← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 67

Sashe 28

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa miƙewa yayi a palorn harda Samuel domin shima soyake yau saiga waye wannan AJ. Daddy ya kalli Sarah ya nuna Aj ya ce "Shine AJ? Sarah da hawaye suka wanke mata ido ta kalli AJ wanda kana ganin sa kasan yasha kuka. Suna haɗa ido gabansu ya faɗa a tare alokaci ɗaya. Dukda irin halin damuwar da AJ keciki bai hana ya ƙurawa Sarah idoba, yana aiyana kodai rashi lafiya tayi. Tana son tace eh shine AJ amma tana tsoro. Aj kuwa kallon Daddy da mommy yayi na lokaci ɗaya ya ɗauke ido, domin kuwa yasan yau ya shiga hannun manyan arna. SAMUEL kuwa kallon AJ yakeyi cikin mamaki ya ce "Ashema yarone ƙarami, domin kuwa Samuel ɗin ya girmeshi, tawani gurin kuma kallo ɗaya zaka masa kagane shiɗin yana cikin hutu, domin yanayinsa ga kuma farar fatarsa da tasha hutu na kwana biyar a Morocco, haka dai Samuel yaketa bin Aj da kallon tausayi.

Bata ankaraba sai ji tayi an zabga mata bari wanda yasa ta rikice ta kurma wani uban ihuu, tana faɗuwa agurin riƙe da kuncinta. Daddy ya ƙara mai-maita tambarsa a karo na biyu. Ai kuwa da sauri ta ce "Shine!. Daddy ya kalli AJ a karona babu adaddi, sai yasa hannu a aljihu ya jiro waya. Kira ɗaya ka ɗaga ya ce "Asaki wannan matan guda biyu sannan kuhaɗa musu da duka. Yana kashewa ya ƙara kiran wani shima ya ce "Ya saki wannan yaron, amma shi kar a haɗa da duka.

Yana gamawa ya kalli matarsa cikin ɗacin rai ya ce "Luk at her? Kalli yaronda yake saka yarinyata sata? Wannan yaron, yafaɗa yana yin kan Aj ya shaƙeshi har saida taga ya fara kururuwa kafin ya sakeshi, aikuwa nann take Sarah ta fashe da kuka domin kuwa ta tsorata sosai da shaƙunda aka masa. Daddy ya kamo wuyan rigar AJ ya ce "Meye haɗinka da ƴata? Kai ɗan gidan uban waye a garinnani. Sannan kana musulmi meye haɗinka yarinyata, AJ ya ce "Ina Innah ta da ƙanwata? Yayi maganar cikin sadaƙarwa. Jin haka yasa Daddy kwasheshi ya kalli sojan ya mai a lama da ido, aikuwa ya jashi yabar palorn dashi yayinda Sarah ta kamo ƙafafun Aj tana kuka. Ganin haka yasa Daddy yin bool da ita harsaida ta daki kujerarr palorn aikuwa take goshinta ya fashe amma bata tsaya bi ta kansa taƙara kamo ƙafafun Aj, Daddy ya riƙeta da ƙarfi harsaida aka fita dashi kafin ya juyo da ita ya kwaɗa mata maruka har guda huɗu, ya turata cikin ɗakin da suka fito itada Samuel, sannan ya sa ki ya rufeta. Samuel kuwa na ganin haka ya bar gurin cikin sauri, yana jin tausayi Aj domin yasan yau sai aj ya kwammaci baisan Sarah a rayuwasaba. Itama kanta saran sanin gurinda za'a kai aj ɗin ne yasa ta wannan kukan da riƙe ƙafafunsa. Momy kuwa tayi muwar tsayar agurin tsabar mamaki ganin Aj ɗin ɗan yaro, ita tayi tunani zata ganshi babba ne.

Ɓangaren su Innah da Nana kuwa, suna zaune kamar yanda tunda aka sake musu guri suke, Innah na kwance a kan cinyar Nana wanda kana kallon Innah sai gabanka yafaɗi, domin kuwa ta fita a haiyacinta, har wani ƙara tsofewa tayi. Buɗe ƙofar gurin akayi da sauri Nana ta ɗago kai ta kalli ɗan sanda da ke ɗauke da sanda a hannu. Shima kansa ganin irin halinda suke cikine yasa ya kasa dukansu ya shiga lallaɓasu kar wannan tsohuwar ta mutu a hannunsu. "Kutashi ku fit. shine abunda ya ce yana kallon Nana. Haka Nana ta ɗago Innah wacce ko buɗe ido batayi. Ita kanta nanar ba kwari garetaba, sai kawai ta shiga jan innar yayinda ƙadafunta ke jan ƙas. Saida suka fito waje tukun idon Nana ya raina fata domin kuwa ganin gurin da suke. Da kyar ta samu mai keke ya ɗauketa izuwa asibiti. Da sauri likitoci suka amshi Innah, yayinda ta ce da mai mashin ɗin bari ta bitu ya kaita gida ya dawo da ita sai ta bashi kuɗin.

Saida taga ɗakin da aka ajiye Inna kafin ta fito izuwa gurin mai keken. Unguwarsu ta faɗa masa ta ce ya kaita. Aƙofar gida ya ajiyeta ita kuwa tana sauƙa ta shige gida domin bataso wanda ya santa ya ganta a yanda take. Gurin da ta ajiye kuɗe taje ta ɗauko dubu ɗaya ta fito ta tsaya daga ciki ta meƙawa mai mashin ɗin, bata ko tsaya ba ta koma ciki da sauri. Tana shiga ɗakinta ta faɗi a ƙasa ta fashe da kuka tana kiran sunan yaya yaya yaya! Wani ɗaci takeji tanajin ta tsani soja da ɗansada domin kuwa tasan basuyi komaiba yayantama tasan baiyi komaiba, tunowa da tayi da Innah sai ta miƙe ta rasa nema zatayi yanzu.

Tashi tayi ta ɗibi ruwa aranda ta shiga bayan gida tayi wanka, sosai ta wanke jikinta da har wani wari-wari takeyi, ta fito daga bayan gida ta zaɓi ɗaya daga cikin dogayan rigunann da Aj ya sayo musa ta saka, sannan ta shiga ɗan ƙaramin kicing ɗinsu ta ɗora ruwa domin samar musu abinci.......✍️

*PAGE.* 2️⃣3️⃣

.........Bayan ta kammala komaine ta zauna taci abincin sosai sannan ta shiga neman wayarta ganin lokaci na tafiyane yasa tabar neman wayar ta fito da kuɗin da AJ ya bata gaba ɗaya. Gaba ɗaya tasaka kuɗin ajaka sannan ta shiga ɗakin Innah itama ta ɗaukar mata doguwar riga guda ɗaya da kuma atamba da zani. Saida ta haɗa komai kafin ta tsaya ta ɗan gyara gidan sama-sama. Haka taci gaba dayin komai cikin juriya da jajircewa domin kuwa ita kanta tana buƙatar hutu. Kasan cewar basuda wani ɗan abunda zata zuba gaba ɗaya kayan nasu harda abincin ne yasa ta ɗauki ledar da AJ ya kawo musu kaya aciki tun wancan lokacin, gaba ɗaya ta zuba kayan aciki kafin ta koma ɗakin Innah domin ɗaukar wayar Innah. Dai-dai jikin ƙofar ɗakin Innah taga leda, tinda tashigo taga ledar amma batabi ta kantaba. Ɗauka tayi da sauri tana buɗewa, da sauri ta zuba kayan aƙasa cikin mamaki ta ce "Waye ya kawo! Sai kuma ta gyaɗa kai domin abinda zuciyarta tace mata.

Abubuwa ne aciki wanda ke nunida cewar kayan tsaraba ne aciki kala-kala...irinsu lemo ayaba biskit madaran ƙwankwani da dai sauran abubuwa harda kayan shayi. Cikin sauri ta ce "Kode yaya yana garine kokuma ya dawo! Kodai yasan abunda ke faruwa damune amma ya share! Kodai da gaske kuɗin yasata ya gudu yabarmu!?. Ta ce "No Yaya bazai iya ba. Take hawaye ya shiga zubo mata, ta miƙe tabar kayan a haka ta fita daga gidan tana kuka.

Farin hijjab ne ajikinta wanda ya rufe mata dukkan jikinta, tana tafiya kamar wacce bata son taka ƙasar. Kowa dake unguwar kallonta yakeyi cikin mamakin ganinta a unguwar, gashi anason yin gulma babu dama, domin kuwa Nana Bama kowane yasanta a unguwarba, ita kuwa batasan sunan kowa a unguwarba saide Kadija da ƴan gidansu. Haka dai takai har bakin titi ta tare me kike izuwa asibitin da Innah take.

*SALIS* *POV*

Koda Æ´an sandan suka sakeshi sai yazo gurinsu ya amshi wayarsa, yana dubawa yaga tarin miss call. Cikin mamaki yakebin numbar Hajiya dake nuni da cewar daga 9j take kiransa. Take ya danna numbar Hajiya Babba yana jin wani farincikin. Dai-dai lokacin da sojan yazo yace dasu Hajiya Babba sushoigo dai-dai wannan lokacin kiran Salis na shigowa wayar Hajiya Babba. Bayan ta É—aga ya ce "Hajiya yaushe kika dawo? Yayi tambayar cikin farin ciki, domin kuwa harga Allah yana son hajiya ta dawo domin asan abinyi. "Kana ina yanzu? Yaji muryar ta acikin kunnuwansa? "Gani a hanyar gida yanzu zan shigo. Hajiya ta ce "Ban gane ba? Salis da baisan cewar Hajiya taji labarinba ya ce "Yes Hajiya na É—an je wani gurine amma ganinan yanzu. Yana faÉ—a ya jashe waya yanufi gida cikin sauri. Ita kuwa Hajiya Babba tayi tunanin ko Salis É—in yana gudan Daniyel, amma hakan bazai hanata shigaba domin yau tanaso ayi komai a gaban yaransu, kowaji abunda yakesonji.

Bayan Hajiya Babba taji ya kashe wayar sai ta kalli laɗifa ta ce "Yau zan ƙarasa baku labarin tsakanin Daddinku da wannan mutumin. Laɗifa ta ce "to Hajiya mu koma gida mn sai muyi labarin agida? Hajiya ta ce "no a gaban sa za'ayi domin kusan asalinsa. Ɗan gajeran message ta turawa Salis kafin suka shiga gidan bayan manya-manyan sojojin sun wangale musu ƙaton get ɗin gidan.

Saida yaje ƙofar get ɗin gidan nasu kafin ya ji shigowar message, yana dubawa ya tsaya yaci gaba da karan tawa, afili ya ce "Gidansa kuma! Why? Hajiya. Ya ɗauki a ƙalla awa ɗaya acikin gidan kafin ya shirya yafito cikin shigarsa ta mlm bahaushe. Ɗanyar shadda ce wacce taji aki ga hular kalar kayan, kana kallon Salis sai ka ƙara tsabar yanda shiga tayi dai-dai da surar da Allah ya bashi. Wata motar ya ɗauka yana sauri domin yasan ya makara tundade minty talatin ta bashi.

Saida yabi ta police station ɗin da aka kulleshi akan ko wani zai sanar dashi inane a ka kai su Nana, amma kowa na tsoro. Sai kawai yabi ta unguwar su Nana ɗin, yana zuwa yaga gidan a ƙulle, da mamaki ya ce "To kodai shima aj ɗin ya dawone, aikuwa ya shiga kiran numbar Aj amma no amsa, numbar Nana kuma har yanzu bata shiga, haka yanufi gidan da zaije batare da yayiwa kowa magana a'unguwar ba.

Dai-dai Hajiya Babba ta saka ƙafarta gidan Comanda Daniyel sai taji wani mugun faɗuwar gaba haɗida jin ƙirjinta nayin wani zafi. Kallon gidan tayi sama da ƙasa kafin ta fara karanto duk addu'ar da tazo bakinta, amma tafi ambaton hazbinalhu wa'ni'imal wakil. Tabbas wannan faɗuwar gaban nata da wani abu da ya shafe ta a cikin gidannan.

*GIDAN SOJA*

Wanka yayi cikin sauri-sauri

, Haka yayi shigarƙananana kaya rigar adides, kallon kansa yayi da kyu yaga yanda ya rame, sai ya ɗauki ledan kuɗin da abokan nasa suka kawo ya fito da kuɗin ya ce "Waoo i love this baby girl so much. Cikin yaran su ya ce "Thanks laɗifa bari komai ya dai-daita zan huta dake kin haɗu sosai, yana kaiwa nann ya bar ɗakin izuwa kicing yana tunanin ƙanwar tasa ko ya zata kaya tsakanin Daddy da kuma aj ɗin.
Chapter 28 · 0% Book details