda kake tsananin so kana Wani rawar kafa sai kaje"ta ciro wayarta cike da farim ciki ta turawa Anty sadiya tex,

su innah a tare suka fito dasu hajiya saude motocinsu na wajen gate iska kawai ke kadawa hadari yayi bakinkirin ta dubi ummah hadiza tace "tou ga husnah nan kisa ido maganinta Dan Allah sanan wanda yake hannun mahaifiyarta kije ki karba ya koma hannunki dan alamu sun nuna zamuyi nasara inata kiram yaserr baya dauka fatana dai ba gidansu hafeez yaje ba dan ba hankali garesa ba zan kirasa daddare inja masa kunne"

"insha Allah zan kula da husnah kamar yadda zan kula da yar dana haifa ai husnah yata ce gaba da baya"sukai sallama dasu innah itada nusrah suna daga musu hannu nusrah cike take da kewar yar uwarta databi momy suka juya suka shiga cikin gidan,

husnah na daki taji kamar motsi a kitchen tadan sa kai ta leko tace "wanene?"shiru bataji kowa ba jim ana wasa da ruwa ta diro daga gadon ta shiga kitchen din inuwar mace tagani dishi dishi ta murza idonta ta bude bataga kowa ba ta waiga su ummah hadiza suka shigo"yadai husnah?me kikeyi a nan me kike bukata"

"motsi naji ummah hadiza shine na fito naga inuwar kamar mutum tsaye na karaso banga kowaba kingani"cike da tsoro take maganar idanuwanta suka cicciko da hawaye rukota ummah hadiza tayi zuwa daki "karkiji tsoro da kinji motsi kice hasbunallahu wabniimal wakeel"ta gyada mata kai tace "kidaina lekowa in kikai magana kikaji shiru,ta sunkuyar da kai tanaso ta tambayi ummah hadiza Yaser ta kasa cike take da kunya tunaninsa takeyi tun dazun tanaso ta gansa tsananin kwadayi takeji yazo ya siyo mata abu tarasa inda zatasa kanta kwantar da kanta tayi a pillow yana can tare da matarsa kenan?ta dago kai ta kwalawa nusrah kira da sauri ta shiga dakin taga husnah shabe shabe da hawaye tadan tsorata "lafiya kike kuka?"

"kiramun yayanki a abunda kike kiransa"dariya taba nusrah waya takeso tace tsananin shagwaba da yayi mata yawa nusrah na dialing wayar Yaser akace mata a kasge,

"nusrah ki zauna da husnah bari nashiga gidan can wajen zainab na karbo magani naga dare ya somayi magriba kar ruwan nan ya kece ko?"tace "toh"ta fice,

Cikim farin ciki sadiya ke labartawa hajiya rabi plan dinsu nasawa Yaser kwaya a abunsha hajiya rabi ta gyara tsayuwa tace "kai nayi matukar farim ciki kinga dik rawar duwawum nan da sukeyi nasan cewar yaseer a dakin muneeba zai kwana kinga nan zasu tabbatar bason renom aljanu yakeyi ba"suka sheke da dariya "wai Anty dazun ina kikaje?"

'umhmm gidan boka naje yanzun zam aiwatar da abinda ya bani ya tabbatarmum in zuba abin nan a cikin abincin hajiya zainab dana badamasi da sumci shikenan"suka sheke da dariya sadiya tayi kasa da murya tana dariya kasa kasa tace "shiyasa kike makale a kitchen?"ta jinjina kai ummah hadiza ta shigo jin taku da sallama daga gate sadiya ta fice tayi sashen hajiya rabi ita kuwa saurarawa tayi taji kamar ba nan bane ta wawwaiga babu kowa ta fito da maganin har ummah hadiza ta gifta ta dawo ta tsaya tsaye tana kallom hajiya rabi tana zuba magani,

Abraham ne ya sauya kamanninsa sak ya koma hafeez ya shigo gidan cike da kudirin karbar maganin da hafeez ya kawo sallama yake dokawa shiru ya dan tsaya yadda hafeez keyi daga window momy ta hango hafeez tayi saurin daukar hijab ta nufi hanyar fitowa.....

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BANYAFEBA*

07042277401
08036953516

*SLIMZY*✍🏻

43
tsaye momy tayi tana kallon ummah hadiza da ta tsurawa hajiya rabi ido ganin inuwar mutum yasa ummah hadiza juyowa nuni tayi mata da tai shiru "shhh kiyi shiru karkice komi"tayi shiru ta had'iyi wani miyaun bakin ciki yau ta tabbatar da hajiya rabi asiri tayiwa daddy ummah hadiza ta tako a hankali ta karasa ta ruko hannun momy su shiga daki Momy ta yafito Abraham dake tsaye yana kallon komi tace "taho hafeez na ga shigowarka ai shiyasa ma nataho dakaina nace bari nazo barka da zuwa"a hankali ya tako ya shigo ya tsugunna har kasa "momy barka da yamma"ya sunkuyar da kai ummah hadiza ta tsaresa da ido haka kawai jikinta be bata ba yuwwww taji juwa na neman kadata ta jingina da jikin kujera,

"da magribar nan ga hadari hafeez ka kamo hanya ka taho?"ya jinjina kai yana wasa da makullin hannunsa yacev"momy dama akan maganin nan ne dana kawo nace bari inzo in karba ashe bana husnah nakawo ba na kanwata ne dama biyu na karbo maganin"

"toohhh hafeez gashi anbawa husnah hartasha kardai akwai matsala"ya jinjina kai ya dago kai yaja gauron numfashi ya sauke yace"babu momy kawo sauran maganin zan kawo natan?"tsare Abraham ummah hadiza dayi da ido tana karanto adduoi jin tsigar jikinta na tashi ta tabbatar akwai matsala tace "kai daga idonka ka kalleni"ummah hadiza tace cike da fada Abraham ya hadiyi wani miyau a ransa yace kardai matar nan ta gane niba mutum bane,,momyn husnah ta mike a sanyaye ta nufi bedroom dinta ummah hadiza ta tsaidata tace "zainab Ashe har yanzun da sauranki bakisan sharrin aljanuba ko?ai inda maganin nan bana husnah bane to take husnah bazata samu lafiya ba maana yadda ta daina ganin wanan shaidanin aljanin wanan da kike ganinsa ba hafeez bane aljanine"momy ta tsorata tana kallon ummah hadiza ta jinjina mata kai tace "tabbas Aljani ne?"momy kasa kallon inda Abraham ke zaune tayi ummah hadiza ta mike cikin azama tana kokarin karanto adduoi ganin haka bat Abraham ya bace ummah hadiza ta girgiza kai tace "shedani"

"tou waigo ki kalla"dakyar momy tayi ta maxa ta waigo ta kalli sashen daya zauna wayam bataga kowaba a wajen wata ajiyar zuciya ta sauke saidai a tsorace take matuka ta kasa ko motsi ummah hadiza ta mike jin ruwa na kokarin sauka tace "ina kika ajiye maganin?"momy tayi mata nuni har yanzun kafafuwanta rawa sukeyi data kalli wajen sai taga kamar Abraham na zaune ta wuceta ta dauko maganin tace "wanan yakin daya rage kece zakiyiwa kanki Kuma tunda kingani da idonki ana zuba muku magani a abinci idan akwai wanda baasa maganinba ki sauya ki ajiyewa mijinki gobe zansa akawomin wani magani da zaki amfani dashi akan alhaji badamasi nabarki lafiya "ummah hadiza ta fuce hawayene suka wanke fuskar momy lallai tayi bacci bayan yunkurin saka mata laya a baki yanzun gashi Ido da Ido tana gani ana barbade a abinci,ajiyar zuciya ta sauke ta kallu kular data zuba abinci a ciki iri daya ne abincin da wanda hajiya rabi ta zubawa magani ta dauka cikin sand'a ta fice ta nufi kitchen din harta zuba masa a kula ta juye abincin a leda ta ajiye gefe ta zuba nata ta gyara Kular ta fice....horn na motar daddy taji cikin sauri ta koma dakinta har yanzun cikin furgici take da Aljanin dayazo dazun ta shiga toilet ta dauro alwala anata kiraye kirayen sallahr magriba....

******
tagumi husnah tayi akan kujera two seater nusrah na zaune akan dadduma ta idar da sallah,ummah hadiza ta shigo da sallamarta "ah ah husnah ya naganki zaune kinyi tagumi?"tayi saurin kurkiro murmushi tace "bakomi ummah"
Chapter 53 · 0% Book details