Sashe 11
Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk abun da Daddy ke faɗa yana sauraro amma tsabar tsoro ya hana ya fahimci komai, yana cikin hakane yaji alamar zai fita, ai kuwa yazo jikin ƙofar toilet ɗin yana leƙawa har yaga fitar Daddy ɗin, sannan ya sauke a jiyar zuciya yayi hanyar fita. SARAH kuwa lokacin da ihu ya kufce mata haɗi da fitsari sai tayi saurin rufe bakinta, amma fitsarin kuwa saida ya kufce. A kan idonta Samuel ya fito daga toilet har ya bar ɗakin kafin itama ta fito cikin tsoro ta nufi ɗakinta. Tana shiga ɗaki ta faɗa toilet tayi wanka kafin ta fito tana cewa "Walhi daga yau bazan sake satarwa Daddy kuɗiba irin wannan tashin hankali da nake shiga! Haka ta ƙirga kuɗin dubu arba'in da uku (43,000) sannan ta shiga neman kayan da zata saka.
*LAÆŠIFA. SALIS POV*
Tana shiga palorn ta tararr da Hajiya Babba sai sakin murmushi takeyi, harda wani lissafi da hannu. Tin daga ƙofar palorn take kiran Hajiya Babba Hajiya. "Wai Hajiya wani irin aiki kika baiwa wannan wawan yaronne!? Allah Hajiya na tsani yaron Please dan Allah a koreshi akawo wani. Cikin mama Hajiya ta ce "Wai wani yaro kike magana a kaine kinzo tin daga waje kina kirana kamar namiki laifi?
Cikin tsananin jin haushin AJ Laɗifa ta ce "Hajiya wannan yaron dayafita daga gidannan mana dashi nakeyi Please wani aiki kika bashi? Kafin Hajiya tayi magana saiga Salis ya shigo yana ƙoƙarin zama laɗifa ta ce "Bro please dan Allah ka fita a harkar yaronnan, kaga abunda yamin yanzu kuwa!? Zaginafa yayi harda cewa wai wai yafi ƙarfin yayi dani! Yana ɗan aiki to Walhi sai ya bar gidannan tinda ba gidan ubansa bane. Cikin kwantar da murya Salis ya ce "Haba my sister meye na ɗaukar zafi haka, Allah yaron baida wata damuwa kece dai kike son saka abun a ranki amma karki damu A.J mutumin kirkine.
Cikin fushi Hajiya ta ce "To naji zan koreshi tundade kince bakya sonsa, amma bari kiji na faÉ—a miki... wallhi nima zanyi aure ko kunaso ko bakwaso, tinda na fahimci saboda ina goyan bayankune shine kuke son Sai kun kasheni da raina ko!? To na gode.
Cikin mamaki Salis da Laɗifa suke kallon Hajiya domin jin abun da take faɗa. Cikin ƙarfin hali Salis ya ce "To yanzu Hajiya ina ruwan auranki da aikin AJ? Sannan ma meyakawo zancen zakiyi aure bayan muna magana a kan ɗan aikine? Sai a lokacin Hajiya Babba ta fahimci katoɓararr da takusa ta tafka. Ai kuwa cikin sauri da rikicewa ta gyara maganar ta da cewa "To ai nasan halinkune yanzu ina faɗa muku aikin da na ɗauke shi sai kuce ku bai mukuba kumani haka nakeso.
Da sauri suka haɗa baki da cewa "Faɗa mana mun yarda? Hajiya Babba cikin farin ciki ta ce "Zai dinga tuƙani duk lokacin da naso haka. Sannan zan dinga aikansa cefane dade sauransu, shikenan fa aikin, ma'ana dai yaron gidana. Da sauri Salis ya ce "To yanzu Hajiya a kan wannan shine kike cewa wai zamuce bamaso?...ai gaskiya ma Walhi daɗima naji kinga shima yaron yanzu sai ya ɗanji daɗi ,Allah ma dai yasa ya iya mota? Hajiya Babba ta ce in bai iyaba za'a koya masa. Ita dai laɗifa bataso AJ yasamu aiki a gidan nasu indai ba aikin gadi bane, amma ya zatayi haka zata haƙura, amma tayi alƙawarin shida kansa zaibar gidan saboda cin mutuncin da zata dinga masa. ( *NI KO S REZA NA CE UMM-UMM FA🤓)* Ta ce "Bro muje nazo da labari? Salis ya ce to muje ɗakina. Haka suka tafi suka bar Hajiya Babba cikin murna ganinn ta shawo kan yaran nata cikin sauƙi.
LaÉ—ifa ta ce Bro Inason namaka wata tambaya dan Allah ka bani amsa?
Salis ya ce "ina jinki.
Ta ce "Shin ADDINIMU ya amince mace musilma ta auri arne? ( KRISTEN)
Cikin mamaki ya ce "Ban gane ba?
Ta ce "To kaman dai ni LaÉ—ifa zan iya auran wanda ba Musulmi ba? Ta basa maganar dalla-dalla domin taga yana son É—aukar abun kamar wasa.
Salis ya ce "Bana son rainin hankali idan zakimin bayani yanda zangane to kimin in ba hakaba Allah zan koreki waje tinda naga bakida abun faÉ—a sai shirme.
Cikin serus ta ce "Bro Walhi sonsa nakeyi... tin jiya da na haÉ—u da shi har yanzu ban manta dashiba, kuma inajin zuciyata namin zafi duk lokacin da na aiyana cewa babu aure a tsakanin mu, ganin ba ADDINIMU É—aya ba.
Salis ya ce "Waye... kuma yaushe kuka haÉ—u... kuma me ya haÉ—aku???
Cikin rashin tsoro da kuma saboda yayan nata wajan sanar masa da duk wani sirrinta ta fara bashi labari abun da ya haÉ—ata da shi kamar haka... LaÉ—ifa ta ce "Jiyane a clup munje taya zee-zee bikin birthday É—inta. "Sai me ya faru? Salis ya sake tambayar ta.
"Farine dogo kansa yayi wani irin É—an iskan aski, zaune muke a teburin gabammu wanda muka cika shi da kayan shaye-shaye (abu buwan sha) dade sauransu, Kasancewar gurin bawai iya mune muke gudanar da fatin ba harda wasu hakanne yasa gurin ya cika sosai. Muna cikin hakane sai mukaga ana ihuu! An zagaye wani teburi, muna zuwa sai mukaga mata da maza ne agurin yayinda ake saka gasar kuÉ—i...
Budurwa da saurayi ne zasu fara yiwa junann su kiss batare da kowa ya taɓa ɗan uwansaba, idan macen ta taɓa namijin to shine yaci, idan kuma namijin ne ya taɓa macen to itace ta ci. Taci gaba da cewa...ana cikin haka layi yazo kansa. Sanda tayi shiru zuwa wani lokaci kafin taci gaba da cewa...Suka saka dubu ashirin-ashiri shida wata yarinya, nann suka fara... yarinyar tsaɓar ta cika cikakkiyar yar duniya batayi komai ba amma shi sai ya ke neman ruɗewa hakane yasa ya faɗi. Sai'a ka fara ihuu!. Shikuma cikin jin kunya ya ce a sakeyi. In ta ƙaice maka zance saida sukayi sau uku duk tana cinyeshi. A'na cikin hakane akazo gurin bada kuɗi, duka-duka kuɗin dake jikinsa dubu sha ukune, kuma dubu sintin zai bata (60,000) nann fa ya rasa yanda zaiyi, shima abokin nasa da alamu dai bashi da kuɗi, amma abokin nasa musulmi ne.
Nikuma tun lokacin da nayi ido biyu dashi naji gabana na faɗuwa, take naji gayan ya kwanta min har cikin raina, shinefa na karɓi acont ɗin sa na tura masa dubu ɗari. Kuma tin lokacin bai kiraniba, Allah Bro ina sonsa kuma zan iya komai a kansa.
Salis ya saki baki da hanci yana sauraron ta. Saida ta gama sannan cikin ihuu!! Salis ya ce "Ya isaaaaa, harsaida laɗifa taji tsoro. Ya ce "Arne, ɗan iska, ɗan clup, mai bin Mata, wanda ya mayar da iskaci sana'a, shine kikeso!? Wanda kika ganshi yana shan bakin wata shine wanda zuciyarki ta gani kuma takeso ko!? Cikin ɓacin rai ya ce "Karki sakemin maganar wannan wawan yaron idan kuma kika sake to wallhi sai na lahira ya fiki jin daɗi, shin ina hankalin ki da tinanin ki, mutumin da ba ADDINIMU ɗaya ba, kuma ɗan iska!!! Tashi yayi yana nunata da hannu ya ce "Karki bari Hajiya Babba taji wannan maganar kuma kema karki sake mai-maita zance domin bazan miki ta daɗi ba a kan haka. Kibar ganin wai ina sonki ina damu da dawarki, hakan ba yana nuna cewa bazan iya hukuntaki bane. Yana faɗa ya tashi yabar ɗakin cikin mamaki haɗi da fushi.
Ita kuma LaÉ—ifa kallon bayansa tayi harya bar É—akin sannan ta share hawayen da suka zubo mata tun lokacin da ya fara mata faÉ—a. Ta ce "Kaman yanda nace akansa zan iya yin komai to tabbas hakane zanyi komai koda kuwa ADDINIMU mai yardaba domin nidai ina sonsa.
*AJ. SARAH*
Gudu-gudu sauri-sauri yakeyi domin kuwa yasan ya ɓata mata lokaci sosai. Wayarsa ce tayi ƙara sau babu adaddi amma yaƙi ɗagawa, saida ya gama shirinsa gaba ɗaya kafin ya ɗauka wayar yana mai ɓoye dariyarsa ganin tarin miss call ɗin ta har guda ashirin da uku (23) da sauri ya fito daga ɗakin nasa cikin shiga irin ta masu zuwa club. Cikin mamaki Nana take kallon yayan nata ganin yanda yayi kyu. Ta ce "yaya ina zuwa ne haka kodai kasamo min Anty ne? "Ya buɗe baki zaiyi magana wayarsa ta sake yin ƙara a karona ashirin da huɗu.
Kallon Nana yayi wacce ke fama da figar kajin da AJ ya kawo ɗazu wai sune abincin dare haɗida dankalin turawa. Ya ce "Idan ban dawoba kisaka min nawa a ɗaki komai dare zan zo na ci. Nana ta ce "to yaya amma dan Allah karka daɗe kaji...kuma ka gaida minda Anty na.ta faɗa tana dariya. Jin wayarsa ta sakeyin ƙarane yasa ya amsa da cewa zataji, sannan ya bargidan.
SARAH kuwa iya ƙuluwa yau ta ƙulu hakanne yasa tayi alƙawarin saita nuna masa fishinta. Kallon sa takeyi cikin mantawa da laifin da yamata ganin irin wani kyu da yayi. Da sauri ta rungume shi tana mai jin cewar ko ina zasu iya shiga dashi ba wanda ya isa ya raina mata saurayi. Yau kan A.J ya ajiye komai a gefe ya kama hannun ta suka nufi gurin da a ke gabatar da birthday ɗin.
Cikin dare misalin ƙarfe 12 Daddy ya dawo gida. Yana zuwa ya nufi ɗakin sa, sai yaga ɗakin a buɗe, hakanne yasa ya nufi ɗakin Mommy yana kiran sunan ta. A'leza! "Da sauri Mommy ta fito aɗaki domin kuwa itama barci ya gagareta, tinda SARAH ta fita bata dawoba, shi kuwa Samuel dama yasaba. Cikin yarunsu na tibi Daddy ya ce "Nace ki rufemin ɗaki lokacin da zan fita amma na dawo naga ɗakina a buɗe? Ya ce gaba da cewa...Shin kunsan irin kuɗin da na ajiye a cikin ɗakin! Kuma kinsan kuɗin waye? Lokaci ɗaya fuskar Daddy ta koma ta asalin sojojin da ransu ya ɓaci. Ya ce "Oyaa muje ɗakin mu duba.