← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 67

Sashe 23

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hajiya ta ce "Yanzu idan na ce muyi sati biyu a matsayin shekara ɗan da nace maka idan yaso tun. A nann na baka kuɗinka muna zuwa Najerya sai kawai ka ci kuɗin shin zaka yarda? Ka daiyi tunani miliyon 50 a sati biyu ba wasaba....📝

*INA KUKE S REZA FAN'S?⁉️⁉️⁉️*

A kwai wani tsohon littafi na da na rubuta, mai suna so ne. Tom na sake dawo muku dashi domin wanda basu karantaba su karanta. Littafin soyayya ne. Soyayya mai taɓa zuciya, littafin da masoyana suka dameni akan na sake dawo musu dashi. Tom in Sha Allah zan dinga haɗa muku da wannan na ADDINIMU zai dinga zuwar muku a tare, domin farin cikin ku. Littafin *SO NE* Littafine da ya ƙunshi soyayya mai tarin abubuwan allajabi, mai rama tsakanin masoya. Ku kasance da littafin domin suna tare da littafin *ADDINIMU* kuma dukkansu free ne, domin jin daɗin ku🥰🥰 *ADDINIMU*.da. *SO NE?* ❤️

*

*PAGE* 1️⃣9️⃣

........Kallonta yayi da kyu cikin wani sabon mamakin da tun da suka haɗu take bashi ya ce "Hajiya ban gane me kike nufiba? Hajiya Babba ta kalleshi cikeda maradin sa ta ce "Inaso muyi sati biyu a nan in yaso muna komawa 9j shikenan kaci kuɗinka? "Kina nufin daga haka mun gama auran kenann? Hajiya ta ce " Eh haka nake nufi. Cikin tsananin mamaki da farin ciki AJ ya shiga tinanin abubuwan da zaiyi idan ya mallaki wannan kuɗin fayan kwana goma. Hajiya ta ce "Bakace komai ba? Ya ce "Na amin ce, saura kwana goma kenan ko? Hajiya ta ce "Eh hakane. Tinda sukazo ƙasar Morocco Hajiya Babba bata ga farin ciki a fuskar angon nataba sai yanzu, domin kuwa ya dawo kamar ba AJ mai surutu da abun dariya da fara'a ba, tashi tayi ta kama hannun sa tana masa alama da ido. Kaman yanda suka saba kullum Hajiya saita buƙaci mijin nata sau huɗu a rana, wani lokaci ma har fiye da haka, shikuwa gogan naku tun bai saki jiki da itaba har ya ware shima ya ɓarzi abarsa domin kuwa da yana tsoro kar wani abu ya faru, idan yaran ta sun gane, amma da yaga ita ko a jikinta sai kawai ya fara abubuwan da takeso, dukda kuwa yana shan wahala domin kuwa wani lokacin har fita yakeyi a haiyacin sa.

Yauma abun da ya faru kenann domin AJ ya nunamata cewar yau fa yana cikin farincin, warewa yayi suka sha love da Æ´ar tsohuwar abokin nasa, amma fa saida ya gaji ya barta, saida yaji ta gamsu kafin ta yayyafa masa ruwa ya farka.

*SALISU*

Yakira numbar AJ ya kai sau goma amma bata shiga, sai kawai ya nufi police station É—in cikin sauri domin kuwa gabansa na faÉ—uwa. Da sauri ya shiga gurin yana kallon sabon É—an sanda da ke tsaye a gurin ba wanda ya saba ganiba, kasan cewar police station É—in tsohone babu wasu ma'aikata a guri sai Æ´an kaÉ—an hakanne yasa gurin ko mai gadi babu. ÆŠan sandan ne ya tareshi yana cewa "Lfy daga ina me kake ne? Salis ya ce "Wasu mata da suke cikin gurinnan É—azu sunake nema Pls?.

Cikin mamaki ɗan sandan ya ce "Kaine AJ? Salis ya mai-maita suna kafin ya ce "Pls ina police ɗin da ke gurin ɗazu? Cikin ɓacin rai police ɗin ya ciro waya yana dannawa kafin a ɗaga ya ce "Police ɗin dage gurin nann kuma an koreshi a aiki, sukuma wanda kazo nema an sake musu guri.

Cak Salis ya tsaya yana kallon police ɗin cikin mamaki, Salis ya buɗe baki zaiyi magana ya ji ɗan sandan na cewa "Yes sir ga wanda yake kawo musu abincin yazo, ina tsammanin ma shine AJ ɗin. Police ɗin yayi shiru yana ƙamewa a gurin kamar wani gunki yana sauraron abunda a ke cewa daga cikin wayan. Saida ya gama jin abunda a kace sannan cikin tsan-tsar girmamawa ya ce "Yes sir an gama. Salis dai sai kallonsa yake cikin mmk. Yana gama wayar ya kira wasu ƴansan dan ai kuwa nan take suka maƙala masa onka, suka turashi a cikin sel ɗin da su Innah suka fita. Yana tambayarsu lfy lfy amma ina saida suka turashi.

*LAÆŠIFA POV*

Salis na fita daga gida itama ta shiga ɗaki ta shirya ta ɗauki ATM card ɗinta ta shiga kiran numbar Umar. Bayan Umar ya ɗaukane ta sanar dashi cewar yazo ya karɓi kuɗin ya kai. Cikin murna Umaru ya amsa kafin ta sanar masa da gurin da zasu haɗu. Shuru tayi tana tunani. Shin meyasa Salis yafi damuwa da matsalar su yarinyar da zai aura! Bayan ga matsalar da nakeciki, kuma yasan cewar ina sonsa. Wata zuciyar ta ce "Shima saboda yana sontane, kamar wacce take zance da wani ta ce "Ok hakane shima sonta yakeyi ko, shine yasa ya manda da tawa matsalar ki, to Walhi nima saide duk abunda zaifaru yafaru, badai abunda yafaru a faya bane zai ƙara faruwa muda Daniyel to walhi muje zuwa. Tana kaiwa nann ta nufi gurinda zasu haɗu da Umar.

Jiniyar motocin sojojine ya karaɗe ilahirin unguwar da mamu wasu mutane a cikinta sai ƴan ƙalilan kasan cewar a bayan garin gurin yake. Babu mota ko ɗaya da ta sabu damar shigowa gurin kasan cewar gurin baida girma kuma ga wata tsohuwar mota a gurin ita kadai ma ta ciki gurin. Parking sukayi sannan sojoji suka fara durgowa daga cikin kowacce mota. Babban sojojin barinki garin wanda a wannan watan yake cika shekaru biyu da samun ƙarin girma daga wani muƙamin zuwa wani, wanda a Yanzu haka shine Comandar ɗin duk wani sojo dake wannan state. Kama yanda kowa yasani mutumne mara imani ga tsan-tsar kishin addinindu wato addinin Christian, mutumne mai ƙiyayya da duk wani wanda ba ɗan addinisuba, hakanne yasa ya samu matsala da manyan ƴan kasuwar dake garin Benue sts.

Baya samun yabo daga sauran addinan dake garin amma kuma duk wani ɗan addininsa yana jin daɗin abunda yakeyi, domin kuwa baya barin a takasu koda kuwa sune basu da gaskiya. Ƙiyayar sa tafi ƙarfi a kan masu bin addinin musulunci domin kuwa sune yake ganin sunfi yawa, bugu da ƙari matemakinsa ma Musulmi ne, mai suna Faruƙ. Comandar Daniyel kenan wanda ke zaune a ɗaya daga cikin gidan da kwamnati ta mallakamasa yanada mata guda ɗaya mai suna Eliza wacce sukecewa Momy, sai yara guda biyu mace da Namiji. Samuel da Sarah. SAMUEL ne babba yabata shekara huɗu. Yayinda dukkanninsu sukayi kama da Eliza sosai domin kuwa Elixa fara ce sosai ga iya cin uban wanka kamar matar shugaban ƙasa. Yanda mijinta ke ƙin musulunci sai ita ta damashi ta shanye domin kuwa ita ƴar gidan wani babban fasto ce wanda duk faɗin garin babu kamarsa.

Daniyel yana son yaransa sosai, itama Mommy hk, amma yafi son ƴar autar su, wato SARAH. Lokacin aihuwa Sarah Saida a ka findda rai da mommy domin kuwa ta wahala, hakanne yasa bayan ta aihu yasa a ka cire mata ma haifar gaba ɗaya a kan ya daina ai huwa. Eh tabbas yana son yaran sa amma hakan baya hana idan suka taɓa masa martaba tofa sai sun gane shiɗin rainun ɗajine. Shine ya fara sakar ma yaransa kuɗi daga baya kuma ya daina sukuma suka shiga satar masa batare da yasabi. a kan kuɗi zai iya komai haka a kan addinmsa ma zai iya yin komai. Wannan kenan.

Bai ko tsaya an buɗe masa ƙofar motar kamar yanda a kasaba, da sauri ya fito daga cikin motar yana nufar cikin ɗan ƙaramin Police station ɗin. Tin lokacin da da ƴan sanda sukaji jiniyar motocin suka miƙe tsaye suna ƙamewa a gurin kamar wasu gunkuna. Shikuwa Salis cikin tsananin tashin hankali yake abin wajan da ido ko zai gano waye zai shigo kodai Daniyel ne, ai kuwa kafin ya rufe baki sai gashi yana shigowa cikin takunsa na mazajen da suka shiga in da rakwaye basu iya shiba, cikin takunsa wanda ke gigita masu da sun hangoshi.

Bai tsaya tambayar kowaba ya nufi gurin da Salis yake a ƙulle, cikin umarnin na shugaba a gurinsu yasa a ka fito da Salis. Tin kafin a durƙusar da shi a gaban sa ya ɗaga ƙafarsa ya buga masa wannan shegen ta ƙalmin nasu, kafin Salis ya ɗago ya ɗauke shi da mari, ya ƙara masa ya ɗagashi ya kwasheshi ya faɗi a rufa ciki, tsabar a zaba yasa Salis kasa yin ko da ihuma. Cikin zafin rai ya ɗago Salis da niyar sake kwasheshi. Chak ya tsaya yana binsa da kallo kafin sakeshi yana nuna shi da hannu cikin mamaki. Ya ce Salisu? Kafin Salis yayi mgn ya sake cewa "na You again?

*ABDLLAH POV*

Eh tabbas baiji daɗin sace Zainab da a kayiba, amma kuma baiji hakan ya bashi wani haushiba. Yana zaune yana jin yanda abubuwan suke ƙara rikicewa a yanar gizo-gizo. Yana cikin haka yaga kirin shek Kabir a karo na babu a dadi, tuno abunda yafaru tsakanin su yayi jiya a gidan su. Yana ɗagawa Daddy ya ce "Kazo gidan yanzu ina son ganin ka? Bai tsaya jin komaiba ya kashe wayar.
Chapter 23 · 0% Book details