← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 67

Sashe 56

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da a suba AJ ya tashi yayi wanka ya shiga tunanin rayuwarsa, haka kawai yaji gabansa na faɗuwa idan ya tuno da mahaifinsa , sai kuma ya kama hawaye yana jin cewar akan Nana da Innah zai iya aikata komai, domin yanzu sune komai nasa, yana jin ba zai barsu a cikin wani hali ba mutuƙar yana raye, zai zauna dasu har gaba da abada, yana son ƙanwarsa da kakasarsa sannan ba zai taɓa yarda susan auran da yayi ba insha Allahu! Yana cikin haka a ka kira sallah , saida yabi ta dakin su Innah ya tashesu sannan ya fita Masallaci. Bai dawoba saida gari yayi haske, yana shigowa ya tarar Nana tana haɗa musu abin kari a gindin murhu. Kallon ta ya kayi cikin dariya ya ce "Daga yanzu dai kin huta da wannan banzan itacen mai sakaki hawaye ko?

"Da murmushi ta ɗago ta kalleshi ta ce "Wallhi yaya kamar kasan na gaji da shi Allah. Ya ce "Ai amma gama daga yau sai dai muma mu koma ɓangaren gass Allah yasa dai kin iya amfani dashi domin nasan Innah ba iyawa tayi ba? "Kai yaya gass ɗinne kuma kake cewa ban iya amfani da shiba?

Ya ce "Idan kin gama ki taso inna zanyi wanka kafin lokacin? Ganin har ta gama Innah bata tashi bane yasa itama ta je tayi wanka sannan ta je É—akin AJ ta tasoshi wanda shima barcin ya É—auke shi.

Bayan yazo gurin da suke cin abuncinne baiga Innah ba ya ce "Innah fa? "Tana barci bari na tasota. Tana faÉ—a tabar gurin daidai shikuma kiran ya shigo wayarsa.

"Ganin sunan Sarah ne yasa gabansa faÉ—uwa, har ya fara tunani sai kuma ya tuna ai yayi Welcome back.

"Salamu'alaikum" ya faÉ—a gabansa na cigaba da faÉ—uwa. "A a a Aj? Sarah ta faÉ—a cikin kuka. "Cikin rainin hankali ya ce "Please waye a layi?

"Sarah ce" Ta faÉ—a tana danne kukanta.

"Wa cece Sarah? Kuma daga ina?

"AJ nicefa Sarah zaka ce ka manta da nu n"....kafin ta ƙarasa ya ya ce "Please is ron Number . Yana faɗa ya katse wayar yana sakin dariya. Kafin ya ajiye wayar yaji muryar Nana ta kwala wani uban ihuuu! Tana kiran sunan sa.

Da gudu ya shiga ɗakin innar ya ganta a kan daddumar da tayi Sallah a kwance idanunta sun ƙafe ga carbin hannunta shima ya sake ya faɗi. Kallonta ya keyi yana kallon Nana da take ta ihuuu tana jijjiga innar. Da ƙarfi ya ce "Innah!!! Ya faɗa yana juyata sai ta sake jiki alamar ba rai a tare da ita. Lokaci ɗaya ya gane cewar Innah tayi tafiyar da ba dawowa. Nana ta ce "Yaya maiya faru? "Innah ta ra ta ta ta rasu! Ya ƙarasa yana fashewa da wani irin kuka yana dukan kasan ......📝

*Hammm* *to fa!*

*Comments É—inku shine abun alfaharina*

*S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*

*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*

*PAGE4️⃣2️⃣*
........"No Yaya a'a Innah bata mutuba ka daina faɗa dan Allah bana son ji...Innah ki tashi dan Allah ki tashi bana son wannan wasan Innah taaaaaa!!!. Nana ta ƙarasa tana ƙara ruƙo hijabin Innar. Kuka take yi sosai AJ ma kuka yake yi yana riƙe da Nana wacce har yanzu kiran sunan Innah take yi. Cikin kuka shima ya fara cewa "Wallahi Innah na daina aikata komai kuma zan sanar miki da gaskiya bana son kuɗin da gidan dan Allah ki tashi. Tabbas dukkan wani mairai mamaci ne, haƙiƙa duk wata rai zata ɗan-ɗani zafin mutuwa, ka na taka Allah na nasa kuma na Allah shine daidai, haƙiƙa rayuwa babu tabbas duk yanda ka kai da lafiya ko ƙarfi ko arziƙi ko mulki ko... ko... ko... ko... ko...koma mai nene to tabbas sai ka tafi, da lafiya ko babu, kana zaune cikin iyalanka ko kana kan hanyar tafiya, kana aikata alfasha ko kana aikata abun kirki, ita dai mutuwa bata jira.(Allah kasa mucika da kalmar La'i'la'ha'illala Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama.)

Haka suna kallo a ka sallaci Innah a ka ɗauke ta izuwa gidanta na gaskiya. Ba shakka Innah tayi jama'a, ƙofar gidannasu cike yake dam da bayin Allah, cikin gida kuwa matan Anguwa da sauran da suka samu labarin mutuwar duk sune aciki. Nana kuwa har lokacin kuka take yi, babu irin rarrashin da Kadija batayiba amma sai kiran sunan Innah takeyi tana kuka. AJ ma kana kallonsa saika tausaya masa, domin ya dawo kamar wani kurma sai kallo da ido. Matar kawunsu da yaranta da ya gujesu a baya yanzu sune a zaune a gidan , kawun nasa ma shine mai riƙe hannunsa izuwa mƙabarta.

Saida kowa ya watse a ka barshi shi kaɗai a maƙabartar sannan ya fara addu'o'i yana yi yana zubar da hawaye yana faɗar laifukan da ya aikata Mata. Ya kai a'wa guda a gurin kafin ya miƙe zai tafi sai sukayi ido biyu da Salis a tsaye a gurin yana kallonsa shima idonsa ya ciko da ruwan hawaye. Kallo ɗaya AJ ya masa ya kawar da kansa ya kama hanyar tafiya yana jin zuciyarsa na masa zafi. Shima Salis bai ce masa komaiba yabi bayansa. Suna isowa suka tarar har wasu sun fara tafiya, Kawu ne yake karɓar gaisuwa. Gurin da kawon yake suka zauna har yanzu babu wanda ya tam kawa juna. AJ ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kuka yana tuno maganganun da sukayi da Innah a daran jiya, a she wasiya take musu. Shi sai yanzu yake jin dama bai samu wannan kuɗin ba sun zauna a talaucinsu, inama lokacin da suke faɗa da Salis da tamai magana yaji, da ba'a kaita asbiti ba da yanzu haka suna cikin sabon gidansu! Inama inama inama.

Haka har akayi kwana bakwai AJ bai ce da kowa komaiba harda kawunsu da Salis da Muhammad wanda kullum sai sunzo gurin, abincin da a ke ci a zaman makoki ma duk Salis ne ya ɗauki nauyi, shi dai AJ baisan waye mai bada abincin ba. Kawu da matarsa da yaransa biyu duk Mata suma sun dawo gidan kafin komai ya kammala. Kasancewar ba komai a gidan ne yasa kawun yasa matarsa ta ɗebo wasu kayan nasu irin tukunya da dai duk abin buƙata, haka a kaci gaba da zaman makokin Innah har a Kayi ba kwai. Daga nan ne a ka fara watsewa kowa na komawa mahallinsa.

*BAYAN KWANA GOMA SHA BIYU DA RASUWAR INNAH*

What!!! Ban gane ba? Mai kake nufi da haka? Cewar Kawu yana kallon AJ cikin tashin hankali da ruɗani. Itama Nana kallonsa tayi tana girgiza kai batare da ta iya magana ba. AJ yace "Eh Kawu da gaske nake na yi aure kuma auran ma na jari ko nace auran kuɗi, auran da Addinimu bai yarda da irinsaba, auran da yanzu haka shine ya sani a cikin da na sani auran ta kaici auran kwaɗayi auran nadama. Ya ƙara sa yana sakin kukan da ki ta damun zuciyarsa.

"Wai Abdul duk mutuwar Innar ce tasa ka koma mahaukaci ko dai yaya? Kazo kanata wasu zantukan da ba kan gado. "Lafiya ta lau Kawu, inada hankalina nasan mai nakeyi. "Cikin dashesshiyar muryarta ta ce "Yaya mai kake cewa ne? Ban fahimtaba Please?

Kuka ya keyi sosai ya fara magana yace ""Nayi aure nayi aure saboda kuɗi saboda Innah da Nana su ji daɗin rayuwa, wallahi badan kaina nayiba amma yanzu na gwammaci da banyi wannan auranba, sannan na rasa wazan aura sai sa'ar mahaifiyata, uwar abokina wanda shine ya sa na fara ganinn kaina a haka, yamin rana nikuma na masa dare daran ma mai mugun duhu. Nan take ya kwashe komai ya sanar musu bai ɓoye komai ba. Cikin sabon tashin hankali Nana ta ce "Whay wahy whay Yaya? Mahaifiyar Salis mai yasa kayi haka! Ka gama da rayuwarmu Yaya. Kawun ne ya kalli yanda suke kuka duk sun fita a cikin haiyacinsu ya ce "Yanzu ba kuka zakuyiba, ai kace kun rabu ko? AJ ya girgiza kai. Ya ce "To yanzu ku tashi muje gidan nasu domin sanin abunyi, dole ne sai mijinta yasan da wannan zancen saboda kar a je a aikata haramci.

Da sauri AJ ya ce "No bazan iya magana dashiba kunyar Salis nake ji na , ga babansa ga Sarah no bazan iya ba wallahi bazan iyaba. Saida sukayi da gaske kafin AJ ya bisu.

Ta kardun gidan da Hajiya Babba ta bashi da makullin motar ya haÉ—o ya tafi dasu. Saida sukazo bank ya tsayar da motarsa ya ce su jirashi. Duk kuÉ—in dake cikin account É—insa ya kwashe ganin kuÉ—aÉ—an sunyi yawane yasa ma'aikatan bank kin sukace saidai yazo da jaka, ya ce bashi da jaka. Dole a tasu suka zuba masa ya fito dasu yasa a matar suka kama hanya.

A gidan Malam Muhammad kuwa washe garin abunda ya faru dasu ne Salis da Muhammad sun shirya domin zuwa gidan su AJ a sanar da innarsa komai sai kuma suka riski rasuwar Innahr. Hakanne yasa suka fasa yin wannan maganar suka bari har sai yaran sun dawo haiyacin su. Shi kansa Salis da ya tsaya ya kalli lamarin sai ya godewa Allah da yasa aure sukayi ba abun kunya ba. Lokacin da suka dawo gida suka sanar wa da Hajiya Babba itama ta tausaya masa domin tasan yanda yakeson kakkar tasa da ƙan warsa. Sarah ko kuka takeyi wai a dole sai an kaita gurin AJ. Dama kuma ita da Samuel sunzo da batun suna son komawa Addininsu Muhammad. A ranar Muhammad da Salis harda Hajiya Babba sunyi godiya ga Allah, sannan sunce gurin shek Kabir kabuga zasu tafi dasu domin ƙarɓar Musuluncin. Dama ga batun auran yaran sa, sai kawai a yi komai a garin, yayi kewar malamin dama kuma yanaso yaje gurinsa, domin ba zai iya mantawa da shiba.

Muhammad da Hajiya Babba sun bari a kan sai sun dawo daga gurin Shek Kabir kafin su tun kari batun AJ. Yanzu dai ana gobe zasu tafi kenan.
Chapter 56 · 0% Book details