← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 67

Sashe 36

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ɗan tsoro ya ce "Ko dai babban yaya ya dawo ne? "Dariya ta yi sannan ta ce "Kai dai bari! Ina ga fa magata ta zama gaskiya. "Ban ga ne ba? Yayi tambayar cikin rashin fahimta? "Idan muka haɗu zaka gane, ta faɗa ta na ƴar dariya ƙasa-ƙasa. Shima dariya ya yi kafin ya ce "Allah babban yaya yana shiga hakkina fa. Ya sake buɗe baki zaiyi magana ta ce "Zan kira ka anjima. "Ok tom i'm werting.

Suna gama wayar ta daka wani tsalle ta na cewa Yes komai na tafiya dai-dai. Numbar Nana ta nemo ta danna wa kira, ai kura ƙara ɗaya a ka ɗaga.

Kallonta ya ke ganin har yanzu kukan ta ke gashi lokaci sai tafiya ya ke. Ba ta re da ya ce ma ta komai ba shima ya kifa kansa a kan matuƙin motar yana jira ta gama kukan kafin su shiga. Cikin kuka ta ce "Ba ka tsoran kayi karo da babanna ko ya ya nane? Bai bata amsaba ya ce "Idan kin gama ki fito mu tafi domin yanzu haka a na jiranane?. Yayi maganar dai-dai ya fito daga cikin motar. Ganin haka ya sa itama Zainab ɗin fitowa tana bin bayansa domin har ya yi gaba. Sai da ya je zai shiga gidan kafin ya tsaya ya na kallon wani ƙatoton hoton da ke ɗauke da suna kamar haka... *SHEK IBRAHIM INYASS* Kallonsa ta yi ganin abun da ya ke kallo. Ai kuwa shima ya kalleta sai kawai ya taɓe baki a lamar norting. Itama kallon hoton ta yi kafin ta kai hannu ta shafo fuskar hoton sannan ta fara tafiya shima ya bita a baya yana saƙe-saƙe a zuciyarsa.

Acikin gidan ku wa Isa da mlm ne ke shirya yanda zaso tona wa Shek kabir kabuga a siri domin kuwa har ga Allah ya tsaya musu a rai, ga kuma wannan ɗan iskan yaron nasa wanda baya ganin kowa da mutunci, yaron da kullum idai zaiyi wa'azi sai ya zagi ni, wai a ce shine ya sa ce min yarinyar da banda kamar ta amma wai kice nayi haƙuri, sabo da ban da hujja ko! Mlm ya ƙara sa ya na nuna gurin da Nama ke zaune ita da au'ta Aisha sun sha kuka har sun gaji. Cikin tsananin ɓacin ran da bata taɓa nunawa a gidan ba tun da sukayi aure da mai gidan na ta ta ce "To ai Walhi mlm Adamu ba ka ɓurgeni ba tundade bakaje kayi gaba da gaba da shi Shek Kabir kabuga ɗin ba domin nuna masa cewar shiɗin ba komai ba ni kamar yanda kake faɗa, walhi baka bani bamaki ba, kullum abu ɗaya to Ni wallahi na ga ji bazan iya da wannan ƙiyayyar taku ba wacce babu komai a cikin ta sai son zuciya . Kafin Malam ya gama mamakin jin sunan sa daga bakin matar ta sa har ta ɗora da ce wa.

"Yanzu gashi yau kwana ɓakwai kenan babu taƙa mai-main labarin Zainab ko kuma labarin gun da ta ke, amma kai da muwar ka sai ka tozarta wani, wato kai hakan ma daɗi ya maka, tunda zaka cimutuncin wani ko, to wallhi mutuƙar wani abun ya samu ƴata to kaine sila, domin ka ba ma ta a samota kakeyi ba, kuma walkhi mutuƙar baka janye wannan ƙarar ba sai na lalata komai walhi. Mama ta ƙara sa ta na fashe wa da kuka, ai kuwa kamar malam jira yake ta gama shima ya ɗora da cewa...

"Eh lailai sai yau na tabbatar da cewar kema kina tare da su, kuma yau na tabbatar da cewar duk abun da ke faruwa ke ce kika bada hanya, yanzu duk irin cin mutuncin da wannan yaron bayan nawa kemin nida ɗiyata har kin manta, haka wannan yaron zai dinga cin mutuncin mu ya na ai batamu harma ya na ciremu daga cikin addinin namu amma wai kice na ji daɗi da abun da ya yi? To walhi idan har ta tabbata cewar wannan yaron shine ya sa ce Abu to walhi sai ya yi mamakin irin hukuncin da zan masa kuma"..."Ai kaji gun da matsalar ta ke, kenan ma baka da hujjar cewar shine ya saceta, kenan za to kakaye, kuma zato mene a addinance? Mama ta katse shi da wanan tambayar. Cikin ɓacin ran jin yanda ta ƙatse shi ya ce "Yanzu ni kike ɗaga wa murya a gida ko wa yana ji domin kare wanda ke son cutar da ɗiya ta? Har kina cemin ina yin za to! Ya ci gaba da ce wa... To ki sani mutuƙar ta tabbata hakan to kema sai kinyi da na sani walhi, domin a kan hakan zan iya tsinke zaran da kike wasa dashi har kike ɗaga min murya. Ai da sauri isa da ke tsaye a gurin jin abun da Mlm ya ce ya riƙe baki yana nadamar wannan abun da ke faru wa a tsakanin iyayen nasa. Mlm na gama faɗin haka ya bar gidan cikin tsan-tsar ɓacin rai. Ita kuwa mama jin abunda ya ce sai ta fara cewa dan Allah mlm ka tsinki ai ban hanaka ba kuma ban riƙekaba.

Mama ta dawo da kallon ta izuwa gurin Isa ta ce "Yanzu kaji daÉ—i hakan ko burin ka ya cika ko! Ta na faÉ—a ta É—auki Aisha suka shiga É—aki ba ta ko tsaya jin maganar da Isa É—in keyi ba.

Jama'ar gari ku wa ko wa abun ya bashi mamaki jin cewar Mlm Adamu ya kai shek Kabir kabuga ƙara kotu. Tabbas abun ya gir-giza ko wa, daga ƴan ƙungiyar su Zainab ɗin harma na su Abdalha ɗin, ko wa ya san dai a kan ɓatar Zainab ne, kuma har zuwa yanzu babu wata hujja da zata nuna cewar ba Abdllah ɗin ba ne ya sa ceta ba, domin kuwa tun da abun ya faru ba'a ƙara jin sa yayi wani wa'azi ba, kokuma ya fito ya yi magana a kan hakan ba. Hatta ƴan ƙungiyar tasu wa su duk jikin su yayi sanyi domin wasu sun yarda da cewar shi ɗin ne ya saceta, hakanne ya sa wasu ƴan a da'war suka dinga yaɗa zan can cewar ya ɗau keta ya gudu da ita ne. Domin ko masallacin da ya keyin sallar juma'a kuma ya yi wa'azi a masallacin to wannan jum'ar babu wani da ya saka shi a ido, gaba ɗaya ma dai ba'a ganin sa yanzu, kenan dai ya tabbata shine ya sa ce ta. Yanzu dai kowa na jiran ranar shiga kotu tazo domin a je a ji Shari'a tsakanin malamai da malamai, wato shari'ar ilimi, tsakani Malam Adamu da shek Kabir kabuga. Wasu da yawa dan kawai gulma zasuje, wasu kuma domin jin gaskiyar lamarin.

*( To koma dai mai zai faru muje cikin labarin domin jin gaskiyar lamarin mu dai Æ´an kallo ne)*

*GIDAN SOJA*

Gudu Samuel ke yi sosai, wanda saida yayi tafiya mai tsayi tsakanin part ɗin su da gurin da aka kai AJ ɗin wato ɗakin *TSARO* Duk gudun da Samuel keyi da shiga lungu haka Salis ke binsa domin shima maganar da Samuel ɗin yayi yasa ya fara zargin wa ni abun. Dai-dai Sojojin da suka shigar da Aj ɗakin zasu fito, su kuma suna ƙaraso wa gurin, kasan cewar Sojojin sun tsaya koya wa Aj hankali. Ai kuwa Samuel ya na zuwa bai tsaya jiran komai ba ya tura kai, shima Salis da ke bayan sa ya tura kai. Ka san cewar sojojin basu san da zuwansu ba, kuma basuyi tsammanin ma bayan mai gidan da kuma matar gidan wani yasan da gurin ba. Ya nayin yanda suka shigo ɗakin ne da ƙarfi yasa ɗaya daga cikin sojan wanda ya ke gaba faɗuwa, su kuma sauran suka shirya biddigarsu. Ganin haka ya sa Samuel da Salis ɗaga hannuwa sa ma suna ƙara shiga cikin gurin.

Ganin Samuel ne ya sa ɗaya daga cikin sojan ya ke tam bayar sa lfy? Cikin tsoro da far gaba ya ce "Daddy ne ya turoni wai ku fito da wannan yaron da kuka shiga da shi yanzu? Ta ke Sojojin suka kalli juna kafin wannan wanda ya faɗi ɗin ya ce "Get aut!!! Ya yi maganar cikin ihuuu! Domin kuwa bai yarda da Salis da ya gani da ga bayan sa ba. Ganin kofar a buɗe ga kuma wata zuciyar da ta turashi izuwa cikin ɗakin da suke da tabbacin a nann komai ya ki, zuciyar sa na tabbatar masa da cewar bazasu iya harbin sa ba. Ai kuwa kafin ka ce me Salis ya nufi ɗakin da gudu, wanda yayi dai-dai da shima Samuel ya shiga, hakan kuma yayi dai-dai da sakin bulet da ɗaya sojan yayi. A lokaci ɗaya abu guda uku ya faru. Shigar su Salis da Samuel cikin ɗakin tsaro, da kuma sakin bulet ɗin da ya sumu ɗaya a cikin su, da kuma ƙarasowar su Elixa da Hajiya Babba da Sarah wacce dama suman ƙarya ta yi domin a buɗe ta, da laɗifa da Daddy.

Ƙarar bulet da ƙarar da ɗaya daga cikin Salis da Samuel ya sake ne yasa sauran mutanen dake cikin ɗakin tsorata, harda AJ wanda tsabar duka har ya fita a hai yancin sa. Cikin mamaki Elixa taga raronta jikin jini yana kurma ihuu! Yayin da Salis ya kai kallon sa izuwa cikin ɗakin domin tabbatar wa da zuciyar sa abun da ta ke cemasa...📝

*Anya kuwa kuna tunanin abunda na ke tunani?*

*Ku ci gaba da bina a hankali, kuma kuci gaba da min uzuri,*

*Yanzu kun rage yin comments fa?🙄*

*S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*

*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*

*PAGE2️⃣9️⃣*
Chapter 36 · 0% Book details