← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 68

Sashe 24

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

karatu sosai malam yake zubawa a kan husnah ko gezau saima toshe toshen hanci da takeyi cike da haushi ko meye wanan oho tana cikin nishadi da mijinta anzo an wani kawo malami yana mata surkulle minti minti malam ke kiran sunan husnah sai yaji ta amsa ya dago kai yacev"tabbad akwai aljani a tare da ita amma baa jikinta yake ba shafarta yakeyi kuma shafar aljanu wuya gareshi gara ace a cikin jikinta yake zama"sosai hafeez ya shiga cikin tashin hankali yace"yanzun yq zaayi?"malam yace"akwai yadda zaayi"hafeez ya gyara zama momy dik ta furgita shigowarsu hajiya rabi yasa momy ta daga ido ta kallesu tayi tsaki tace "aikin banza wani irin iskanci ne anzo ana mana surkulle a gida bari daddy ya dawo"bata tanka mata ba malam ya cigaba da bayani yacev"wanan maganin da kika Shiga dashi daki shi zai zama kina bata safe da yamma a kofi sai wadanan turarrukan zaki rinka shafa Mata idan har kikayi nasarar shafa mata bazai taba iya rabar inda take ba"momy cike da gamsuwa ta jinjina kai malam ya tafi husnah ta mike zata shiga daki momy ta kirata ta tsaya bata waigo ba....

hafeez ya zaro takerdar sakin husnah daga aljihunsa yacev"momy dama wanan...."yaseeer ne ya shigo yana zuba kamshin turare yana waige waigen inda zaiga husnah yace "momy ina matata husnah?"damm gaban momy ya fadi ta kalli yaseer dakyau husnah kallonsa takeyi tana tsaye amma be ganta ba momy ta kalli husnah wadda ke kallonsa galala ya wuce ya nufi daki ya bude kofar yaji an hankadoshi da karfi yayi taga taga baya zai fadi ya kalli cikin dakin babu kowa yace "momy dama husnah ce yarinyar da hafeez abokina ya kawo gidan nan?"gaba Daya momy ta kasa amsa tambayarsa mamakin yadda gashi ga husnah baya ganinta takeyi tace 'ga husnah nan a gabanka?"ya wawwaiga bega kowa ba husnah ta tabe baki ta wucesa ta shige ta bugo kofa ta danne kofar da bayanta tana maida numfashi ina Abraham?tace a zucuyarta bullowa yayi kawai ta ganshi gabanta yace"gani "mamaki ya kasheta tace"ya akayi kaji abinda nace a zucuyata?"yayi murmushi yace "a zahiri zuciyarki na tare dake amma a bad'ini tana cikin kirjina"ta wawwaiga tanaso tayi magana,

kishi ne ya lullube hafeez ya mike ya zura hannu a aljihu yace "momy zan tafi yau daddyna zai dawo na gabatar da maganar auren husnah wajen ummahnta zata sanar dashi zuwa gobe ko jibi zaazo ayimun tambaya"wani miyau ta hadiye tausayin hafeez ya kamata tabbas hafeez nason husnah amma ya zaayi da auren yaseer dake kanta?takardar ya mance ya zura a aljihu yayiwa yaseer wani kallo ya fice muneeba ce ta kira wayar yaseer da sauri ya dauka yace "yadai munee?"yaji tana kakarin amai ya rikice yace "momy bari inje indawo muneeba batada lafiya naji amai takeyi ma"ya fice cikin sauri narjisu ce ta fito cikin suffar mutum kyakkyawar budurwa ta tsaya a jikin kofar shiga sashen su yaseer tana ganinsa tayi masa sallama tana murmushi kallon rashin sani yakeyi mata da kallon tuhuma.....
*Afwan my people gobe akwai bikin sister na adan dagamun kafa zuwa jibi insha Allah kunsan hidimar biki nagode sosai da kauna*

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN KIKA KARANTAMUN BAKI BIYANIBA BANYAFEBA*

GA MAI BUKATAR SHIGA WANAN TAFIYAR YA TUNTUBI WADANAN NUMBERS DIN...

07042277401
08036953516

*SLIMZY*✍🏻

24

kallon rashin sani yaseer yakeyiwa narjisu tayi murmushi tace "nasan bakasan koni wacece ba ko?"ya jinjina mata kai cike da kosawa yace "bansaniba saikin fada ke wacece daga ina kuma kike?"shiru tayi daga bisani ido cikin ido tace masa "ni aljana ce,"damm gaban yaseer ya yanke ya fadi bakinsa ya shiga karkarwa yana kokarin fara addua ta daga masa hannu cike da isa narjisu tacev"dakata karkayi addua ka cutar dani ka kona ni don niba cutar dakai nazoyi ba"dakyar ya hadiye wani miyau yace "Mai kikazoyi?dama aljani yana kulla alaka da dan adam ne bata cutarwa ba"muneeba ta sake kiransa ya kalli wayar a gaggauce yana takawa zai wuceta tace "nazo in taimakeka ne akan husnah na tabbatar kaje wajenta baka ganinta ko?"da sauri ya juyo yana kallonta yace "ya akayi kikasani"murmushi Narjisu tayi tace"ba saika tambayeni ba saboda ina bibiyar rayuwar husnah sakamakon mijina dake aurenta shi yasa mata abinda ko kazo bazaka ganta ba ya zuba mata abun a jikinta sakamakon tsananin kishi da yakeyi dakai da waccen abokin naka"gumi ne ya karyowa yaseer bata jira mai zaide ba ta daga hannunta sama ta bude baki wani abu na fitowa daga cikin bakinta fari kalll hannunta da wani ruwa mai haske mamaki ya kashesa yadda ruwan baya zuba daga hannuta kafin yayi magana ta watsa masa yaji wani yarr yayi baya ya runtse idanuwansa take ta bace ya wawwaiga bai ganta ba cike da tsoro yake kallon gefe da gefensa bai gantaba dakyar ya taka kafarsa yana tafiya yana waige bai ganta ba gashi ta tafi bai ganta ba bata bari taji ta bakinsa ba tura kofar dakin yayi da sauri ya shiga ganinta warwas a kasa tana juyi tayi amai ko ina ya karaso da sauri ya tallabota jikinta yayi mugun zafi yace "yadai muneeba lafiya?maike damunki umm?"cikin rudewa yake tambayarta ya ciccibeta cak ya nufi toilet da ita dikda baya cikin hayyacinsa a wahala tace "naci abinci ne nayi amai ina ganin jiri kaina nayi mun ciwo"cike da shagwaba take maganar ya zare doguwar rigar dake jikinta ya cillar gefe ya tara ruwa yayi mata wanka tas ya fito da ita ya nadeta a towel ya nufi parlor ya gyara wajen sanan ya dawo ya tallabeta yace "yanzun muje asibiti ne?"ta yatsina fuska ta girgiza kai ya shafa gefen fuskarta yace "meyasa bazamuje ba a duba aga maike damunki?'cikin shagwaba tace "nafada maka ciki ne?"ta tura kanta cikin jikinsa cike da kunya yayi murmushi ya shafa kanta ta kara shigewa jikinsa yace"to zan Kira likita azo gida a dubaki"ta gyada masa kai yana kokarin tashi ya fita tace"ina zakaje?"ta tsaresa da ido ya sosa keyarsa kamar bazai fada Mata ba yace "zani sashen momy ne akwai maganar da muke tattaunawa kinga husnah gata nan ta dawo"da sauri ta mike ta zauna kishi ya taso mata tana masa wani kallo kawai saita fashe da kuka nan da nan hankakinsa ya tashi yace"ya isa kukan me kikeyi?meyasa kike kuka kidaina kuka karki cutarmun da abinda ke cikinki kinji kiyi hakuri"a rude yake maganar ganin yadda ya rude yasa ta kara rurewa da kuka.....

******
sauke numfashi takeyi ta danne kofa ya tsura mata ido waige waige takeyi ta fada jikinsa ya rungumeta sosai yace "kina sona?"ta dago kai da sauri ta kallesa tace "ina sonka mana Abraham ina tsananin kaunarka meyasa akeson rabamu nidakai?"ya shafa kanta ya kwantar da kai a kamta cikin murya mai kama da rad'a yace "saboda ni aljani ne shiyasa akeson rabamu kuma ni ina sonki kema kina sona"sosai ya bata tausayi "tou meyasa bazaka koma kamar mu mutane ba kaga shikenan sai mu cigaba da zaman auren mu ko?"ta dago kai tadan janye jiki daga jikinsa ya jinjina mata kai yace "babu yadda zaayi in koma bil'adama nima da inada halin hakan husnah da nakoma kodan in cigaba da rayuwa dake cikin kwanciyar hankali"....
bankado kofar akayi "husnaj husnah fito nan kin makale a daki tare da aljanin ko?"cewar momy fuskarta a daure husnah ta kalli Abraham ta wayance tace "baya nan fa momy niba kowa a tare dani"tanayi tana kallon sashin da Abraham yake momy tace "tou wanan waige waigen na meye kikeyi ko sunzo ne?fitowa zaki parlor mu zauna kinajina ko dan malam yace a daina barinki kina zama ke kadai a daki"ta nunawa husnah kofa "wuce mutafi"husnah ta saci kallon Abraham ya jinjina mata kai alamar ta fita momy tayi gaba husnah na biye da ita Abraham ya matso ya rike hannunta a tare suka fito parlorn ta nemi karshen kujera ta zauna momy ma ta zauna daga gefe kamar ance ta waiga ta juya taga husnah na murmushi tana gintse fuska tana gabtsarewa Abraham ne ke mata cakulkuli hannunsa daya ya damki nononta yana matsawa ta saki yar kara momy ta zabura tace"ke lafiyarki kuwa meye hakan?"husnah ta daure ya zumburo baki tana gunguni tana fadin 'ni babu mai rabani da mijina"ya matse yatsanta tayi yar kara tace "ahhhnnnn kabari nidai"momy ce ta shiga waige waige tana neman turaren da malam ya bata sama ko kasa ta nemeshi ta rasa ta mike ta nufi dakinta tana dubawa tuni Abraham ya dauka ya bude hannuwansa yana nunawa husnah ta zaro ido murya kasa kasa tace "kadauka ashe"yayi murmushi ta nemi abun ta rasa momy saude ce ta shigo da yan matanta guda biyu Abraham na ganinta ransa ya baci husnah ta kallesa da ido gudun kar hajiya saude ta fahimci ba ita kadai bace yace "banason wanan matar idan naganta raina baci yakeyi ji nakeyi kamat inshaketa"nan da nan jiniyoyin kansa suka fito husnah ta bata rai momy cikin faraa tace "ah ah husnah kece zaune a nan ke kadai ya naji shiru ina momyn naki take'a dakile husnah tace "tana ciki"a fusace momy ta fito tana surutai tana fad'in "shikenan sun sace sun sace turaren shima maganin dake cikin dakin can bari in dauko kafim shima su dauke"
Chapter 24 · 0% Book details