Sashe 37
Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.........Ko wa da ke cikin ɗakin tsorata ya yi saboda ƙarar harbin bindigar, hakan ne ya sa gaba ɗaya suka cure a guri ɗaya ko wa na neman hanyar da zai tsira da rayuwar sa, shi ku wa Salis lokaci ɗaya idon sa ya sauƙa a kan abokinsa wanda ya ke gefe ɗaya cikin tsananin wahala. Da ƙarfi ya kira sunan sa ya na ƙarasawa gurin da ya ke. Da sauri Momy ta ƙara sa gurinda Samuel ke kurma ihuu domin harbin da a ka masa a ƙafar dama. Shima Daddy da sauri ya je gurin ya na kamo yaron nasa cikin tashin hankali. Yayinda ita kuma Hajiya Babba ta bi bayan yaron ta domin jin kiran sunan AJ da ya yi. Itama Sarah cikin kuka tayi gurin ɗan uwan nata haɗi da rushewa da wani sabon kukan. Ita kuwa Laɗifa tsayawa tayi a bakin ƙofar ta rasa gurin wa zata je, domin ganin jini a ƙafar Samuel ya tasher mata da hankali, hakanne ya sa ta tsaya ta na kallon sa cikin damu wa, ai kubwa bata san lokacin da kuka ya kuffce mata ba tana rufe bakin ta kar kowa ya ji.
Da sauri Salis ya ɗago Aj da ga kwancen da ya ke yana kiran sunan sa AJ...AJ... Amma ina AJ ko magana ma yakasa domin kuwa ya daku ba da wasaba, shi kuwa sai gir-gizashi ya kayi ya na ƙara kiran sunansa, kuma yana tunanin me ya kawo AJ ɗin cikin wannan gidan! Daddy ku wa ganin Hajiya Babba na ƙoƙarin shiga ɗakin ne yasa da sauri ya sha gaban ta ya na tambayarta ina zata je? Cikin tsananin ɓacin rai da tsanar da ta kewa yayan mijinta ta fara surfa masa masifa ta na cewa idan bai bata hanya ba zata zabga masa mari, ai kuwa Hajiya Babba ta man ta a gaba wa take domin kuwa ranta yayi mugun ɓaci idon ta duk sun rufe, har wani ruwa ne ya cika a cikin idanuwan na ta. Kafin ta gama rufe baki taji sauƙar mari guda biyu hagun da dama. Cikin ɓacin rai da ganin komai ya lalace ya nunata da hannu ya fara magana cikin fushi.
"Walhi saina kashe ki idan baki bar gidan nan ba, shegu dangin tsiya, ai dama nasan mutuƙar mutam ya zama mai yin salla to shikenan kun gama shanyeshi, to dan uwarki harda ubanki ki bar gidannan ko kuma na sa a"...Bai ƙarasa ba yayi ido biyu da Salis reƙe da AJ ya fito daga cikin ɗakin. Da sauri dukkansu suka kai kallon su izuwa gurin da Salis ke tsaye. Da sauri Sarah ta bar gurin da Samuel ke ihuu har zuwa yanzu wanda dukkansu kuka sukeyi an kuma rasa wanda zai ɗauke shi izuwa asbiti sai ihuu sukeyi. Da sauri ta ƙaraso gurin ta na mai kamo hannun AJ ɗin cikin wani sabon kukan. Sai ji kayi itama Daddy ya ɗauke ta da mari sannan ya turata waje, yana ƙara tabbatar ma da cewar babu ita babu AJ.sojoji ku wa Tinda sukayi wannan harbin suka shiga cikin tashin hankali ganin Samuel suka samu ba Salis ba, sannan tunda Ogan na su ya zo bai ce musu komai ba sai yanzu. Ya basu umarnin fita da Samuel. Ai kuwa da sauri sukayi waje dashi. Hajiya Babba kuwa ta na riƙe da hannu a kunci.
"Eh tabbas shekarun da ya wa, kuma abubu wa da dama sun sauya, sannan kuma yanayi ya sauya ha ka zalika duk wani abu mai rai to tabbas yana ƙara girma ne, sannan abu mai muhimmanci baya taɓa gushewa da ga mahalli da. Tin lokacin da ya yi ido biyu da yaron da ya shigo ɗakin jikin sa ya sanar masa da cewar tabbas yau Allah ya karɓi addu'ar da suka daɗe sunayi, ya na cikin kallon yaron ne har yaron ya taso riƙe da ɗaya yaron da a ka shigo da shi ɗa kin nasu ɗazunnan. Kukan da yazo masa ne yasa ya kasa yiwa yaron magana har ya fita. Yana cikin haka ne yaji muryar da ba zai taɓa mantawa da itaba koda kuwa mutuwa yayi kuma ya dawo wannan duniyar bare kuma bai mutu ba. Tabbas baiyi niyar tashi ya fito gurin ba, amma jin yanda yayan nasa yake cin mutuncin Addinin nasa da kuma yana jin cewar Allah ne ya turo wannan ranar domin ta zama warakar damuwar da suke cikin Sudan ƴan u'wansa, hakanne ya sa ya miƙe daga gurin da yake zaune cikin wa su kaya yagaggu sun gama fita a haiyacinsu ga tarin gashi da ya gama mamaye masa fuska, gashin kansa yayi jaa ,sannan ya mur-murɗi, ha ƙoran sa sunyi jaa sun fita a haiyacin su, gaba ɗaya kamarsa ta canja, daga gurin da kake zaka hango ƙashin ha ƙaƙƙarin sa a waje. Ganin yayi hanyar fitane yasa sauran mutum ukun da suke ciki suma miƙewa suka biyo bayan sa, suma cikin irin halin da yake ciki.
An fita da Samuel, shi kuma Salis yana tsaye a kusa da Daniyel ya kafeshi da ido, yayinda Hajiya Babba tayi kan Salis cikin tashin hankali tana kiran sunan AJ. Lokaci ɗaya Hajiya Babba ta fita a haiyacinta tana ƙoƙarin kamo ƙafafun Aj domin fita dashi sai suka tsikayi muryarsa cikin rawar mur yaya ce " Ai ais Aish Aisha? "Timm ka keji Hajiya Babba ta saki AJ ya zube a gurin tsabar ruɗu da harƙizi da suka dirar mata a lokaci ɗaya. Da sauri ta juyo domin kuwa tabbas bazata taɓa mantawa da wannan muryarba har gaba da abada. Tana juyowa sai taga fuskokin mutane har guda huɗu a bakin ƙofar ɗakin, amma hakan bai hana ta gano fuskarsa ba cikin sauri da ruɗani ta nufi gurin sa bata iya ko magana ba tana nunashi da hannu.
Salis da laɗifa sai kallon Hajiya Babba sukeyi domin su dai basu gane waye wannan mutumin mai kama da wanda baya cikin haiyacin sa ba, suna kallo har Hajiya Babba ta rungumeshi dukda irin kayan da ke jikin mutumin. Shi kuwa AJ jin yanda a ka sakeshi ne yasa ya saki wani ihuuu yana buɗe idonsa cikin wahala, domin kuwa tsabar duka har saida ya suma.da sauri Salis ya zo gareshi ya na kiran sunan sa. Cikin mamaki Salis ya duba cikin ɗakin amma baiga Daniyel ba, ai kuwa da sauri ya tashi domin fita waje, ai kuwa yaji ƙofar ɗakin a rufe, ya kalli ƙofar da kyu, ya ja da baya ya zo da gudu ya daketa amma ko motsi batayi ba. Abun da kamar wasa har yayi har ya gaji amma dai ƙofar na ƙulle.
Cikin wata iriyar murya wannan mutumin ya ce "Ya ƙulle ƙofar ne ko? dama nasan bazai barmu mu a gidan nan cikin kwanciyar hankali ba tabbas kashemu zaiyi baida imani, dama ya sanar min cewar duk ranar da wani yasan ina raye to tabbas zai kashe ni kuma ya kashe ku.
Duk wannan maganar yanayi ne a bakin ƙofar da suka zo domin fita. HAJIYA BABBA ta kalli Salis da Laɗifa ta ce "Sa sa Salis shine ba ba ban babanku, shine babanku. Tana faɗa ta sake fashewa da kuka, yayin da Salis da Laɗifa harma da Mlm AJ suka kai kallonsu gurin mutumin, suma sauran ƴan ɗakin da mamaki suke kallon yaran da kusan kullum sai mutumin ya basu labarin cewar ya bar yaransa da matar yan zu baisan a wani hali suke cikiba. Lokaci ɗaya dukkansu kuka ya kuffce musu, sun kasa zuwa gurin baban na su, sai tuno irin wahalar da yashe sukeyi da kuma tuno abun da ke faruwa yanzu sukeyi. Hannu ya ware musu alamar ku taho gareni ai kuwa dukkansu suka nufeshi suna kukan farin ciki.
Alokaci É—aya Mlm AJ ya sake jin wani sabon ciwon da baisan daga ina ya fito masa ba, shin wai shi yanzu a wani hali yake ne, kuma yaji ana zancen kisa, to har dashi za'a kashe! Lokaci É—aya ya nemi ciwon da ya keji ya rasa, ya fara tuni Innah da Nana. ita kuwa Hajiya Babba za mu iya cewa harga Allah ta ma manta da wanzuwar wani mai suna AJ agurin.
Sun kwashi lokaci suna koke-koke kafin suka ƙara shiga ƙoƙarin buɗe ƙofa amma shiru. Hakanne yasa suka haƙura suka zubawa sarautar Allah ido.
*(Shin kuna tunanin Daniyel zai buɗesu? Kodai a ciki duk zai haɗa ya kashe kamar yadda ya ce? To wai ta yaya zasu fita daga cikin gurinnan, ga shi dukkansu kowa na ciki😪 Tom koma dai menene muje zuwa domin ganewa idon mu)*
Ganin Muhammad ya fitone yasa Daniel za me jikin sa ya fita daga ɗakin sannan ya sa ɗan mukulli ya rufesu ta waje sannan yayi cikin gidan cikin sauri. Ya na shiga palon gidan nasa yaga har angama cirewa Samuel bulet ɗin an masa aiki agurin ana ƙoƙarin ɗaurewa. Da sauri ya da katar da sojan daga aikin da ya keyi, sannan ya ce ya kira masa sauran sojojin da suke gidan gaba ɗaya. Cikin minti kaɗan sukazo, dukkansu ya sanar musu da cewar zaibar wannan gidan nasa izuwa gidan sa da ke cikin Bokon, kuma gaba ɗaya har da iyalansa zai tafi, saboda haka a je a shirya yanzu-yanzu, ya ware mutum biyu ya ce su tsaya. Bayan waɗan can sun tafi ya kalli sauran ya ce...
"Ku biyu zaku tsaya a nan idan mun tafi kamar da awa ɗaya ku sakawa gidan wuta kuma kubi bayanmu, idan an tararr daku kuce gobara ce. Haka suka yanke shawara sannan suka shiga haɗa kaya, komai na amfani saida suka ɗauka, cikin lokaci ƙanƙani Sojojin sun gama haɗa musu kayan a mota harda sauran motocin gidan duk dasu zasu tafi. Ran Daddy ya gama ɓaci ji yake kawai ya kashesu kowa ma ya huta.
Sai da a kazo tafiya kuma a ka duba sama da ƙasa amma babu Sarah babu dalilin ta. Anduba gidan ko ina amma babu ita, kuma harda ita a ka dawo palon. Nan fa hankali Elixa ya tashi domin kuwa ta damu, aka tam bayi sojojin kodai ta fita ne sukaje su basu ganta ba. Cikin tsananin ɓacin rai da kuma ganin tana son ɓata musu lokaci Daddy ya ce kawai su tafi su barta.