Sashe 58
Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin zuciyarta na mata zafi kamar ana ƙoƙarin cirota da ga ƙirjinta. Tashi ta yi izuwa gurin Mama. Tana zuwa mama na magana da watar ƙanwarta da tazo gidan bikin, domin dangi na kusa-kusa duk sun fara zuwa. Ganin Zainab ɗin yasa Mama mayar da hankalin ta izuwa gareta. "Lafiya dai ko Zaiban? Cewar Mama tana jin tausayin ta, domin tasan Zainab bata son wannan auran kawai dai ba yanda zasuyi da Malam ne. Zainab ta buɗe baki zatayi magana kira ya shigo wayarta, ganin sunan Abdalha yasa ta kasa cewa Mama komai sai ta bar ɗakin tana ɗaga wayar.
"Isa zaizo dubani inaso kuzo tare ko da ganinki ne nayi ko zan samu sauƙin zuciyata? "Kamar bazatayi Magana ba ta ce "Ba zan iyaba! Bana fito ko ina ina gida, tun ba yauba na sha faɗa maka cewar ba'a barina fita ko ina. "Kinaso na shiga wani haline Zainab? Ya faɗa da wata murya da tasa jikinta ƙara yin sanyi? Kinsan mai nakeji a zuciyata kuwa? Wallhi ji nakeyi idan har ban gankiba zan iya rasa rayuwata? Ya ƙarasa yana tari. "Abdalha dole muyi haƙuri mu rungumi ƙaddara mubi zaɓin iyayenmu domin samun albarkasu, ka daure ka manta da ni a rayuwarka ka zama mai girma-ma zaɓin mahaifanmu domin bazasu zaɓar mana abunda zai cutar da muba, saboda haka kayi haƙuri ka daurewa zuciyarka da rashina yanzu saura kwana kaɗan na zama mallakin wani, kuma daga ranar dole mu rabu, rabuwa ta har abada Please! Tana kaiwa nan kuka yazo mata. Tana faɗa ta kashe wayar tana fashewa da kuka.
Da a ce wani ne zai faɗa mata cewar ita Zainab Adam zata iya yin kuka saboda mutumin da tafi tsana a rayuwar ta to da tabbas kallon mahaukaci zata ma koma waye wannan ɗin. Bata damu da duk abunda zaifaru a gurin al'ummar gari ba, mutuƙar zata samu abunda takeso, amma hakan ba zaisa ta yi abunda mahaifin ta zaiyi fushi da itaba kamar yanda ya ce mata.
Kulawa da kyautatawa da damuwa da ita da irin soyayya da yake nuna mata ba dare ba rana hakanne yasa itama ta faɗa a cikin soyayyarsa batare da ta shirya ba. Ya bata kulawar da wani ɗan Adam bai taɓa bataba, sannan shine sanadiyar kuɓutarta daga hannun ƴan iskan da suka kamata, bazata iya mantawa da Abdalha a rayuwarta ba, Haka ta koma ɗakin mahai fiyar tata tana ƙirƙiro fara'a ta maka a kan fuskarta.
Da ƙarfi Maryam ta saki plet ɗin abincin da ta kawo masa a ƙasa tana kiran sunan Momy. Momy da ke palo ita da Daddy tana ƙara sanar dashi irin halin da Abdalha ke ciki ya ce "Indai a kan auran wannan yarinyar da kowa ya mata shaidar banzanne to wallhi na cire hannuna a kan Abdul, ƴar bidi'a a cikin zuri'a ta! kuma ma yar gidan Adamu! To Wallhi ko mata sun ƙare a gari sai dai Abdul ya zauna a h"....'Ai bai ƙara sa ba suka jiyo ihun Maryam.
Kwance suka sameshi a ƙasa yana tari jini na fitowa daga bakinsa idanunsa sunyi jazurr kamar gauta. Ihuu Maryam take yi tana kiran sunan Daddy, hakanne yasa Sadiya da Nusaiba suma suka fito daga ɗakunansu. Kuka sukeyi dukkansu suna kiran Abdalha amma tarin bai tsayaba, duk tari sai jini ya fito daga bakinsa, ana haka Maryam ta hango wayarsa a ƙasa taje ta ɗauka. Haka suka daukoshi dukkansu suka fito da shi izuwa mota. Shek Kabir kabuga kuwa kallo ɗaya ya musu ya kawar da kansa ya na jin cewar ba a'man jiniba ko aman kwata zaiyi shidai ba zai yarda ɗan sa ya auri ƴar bidi'a ba. Nusaiba ce taja motar batare da sun jira dreban nasuba. Maryam da Sadiya ne suka shiga motar Momy kuma ta koma domin shiryowa tabi bayansu. Tinda suka shigar dashi mota Momy ta kira Dr Musa ta sanar masa, hakanne yasa tun kafin su isa a ka shirya tarɓarsu.
Momy na shiga palon ta ga ba kowa sai ta nufi sama É—akin Daddy. Tana shiga ta sameshi yana waya yana dariya alamar dai wanda yake wayar dashi mai muhimmanci ne a rayuwar sa. Cikin damuwa da halin da ta ke ciki ta ce "Haba Shek yanzu wannan abunda kakeyi ya dace kenan bakaga halin da yaronnan ke ciki bane? A'man jini fa ya keyi, ciwon zuciya fa kenan baka tsoran mu rasa shi? Saida ya kashe wayar sannan ya juyo ya kalleta cikin rashin nuna damuwa da zan cen nata ya ce "Idan muka rasa shi ai ba shi kaÉ—ai muka haifaba, kuma karki sake zuwar mini da zancen yaron da ban isa dashiba. Ya na faÉ—a ya kawar da wannan zancen ya É—aoko wani yana sakin fara'a a fuskarsa.
"Idan zaki iya tuna wa da wani mutumi da ya musulunta yaran Alhaji Salisu, dake garin Benue Makurdi, har Alhaji Salisu ya bashi auran ƴarsa, lokacin da suka samu ƙaruwar yaro na miji har suka gaiyaceni garin nayi wa'azi? Momy ta ce "Eh ai bana manta lokacin domin a ranar na haifi Abdalha. "To amma ba kace mutumin ya rasuba? Momy ta faɗa tana tuno ranar da a ka sanar musu da rasuwar mutumin saida Shek ya kwanta rashin lafiya.
Daddy ya ce "Eh haka a ka ce, amma wai a she yana raye bai mutuba, yanzu haka yau ɗinnan yana hanyar zuwa gidannan iji Malam Nura abokinsa. Momy ta waro ido waje ta na cewa "To ina yaje tsawon shekaru? Ko dai ya gudu yabar Musulunci ne? Daddy ya ce "Yanzu haka ma wai da wasu zaiso suma zasu koma ADDININMU. Sannan ya ce "Ki ajiye tambayoyinki har sai yazo domin nima bansan komaiba, abunda nasani dai shine mutumin kirki ya dawo. Daddy ya ƙara sa yana tunano irin abun arziƙin da ya masa lokacin da ya je garin.
Daga haka Momy ta dawo da maganar Abdalha, amma Daddy ya ce "Yanzu haka yana cikin farin ciki karta ɓata masa rai. Hakanne yasa ta ce "To zan tafi asbitiin Yanzu idan ka amicen? Amma Daddy ya mata Wani irin kallo ya maka mata ya ce "Yanzu nace miki munada baƙi amma kina zancen tafiya yawo, to yanzu inaso ki kira su Sadiya su baro gurin su dawo domin a haɗa musu kayan tarɓa. Momy ta ce "Wato yarona na gadon asibiti zanje gurinsa shine zakace zanje yawo ko? Ta faɗa tana jin zafin kalmar yawon da ya ce. Daddy dai bai ce komai ba ya bar ɗakin domin zuwa tarɓar babban baƙonsa. Haka Momy ta kira Nusaiba da Sadiya ta ce Maryam ta zauna a gurin Abdalh ɗin.
A ranar suka iso garin Kano, amma basu iso gidan Shek kabuga ba suka nufi gidan su Ogan sa kuma sirikinsa wato Salisu uba ga matarsa Hajiya Babba. Su kansu basu san da dawor Muhammad É—in ba , domin Hajiya Babba tayi hannun riga dasu tun rasuwar mahaifinta da mijinta. Ita Hajiya Babba ganinta dunta iyayen ta suka rasu a hanyar zuwa garin sai ta É—auki abun tasa a ranta, hakanne yasa ta daina nemansu kwata-kwata.
Suma sunyi mamakin ganin Muhammad kuma sunji daÉ—i da ya zo musu da jikarsu gida. Lokacin da sukaji bayanin auran da Hajiya Babba tayi ne kuma ransu ya É“aci , amma a ka basu haÆ™uri da cewar ai yanzu sun rabu da mijin amma tana É—auke da cikinsa. Haka suka dinga lallaÉ“ata Salis da laÉ—ifa dama su suna É—an zuwa garin, hakanne yasa suka saki jiki dasu. Samuel da Sarah dai sai bin laÉ—ifa da Salis sukeyi. Washe gari suka shirya izuwa gidan Shek Kabir kabuga.....ðŸ“
*MUHAÆŠU A GIDAN SHEK*
*COMMENTS ÆŠINKU SHINE ABUN ALFAHARINA*
*S REZA âœï¸*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADM*
*S REZA...âœï¸*
*First Class writer's asso...*
*PAGE4ï¸âƒ£4ï¸âƒ£*
........Misalin ƙarfe tara na safiya suka isa gidan Shek Kabir kabuga, kana ganin Shek kasan yana cikin farinciki da zuwan wannan baƙon nasa. Kafin Hajiya Babba ta tafi saida tasa a ka kira yayan mahaifinta Malam Adamu. Tarɓa ta mutunci Muhammad da iyalansa suka samu daga gurin iyalan Shek. Sosai Shek da Muhammad suke cikin farincikin ganin junansu, kana ganin kabuga kasan a kwai magan-ganun a bakinsa. Itama dai Momy tana nunu nata farincikin daidai yanda zata iya. Bayan an kawo musu abubuwan da a ka tana dar domin sune kowa yaci abunda zai iya ci kafi a ka sake sabuwar gaisuwa tsakanin su. A taƙaice Muhammad ya basu labarin abunda ya faru da su tsawon wannan lokacin, kuma ya tabbatar musu da cewar ɗan uwansa ne ya masa. Da mamaki Momy taga Shek na kuka yana tausayawa Muhammad, shima kansa Muhammad ɗin yayi mamaki. Bayan ya gama ne ya fara masa nasihohi a kan wannan jarabtar da ta sameshi. Sosai Muhammad da su Samuel suka ƙara yarda da Addinin musulunci, yanda sukaji irin alkairin da Allah ya tanadar ga masu yafiya idan an cucesu, sosai son Addinin Musulunci ya ƙara shigarsu har suna ji cewar zasu iya komai cikin koyarwar Addinin Musuluncin.
Shek ya kalli Salis ya ce "Kardai ka ce min wannan shine mai sunan Alhaji har ya gyrma haka? Muhammad yayi murmushi ya ce "Eh fa shine har ya zama saurayi. Ya faÉ—a yana dariya dukkansu. Hajiya Babba ma saida abun ya bata dariya, itama Momy dariya tayi tana kallon Salis É—in da ke sunne kai. Ganin shek na ta kallon su Sarah ne yasa Muhamd gyra zama ya ce....
"Wannan shine babban ɗana. Ya faɗa yana nuna Salis. Sai ya ƙara nuna laɗifa ya ce "Wannan itace auta Ladifato. Sai ya dawo da kallonsa izuwa gurin Samuel ya ce "Wannan kuma shine ɗan gidan yayan nawa, shine babba sai ƙanwarsa gata nan ya faɗa yana nuna Sarah. Sannan ya ɗora da cewa..."Sannan sune suka buƙaci shiga Addinin Musulunci da kansu. Momy da shek da su Maryam da sauran suka amsa da AllahuAkbar! Fuskokinsu cike da annuri jin cewar ADDININMU zai samu ƙarawa. Momy ta ce da Maryam ta je ɗaki ta taso Abdalha. Tayi maganar ne batare da kowa yajitaba. Maryam ta sanar mata da cewar ai tun jiya da sukawo daga asbiti bai fito wajeba, ya ce kar kowa ya dameshi, sannan Dr Musa ya ce a barshi ya samu barci sosai. Badan Momy tasoba ta bar maganar amma hankalinta naga ɗanta.