← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 67

Sashe 8

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri AJ ya ce "An gama ranki shidad'e, yanda kikeso haka za'a yi. Nann ya kashe wayar dai-dai lokacin inah ta fito daga bayan gida. Ta ce "Yanzu Abdul jabaru inayin magana kafini baki, kacemin kai baka sata, yanzu a ina kasamu kud'ad'an nann da kake cewa zaka siyamana waya?

AJ ya ce "Yanzu Innha fisabillhi sokike mu ƙare a wannan talaucin? Abun arzuƙi ya samemu amma kicewai... to Innah in baki son wayar ai sai kibarta, yanzu ki dubeki daga jiya zuwa yau dan Allah baki ji kinfi samun kuzariba?kinci kaza kin sha yourgot ga kaya mekyu, amma bazaki samin albarkaba.

NANA ma ta amsa da cewa, mudai innah muna son wayar please yaya kabani taka kaji?. Haka innah tayi shiru badan batada da abun cewaba sai dan anfita baki.

Washe gari, kamar yanda A.J ya ce, ya siyowa Nana layi, yabata wayarsa, itama Innah yasiyo Mata ƙarama da layinta, yayinda shima yaje shagon siyarda waya ya siyo wayarsa mai kyu. Ƙarfe goma na safe dai-dai aka tafka saɓani tsakanin Salis da A.J. yayinda Salis yake kan hanyarsa ta zuwa neman soyayyar Nana. Shikuma AJ yaje domin jin wani aiki Hajiya zata bashi.

*A.J. SALIS POV*

Kallon Hajiya babba yakeyi cikin tsanani mamaki, haɗi da kallon jakar kuɗin gaban sa. AJ ya ce "Hajiya ban fahimci abun da kikenufiba?. Cikin shawƙin abunda ta keji ta ce "Yes kamar yadda kaji na sanar dakai, aure nakeso muyi da kai amma cikin sirri, karkowa yaji, in har ka amin ta, kasanar dani duk abun da kakeso tin daga kan miliyoyin ɗari da kuma gida da kuma mota, zan mallaka maka.

Sanye take da dokuwar riga sai gyale fari. Kallon sa takeyi ganinn shima ya zuba mata ido. Cikin jin kunya ta ce "ina u'ni? Salis kuwa ganinn irin shigar da tayine yabashi damar kafeta da ido, yana jin sonta har zuciyarsa. Bai ankaraba yaji tana cewa "Yaya ɗin AJ bayanann kunyi saɓani yanzu ya fita, amma in yadawo zance masa wannan da yazo jiya yazo neman sa. Tana kaiwa nann ta juya zata koma ciki.

Cikin sauri salis ya ce "Ji'mana, bagurin sa nazoba gurin ki nazo. Ta ɓangare ɗaya kuma yana tinanin meyasa bata riƙe sunann saba. Cikin mamaki Nana ta nuna kanta da cewa ni?.

Duk da uban fankoki da asi da suke aiki a palorn hakan bai hana AJ jiƙewa da zufaba. Cikin rikicewar ya ce "Hajiya aure fa kikace? Kuma dani!?... gaskiya bazan iya ba, yazanyi da salis wanda agirme. Ya girmeni kuma abokina wanda yake temakamin a komai, amma na auri uwarsa!!? Ina Hajiya dan Allah kibar wannan zancen Please. Ya ƙarasa yana kallon jakar kuɗin da yasan in har ya mallakesu to tabbas shida talauci har abada.

Salis ya ce "Yes gurinki nazo. Nana ta juya tana neman wacce salis ɗin ke magana da ita, domin kuwa tanada tabbacin bada ita yakeba, domin kuwa babu haɗin kwanda da gula. Kayanda kejin sama tasan ba na ƙananan yara bane, bare motar da yake jingine a jikin ta. Cikin mamaki ganinn yanda take ta dube-dube ne salis ya ce "Keɗayace a gurinan, kuma dake nake...kamata yayi a ce kiyi maraba da zuwana domin da alkairi nazo....📝

_
*PAGE* 👉7️⃣

............... Kallon jakar kuɗin yakeyi yana aiyana abun da zai faru in ya mallake su. Cikin ransa yace "Anya kuwa in nabar wannan garaɓasar ban cutuba!?. Zuwa wani lokaci ya ɗago ya kalli Hajiya Babba sannan ya ce "Yanzu dan Allah hajiya meyasa kikeso ki aureni?. Hajiya Babba tayi dariya sannan ta ce "Banice zan aurekaba kaine zaka aureni...Kuma ba wai in ka aureni shikenan bazaka sakeyin wani auran bane, a'a zaka auri wacce kakeso, amma kafin nan zan baka labarin abin da yasa zanyi aure.

Cikin gamsuwa da abunda ya ce Nana ta ce "Ok tom barka da zuwa. Salis ya gyara tsayuwar sa sannamallak "Barkade...da fatan dai ba dole namikiba? Nana ta ce "kusan dai hakan...yanzu dai kafaɗi abunda ya kawoka tunda kace gurina kazo, kafin innah ta fito nemana?. Cikin dariya Salis ya ce "Afito nemanki fa kikace kamar wata ƙaramar yarinya?.

"Eh dama ai ƙaramar yarinyar ce baka gani bane?. "Dan Allah karki ƙara kiran kanki da ƙaramar yarinya, kallekifa kin isa aure amma kice wai yarin ya ceke?. "Cikin jin kunya Nana ta rufe fuskarta haɗi da cewa... Please dan Allah zan tafi gida.? Salis yace "Muga wayar ki?. Ya mata wannan tambayar ne ganin wayar a hannuta. Ita kuwa Nana tinda a ka bata wannan wayar haryanzu bata barta ta hutaba.

Hajiya Babba ta ce "Nakasance tin ina yarinya Allah ya ɗoramin wani irin ciwo, wanda tin kafin na kai mizanin aure a kamin. Na kasance daga cikin mata harijai wato masu mutuƙar sha'awa. Hakanne yasa iyayena sukayi saurin aurarr dani, aurena uku (3) zan faɗa maka abun da yake rabani da mazajena. Har Allah yayi na auri mahaifin su Laɗifa, shima ɗin dan Allah yayishi jarimin gaske ne, shiyasa zamanmu yakai har lokacin da Allah ya amshi abinda.

Lokaci ɗaya AJ ya zaro ido waje jin abunda Hajiya ke faɗi. Ya ce "Hajiya menene harija? Hajiya tayi murmushi tana jin wani matsananci sha'awar yaron na ƙara taso mata a duk lokacin da yayi magana.

Zaro ido waje Nana tayi ta ce "Mezakayi da wayana? Salis ya ce "kinga rufe bakin kar..."ai kafin ya ƙarasa ta rufe fuskarta tsabar kunya. Haka ta ciro wayar ta bashi, domin kuwa babu fuskar masa musu, domin kuwa ya mata kwarjini sosai. Bayan ta bashi sannan ta zuba masa ido domin ganin mai zaiyi da ita. Hoton ta da AJ ne a gaban wayar. ganinn yanda sukayi kyau ne yasa ya ce "Kunyi kyau sosai kamar ba keba ya ci gaba da cewa "Badan AJ ya girmekiba da sai ace ko ɗin ƴan biyu ne. Dariya tayi tana jin daɗin yanda ya yabesu.

Number sa ya saka mata sannan ya ƙwada kira ko tanada kuɗi, aikuwa sai gashi ta shiga, yayi seveng number sa da (my sweetheart) sannan ya nuna mata. Haɗi da cewa wannan number nane zamu dinga gaisawa.

Hajiya Babba ta ce "Karka damu duk zan sanar dakai. Taci gaba da bashi labari. Yanzu haka shekarar Alhaji huÉ—u da rasuwa, kuma tun baya ya rasu yarana suka hanani yin wani auran, kuma sunsan da cewar addinmu bai hanaba amma duk wanda yazo sai sun korheshi. Jiyama sun koriwani, shine yasa nayi amfani da kai domin cimma wani burina, inaso ka yarda babu abun da zai faru, domin kuwa ADDINIMU bai haramta ba.

Zamuyi aure na shekara ɗaya, Sannan zan baka miliyoyin hamsin da gida harda mota... sannan babu abun da zai shiga tsakanina da kai har muyi wannan shekara ɗaya ɗin, abin da nakeso shine Karka sanarwa da kowa, harda kakarku domin kuwa nasamo labarin ka gaba ɗaya, iyayenku sun rasu, daga kai sai ƙanwarka sai kakarku, to banaso susan da labarin, da so samunema wata ƙasar samu tafi mufara yin wats ɗaya kafin mudawo, kokuma kawai zan cewa su Salis na ɗaukeka a matsayin yaron gidana, zaka dinga zuwar min aike da cefane. Kaga kassmu damar shiga ɗakina duk lokacin da na kiraka koda kuwa kana inane?.

Nana bata tsaya karanta abun da yayi seveng number ba, domin ita duk a tinanin ta kawai yasa number ne bai ajiye taba. Hakan ne yasa ta karɓa tana cewa "Tom zan shiga gida? "To sai kinga kirana. Batace komaiba ta shige gida, shikuma ya tsaya yana Kallon ta har ta shiga gidan. Sannan shima yayi murmushi ya huce gida. Yana hanya yana tinanin hirarr da sukayi.

A.J. Ya ce "Shekara É—aya kawai? Hajiya ta bashi amsa da cewa "Eh shekara É—aya. Amma bazan baka kuÉ—in gaba É—aya ba, zan baka miliyoyin biyu yanzu, bayan shekara É—aya kuma zan baka sauran, amma gidan da nace shima zan baka, motarma saboda gudun tambaya da zan baka, amma yanzu itama motar sai bayan aure.

"Waiyoooo daɗin kasheni AJ ya furta a zuciyarsa sannan ya ce "Hajiya na yarda, amma ki bani miliyoyin biyun yanzu, sai kuma ki kaini gurin gidan nawa. Hajiya ta ce "wannan duk mai sauƙi ne, amma ai ban gama kafa maka sauran sharuɗan da suke cikin auran ba?. AJ ya ce "i'najinki.

Hajiya ta fara bayani kamar haka...."In na fara karkace komai sai na kammala sai kayi tambayar ka? AJ ya ce "Kede Hajiya muje bayani.

"Duk lokacin da na nemeka to ko a i'na kake ko me kakeyi zaka bari kazo?. Sannan wasu lokutan a gidana zaka kwana kuma a ɗakina, zan sanarwa da mai gadi cewar in kazo yabuɗe maka koda cikin dare ne. Ba kai ba kula wata macen ko wacece harsai auranmu ya ƙare. Karwani yasan wannan labarin koda kuwa Salis ne, ko abokanka, ko ƙanwarka, koma de waye. In kayarda gobe inada gurin da zamuje a ɗaura auran.

Abun da Hajiya Babba bata saniba shine...duk wannan bayanin da takeyi, shi AJ kuɗin kawai yake hange, amma abu ɗaya ya tsaya masa a'rai, wato kwana a gidanta. Tayaya!? AJ ya tambaya? Hajiya ta ce "Karka damu duk wannan mai sauƙine, nidai karka bari Salis da laɗifa suji wannan zancen? AJ yace "ya yarda. Nann take Hajiya ta ce "bani acont number ɗinka yanzu na tura maka?.

Nann take miliyoyin biyu suka shiga acont ɗin A.J. kallon message ɗin yakeyi, tamkar ya ƙwala ihu tsabar daɗi. Haka ya tashi ya fita, tsabar ruɗewama ya manta da maganar gidan. Hajiya Babba kuwa, duk abinda yaron keyi sake ɓurgeta yakeyi, badan tana tsoran saɓon Allah ba, kuma tin tana yarinya batayiba, da babu abun da zaisa bata zuba masa magani a ruwa don tayi amfani da yaron ba. Tabbas tana buƙatar na miji kuma, yaranta sun hanata, akan ta je ta aikata haram ƙwara tayi haka, tinda ADDINIMU bai haramta ba. Tawani ɓangaren kuma tana ganinn tsan-tsar son kud'i da ƙuruciya da suke damun AJ.

A.J. Yana fita sukayi karo da LaÉ—ifa zata shiga palorn. Shi AJ tsabar rikicewane yasa bai gantaba. Ita kuma laÉ—ifa tsabar zuciyarta ce take suya tsabar halin da take ciki. Tabbas yau tayi gamo, tana tafiya tana tinanin abun da yafaru tsakanin ta da shi, wanda tanada tabbacin ba musulmi bane. sai kawai taji tayi karo da mutum.
Chapter 8 · 0% Book details