Sashe 45
Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tafiya yake cike da ɗinmun dana sani a cikin rayuwarsa, yanzu shi babban damuwarsa ta ya ya kuɗaɗensa zasu fito. Babu komai a hannunsa da ga shi sai kayan jikinsa wanda su ɗinma Usha ne ya ɗauko masa daga cikin kayansa, fuskarsa anyi bandeji ga gefen bakinsa shima a rufe, gaba ɗaya fuskarsa a gumbure take. Kana kallon AJ kasan baya cikin haiya cinsa tsabar wahalar da yasha a hannun Sojoji. Tsakanin asbintin da unguwarsu a kwai nisa amma haka ya tako a ƙasa yana tafiya yana tanƙaɗi kamar ɗan ƙwaya. Ya daɗe yana tafiya kafin ya iso layin unguwarsu. Tsayawa ya yi a bakin wani gida yana kallo gidansu daga gurin. Lokaci ɗaya ya tuno da abunda wannan gayan ya sanar masa cewar an kama su Innah da Nana. Tunaninsa izuwa yanzu an sakesu ne kodai har yanzu suna a ƙulle? Kafin ya kaiga yin tunanisa ya hango wata baƙar mota ta tsaya a ƙofar gidan...
Gaban sa ne ya ƙara bugawa kamar zuciyarsa zata fito. Ya ƙurawa motar ido yana son ganin wanda zai fito daga ciki. An ɗauki tsawon minti goma sha biyar kafin ya ga Nana ta fito, sai kuma yaga wani saurayi shima ya fito daga motar. Lokaci ɗaya yaji wani sanyi a ransa ganin Nana. Sai kawai ya nufi gurin cikin ƙwarin guiwa.
Tin kafin ya ƙaraso yake ganin yanda Nana ke dariya da a lamar dai koma waye wannan to sun saba dashi sosai, amma a ransa yana jin baya son haka. Kafin Nana ta baiwa Dr amsar tambayarsa idonta ya sauƙa a kan yayanta, shima ya sauke fararan idanunsa a kan na ta. "Ya ya!!! Ta faɗa da ƙarfi ta na nufar gurin da yake. Kasa rungumar sa ta yi ganin fuskarsa duk ciwuka, sai tazo gabansa ta tsaya tana kallonsa kuka na son kufce mata, sai tasa hannu biyu ta rufe bakinta dai-dai kukan ya kufce. Juyawa tayi ta shiga gida da gudu tana kuka tana zuwa ta faɗa jikin Innah ta na cewa "Innha ya ya ya ya ya dawo gashi a waje. Lokaci ɗaya gaban Innah ya faɗi amma ta kawar da kai ba tare da ta ce komai ba saina wani dogon tsaki da taja.
A waje kuwa AJ da Dr ne a ka fara kallon-kallo, AJ na son tuno a ina yasan shi, shi kuma Dr yana mamakin ganinsa a nan. "Dama shine yayan Nana! Ganin AJ ya kasa tuno inda ya sanshi ne sai Dr ya miƙa masa hannu ya ce Dr Lurwan likitanku. Lokaci ɗaya ya gano shi, bayan sun gaisa Dr ya ce "Zaka iya shiga gida ka huta saboda jikinka, idan ka samu nutsuwa sai muyi maga babban yaya.
Babu sallama ya shiga gidan jiki a sanyaye. Yana shiga Innah ta meƙe tsaye kamar dama jiransa ta ke. "Walhi idan har ka kuskura ka shigo gidannan ni kuna zan bar maka gidan ka? Ta na faɗa ta shiga ɗakinta ta fara haɗo ƴan tsummokaranta. AJ na tsaye a gurin har ta fito da kayanta a ɗaure a ɗankwali. "ka fita ka je duk inda kaga dama mu zamu iya rayuwa a matsayin da Allah ya ajiyemu ba sai mun kai kanmu inda Allah bai nufemu zuwaba. AJ ya buɗe baki zaiyi magana Innah ta katseshi da cewar "Idan har ka sake ka furta maga ta shiga kunnuwana to Allah ya isa ban yafeba, kuma mutuƙar kana gidannan to ni ya haramta a gareni, ba dai kai kace a kan kuɗi zaka iya yin komai ba, to kaje ka nemi kuɗinka mukuma ka barmu a inda ka ganmu, zamu rayu cikin talaucin da muke ciki. Innah tana maganar hawaye sun wanke mata ido, aduk lokacin da zata furta wata kalma to tana tuno irin cin mutuncin da wannan arnan ya musu , da kuma zaman da sukayi a ƙulle, ga zaman asbiti duk a kansa. AJ da Nana suma kuka sukeyi duk sun kasa cewa komai tsabar tausayin kakar tasu...
"Idan kuma har so kake sai kaga bayana to Abduljabaru gani dan Allah ka zo ka kasheni sai ka ci gaba da abunda kake ai katawa, a ce ka rasa da wa zakayi a bora sai Æ´aÆ´an arna, to ni dai na fa É—a walhi bazan taÉ“a yafewa ba. Ta Æ™ara sa tana dur Æ™ushewa a gurin nunfashinta na fita kaÉ—an kaÉ—an. Da sauri Nana tazo ta rungumeta ta zaunar da ita tana bata baki akan ta manta abunda Dr ya ce ne. AJ kuwa na tsaye a gurin duk ya fita a haiyacinsa yana jin tausayin Innah ji yake inama ana dawo da hannun agogo baya da baiyi wannan kasadar ba, Allah ya isan da ta masa yake ji na masa yawo a kai, lokaci É—aya kansa ya fara juyawa, take shima ya sulale a gurin tamkar macacce. Ai da sauri Nana tazo gareshi ta rungumoshi tana kiran asalin sunansa " Abduljabaru" "Abdul". "Abdul dan Allah ka tashi karka tafi ka barni Pls yaya. Tana cikin haka ita kuma Innah ta É—auki Æ™ullin kayanta ta bi ta bayansu ta bar gidan ba tare da sun saniba......ðŸ“
*Da yardar Allah zan koma yin posting kullum har mu kammala, domin an dameni a kan a gama wannan labarin to in sha Allah zamu kama shi yanzu. Amma fa yin hakan dole saida gudun mawar na ƙaramin ƙwarin guiwa ta hanyar comments da addu'o'in ku. Ina alfarari da ku S REZA na kune*
*ADDININMU is a Normal* *book*
*By S REZA âœï¸*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*
*S REZA...âœï¸*
*First Class writer's asso...*
*PAGE3ï¸âƒ£5ï¸âƒ£*
..........Kuka Nana takeyi ta na mai gir-giza AJ wanda har zuwa yanzu bai motsa ba, Tashi ta yi cikin sauri ta ɗebo ruwa ta watsay masa ta na binsa da ido kamar wacce bata taɓa ganinsa ba, ganin bai motsa bane ya sa ta ƙara watsay masa ruwan a karo na biyu. Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke ya na mai buɗe idonsa a kan Nana, sai kuma ya riƙe kansa ya na jin yanda kan ke juya masa, hannunsa ta kama ta na masa sannu cikin kuka. Ya buɗe baki ya ce "I'na Innah? Sai a lokacin Nana ta kai kallonta gurin da ta bar Innah ta na ce wa "Ga ta ce"...."Tsaya wa ta yi da hannun na ta a yanda yake ta na bin gurin da kallon mamaki. Da sauri ta miƙe da gudu ta shiga kiran innar ta ko ta ina. Da gadu ta ƙara fitowa ta na ce wa "Yaya Innah ta gudu walhi bata gidannan ta taffi. Ta na magar ta na kuka. Da sauri AJ ya miƙe tsaye yana nufar waje da sauri riƙe da kansa dake mugun sara masa. Itama Nana tabiyo bayansa ta na kuka. Ya na fita ya ci karo da Innah a ƙofar gidan a duƙe tana kuka tana sharar hawaye.
Da sauri ya faɗa jikinta yana fashewa da kuka ya kasa magana, itama Nana ta na zuwa ta faɗa jikinsu ta na mai sakin nata kukan. Kuka sukeye duk su ukun babu mai rarrashin wani a cikinsu, inna ta shiga shafa kan AJ tana mai jin tausayin sa a ranta. Cikin kuka ta fara magana "Tabbas bazan iya tafiya na barkuba domin bakuda kowa sai ni, kaman yanda nima bani da kowa saiku, amma tabbas Abduljabaru ka ɓata min rai wanda bazai musaltuba, amma na maka uzuri kaman yanda mahaifinka ya ce min a kanka, tabbas kai ɗin ɗan arziƙine, ka ɗauki nauyinmu alhalin kai kanka kana buƙatar mai tallafa maka, cinmu shmmu suturarmu gurin kwanan mu duk kaine, amma ka ƙi ka tsaya ka faɗa min gaskiyar sana'ar da kakeyi, sannan meye ya haɗa ka da wannan ar'nan? Allah dai yasa ba da gaskene sata kamasa ba? Shin Abduljabaru me kake ɓoye mana a tattare da kai? Muna son sanin gaskiya amma dan Allah kar ka ƙara mana ƙarya?
Cikin kuka AJ ya ce "Tabbas Innah nayi muku ƙarya wanda yanzu haka ta sakani a halin da na sani, kuma tabbas yau zan sanar muku da komai a kan kuɗin da nasamu, amma dan Allah Innah karki gujeni kisan cewar duk abun da na ai kata danku nayi pls innah? Innah ta ce "Innalillahi wa inna i'laihim raji'un, Allah dai yasa ba wani abun kaje ka ai kataba, shin ka manta lokacin da kake cemin AJ baya sata? AJ baya neman mata? AJ ba zai aikata duk wani abun da Addininmu ya yi hani da shiba? To Allah dai yasa baka ai kata ko ɗaya daga cikiba? AJ ya ƙara jin cewar lallai ya aikata kuskure, ita kuwa Nana ta ke ta tuno da zancen Kadija na cewar ya yi wa yarinyar cikine, sai kukanta ya ƙaru domin izuwa yanzu ta fara yarda da hakan.
AJ ya ce "Innah mushiga gida sai muyi zancen a ciki.
Bayan sun shiga gida Nana ta ɗora ruwa saida yayi zafi sannan ta juye a bokiti ta ɗauka izuwa banɗaki. Saida AJ yayi wanka sannan ya ɗauki kayan adides riga da wando ya saka sannan Innah ta ce yaci abinci tukunna. Itama innar wanka tayi tazo ta zauna kusa da angon na ta ta ce "Abduljabaru kaji tsoran Allah karka sake ɓoye mana damuwarka, kasani duk abunda ya sameka muma ya samemu, duba fuskarka tunda ka shigo na ganka a haka saida gabana ya faɗi, yana daga cikin abunda yasa kaga na kasa tafiya na barku, kullum addu'a'ta Allah yasa kana lafiya ya kuma dawo mana da kai gida lafiya a duk inda kake, haƙiƙa kullum cikin dare sai na tashi na roƙi Allah a kanka, amma a fili ina nunawa Nana cewar bazan yafe makaba domin ta gane cewar abunda kayi ɗin ba dai-dai bane. Inna ta ƙara sa ta na ruƙo hannunsa tana mai kallon fuskarsa dake a kumbure. Inna ta ce "Bari kaji halin da muka shiga a dalilinka?