← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 67

Sashe 22

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdalha kuwa yana kashe wayar yayi hanyar fita ba tare da yayiwa kowa maganaba. Jin kiran da Momy kemasa ne yasa ya tsaya yana kallonta, kafin Mommy tayi magana ya ce "Momy bansan me zanceba ban saniba!, ni dai abun da nasani shine tabbas ana bibiyan rayuwana, amma koma waye zan gano!. Cikin ɓacin ran jin maganar da ya ke cewa mommy ta zabga masa mari ta ƙara masa sannan ta ce "Tsabar ka rainamu, ina ji yanzu kuna magana da Daddy ka kashe waya batare da kace komai ba. Nikuma ina maka magana kana fita yanzu kuma kana min wani zance saban. Shin da gaske kaine ka sace ta!? Mommy ta tambayeshi tama mai ƙara fashewa da wani kukan. Abdalha ya riƙe gurin da mommy ta mareshi yana jin abunda tinda yake Mommy da Daddy basu taɓa masaba amma a kan ta amma mareshi. Yanzuma shiru yayi domin kuwa tabbas baisan me zaiceba, abinda yasani shine ana bibiyar rayuwarsa....✍️

*
*PAGE* 1️⃣8️⃣ *Babu editing*

..........Cikin tsananin mamaki Abdalha yake kallon Mommy wacce ta ɗaga hannu ta mareshi a kan abunda batada tabbacin sa, ya kalleta cikin mmk ya ce "Momy ban saniba bansan komai ba wasune suka saceta amma ni bani bane pls Mommy ki yarda dani karki bari zuciyarki ta aminta da wannan zancen. Momy ta kalli ɗan nata cikin tausaya masa tace "Shin me ya kaika gurinta lokacin da abun zai faru? "Mommy bansan komaiba kamar yanda na sanar miki, kuma nuda kaina zan gano komai pls ki yarda dani. Yana gama faɗin haka yabaar gidan cikin tsananin mamaki abubuwan da ke faru kamar wani shirin Film. Lokacin da Abdalha ya isa ƙofar gidan nasu har police ɗin nan sun kama na kamawa sauran kuma sun gudu, kallon police guda biyu da ke jikin ƙofar gidan nasu yayi wanda a ka bari domin basu tsaro yayi, kallon su yayi cikin takaici domin kuwa kallo ɗaya ya musu ya gana ba musilmai bane, a zuciyarsa ya ce "Tabbas wannan shirine kuma zan kawo ƙarshensa yau. Police ɗin dake nufoshi ya ɗagawa hannu a lamar bayan tsaron nasa , amma police ɗin yace ai hakan umarnine dole sai yayi. Haka badan Abdalh yasoba suka shiga motar shida ɗan sandan suka fita.

Ɓangaran gidan su Zainab kuwa har yanzu babu labarinta, yayinda Isa ya dinnga yaɗa cewar Abdalha ne ya saceta kuma tabbas yanda labarin ke bazuwa idan kagani dole ka yarda. Ƴan gurgiyar Abdalh da sukaga abun ya fara yawa sai suma suka fara mayar da martani akan ai shi Abdalh baɗan bidi'a bane yana amfani da ilimin sa, saide kaga majalista ta samari daga hira sai zage-zage sai faɗa. Har takai ta kawo wasu daga ciki suna tono tsoffin asirin wata gurgiyar. Budurwa da saurayi aboki da aboki mata da miji, malami da ɗalibai, uba da ƴaƴansa, maƙofci da maƙofci, dukkan su mutuƙar ba kungiyar su ɗayaba to Tabbas sanadiyar wannan abun Kai ya ƙara rabuwa. Kai abundai ba'a cewa komai domin kuwa lamarin ya gawarta.

*SALIS LAÆŠIFA POB*

Cikin sauri kamar zata tashi sama tsabar ruɗewa ta banko ƙofar palorn tana ƙoƙarin haurawa sama, sai tayi ido biyu da Salis yana zagayawa a ɗakin cikin tashin hankali. Da gudu ta ƙaraso gurin da yake ta buɗe baki zatayi mgn, cikin harɗewar murya ya ce "Com com comand Comandar Daniel ne ya kullesu?. Ya ƙarasa maganar yana kallon laɗifa wacce Salis ɗin ya ƙara sakata a cikin duhu domin ita bata gane me yaceba, ta daiji yace Daniel amma fata fahimci gaban ba. Ta ce "Pls Yaya banji me kace ba, itama ta faɗa tana kallon cikin idonsa? Salis ya ce "Gajiya Babba dole ta dawo yau ɗinnan domin kuwa a kawai matsala?.

LaÉ—ifa ta ce "Pls Yaya sanar dani abunda ke faruwa ban ganeba fa? Ni nashigo da maganar Comandar kuma kaima naji kana min shin wani abun ya haÉ—oka dashi ne?

Cikin sauri Salis ya fasa danna kiran numbar Hajiya Babba ya dawo da kallonsa izuwa gurin LaÉ—ifa ya ce "Me zaki sanar min akan Comandar É—in?

Da sauri Laɗifa ta ce "Shine baban wannan yaron da nace maka inaso wannan Kristen ɗin..."Ai tin kafin ta ƙarasa Salis ya ce "No no no, ya miƙe tsaye yana kallonta wacce itama ta miƙe tsaye ya ce "Bakida hankaline kin matan waye Daniel da har zakije kifara soyayya da yaronsa ko? Kafin ya samu matsayin Comanda ma ya muka ƙare dashi bare yanzu...damade baki sanarwa da yaron cewar kina sonsaba? Ya tambayeta yana son yaji tace masa bata sanarba.

Cikin kuka ta ce "Wallhi Bro bansan shine babansa bane ban saniba, ta faɗa tana ƙara fashewa da wani sabon kukan.

Salis ya ce "kin faÉ—a masa?

Ta ce "Eh harma mun zama...

Da sauri Salis ya ce "Yanzu haka shine ya kulle yarinyar da nakeson aura tare da innarta basu san hawaba bare sauƙa, kuma ya ce bazaibada Berlin ɗinsuba sai yaga wanda yake nema.

Ta ce "Pls bro mukira Hajiya Babba? Ai kuwa take suka shiga kiran Hajiya Babba amma bata shiga. Itama laÉ—ifa ta shiga kiranta da wayarta, amma duk É—aya.

Salis ya kalli laɗifa ya ce "Akwai matsala domin kuwa Hajiya bata ƙasar nannn tin jiya number ta bata shiga. Laɗifa ta ce "To ina yaron da suka tafi tare? Sai a lokaci Salis ya tuna da cewar a shefa Hajiya tare da A.J suka tafi, sai kawai ya nemo numbar AJ ɗin domin kuwa yasan tunda ita bata ƙasar to shi yana 9j. Da sauri ya shiga kiran numbar amma shima yaji bata shiga. Kallon juna sukayi suna mamaki, laɗifa ta ce "To ko zamuje gidan su yaron mu tambayeshi da gaske Hajiya tabar 9j?

Cikin ɓacin rai Salis ya ce "Dan Allah malama sunansa AJ ba yaroba! Ko bai girmeki bane? Kuma bari kiji yarinyar da zan aura ɗin ƙanwarsa ce, kuma itace a ka rufe a police station itada innar su, kuma Comandar ne sannan kuma AJ ɗin yake jira ya dawo kafin ya sakesu.

Wani abu taji shuuu ya shiga kunnenta kafin taji alamar iska, ta ce "Ok sai yanzu na gane abunda ya sakaka a tashin hankali a shedai saboda soyayya ne ba dan abunda wancen tsohon arnan ya manaba. To walhi bazamu taɓa haɗa jini da wannan matsiyatan ba, har kake cewa wai ita zaka aura to dan ubanta tazo gidan mu gani.

Cikin kwantar da hankali ya ce "Yanzu dai ni bama wannan ba, yanzu meye abunyi? Ta ce "kawai ka manta da su domin banaso mu ƙara shiga sabgar wannan ƙaton arnan. Abunda Salis bai saniba shine, laɗifa ta gama haɗa kuɗin da zata ƙwato Samuel domin kuwa ta so ta sanar dashi gaskiya amma jin shina Musa soyayya ce ta kaishi sai kawai tayi fuska a kan kowa yaji da damuwarsa abunda Basu samaba.

Salis ya ce "Ban gane na barsuba! Kinaji nace matar da zan aura amma kice wai na barta? Jin tambayar da tamasa yasa ya shiga tunani, tabbas abunda ya kamata ya fara sani kenan Amma ya manta.

"Wai ma me sukayi har ya kaisu police station suna mata? kidan yaga su É—in musulmai ne ba addininsu É—ayaba. SALIS ya ce "No suma basu san me sukayiba domin bai sanar musuba, amma dolema na sani yau É—in nan, ya kamata muga AJ. It's dai laÉ—ifa waya ta É—auka tana kiran Umar domin ita dai bazataje gidan su Sameul É—in ba.

*GIDAN SOJA*

Da sauri Daddy ya shigo palorn yana kiran Mommy Eliza! Eliza! Kai da jin irin kiran kasan cikin ɓacin rai yake, itama Momy ɗin da sauri ta fito daga ɗakin tana cewa "I'm coming sir. Tin kafin ta ƙaraso ya ce "Zuwa gobe naba yaranki a kan su kawo min kuɗaɗena kokuma namu hukuncin da babu wanda zai yarda cewar nune ubansu, barinma wacce muna fukar da ta ɗauki kuɗinan tana kaiwa musulmi wanda nakejin da nayi ido biyu da su ƙwara a ce bani da idon, bazan taɓa ƙwanar mutanananba na tsanesu , Walhi inajin idan na kama wannan yaron AJ to tabbas zan iya kasheshi. Cikin tsananin ƙiyayar da sukewa musulmai itama mommy ta ce "Ni sonake ka kaini police station ɗin da kakai ƴan uwansa na fara zuwa naci mutuncinsu tukunna Amma kace wai ba hakaba.

Daddy ya ce "Yanzu haka daga chan nake, nasa an ci ubansu sannan ance wai ana kawo musu abinci, nasa an kori police É—in da yabada umarnin shiga da abincin, yanzu haka nasa wani mai kula dasu É—in kuma nace masa duk wanda yazo gurinsu ya barshi ya shiga amma ya kirani. Cikin jin daÉ—i Mommy ta ce "God! Idan ma yaronnane yake kai musu abincin ai zamu ganeshi. Daddy ya ce "Nima hk nake tunani kodai yaronne?.

Samuel da Sarah kuwa duk abunda akeyi suna ji. Kuka Sarah takeyi tana cewar Pls Samuel call AJ please. Shima kansa Samuel É—in yana son yaga waye wannan AJ É—in, sannan shima yana kiran numbar Umar amma no amsar.

*HAJIYA BABBA AJ POB*

Tafiya sukeyi a bakin wani ƙaton hotel ɗin da suka kama a ƙasar morocco mai ɗauke da sunan *HALIDYS HOTEL* Kusan duk wanda ya gansu saiya ƙara kallonsu domin kuwa kana ganin su kaga uwa da ɗanta, amma yanda suke a manne da junane zaisa ka ƙara kallonsu domin kuwa sunyi kama da masoya, bakin ƙofar hotel ɗin suka tsaya kafin Hajiya Babba ta kalleshi cike da tsananin sha'awar sa da kullum take zamar mata sabuwa da kuma yanda yake iya jure buƙatarta fiye da sauran mazan da ta zauna dasu. Kallon fuskarsa tayi wacce kana gani kasan yana cikin damuwa sosai ta ce "Aj angon Hajiya Babba inji yaranta! Yanzu idan muka koma Nijeriya yazamuyi da su Salis da laɗifa? Domin fa ni gaskiya ko mun koma 9j to Muna tare dan bazan iya nisa dakaiba.

Idan bai mantaba yau suke kwana huɗu kenan da zuwa Morocco sannan kuma yana jin cewar daga wannan kwana baƙwaɗin tofa komai zaifaru bazai ƙara kwana batare da yaga Nana da Innah ba harma da Sarah waccce yanzu yake yawan mafarkin tana cikin wani hali na taimakonta. Ya ce "Ai bamuyi cewa zamu zauna a gidankiba idan mukakoma Naiger, kodan saboda yaranki, saboda haka a gidanmu zan zauna.
Chapter 22 · 0% Book details