← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 67

Sashe 47

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanye da jallabiya fara ya fito ƙafarsa ko ta ƙalmi babu, yana fitowa ya ci garo da Sarah domin itace ta farko jikin gidan nasu, sai kuma ya ga Hajiya Babba. Da mamaki yake kallonsu, sai kuma ya kawar da mamakin nasa domin kuwa yasan dama doke ta nemeshi . Lokaci ɗaya ya kafe Sarah da ido wacce itama shi take kallo idonta har ya fara cikowa da hawaye. A hankali ya ƙaraso kusa da ita wanda yayi dai-dai da ƙamshin tirarensa na fashion ya shiga ƙofofin hancinsu dukkansu. Take Sarah ta lumshe ido, ita kuwa Hajiya Babba tsabar damuwar da take cikima sai taji bata son wannan ƙamshin turaran nasa, take tashin zuciya ya fara zuwar mata. Kallon juna sukayi ita da shi sannan ya ce "Kinsan Sarha ne? Yayi tambayar ne cikin mamaki? Domin shi dai bai san asalin komai ba.

Ta ce "Eh amma ba wannane ya kawoni ba, ta faɗa tana mai jin a'mai na ƙoƙarin zuwar mata? Ya ce "Eh dama nima ina son muhaɗu domin kuwa a kwai ma tsala? Kallon Sarah Hajiya Babba tayi sai AJ ya mata a lama da bata jin Hausa. Hajiya ta buɗe baki ta ce.....📝

[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*

*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*

_*Bansan da wani irin alƙalami zan rubuto muku ɗinbun godiya da irin addu'o'in ku a gareniba, tabbas LITTAFIN ADDININMU yana samun yabo sosai a gareku makaranta ina godiya sosai da sosai.*_

_*PAGE3️⃣6️⃣*_
..........Ta ce "Bana son wannan ƙamshin tiraran naka pls kaje kacire wannan rigar kazo muyi magana? AJ ya kalli jikinsa sannan ya kalli Hajiya Babba sannan ya dawo da kallonsa izuwa ga Sarah wacce tunda ya fito ta kafeshi da ido ko rin tsawa batayi. Juyawa yayi ya koma cikin gida ya cire rigar ya sako wata jallafiyar sannan ya fito. Yana fitowa bai ce musu komaiba ya ƙarasa jikin motar ya na cigaba da kallon Sarah. "Ta ce ina wayarka? Kuma me ya kaika gidan Comanda Daniyel? Hajiya Babba ta watso masa wannan tambar. Acikin jimilla ɗaya ya bata amsar tambayoyinta. "Babu ruwanki wannan bai damekiba faɗi abunda ya kawoki? Shima ya bata amsa cikin tsananin jin haushin halin da ta jefashi. Da mamaki Hajiya Babba ta kalleshi sai kuma ta kawar da kai gefe tana danasin abunda ta aikata, yanzu wannan ɗan yaron shine har na yarda ya sanni a matsayin ma ce! Inalillahi wa inna i'laihim raji'un! Ta furta a zuciyarta kafin ta koma serus ta ce....

"Kaman yanda mukayi wannan auran ba tare da kowa ya sani ba to haka nakeson yanzu-yanzu ka sakeni na baka kuɗinka kuma karka sake ne ma na, sanan duk wata alaqar da ke tsakanin ka da Salis itama inaso ta yanke daga yanzu, zan baka kyutar gida kubar wannan unguwar domin bana son wani abu ya ƙara shiga tsakanina da kai har a bada. Da ɗan mamaki AJ ya ce "Ai dama a cikin sharuɗanmu harda gida a ciki saboda haka ba kyuta zaki baniba hakƙinane, sannan kuma nima nafi son hakan, amma kinsan fa a tsarin Addinin Muslunci dole sai an ɗaura muku wani auran kafin zamanku ya halarta keda shi mijin naki, kenan ya zakiyi? Hajiya Babba da gaba ɗaya kanta ya ɗau zafi, ga kuma taga kamar yanason yin amfani da wannan damar ya raina mata hankaline ta ce "Wannan ba damuwar ka ba ce, kaidai ba damuwar ka kuɗi ba? AJ ya ware hannu haɗi da karkatar da wiya alamar yes. Ta ce "Ok yanzu nawa ne sauran kuɗin naja? Ya ce "Gidaa nafi buƙata a yanzu, sannan kuma kuɗi inaso ki bani miliyon hamsim idan kinga zaki iya ? Ya faɗa yana haɗe fuska kamar yanda tayi.

Cikin tsawa ta ce "Kai ɗan matsiyata walhi kai baka isa ka iya tonamin asiriba kayi kaɗan, kaiɗin banza miliyon goma zan baka ai bamu gama cika watannin da muka yankeba, saboda haka idan kaga dama ka amsa idan bakaga danaba ka barshi aurene dai ya ƙare tunda mijina ya dawo? Hajiya Babba ta ƙarasa maganar tana buɗe gaban motarta ta ciro wayarta ta ce "Bani account numbar ka yanzu na tura maka, suma ta kardar gidan nazo dasu, inaso daga nan ƙarna sake jin labarinka. Cikin jin jewar shawar da zuciyarsa ta bashi tayi ya ce "Idan har kina son saki daga gareni kuma nayi nisa dake har abada to inada sharaɗi? "Sharaɗinkan na banza, walhi yaro sai ka sakeni kuma yanzu idan ba hakaba walhu sai kayi da kasanin sanin Aisha Salisu.

AJ ya ce "To shikenan tinda kince haka, zaku iya barin ƙofar gidannan yanzu kafin na tara muku jama'a kuma ki sani auranmu zai baiyana ga duniya, kuma zaki bar gidanki kidawo gidana ki tare, badai sai na sakeki za'ayi auran ba to muzuba mugani? Yana faɗa ya juya zai shiga gida. Ai da sauri Hajiya Babba ta kamo hannunsa ta yi ƙasa da murya cikin sanyin rai ta ce "AJ karkamin haka ka tuna cewar aurannan fa dama munyishi a cikin kuskurene kaga rabuwar shine mafi dacewa, kokai bazakaso ace kaine mijin uwar abokinkaba, kaga Salis bazaiji daɗiba pls kayi haƙuri kafaɗi sharuɗan naka? Hajiya Babba ta ƙarasa maganar da muryar roƙo kamar zatayi kuka. AJ yayi shiru yana tunano irin dukiyar da ta mallaka, sannan yana tunano irin wahalar da yasha kuma duk itace, sannan ya tunano su Innah yanajin cewar wahalarsu ta ƙare a rayuwa, ya tuno lokacin da take bashi umarni kuma tace a cikin sharuɗan auransune. Afili ya kalli gurin da Sarah ta ke yaga har yanzu su take kallon ko magana batayi, take yaji gabansa ya faɗi ganin irin kallon da take masa, lokaci ɗaya yaji wani tausayinta sai kawai ya lumshe ido yana son sanin alaqar Hajiya Babba da ita ɗin. Ya ce "Sharuɗa na guda ukune? Idan kin yarda yanzu zan rubuta miku saki na baki idan kema kin bani nawa? Hajiya Babba ta haɗiyi wani yawu muƙut ta ce "Ina jinka?

*SALIS POV*

Gaba ɗaya hankalinsa kacoƙan ya tattara izuwaga Nana ya na son yaje yaga a wani hali suke, shin bayan da suka fito daga gidan ƴan sanda ina sukaje? Anya kuwa lfy? Gashi numbar ta ta daina aiki. Har sukaje gidan abokin Daddy suka dawo bai daina tunaninta ba. Afili ya ce "Yanzu lokaci yayi da Hajiya zata san da magar aurane tunda Daddy ya dawo, kokuma na fara sanar da Daddy. Haka dai ya keta saƙe-saƙensa shi ɗaya, ya bari a kan zaije gurinta da yamma.

Ɓangaren su Muhammad da Umar da Usman kuwa, izuwa yanzu sunce sumafa sun matsu da son zuwa gida suga iyayensu, domin kuwa dukkansu babu mai aure. Hakan yasa Muhamd ya yanke cewar suyi haƙuri zuwa gobe sai su tafi. Sunyi yawo sosai a cikin gari, duk gurin da Muhamd yaje indai ansanshi sai kowa yayi mamaki. Lokacin da sukaje gurin abokin nasa kuwa yana ganinsu ya fara Ambato sunayen Allah cikin tsoro. Sai da yaji yayi maga kafin ya nutsu.

Bayan yaji duk abunda ya faru ne ya shiga mamakin rashin imanin Daniyel, a ce ka ɗaure mutum kusan shekaru har ashin(20) saboda kawai ya koma addinin Allah. To walhi sai anyi masa hukumci ai samun matsayi ba hauka bane. Malam fa ya shiga surfa faɗa yanajin abunda a kaiwa abokin nasa babu daɗi, domin kuwa ko bayan abotar dake tsakanin su ai shiɗin musulmine, musulmi kuma ɗan uwan musulmine. Da ƙyar dai Muhammed ya taushi Malam har yayi shiru, sannan ya ce "Ni Walhi na yafe masa duniya da lahira, in de domin abunda yaminne za'a masa hukumcin to walhi na yafe. Cikin mamaki Malam ke jijjiga kai ya ce "Eh laillai kam kaci sunanka Muhammad domin kuwa wannan shine irin halin mai sunanna, kuma haka yayi mana nuni da muyi, rama kairi d
ga wanda ya aikata maka shirri yin hakan imanine, haƙiƙa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama zaiyi alfarahi da kai, kuma wannan halin naka shine ya kamata adinga yin koyi dashi. Malam ya ci gaba da cewa ..."A kwai wani maƙofci da Manzon Allah ya taɓayi wanda ba musulmibane baya ƙaunar mudulmnci da kuma musulman gabaki ɗaya, tsabar ƙiyayarsa da manzan Allah, kullum idan yayi shara a gidansa sai ya tattara ya watso gidan Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama, shi kuma idan ya watso sai ya kwashe. Sai Manzon Allah yaga kwana biyu wannan kafirin bai watso masa sharaba sai ya tambaya ko lafiya kuwa kwana biyu baya jin ɗuriyar maƙofcin nasa? Sai a ka shida masa cewar ai bashi a ke binsa kuma bai biyaba shine a ka kamashi a ka kulle. Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama sarkin tausayi Sarkin adalci ya bada wannan kuɗin masu yawa a kaje a ka fito da wannan mutumin. Bayan ya fito ya tambaya cewar waye ya fito da shi?

Sai a ka ce masa Muhammad Rasulullah. Sai ya ce "Shiɗin ne ya bada kuɗin da a ka fito da Ni? A ka tabbatar masa da haka. Ai kuwa take kafirin ya miƙa wiya ya musulunta. Take su Muhammad da Umar da Usman da Salis suka ce Allahu Akbar! Malam ya ci gaba da cewa "Haƙiƙa Muhammad kaiɗin masoyin manzan Allah kuma da yardar Allah bazaka taɓa wulaƙanta ba, daga kai har zuri'arka.

Nan dai malam ya masa bayani game da matarsa cewar idan har tayi wani auran to zata zaɓane ko shi ko waccen mijin nata, idan kuma batayi wani auran ba to auransu yananan kawai dai zasu cigaba da zamantakewar su a matsayin ma'aurata ne. Muhammad yayi godiya sosai sannan ya tambayeshi labarin malamin su wato shek Kabir kabuga. Malam ya sanar masa da cewar yana nan lafiya, kwanan ma zai aurar da yaransa mata guda biyu. Muhammad ya ce "Ikon Allah malam har zai aurarr da yara. Sun daɗe a gurinsa ya ƙara jaddadamusu cewar suma su Umar da Usman so je gida domin a sanar cewar sunraye.
Chapter 47 · 0% Book details