← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 67

Sashe 25

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka Mommy keyi taƙi ta tsaya ta saurareshi ganin haka yasa ya miƙe tsaye sauran ƙannan nasa suka bishi da kallon mamaki, yayinda Sadiya tayi ƙarfin halin cewar "Yaya me zaisa ka sace..."hannu ya ɗaga mata yana barin ɗakin cikin tsanani ɓacinrai, domin kuwa ransa yayi mugun ɓaci sosai, harma baisan meye abunyiba. Tunawa yayi da maganar daddy "Kaje ka fito musu da yarinya a duk inda ka ɓoyeta kuma mun gama magana da baban yarinyar da na zaɓa maka, indan kaga damar zuwa ruwanka idanma bakajeba to bazamu fasa daga ranar da muka yankeba...Na gaji da maganganu da mutane keyi a kanka, idan kai bai damunka toni yana damuna...Kin gaji ko to idan kin gaji daga ke har yaranki ai ga hanya nan kunada damar zuwa duk inda kukaga dama acikin ƙasarnan.

Ajiyar zuciya ya sauke yana shiga motarsa, tafiya ya keyi yana tunanin abunyi. Nan ma maganar Mommy ta dawo masa kansa. "Komai É—aya Al'adar mu É—aya, yarenmu É—aya Allahnmu É—aya Annabinmu É—aya, ADDININMU É—aya Amma kunÉ—auki tsana kun É—ora a kan junanku, Walhi kuji tsoran Allah domin wannan abun ba addini bane.

"Kallon agogon hannusa yayi sannan ya koma gidan sa domin shiryawa zuwa gurin su.

"Haba mlm yanzu dawanne kakeso muju da ɓatar ƴata kakeso kokuma da wannan masifar naka!? Shi wannan yaron da kuketa zargin shine ya saceta shin kunyi magana dashi ya ce shine ya saceta ne? Kudinga yiwa kanku a dalcifa, ni yanzu damuwata kawai yarinyata ta baiyana koma waye yaje shida Allah, kaikuma Walhi idan na ƙarajin kace wani abu a kan wannan yaron to Walhi sai na saɓa maka, banza mara zuciya. Mama ta faɗa tana nuna gurin da Isa yake staye yana ƙara zuga mahaifin nasu akan cewar Abdalh ne yasaceta shi kuwa mlm dama a sama yake ya tsani mutanann baya son duk abunda zai haɗa shi dasu, yanzuma jiyake da yanada dama da ya tashi duk wani ɗan aƙidar su Abdalh ɗin gaba ɗaya kowa ya huta. Mama ta ci gaba da cewa ...."Gashi tunda abunnan ya faru kuna gida babu wanda yafita domin nemanta amma kunzo kuna ta zancen banza a kan yaronda inada tabbacin baima san suwaye suka ɗauketaba. Ni dai Allah ya bayyana min yarinya.

Cikin tsananin faɗa da yasa muryarsa har rawa takeyi mlm ya ce "Walhi kin yi ƙarya ba a gidannan ba! Dama na lura dake bakison kuji ana faɗar laifin wannan yaron ko? To Walhi bari kiji kotu ce zata rabamu da wannan yaron mutuƙar yarinyata bata dawo gida yauba, ga alamu sun nuna cewar shine ya saceta, kuma har yanzu daga shi har uban nasa wanda shine mai ɗaure masa gindi babu wanda ya fito yayi magana. Shegu dangin tsiya munafukan Allah, Walhi sai sun tozarta idai irin wannan rayuwar satar yaran mutane itace halaiyarsu. Caraf isa ya cafe da cewar...

"Walhi haka sukeyi, kwanakin baya ma haka yaran da suka ɓata a hanyar school ance sune suka sacesu. Momy ta ce "wallhi kuji tsoran Allah domin wannan abun da kukeyi ba shine mafitaba, dama kishin neman ilimi kukeyi da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yayi alfahari daku, bawai zagin juna kuba, idan anyi magana kuce kune nagari, Walhi addinmu bai koyar damu cin mutuncin ɗan adam ba, ɗan adam ɗin ma wai musulmi. Kuma yanzu gashi ai kunju daɗi tinda gashi sai raba kawunan al'umma kukeyi, kullum tashin hankali kuma duk kune dalilin hakan, yara marasa sanin ciwon kansu sai zage-zage sukeyi a gari. Cikin ɓacin rai mlm ya ce "Walhi ki kiyayeni ki fita daga idona "Nidai a je a nemomin yarinyata shine kawai, ai ADDININMU baiyi hani da sace yaran mutanebako? Kuma Walhi sai munje kotu. Yana kaiwa nan ta rushe da kuka, isa da mlm suka fita suna cewa ai shine ya saceta kuma sai ya fito da ita.

*ABIN DUBAWA. TUNANI MAI KYU*

Waya ya ɗauka ya danna kira, sai da ta kusa tsinkewa aka ɗaga. Kafin ayi mgn ya ce "Gani nazo gurin wani gidane? Ya ce "Ok gani kubuɗe min get ɗin ina ƙofar gidan. Bayan ya shiga da motar tasa ya fito ya nufi wata ƙaramar hanya da ita ce kaɗai zata sadaka da cikin palorn gidan. Yana shiga ya ƙara kiran numbar taso suka ce ya dawo baya, ba'a wannan gidan sukeba dama sun kwadashi ne ko tafe yakeda ƴan sanda, cikin mamaki ya ce "Bayan munyi mgn daku maizaisa nayi ƙarya? Ta cikin wayar a kace ayi haƙuri shek ɗan gidan Shek kasan yanzu duniyar ce ba'a yarda da kowa. Ya nufi gurin da sukace masa, bayan yaje ɗaya gurin da suka cemasane ya shiga gidan domin ƙofar gidan a buɗe take, ya ce "Ina take? Da sauri sukace tana ciki! Ya ce "Damade baku taɓataba?, nann suka fara sun guyar da kai alamar aikin gama ya gama. Yana tura ɗakin da tage ya tsaya chak cikin mamaki haɗi da zaro ido waje.

Da sauri ya fito daga motar ransa a ɓace ya shiga kiran matar tasa "Elixa!!! Kafin ya rufe baki idonsa ya sauƙa a kan wasu samari guda biyu, zaune a cikin palorn nasa. Cikin tsananin mamaki ganin harda musilmi a cikinsu ya ce "Meya kawo su? Mommy ta ce "wai kuɗin Samuel sukazo biya shine nace sujira ka kadawo. Cikin mamaki daddy yake binsu da kallo haɗida zubawa shigar wannan ba haushen da kallon tsana domin kuwa doguwar riga ce a jikinsa sai hula mai kyin gaske. Ya ce "Suwaye kuɗin? menene haɗinku dashi? kuma yaushe ya baku aron kuɗinsa?.

Kowa yabar gida tabbas gida ya barshi! Yau dai ga Hajiya Babba tareda AJ a ƙasar 9j. Kana kallon fuskar Hajiya Babba kasan babu annuri ko kaɗan, harma wani jajaja fuskarta keyi. Yayinda shi kuwa AJ ya buɗe ido yana kallon ƙasar tasa wacce bai taɓa barintaba koda kuwa na kwana ɗayane Amma yanzu harna kwanaki biyar. Mota suka shiga izuwa gida, yayinda AJ yake kallon komai kamar a mafarki. A ƙofar gidan Hajiya Babba sukayi parking ta ce "Ya fita yaje gida in yazo anjima zata kirashi, kuma zata tura masa kuɗin idan ta shiga gida. Kasan cewar da yamma ne sai kawai AJ ya ce "To angama dama nimanna matsu naga Innah da Nana. Saida tafiya wani shafi yayi musu soyayya mai yawa kafin ya nufi unguwar tasu.

Tin daga bakin layin unguwarsu yaga ana ta kallonsa sai kawai ya bar hakan akan irin kayan dake jikinsane yasa, yana tafiya baya ko kallon kowa kamar yanda ya saba a da bare yanzu da yake ganin shima wanine, suma ƴan uwarsa da yake sun san halinsa na ɗaukar kansa yafikowa yasa babu wanda tanada mgn sai kallonsa da sukeyi. Kallon ƙofar gidan nasu yayi a buɗe, sai kawai yasa kai ya shiga yana sallama haɗida zabgawa Innah kira cikin muryarsa dake nuna cewar yayi kewarsu sosai.....✍️

*Abin tambaya. Shin meye tsakanin su Hajiya Babba da Comandar Daniyel? Shin ina ne Abdalha yaje? Shin da gaske shine ya sace Zainab? To gadai AJ ya sauƙa a 9j? Me zai faru? Yanzu komai zai warware. KUKASANCE da S REZA. Domin jin me zaifaru.*

*

*Kafin kufara karanta wannan page ɗin, inaso kutuna abunda nace a page ɗin farko, Pls* 🙏

*PAGE. 2️⃣1️⃣*

......... Innah! Innah! Innah! Cikin murna da ɗokin son ganin Innar tasa yake ranƙaɗa mata wannan uban kiran kai ka rantse da Allah irin ya hangota daga nesane amma bata jisaba. Saboda tsabar ɗoki da AJ keyine yasa bai ko kula da kurarr da gidan ya ɗanyiba, sai kawai ya nufi ɗakin Innah da sauri yana cigaba da kiran sunanta, wannan karan harda sunan Nana yake haɗawa. Cikin mamaki yake kallon ƙofar innar tasa abuɗe gakuma kwanukan abinci da sauran abincin dake ciki alamar dai andaɗe ba'a cikin gidan, da sauri ya fito daga ɗakin Innah ya nufi ɗakin Nana. Yana zuwa itama yaga ƙofar ɗakin abuɗe, har yanzu bai daina kiran sunan Nana ba, yana shiga idonsa ya fara sauƙa a kan kadonta, sai ya hango wayarta a kan gadon, ai kuwa da sauri ya ɗauka yana ƙoƙarin kunnawa, amma wayar taƙi kunnuwa, domin kuwa babu caji. Fitowa yayi da wayar izuwa tsakar gida jikinsa har rawa yakeyi domin kuwa izuwa yanzu jikinsa ya fara aiyana masa mugayan abubuwa a kan su innah. Sai a lokacin yabi ko'ina na gidan da kallo yaga tabbas babu kowa a gidan. Afili ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ina su inna suka tafi!? Cikin zafin rai ya ɗauki wayarsa ya shiga kiran Hajiya Babba, ai kuwa kira ɗaya ta ɗaga, tana cewa "Pls ina zuwa zan kiraka. Tana gama faɗa ta kashe wayar batare da tajira abunda zaiceba.

Sai a lokacin kuma ya fashe da wani irin kuka ya ce "No no no yana faɗa yana girgiza hannunsa yana jabaya, ya ce "Noooooooo! tabbas bai yarda da abunda zuciyarsa take cemasa akan su innha ɗinba, hakanne yasa yayi waje izuwa ƙofar gidan su, yana zuwa kuma ya tsaya yana kallon al'ummar gurin cikin rikicewa yarasa abunyi sai kawai ya nufi gurin taron samarin da ke kusa da wani ɗan shago, wanda shi a tunaninsa dai idan bai mantaba bai taɓa zama a gurinba ko kuma yayi musu mgn ko sallama aganin sa su ƴaƴan talakawa shima haka to me slamar zata ƙara musu, saidema idan yazo hucewa ya dinga musu kallon banza yayinda sukuma suka ɗaukeshi mai gyrman kai, domin kuwa sunsan bai ajiyeba kuma bai baiwa kowa a jiyaba sai shegin iyayi da nuna shi wanine.
Chapter 25 · 0% Book details