← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 68

Sashe 61

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

48
yaseer ne ya saci kallon husnah da tayi kur'i tana kallon jinjirin dake hannunta wanda tuni ta fada duniyar tunani cike take da takaicin muneeba da tasan dik abinda tayi yanzun tayine dan ta shakar da ita idan hakane kuwa tabbas ta taro march,ji tayi a jikinta ana kallonta ta d'ago kai ta zuba masa kyawawan idanuwanta wani kallo tayi masa mai tada jijiyoyin jiki saida yaserr yaji wani yarrr dikda yasan mai kallon ke nufi hajiya saude taja gauron numfashi ta katse shirun da dakin yayi "niko ina tsananin mamakin yadda akayi badamasi ya auri rabi baya cikin hayyacinsa"ummah hadiza ta gyara zama "ashe abinda yake ranki shine a raina tun fitarsa nake sakawa ina warwarewa gashi innah na neman hanasa rabuwa da ita"innah tayi murmushin manya tace "bani na aikesa aurenta ba dan Haka shine da kansa zaisan yadda zaiyi da ita yasan nayi da ita in yana sonta su cigaba da zama"husnah ta mike tana yatsina fuska "yadai husnah?"ta girgiza kai "inaso in d'an kwanta ne kaina nadan ciwo inajin zazzabi"ummah hadiza ta yunkura "umm bari intashi inje inji da tawa yar"ta ruko husnah "munyi gida sai mundawo"dariya hajiya saude tayi ta girgiza kai suka fice,
gyara zama hajiya saude tayi ganin yaseer na waigensu husnah tasan binsu yakesonyi kafin tayi magana ya ajiye jinjirin "amm nima"

"kaima mene ina zaka?ai zama zakayi akwai maganar da nakeso mu tattauna"ya gyara zama hade da natsuwa dikda hankakinsa rabi yana wajen husnah da suka fita momy ta cigaba da magana "ai shiryawa zakayi ka dauki husnah kuje gidansu hafeez kayi masa godiya dan wallahi harda maganin da hafeez ya kawo ya taka babbar rawa wajen warkewar matarka kuma na tabbatar ba wani abubane ya hadaku babu wani kwakkwaran dalili kawai dalilin be wuce akan husnah ba kar kabari mace ta shiga tsakaninka da Amininka kaji nafada maka"shiru yaseer yayi jikinsa yayi sanyi hafeez amininsa ne tun yana primary school tare sukai makaranta har university sukasamu aiki yanzun gashi sun samu matsala kuma hakan be hana hafeez zuwa gidan ba,sallamar wadda sukajine yasa yaseer jikinsa yin wani shock ya dago da sauri sukai Ido hudu da hafeez da ummahnsa da meenahl ya sunkuyar da kai hajiya saude cike da faraa tace "d'an halak kaki ambato yanzun maganarka nakeyi sai gaka kunzo sannunku da zuwa sannu da zuwa hajiya"ummahn hafeez ta dire jakarta yaseer ya sosa keya yace "sannu da zuwa ummah,ina yini ummah"wani kallo ummah tayi masa tace"haba yaseer ni baxan amsa gaisuwarka ba ai tunda niba uwarka bace ai kabani mamaki koda kuke fadanku kaida abokinka ai be kamata ya shafeniba"yaseer ya sunkuyar da kai cike da kunya ummah tace "toni gani nazo hajiya hafsat ce ta sanar dani haihuwar hajiyq zainab daxun mun hadu a saloon tace ai ansamu yan biyu nace bazaa kwanaba komi yamma sai nazo naga wad'anan jarirai nasa musu albarka"innah ta dauko daya ta mika mata tana fadin "wadanan mazajen masu kama daya bansan ya zanyi dasuba in rinka ganesu"yaseer dakyar ya dago kai suka hada ido da hajiya saude ta kashe masa ido alamar yaja hafeez su fita shine ya mike ya tabo hafeez ,da sauri hafeez ya kallesa yace "man muje mana"shiru hafeez yayi ya mike yabi bayan yaseer ummah ta bisu da murnushi tace "j'airan yara"nan ummah dasu momy suka baje suna zuba hira cike da nishadi minal tuni ta mike ta fice wajensu nusrah a sashen husnah...

yaseer dakyar yasamu ya shawo kan hafeez yayi fushi sosai suna tsaye jingine jikin mota ana kiran magriba yaseer yace"mu shiga ciki mana sashen husnah kaci abinci muyi sallah sai mutafi maida ummah tare"hafeez ya jinjina kai yace "tou muje"tsayuwar motarsu hajiya rabi ce ta dakatar dasu suka tsaya dakyar hajiya rabi da sadiya suka fito da muneeba daga cikin mota wadda idanuwanta suke a rufe taki bude idonta sai wasu maganganu takeyi tana shafa cikin kallo daya zakayiwa hajiya rabi ka hango tashin hankali karara a fuskarta nan da nan tayi bakin kirin ta fita hayyacinta yaseer jikinsa na rawa ya karaso ya taimaka musu aka fito da muneeba daga cikin motar yace "ummah lafiya meke faruwa naganku cikin wanan yanayin"hajiya rabi ta kalli muneeba ta hadiyi wani miyau mai daci cike da damuwa tace "yaseer akwai matsala asibiti biyu mukaje dangane da cikin nan na muneeba baa ganinsa kwata kwata shine kaganta cikin wanan halin gashi dik ya burkice sai kiran sunan husnah takeyi wai husnah ce da aljanunta suka dauke mata yaro"wani kallo yaseer yayiwa hajiya rabi take tayi gumm da bakinta Tasha jinin jikinta dama ba haka ta fada ba yace"badai husnah ba kam saidai in wata matsalar ce tafaru idan hakane zanyi magana da malam da yayiwa husnah magani yazo akan matsalar muneeba "kallon juna hajiya rabi da sadiya sukayi gaban hajiya rabi ya fadi karfa malam yazo ya fadi cewar cikin jikin muneeba bana yaseer bane,cak yaseer ya dauki muneeba dikda nauyin ta hawaye kawai ke gangarowa daga idanuwanta dake rufe ciki bakinta na motsi tana fadin "ni wallahi sai nasamu ciki irin na husnah cikin yaseer shi nakeso banason wanan cikin ummah ki taimakeni ina tsananin son Yaseer kinga ita anga cikinta"yaseer wani damm gabansa ya Fadi mamakin kalaman muneeba yakeyi yana rike da ita suna tafiya tare dakyar hajiyq rabi ke daga kafarta kamar an dora mata Kaya haka suka shiga tare dakin muneeba ya kwantar da ita ya tsugunna a gabanta cikin tausayawa ya kira sunanta cikin wata irin siga mai cike da tausayawa da kulawa "muneeba ki kwantar da hankalinki zaaga cikinki kema ba likita ya fada miki cewar wasu na haihuwar dansu haka ba?inasonki ina son abinda kw cikinki kidaina damuwa"ta bude idanuwanta a hankali saida yaseer ya razana ganin yadda kwayar idonta ta koma kamar gudan jini saboda ja tace"bazaa gansa ba yaya yaseer nafada maka bazaa gansa ba yaseer nidai inason wani cikin banason wanan?"yadda take maganar a wahale yasa yaseer jikinsa mutuwa ya shafa fuskarta yace"shima kina sonsa kuma zaki haifesa ko? inace nine mijinki kuma uban d'an?"ya kafeta da ido itama shi take kallo wasu zafafan hawaye madu zafi ke zubo mata kafarta ya kalla ruwa ke biyo kafarta yayi saurin kauda kansa ganin yadda take hawaye dakyar ya fito daga dakin,hafeez ya ruko hannunsa jiki a sanyaye suka fita,

hajiyq rabi gyara tsayuwa tayi tace"muneeba na rokeki wadanan surutan da kikeyi sune zasusaka asirinmu ya tonu nidake asan abinda muka aikata kiyi shiru ki kwantar da hankalinki gobe zan fita Nemo maganin da zako rabu da cikin ko ki haifesa"wani kallo muneeba tayiwa uwar saida taji hantar cikinta ya kada dakyar ta yunkura ta tashi cike da tsana take kallon hajiyq rabi tace"ummah idan har ban rabi da cikin nan ba to kisani zan fadawa yaseer ba cikinsa bane cikin boka ne!!!!"cike da masifa kamar zararriya take kallonsu yadda take wurga kwayar idonta da sukai ja ba karamin tsorata tayi ba "bana son ganin kowa ku fita kawai ummah ina cikin tashin hankali da damuwa nayi nadamar abinda na aikata ummah saida nafada miki bazanyi zina da boka ba kikace inyi ga abinda kikajawo nan gashi yanzun yq mutu ya barni da cikinsa a jikina bayan ba cikin mijina bane"da sauri hajiya rabi ta rufewa muneeba baki wani karfi ne yazo mata ta fizge ta nuna musu hanyar fita batason ko ganinsu, haka suka fice cikin tashin hankaki ko takalmi hajiya rabi ta gagara sawa yadda muneeba ke sambati na bata tsoro karfa taje ta fadi abinda zai fallasa sirrinsu dole Zata kira aminiyarta dikda ba wani shiri sukeyiba ta taimaketa inda malamin da zai cirewa muneeba cikin nan a haka suka shiga cikin gida ummahn hafeez da minal sun fito hajiyq saude ta rakosu da innah "ah ah kundawo sannunku da zuwa"cewar hajiya saude ko saurarenta hajiya rabi batayiba batamasan ana mata sannuba bin ta sukai da kallo yadda sukaga kafarta ko takalmi babu hajiya saude ta kalli innah tace "toohhh Allah ya kyauta kinga matar nan kamar mahaukaciya"suka fito,

cikin damuwa hafeez ke kwabtarwa da yaserr hankalin abinda ke damun muneeba "Insha Allah komi zai warware babu abinda yasameta lafiyar kwakwalwarta kalau"a haka su ummah suka karasa "lafiya naganku jingun jingun kamar kuna cikin damuwa?"ummahn hafeez ke tambayarsu tana binsu da kallo hafeez ya nisa yace "akwai matsala ne dangane da muneeba"nan ya kwashe ya fada musu hajiya saude tace "haba shiyasa naganta kamar kwancen hauka kamar sabon kamu dubi yadda take a furgice ko takalmi babu aidata fada da ansan abinda zaayi Bari nashiga na sanarwa da alhaji kawai a nemi mafita in aljanune ma asani"nan sukai sallama dasu hafeez suka shiga mota hafeez yacewa yaseer"sai munyi waya"ya ja motar suka tafi,

a sanyaye yaseer ya nufi sashen husnah yabar su innah tsaye da sallamarsa ya shiga mamaki ne ya kashesa ya kasa magana jin yadda husnah ke zuba kamshi taci ado da kwalliya wata farar riga tasaka da dogon wando yadan wuce gwiwarta an gyara mata gashi "ah ah matar datacemun batada lafiya kenan?"cuno baki tayi gaba tayi murmushi a ranta tabbas ummah hadiza tasan kan lagon maza wanan karatun da tayi mata gashi yadda yaseer ya rude kadai tasan abinda sukeso kenan ta mike tsaye tadan rusuna "sannu da zuwa"kasa amsawa yayi cikin mamaki yake tini ya nemi damuwar muneeba ya rasa tsaresa tayi da ido yadda yake bin ta da kallo ta juya cike da kwarkwasa tace "tunda bazaka amsa ba ni kaga tafiyata"cikin shagwaba ta juya baya ya kalli yadda mazaunanta suka fashe cikin wandon wani miyau ya hadiye nan da nan ya rungumota ta baya yasa kansa seting wuyanta yayi kissing din gefen wuyanta tana zillewa yana rungumota suna dariya suka shige daki,

gefen gado ta zauna tana kallonsa shima ita yake kallo cikin mamaki yace"kinga yadda kika canja hussy?"tayi murmushi "Allah ko?meye ya canjani?"
Chapter 61 · 0% Book details