← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 67

Sashe 24

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke dukkanin su a gaban Shrk Kabir kabuga. Abdllah Sadiya Nusaiba Maryam Nura sai Mommy. Cikin yanayin da yake nuni da cewa babu wasa ya kallesu ya ce "Abdalha kabani mamaki! Dama ashe a kwai wani abu tsaka ka da wannan ƴar iskar yarinyar wacce bata samu tarbiyaba, wacce bata san girman manyaba! Waccce ke rwwa da waƙa a gaban maza! Wacce take aikata saɓo ta sigar isgilanci, har ina kiranka kana katsemin waya a kan karna maka maganar ta ko? To naji kuma ka saurareni da kunnab basirar ka. Kaman yanda kasani ni dai bana amfani da duk wani abunda Allah da manzan sa basuceba, kuma duk inda ka je ka kaimusu yarinya to ina mai sanar dake yan ɗinnan kaje ka dawo musu da yarinya? Kuma nagaji da zagin da mutane suke maka akan zaman ka haka, idan kai abun bai damunka kaida ma haifiyar taka to ni yana damuna, saboda haka kaje gidan mlm Aliyu ka ga ƴarsa idan tayi ko batama mun gama mgn da mahaifinta mun tsayar da rana, idan kaga dama kaje ka ganta idan ma bakaga damaba ruwanka. Kowa shiru yayi yana sauraron Daddy domin kuwa abun ya basu mamaki, kenan daddy ma ya yarda cewar mommy da Sadiya suna bin Daddy da kallo ganin zai bar ɗakin.

Tinda take Tare da mai gidan nata bata taɓa tsayawa tayi masa magana cikin zafiba, dukda bata son wannan ƙiyayar da yake nunawa ga abokan takun saƙar dasu. ta ce "Kabiru? ba daddy ba, ba kuma Maryam ba ba kuma Abdalha ba hatta Nura dake ɗan yaro saida ya kalli Mommy jin yanda ta kira sunan Daddy. Taci gaba da cewa...

"Na gaji! Walhi na gaji da wannan baƙin ƙiyayar da kunewa junanku. Muna Musulmai ƴan uwa ɗaya Amma duk kun raba kahunanku, wasu suna yiwa wasu kallon kafurai, har takai ta kawo yanzu kana nema kayiwa yaronka aure da ƴar gidan mutumin da kowa yasan halin matarsa a garinnin. ADDININMU ɗaya al'adar mu ɗaya yaranmu ɗaya Allah mu ɗaya, annabinmu ɗaya, shin me mukeso muzama!?...

Yanzu kazo ka hau kan maganar da kaji anayi a gari a kan shine ya saceta, baka tsaya kaji daga gareshiba ka yanke hukunci, shin hakan..."Ya isa haka ya isa . Cewar Daddy Yana ɗaga mata hannu ransa a mugun ɓace.

Ya ce "Badai kince kin gajiba, to ga hanya nann daga ke har ɗan naki ai ban ɗaurekuba, kunada damar da zakuje duk inda kukikeso a cikin ƙasar nann. Yana kaiwa nann ya ce "Indai a kan su kike zance to damar kice. Ya juya yabar gidan gaba ɗaya.

Gaban Mommy ne ya faɗi, yayinda Abdalh ya ɗago ya kalli Mommy ya kalli daddy, Sadiya ma kallon daddy tayi tana riƙe ƙurji. Abdalha ya ce "Dan Allah Mommy kibar wannan zance kar a je wani abu ya faru, ina dai nune zanyi duk abunda yakeso, badai aure bane zanyi. Kuma zan fito da Zainab. Cikin mamaki suka kalleshi har suna haɗa baki gurin cewar dama kaine ka saceta ɗin? Mommy da sauran yaranta suka haɗa baki. Abdalha ya ce "Eh nine kuma kamar yanda ya ce yau zan fito da ita, amma dan Allah Mommy ku fahimcen... "Kafin ya ƙarasa Mommy ta fashe da kuka....📝

*
*PAGE.* 2️⃣0️⃣

.........Cikin mamaki suke kallon juna yayin da Comandar Daniyel ke bin Salis da wani irin kallon tsana yana nunashi da hannu. Cikin tsoro da fargaba Salis ke kallon sa yana jin tamkar a ce mafarki yakeyi ba gaske bane. Da sauri Comandar Daniyel ya kamo hannun Salis cikin tsanin ɓacin rai da ƙiyayar da ke fitowa daga fuskarsa cikin harshin English ya ce "Waye kai? Yayi tambar cikin rashin mutunci kai ka rantse da Allah baisan waye Salis ɗinba. Cikin mamaki Salis ya ɗago kansa ya kalleshi sai kuma ya sun kuyar da kansa ƙasa bai iya magana ba. Ganin haka yasa Comandar Daniyel cewa "Wato bayan duk abunda ya faru tsakanin mu daku saida kuka sake shigowa rayuwarmu ko? Wai ku meyasa musilman nan bakuda tunanine, Walhi na tsaneku bazan taɓa sonkuba, bana kwanarku. Sai kuma yayi shiru ya kalli Salis ɗin ya ce...

"Waye AJ? Kuma me nene haɗinku da shi? Cikin tsananin ɓacin rai Salis ya ce "Abokinane kuma bansan ina yake ba a halin yanzu. Cikin jin haushi ya ce "To idan har kuna son fita daga Hannuna to sai kun kawo min shi kuma yau ɗin nan ya faɗa yana karewa Salis ɗin ido. Salis ya ce "Pls wai me Aj ɗin yayi? "Wani wawan mari yaji ya sauƙa daga gefen daman sa wanda kafin ya an kara an sake ƙara masa.

Cikin tsananin ɓacin rai ya ce "Ina AJ na tambayeka ba wai nace kaima ka tam bayeniba, kasan waye Ni kuma kasan abunda zan iya akan duk wani musulmi... Waima ba ubanku yayi muku iyaka da niba!? Bashi da kansa yace babuni babukuba? Akan wannan addinin naku addinin da yace yafi masa wanda ya tashi yaganshi a cikiba. To Walhi na tsaneku daga ku har duk zuri'ar ku, kuma Walhi in dai baku fito da wannan yaron ba kaima sai na ɓatar dakai baza'a sake ganin kaba har gaba da abada. Yana gamawa ya bar gurin ya shiga motarsa sauran sojojin suka take masa baya suka bar Salis a gurin. Daniyel yana zuwa gida ya tararr da wani sabon tashin hankalin.

**HAJIYA BABBA*AJ*

Zaune take tana rangaɗa kwalliya yayinda shi kuwa uban gaiyar ke tsaye yana bata amsar ta bayar da ta ke masa. "Nima yau gaba ɗaya bana jin daɗin jikina sosai sai naji gabana na faɗuwa wani lokaci. AJ ya ce "Nima har zuwa yanzu ban dai jin hakaba amma in Sha Allah komai lafiya. Ta ce "To amin Allah yasa hakanne, amma dai yau inason muyi waya da su Salis ko hankalina zai kwanta. AJ ya ce "Eh to hakanma dai-dai ne. Take ta ciro waya ta kira laɗifa, ai kuwa kira ɗaya ta ɗaga haɗi da cewa "laɗifa lafiya...kafin ta ƙara da laɗifa ta ce "Hajiya ina kika je ne, ta faɗa kamar tayi kuka. Saida hajiya Babba ta sauke a jiyar zuciya kafin ta ce "Laɗifa fatan dai kuna lfy ko? Cikin muryar shaƙwaɓa ta ce "Dan Allah Hajiya ki dawo Walhi min yi kewarki Pls and pls dan Allha mun gaji, waima kuna inane? number ki bata shiga tun lokacin da kika tafi. Hajiya ta ce "Ina lafiya very soon zaku ganni..."Waima to Hajiya inane kikaje? Bakince Abuja zakujeba wai ma dan Allah yanzu kina ina? Cikin son kawar da zancen Hajiya ta ce "Ina Salis? Dama de yana zuwa aikin bai tsaya wasa ba? Cikin ƙwantar da hankali ta ce....

"Hajiya ai Salis ya zama ɗan soyayya, domin kuwa yasa rayuwarsa a cikin damuwar da tafi ƙarfinsa. Cikin sauri ta ce "Ban gane ba? Wacce irin matsala? Laɗifa ta ce "Yanzu haka yana hannun Daniyel... "zumbur Hajiya Babba ta miƙe tsaye haɗi da cewa "Wani Daniyel? Laɗifa da take jin ita ai hakan shine samuwar muradinta ta ce "Comandar Daniyel dai Daddy brother. Cikin wani tashin hankali Hajiya Babba ta ce "No no karna ƙara jin haka daga bakinki, Walhi ƙarya yakeyi bai isa a karo na biyu yaci mutuncina na barshiba. Cikin Muryar da tasa ita kanta laɗifar tsorata Hajiya Babba ta ce "Menene ya haɗasu? Shi Salis baisan waye Comanda Daniyel bane, kodai bashi da hankaline baisan me yakeyiba kodai ya manta da abunda Daddy yace muku ne? Laɗifa ta ce "Haba Hajiya wannan fa ba wani abun tashin hankali bane, ai shima Comandar Daniyel ɗin ai ya isa da mu...."Ya isa da uwarki nace ya isa da uwarki! Walhi laɗifa kikiyayeni banza mara mutunci ke idan har kinada hankalima har zaki ƙara kallon wannan ƙatin arnan da idon mutunci, mutumin da ya kasha ɗan uwansa saboda ya bar addinin ƙarya izuwa na Gaskiya, to Walhi ki shiga hankalinki, kuma ina hanyar dawowa gobe gobe in Sha Allah!, Wlhi wannan karan sai yasan dadayanzu ba ɗaya bane,.

Tana gama wayar ta kashi tana haɗa wani uban zufa, kallon wayar tata tayi ta danna kiran numbar Salis amma bata shiga. Kallon AJ tayi tace gobe zamu koma 9j. AJ tin lokacin da Hajiya Babba take yin wayar ya nutsu yana jin me take cewa. Lokacin da yaji sunan Comandar Daniyel sai yaji kamar yasan mai wannan sunan amma ya kasa tunawa, yana da niyar idan tagama shima yayi waya da Innah ko Nana kokuma Sarah wacce izuwa yanzu kullum sai yayi mafarkin ta. Amma yanda yaganta cikin ɓacin rai yasa ya fasa tambayarta. Cikin wani murya ta ce "Walhi wannan mutumin sai yagane cewar yanzu bada bane, da ba dan yamma tayiba da yau zamu tafi, bazan barshiba Walhi. Shidai sai kallonta ya keyi yana jin shi a wani yanayi, shin murna zaiyi kodai baƙin ciki, yanzu kenan idan sun koma sai sunyi wata biyar ɗin kafin yaci kuɗin! (Kai AJ sarkin son kuɗi) afili ya ce "Hajiya mubari mu kammala sati biyun mn kinga ai komai zaifi tafiya saiti ko? Cikin tsananin fushi da bai taɓa gani a fuskartaba ta ce "Kasan wacce masiface ta tasomin a gida!? Kasan me yake shirin faruwa? To gobe zamu tafi bazan iya zamaba. Tana faɗa ta shiga ɗaki ta ciro masa wayarsa ta bashi tace ga wayarka nann zaka iya kiran kowa. Ganin haka yasa AJ yin shuru yana buɗe wayar yasa sabon layin nasa na wannan ƙasar kafin ya shiga kiran numbar Nana.

*ABDALHA POV*
Chapter 24 · 0% Book details