← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 67

Sashe 15

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sojan ya faɗawa Daddy ai kuwa Daddy ya shigo gidan yana zagin sauran sojojin akan mai sukeyi bazasu kawowa ƴansanda suba. Sannan ya ce "Ni na tsani duk wani musulmi koda kuwa macece, idan har tana Salha to wallhi babu mutunci, mutanan da suka mayarda kisa ba'a bakin komai. Nidai ADDINIMU bai aminta da kisaba amma yau sai na nunawa wannan A.J ɗin cewar ADDININMU ba ɗayabane, shege inama shi muka kama. Haka Daddy ya sa aka watsawa innah ruwa ta farko sannan a ka yi waje dasu.....📝

*Oooo ni Allah!! Kaima AJ Ina kai ina taɓa irin wannan bala'in. Allah sarki innah da Nana😓.*

*PAGE1️⃣2️⃣*

.........Haka sojojinnan suka tasa ƙeyar Innah da Nana har bakin motar Police ɗin da suka iso gurin, al'ummar unguwar kowa yafito yana kallon ikon Allah, wasu daga cikinsu kuwa kuka sukeyi ganin yanda Innah tayi kamar wacce bata cikin haiyacinta. Nana kuka Innah kuwa ta kasa magana tsabar ruɗewa. Babu ko imani suka turasu a cikin motar sannan sukayi gaba. Ana zuwa police station babu wani bincike saboda ganin wanda ya kawosu, haka Daddy yasa aka turasu cikin sell sannan ya kalli police ɗin daya ƙarɓi ƙarar ya ce "Kar a sake a bada belinsu harsai yaron yazo gidana da kansa. Cikin sauri police ɗin ya ce "Yes sir. Daddy ya bar police station ɗin cikin ɓacin rai. Bai taɓa kawo cewar Sahra zata iya satar masa kuɗiba, dama yasan saide wani ya zigata wanin ma wai musulmi mai Sallah shine yake tura yarinyata tana satar min kuɗi!! Haka Daddy ya shiga mota yana tinanin idan ya kama A.J Allah ne kaɗai yasan abunda zai masa.

*SALIS. LAÆŠIFA. POV*

Bayan Hajiya Babba da A.J sun tafine Salis ya koma cikin gidan domin yin mgn da laɗifa, amma taƙi buɗe masa ƙofa, hakanne yasa ya kira Nana yace mata yana zuwa, dama sunyi a kan zasu haɗu idan AJ ya tafi. Aikuwa bai bar ƙofar gidan ba sai wajan ƙarfe biyu, sannan ya ce zai tafi, amma gobe da safe zai kawo mata kyutar bazata. Haka sukayi sallama ya tafi gida cikin farin ciki.

Laɗifa kuwa abubuwan ne suka haɗe mata biyu. Ga haushin A.J da takeji wanda batasan meyasaba, gakuma haushin hanata zuwa club ɗin da Salis yayi jiya, tabbas taso taje tasake haɗuwa da wannan gayan, kodan tasamu sukuni a zuciyarta . A kowani lokaci idan zatayi ƙoƙarin kawar da tinaninsa sai taji soyayyar sa na ƙaruwa a zuciyarta.

Tana cikin hakane wani tinani ya faÉ—omata, aikuwa afili tace "Tabbas shine Walhi shine, take ta shiga wanka domin kuwa gurinsa zataje, to amma ai tamasa rashin mutunci, take abunda ya faru tsakanin ta da Umar abokin Samuel ya shiga dawo mata a kanta.

Fitowarta keda wiya daga gidansu ƙawarta Yusra wacce ke unguwar su Umar ɗin ne ta hango wani saurayi shida wata budurwa a jikin motarta suna hira. Kallon gurin tayi cikin tsananin mamaki ta ce "Yusra kinga irin abubda yasa bana son zuwa unguwar ku ko? Yanzu-yanzu daga ajiye motar har wani wawa ƙazami zai ɓatamin Itaki? Ai kafin Yusra tayi magana har Laɗifa ta kai gurin da Umar ke tsaye.

Yana cikin hirarrsa irin ta mayaudara yaji muryarta tana cewa "Uban waye ya baka izinin tsayuwa a jikin motana?. Dagashi har yarinyar da ya tare yake zuba mata ƙarya akan cewar motar sace suka juyo suna kallon ta. Kafin suyi magana ta ci gaba da cewa...inbanda hauka da rashin tunani daga ganin mota sai kawai ka zoda wani ƙazamin kayanka ka jin gina ajiki, kalleka fa kamar wani ɗan almajiri wai kai saurayi har kana kawo budurwa jikin motana.

Cikin jin kunya Umar ya kalli yarinyar da ya gama shirya mata ƙarya, zaiyi magana taja wani dogon tsaki mtsiiiiiiii sannan ta bar gurin. Laɗifa ta ce Mlm kobazaka ma tsa bane? Umar kuwa ya kasa magana tsabar kunya haka ya bar gurin motar yana sosa kai ya kasa magana, amma abunda tamasa ya tsaya masa a'rai.

Laɗifa tace "Sune irin ƴan isakan samarin da suke zuwa wajan ƴan Mata da yaudara, kukuma kuna jin zancen su saikuyi sauri kuce kun amin ta dasu, daga baya kugane ashe matsiyata ne. Yusra ta ce "To mlm bansan iskanci ni kinga ina kula irinsune? Kuma wannan ma ai ɗan unguwar nann ne kinga gidansu can? Laɗifa ta ce "Au shi ƙaryar tashima har a unguwarsu yakeyi? Yusra ta ce "Tom kindai gani.

Ajiyar zuciya LaÉ—ifa ta sauke tana tinanin cewar to idan taje gurinsa me zatace masa! Nan take ta kawar da wannan tunanin ta shirya domin zuwa gurin Umar. Tayi niyar zuwa a yau amma ta bari sai gobe.

*SALIS* yakira number Nana a karo na babu a dadi yana son sanar mata dacewar bazai samu damar zuwaba sai da yamma, amma ba'a É—auka, hakanne yasa hankalin sa ya kasa kwanciya, kuma ga yasan A.J baya gari, tin jiya Hajiya Babba ta kirashi tace masa zasu kwana a can sai yau zasu dawo, hakanne yasa Salis ya nufi gidan su Nana, domin yasan Nana bata barin waya da nisa hk.

Abuɗe ya samu ƙofar gidan, hakanne yasa ya samu yaro ya tura ya kira masa Nana, aikuwa yaron ya ce "Wasu sojoji da ƴan sandane suka zo ɗazunnan suka kwashe su itada innar su, kuma sunada yawa. Ganin Salis bai fahimci abunda yaron kecewa bane yasa ya ƙarasa gurinda yaga wasu samari na zaune. Tambayar su yayi gameda abinda yaron ya ce. Aikuwa nan take suka sanar masa da komai. Cikin tashin hankali Salis ya tambaye su wani police station aka kaisu? Sukace walhi basu saniba. Haka Salis ya shiga bin duk wani police station da yasani amma ko ina yaje zancen ɗayane wato basu san inda a kakai suba. Yayi yawo a cikin Benue MKD amma bai samu gurin da a kakai suba, hakanne yasa ya dawo gida yana tinanin shin mesukayi haka harda sojoji!.

Washe gari laɗifa ta shirya izuwa gurin Umar. Dama ƙawarta Yusra sun daɗe da barin unguwar, hakanne yasa bata ma san inane a salin gidan ba. Bayan tazo unguwar ne ta kalli unguwar taga an sakeyin gine-gine, sai tarasa gane wannene gidan. Tana nan tsaye saiga wata rarinya kusan sa'ar ta zata huce. Laɗifa ta ce "Jimana yarinya?

Yarinyar ta kalleta ta ce "Wacce yarinya?

"Idan bakeba wacce agurin nann ko kina nufin keba yarinya bace?

Cikin jin haushin sunan da takirata dashi na yarinya tazo har gabanta ta ce "Kalleni nafi ƙarfin kikirani da yarinya walhi, domin na huce nann, duk abunda kike taƙama dashi inadashi sabada haka karki sake cemin yarinya.

Laɗifa ta buɗe baki da hanci tana kallon ƴar ƙaramar yarinyar da kecewa tanada komai. Ai kuwa ta ce "Ina komai ɗin yake anan kina tafiya kamar wata sabuwar kamu babu ko kintsi, hakanne kuma baza'a kiraki da yarinya ba?

Nan fa yarinyar ranta ya ɓaci ta ce "Uwarki ce mara kamun kai! Kalli irin shigar da ke jikinki ko gyale babu bare hujjabi wai a hakan ke musulmace! Kai Allah ya wadaran irinku da basa ɗaukar ADDINIMU da muhimmanci...ai bata rufe bakiba taji sauƙar tagwayan mari...

Jikake tass-tass. Itama zata rama Laɗifa ta riƙe mata hannu tana cewa "Idan kika sake wannan ƙazamin hannun naki suka taɓani sai kin gane Allah ɗaya ne. Aikuwa hankalin mutanan dake kusa da gurin ya dawo kansu ganin Hadiza riƙe da kumatu. Da mamaki suka nufo gurin ganin yau ansamu wacce tafi Hadiza rashin kunya harda marinta. Ai kuwa Hadiza ganin ƴan unguwar su sunga marin da a kamane yasa ranta ya ƙara ɓaci. Duk unguwarsu kowa tsoranta yakeyi daga maza har mata, batada kunya ko kaɗan ga rena na gaba da ita. Kafin laɗifa ta ankara taji sauƙar mari har biyu. Dai-dai mazan sun iso gurin. Nann fa faɗa ya ɓarke da kyar aka rabasu Hadiza sai zagin ta takeyi tana cemata karuwa.

Laɗifa kuwa ranta yayi mugun ɓaci, wani saurayi ne yazo yana tambayar ta meya haɗata da wannan mahaukaciyar? Laɗifa ta kasa magana sai jan nufashin ɓacin rai takeyi. Ana cikin haka ne Umar yazo gurin wanda shiɗin yayane ga Hadiz. aikuwa yana ganin laɗifa ya ganeta da sauri ya iso gurin da take ya ce "Amm umm, alamar dai yana son tuno sunan ta. Ai kuwa laɗifa na ganin sa taganeshi. Umar ya ce "Kaman nasanki? Amma maiya haɗaki da wannan yarinyar har kika biye mata kuna faɗa, ƙanwata ce batada kunya?

"Wai saboda na tambayeta shekenan zatamin rashin kunya!

Umar ya ce "Kidaina biyewa irin wannan yaran barinma ita da kowa yasanta a unguwar nann bata da kirki, nima yayanta bata barniba. Amma ina zakije? Cewar Umar?

Bata bashi amsaba, tsabar haushin abunda ya faru, kuma tayi alƙawarin saita ci uban wannan yarinya dukda kuwa ƙanwarsace. Haka ta shiga motar tamasa alamar ya shigo, ai kuwa ya shiga, suka bar unguwar.

Tun lokacin da tayi magana ya gane itace yarinyar da Samuel yake nema, amma bai gane itace ta masa wannan cin mutuncin ba domin kuwa abun ya É—an daÉ—e. A bakin titi ta tsaya sannan ta kalleshi ta ce "Ina fatan ka ganeni ko? Umar ya ce "Eh naganeki...kece ta club ko? LaÉ—ifa taji daÉ—in da bai tuna abun da tamasa ba.

Ya ce "Jiya munje domin biyanki kuÉ—inki amma bamu haÉ—uba lfy kuwa?

"No jiya banje ba... sannan wani kuÉ—i? Dama ni auro na baku?

"A'a Samuel ne yace muje ya biyaki.

"Samuel Samuel, ta mai-maita sunan a ranta sau biyu sannan tace "Please yanzu ina zan ganshi?

Umar ya ce "yanzu dai bazaku haɗuba saboda baya gari, amma zan baki number sa, kuma kema kibani taki number zan masa bayani dama shima nemanki ya keyi. ( Yamata ƙaryar cewar yayi satane😆)

Cikin jin daɗi ta bashi number ta sannan Itama ta amshi ta Samuel ɗin da kuma ta Umar ɗin. Aikuwa ta zaro kuɗi ta bashi haɗida masa godiya sannan tayi gida. Yayinda Umar ya girgiza kai alamar dai da wani abu a ƙasa.

*HAJIYA BABBA.* *A.J*

Haka ta rabashi da komai na jikinsa ta cigaba da gudanar da sunna. Tabbas Hajiya Babba tayi mutuƙar ƙoƙari wajan danne zuciyarta daga aikata zina. Hajiya Babba tanada mutuƙar juriya domin kuwa ita ɗin ta daban ce acikin mata. Abun da yafaru da ita da AJ kenann a wannan daran.
Chapter 15 · 0% Book details