← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 67

Sashe 62

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Shin dama da gaske kake nufin kanada wacce kakeso? Dama ba sona kakeyiba yauda ta kayi kenan? Ibarahim ya ce "Please zo ki zauna muyi magana dan Allha. Yayi maganar yana binta da kallon tausayi. Ba dan tasoba ta zauna kusa dashi tana jiran taji yace duk wasa yakeyi itace zaɓinsa. ya ce "Laɗifa bazan ɓoye mikiba tunda nake dake ban taɓa sonkiba, da farko dai nayi sha'awar ki har na ƙudirta a raina saina sameki kota yaya, amma da naji cewar keɗin yar uwata ce ta jini sai naji hakan ba zai taɓa faruwa tsakanin nina da keba, hakanne yasa na yaƙi zuciyata har na samu nacire abun da nakeji a kanki, yanzu ina miki kallon Fatima ne, inasonki so irin wanda yaya yakewa ƙanwarsa wallhi Laɗifa bansa haka so yakeba saida na haɗu da Hadiza, kallo ɗaya na mata yarinyar ta tafi da imanina ina sonta sosai Please dan Allah ki fahimceni ba yaudarar ki nayi ba.

Ladifa ta kalleshi da kyu cikin kukanda ta ke yi ta ce "Dan Allah karka min haka wallhi ban taɓa son wani ɗan namijii a duniya ba in banda kai! Shin kasan tun yaushe nake sonka? Tana kuka ta na ce wa "Tun lokacin da na ganka a club kuna wannan wasan game ɗin kiss tun alokacin na fara sonka kuma har yanzu yi nakeyi amma yanzu lokaci ɗaya kace wata ka keso! Yanzo kodan dangantakar da ke tsakanin mu bazaka iya daurewa ka aurenuba haba Ibrahim!

Ibrahim ya matso kusa da ita kamar zai shiga jikinta ya ce "Laɗifa bakisan so ba, haƙiƙa da farko naso na cuci kaina da cewar inason ki, kuma duk sha'awa ce sai yanzu da na haɗu da wacce nake so sannan na banbance so da sha'awa, shi so ba'a masa alfarma ko tilastawa shi ɗin gaban kansa yakeyi a kan abun da yake so, baya shawara da kowa yake shiga zuciya, saboda haka ki daure ki fahimci me cece s"...."Cikin fitar haiyaci da rufewar ido ta ƙatse shi da cewa "Ya isa haka!² bana son jin komai naji kaje ka aureta ba sai kana faɗa min irin abunda kake jima, dama ai haka ɗan Adam yake barinma wanda tun farko zuciyarsa ta fara tashi a cikin duhun jahilcin kafirci, ai dama idan bakayi hakan ba ai baka cika jinin wannan ƙaton arnan ba wanda bai son komai ba sai cuta da zalunci, to ai kai abumma biyu ya haɗa maka uwar da uban duk haka su"...Bata ƙarasa ba taji sauƙar wasu lafiyanyun mari a kuncinta wanda yasa ta saki wani ihuuu mai ƙarfin gaske. Hajiya Babba ce da Muhammd suka shigo ɗakin domin jin laɗifa tana faɗin irin wannan magan-ganun.

A wannan ranar Laɗifa tayi na damar wannan furcin nata domin kuwa ba ƙaramin duka tasha a hannun Hajiya Babba ba, dama kuma itama tanada cikinta so take wata tara ya cika kafin ta haifeta, ai kuwa sai gashi yau wata taran ya cika. Shi kansa Muhammd maganar ta taɓa masa zuciya domin kuwa wannan maganar har dashi takeyi ba iya Ibrahim bane, ganin dukan yayi yawa yasa ya hana Hajiya Babba. Hajiya Babba ta ba Ibrahim hakuri a kan karya bi takan zancenta. Ibrahim kuwa a lokacin tunanin iyayensa ya zomasa ko yanzu a wani hali suke ohoo! Ai kuwa dole ya nemo su ko ma a wani hali suke, iyaye ba abun wasa bane, sannan yayi mamakin jin wannan furcin daga bakin Laɗifa, ita batasan cewar abunda yayi daddynta shine yayi naduba, sai kuma ya mata uzuri domin yasan ba'a cikin haiyacinta takeba.

Muhammad ya tambayeshi abun da ya haɗasu. Bayan Muhammd yajine ya ce ya sanar masa gidan su yarinyar da yakeso gobe zaiyi magana da Titi za'a je nemomasa auranta shida Salis. Ibrahim yayi murna sosai, sannan Daddy ya ce "kar Salis da Fatima suji abunda ya faru tsakanin ka da laɗifa, itama zan mata faɗa bazata ƙaraba, kuma kar abun ya dameka a cikin fushi ya take. Shi kam Ibrahim zuciyarsa cike da murnar za'a je zancen auransa ya ce babu wanda zaiji ni harna manta ma.

*AJ POV*

Da sallama ya shigo palon yana raba idanunsa ko zai ganta amma sai yaci karo da Ibrahim zai fita. Gaisawa sukayi yana tambayar ss Sarah. Ibrahim yayi murmushi ya ce "AJ yanzu ta bar Sarah ta koma Fatima, Allah ya nufa mun gane hanyar gaskiya dagani har ita saboda haka ka ajiye sunan Sarah ka koma ce mata Fatima. AJ ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Alhamdulillh Masha Allah! Ina tayaku murnar komawa Addininmu Addinin gaskiya da gaskiya addinin Allah maÉ—aukakin sarki!. Ibrahim ya ce "Muna godiya sosai. "To kai ya sunan ka? Ya ce "Ibrahim Khalil. AJ yace "Masha Allah sunan kakan fiyeyyan halittu kenan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama! Dukkansu suka shafa harda Muhammad dake bayansu yana jinsu.

"Fatima nakeson gani na kirata bata amsaba shine yasa nazo gidan ko lafiy"..."kafin ya rufe baki sai gata ta fito daga ɗakin riƙe da waya a hannu. A zuciyarsa ya ce "Kenan duk kiran da nake mata tana gani ɗaukane bazatayi ba! Kafin kowa yayi magana Muhammd ya ce "Fatima je ki karɓo masa Hajara ya ganta ko? Ya faɗa ne domin yasan abinda ya kawo AJ ɗin kenan wato ganin Hajara da kuma Fatima. Domin kuwa tun ranar da a ka tambayeta wanda takeso ta ji kunya shine Muhammd ya tambayi Ibrahim ko tanada wanda takeso . Shikuma ya kwashe komai ya sanar da Muhammd tsakanina AJ da fatima. Muhammad yayi mamaki sosai jin cewar a she dalilin zuwan AJ gurin su kenan a gidan Comanda Daniyel. "Ok Daddy. Fatima ta amsa tana shiga gurin Hajiya Babba domin ɗauko Hajara. Saida AJ ya sunkuya har ƙasa ya gaisa da Daddy yana mai jin kunyarsa a dun lokacin da suka haɗu. Yana mamakin irin halin sa domin kuwa shiɗin na dabanne

Zaune ta sameshi ya ɗora hannayensa a kansa kamar dai kanne ke masa ciwo. Da sallama ta iso cikin palon har gurin da ya ke ta miƙe masa yarinyar tana jiran ya karɓeta ta bar gurin. Ganin bashi da niyar karɓa ne yasa ta ɗaga kai ta kalleshi sai idanunsu ya harɗe a na juna, ai da sauri ta kawar da kanta tana tsaye a gabansa. "Fatima" Ya kira sunanta da muryar da tasa tsikar jikin tashi, taji yanayin sunan kamar shi kaɗai ya iya kira. "Mai yasa bakya amsa kirana ko kin daina sonane? Ko kinaso zuciyata ta buga ne? Shiru tayi tana jin anya zata iya abunda tayi niya kuwa a kan AJ! Son da take masa a jinin jikinta yake, da shi kaɗai ta saba kuma ita son gaskiya take masa. "Kujerar dake kusa dasu ta ajiye Hajara zata fita sai ji tayi ya kamo hannunta ta baya.

Chak ta tsaya ta juyo tana masa wani irin kallo, hakan yasa ya saketa batare da ya shiryaba. "Karka kuskura hannunka ya ƙara taɓani a karo na biyu, tana faɗa tabar palon da sauri tana tare kukan da ya zo mata. AJ ya tsaya a gurin yana dukan kansa yana tunanin kodai ramawa takeson yi! Haka ya ɗauki Hajara yana kallonta cikin so da soyayya har ya gama wasa da ita ya kira mai akin gidan ta karɓeta. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ya dinga furtawa har ya bargidan.
Chapter 62 · 0% Book details