← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 67

Sashe 31

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

......Daniyel cikin ɓacin rai yaci gaba da cewa "Nace kafitamin daga gida yanzunnan kafin ranka ya ɓaci!! yana faɗa yana nuna masa hanyar waja. Shi kuwa Alhaji Salisu sai murmushi yakeyi yana ƙoƙarin zama acikin kujerun da ke cikin palorn. Da ƙarfi Daniyel ya sake daka masa wata tsawa wacce tasa dukkansu saida suka tsorata. "I see get aut in my home? Da sauri Alhaji Salisu ya meƙw tsaye cikin tsoro da jin irin tsawar da ya masa ya ce "Da ka tsaya munyi mgn cikinnutsuwa da ka faɗa min laifin me nai maka hk? "I don't like to see duk wani Muslim in my from I don't like you. Sai yanzu ya fahimci abunda yasa yake ta wannan ihun. A ƙalla Alhaji Salisu zai girmi Daniyel sosai amma ya kwantar da muryarsa ganin ya ɗauki lamarin da zafi, tabbas Alhaji Salisu yasa da yawa wasu arnan basa ƙaunar musulmai amma baiyi tunanin harda dangin solo ba domin ganin shi solo ɗin babu ruwansa.

Ya ce "Ko zan iya sanin abinda musulmai suka ai katamaka haka da yasa dukkansu kake ɗaukar su ɗaya? Cikin ɓacin rai Daniyel ya kamo solo ya jefashi jikin ahj Salisu ya ce "Walhi idan baibar gidannan ba zan sa a halakashi. Yana faɗa ya bargurin cikin cewa kafin ya fito yabar gidannan. Titi kuwa itama wani kallo tabi Alhaji Salisu dashi irin kallon nan na tsana kafin tabar gurin izuwa ɗakinta. Da sauri solo ya kamu hannun Alhaji Salisu suka bar palon yayinda Alhaji Salisu ke binsa da kallon mamaki.

Bayan sunje gidan Alhaji Salisu ɗinne ya ce "Mai gida dan Allah kayi haƙuri da abunda yayana yamaka, Walhi haka yake baya son musulmai ko kaɗan, Ni kaina hk nake, amma zamana da kai yasa na gane ashe duk abunda ake faɗa mann akan ku ba haka bane.domin gaskiya kuna bani mmmk musamman ma kai, saboda hk kayi haƙuri pls? Alhaji Salisu ya ce "Ai yanzu kaine abun tausayi, domin kuwa Allah ne kaɗai yasan idan ka koma gida me zai maka domin naga ransa ya ɓaci sosai, sannan kuma ɓangaran addini nima kaina kana bani mmk domin kuwa ni baka taɓa faɗamin komai game da yayanka ba. Solo ya ce "Eh kayi haƙuri a kwai abunda yasa ban faɗa maka ba.

Nan dai alhaji salisu yaci gaba da baiwa daniyel ha ƙuri a kan yayi haƙuri da ɗan uwansa. Kuma ya sanar masa da cewar duk abunda yace yayi to karya masa musu.saida solo ya tashi zai tafi kafin Alhaji Salisu ya ce "Shin ko zan iya sanin dalilin kiran da ɗan uwanka yaymin? Solo bai ɓoye masa komaiba ya sanar dashi akan wai zai bashi jarine shine zai shawarci mai gidana. Alhaji Salisu ya ce "karka damu dama nima na gama shawara da mai ɗakina a kan zan maka free domin kuwa ka cancanta, saboda hk yanzu kaje gidan duk abunda yafaru sai ka sanar min?. Cikin ruɗewa da mmk solo ke kallon uban gidan nasa jin abun dayace. Alhaji salisu ya ce "Addinimu wato Addinan musulunci yana da sauƙi haɗi da tsafta, sannan yanada dokoki haka kuma komai munayinsane cikin hukuncin Allah. Addininmu bai banbance mana kowaba wajan keytatawa, sannan bai sa muna kallon kowa a matsayin mai kuskureba, domin kuwa Allah ne mai shiryawa, mutuƙar mutum ya kyautata mk koda kuwa ba Addiniku ɗaya ba to kaima zaka iya kyautata masa, a koyarwar manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama, ya ce koda mutum ya nufeka da sherri to kaikuma ka saka masa da alkairi, duk wani musulmin gaskiya to tabbas ya yarda da wannan. Solo yayi shiru yana jin wani annashuwa na shigarsa, idan ya tuno da kyutar da mai gidan nasa zaimasa, gakuma yanzu wani irin zance da yake masa wanda shi bai fahimci komai ba. Alhaji Salisu ya ce "Karka damu hankali zaka fahimci komai. Cikin bazata Alhaji Salisu yaji solo ya watso masa tambayar da baiyi zatoba.

"To ance wai ku musulmai idan mutum ya kashe wani wai shi ɗan aljannane shi yasa ku kashe mutane babu wahala a gurinku, sannan kuma ana faɗa mana cewar addinin musulunci kashe mutane shine aikinsu, sannan ana cemana wai ku ba Allah kuke bautawaba, wai wannan Muhammad (S a w) ɗin kuke bautawa, Ni kaina na yarda da hk amma zamana da kai sai abun yake bani mamaki domin naga halaiyarku ba hk takeba. Amma abunda ya bani mamaki shine bautar Muhammad (S a w) da kukeyi, ko yanzu naji da idan zakayi mgn shi kake cewa ba Allah ba , kuma naga Allah ne kaɗai abun bauta sai kuma wanda shine ya kamata ace kuna kalla wato jesus domin shine maganar Allah. Shin me yasa kuke bautar Muhammad? (S a w), bayan kuma yanzu haka baya raye, kuma shima mutumne kamar kowa, kuma idan an taɓa shi kuke ɗaukar fansa, me yasa tunda shi Allahnkune ba zai dinga kare kuba, kuma mai yasa..."Cikin sauri da mamaki haɗi da murmushi Alhaji Salisu ya katse shi sannan ya kalli solo jin irin fahimtar da wasu addinin sukewa addinin Musulunci.

Cikin muryarsa mai ɗauke da sanyin murya irin ta wanda yasaba da ambaton Allah ya ce "Duk wani musulmi da kasani aduniya to Allah yake bautawa, shima kansa Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ɗin ma Allah ya ke bautawa, sannan shine ya koyar damu yanda za'a bautawa Allah ɗin. Sannan kuma shi abunda yasa kaka kamar muna bauta masa kuwa shine...shi wannan Muhammad ɗin da kake gani to duk duniya albarkacin sa mukeci harda shi Annabi Isa Alaihissalam ɗin wato jesus. Saboda Allah da kansa ya ce idan muka zo gareshi da soyayyar annabinsa to tabbas zai karɓemu hannu bibbiyu...

Duk wani musulmi da kasani to yana son Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama fiye da kansa, amma duk Allah muke bautawa Bama haɗa shi da kowa wajan bauta domin shiɗin shi kaɗaine, sallah da kaga munayi to Allah muje bautawa, azumi dakaga mukeyi shina ibadane. Solo ya sunkuyar da kansa izuwa ƙasa yana ɗagowa sai ga hawaye suna bin idonsa. Cikin zuciyar Alhaji Salisu ya ce "In sha Allah zuciyar ka irinta masu rabautane da yarda Allah sai Allah yasa ka gane gaskiya yau. Afili kuma ya ce "Solo lafiya kuwa? Cikin kuka ya ce "Walhi mai gida an ɓatar da zuciyoyinmu wajan saka mana ƙiyayar abinda bamuda masaniya akansa, tunda nake ban taɓa zama da wani musulmiba, amma an sakamin ƙiyayar su fiyeda yanda baka tunaniba, ko farkon haɗuwata da kai saida zuciyata ta haneni amma da yake alokacin ina buƙatar taimako sai kawai nace zan ƙwada zamada wanda ba ɗan addininmu ba nagani ko dagaske hk kuke.

Alhaji Salisu ya sauke ajiyar zuciya afili ya ce "Allah sarki, dama ai ba'a yankewa mutum hukunci sai ka zauna dashi kasan halinsa. Haka dai Alhaji Salisu ya ci gaba da nunawa solo cewar duk wannan abunda ake faɗa musu akan musulunci to duk ƙaryane, sannan ya ce masa musulmai basa kashe mutane haka kawai saide idan sunci mutuncin addinisu kokuma Allah da annabinsa, to idan hk ta faru to tabbas addinin musulunci ya tanadar da lada mai tarin yawa ga wanda suka kashe wannan mutumin koda kuwa shiɗin waye. Saida yaga jikin solo yayi sanyi sosai kafin ya barshi ya tafi. Bayan ya fitane allhji Salisu ya ɗaga hannu sama ya ce "ya Allah kasa wannan bawan naka yanada rabon musulumta acikin kwanannan, kuma kasa yayansa karya iya hanashi, shima yayan nasa idan yanada rabon musulumta kasa shi a cikin rahamar musulumci.

Koda solo yaje gida sai titi tahau shi da surutu da ihu a kan mai ya haɗashi da wannan mutumin. Baiko kulataba ya shiga ɗakinsa yana jin kansa na juyawa, kwanciya yayi yana kallon sama yana tunano abubuwan da mai gidansa ya faɗa masa akan addinisu. Tabbas ya yarda da wannan mutumin sannan shi kansa shedani ogansa baida damuwa baida abokin faɗa, yana cikin hk titi ta shigo ɗakin cikin sauri tana cewa "Solomon kamanta abinda Momy tace mana a kan yin alaƙa da wasu wanda ba addinimu ɗayabako? Cikin sauri solo ya miƙe zaune yana tunowa da nasihar mamarsu, hk titi ta cigaba da tuno masa da abubuwa da yawa. Da sauri solo ya ce "Pls titi is ok! Ya faɗa cikin ihu da yasa titi nutsuwa. Ya ce "ina yaya Daniyel? Cikin rawar muryar tace ya fita. Shima fita yayi yana cigaba da nazarin komai.

Yau ranar juma'a ranar da Alhaji Salisu yake aurar da ƴarsa, wanda kowa ke cewa tayi yarinya ganin a lokacin shekararta batafi sha huɗu zuwa sha biyarba, shi kuwa shi yasan dalilin aurar da ita ɗin. A ranar kuma bayan al'umma sun sheda aurarrne kuma solo yazo gurin mai gidan nasa da himmar shiga addinin Musulunci. Alhaji Salisu yayi mmk domin kuwa tun ranar da sukayi mgn bai ƙara ganin saba yau kwana biyar kenan. Cikin mmk yace "Solo kayi shawara da ɗan uwankane? "Idan mutum zai shiga sai yayi shawara da wanine dama? Alhaji Salisu ya ce "a'a ai ka mallaki hankalin kanka.

Babban malamin da ya ɗaura auran shene ya baiwa solo kalmar shahada kuma ya ƙarɓa. Ya ce "Ashi'hadu allailahaillallha wa'ashi'hadu anna buhammadur Rasulullah. Shima Solo ya mai-maita sannan mlm ya fassaramasa cikin turanci wato...

(ka sheda babu anin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan ka yarda cewa Annabi Muhammad manzan sane kuma bawansane)

solo ya ce eh na sheda. Take kuwa gurin kowa ya ɗau ƙabbara cikin farin cikin cewar yau addinin Musulunci ya samu ƙaruwa. Nann aka tambayeshi wani suna ya keso? Babu wata-wata ya ce "Muhammad! Nan fa al'umma suka ƙara yin kabbara.

Bayan an gama komaine anyi wankan shiga musulunci da dai sauran abun da shari'a ta hukunta, saikuma aka fara sanar masa da komai na cikin Addinin. Alhaji Salisu ya ce "Shi indai wannanne zai koya masa komai cikin ƙanƙanin lokaci cikin yardar Allah. Masu masa kyuta nayi masu masa addu'a nayi, haka dai ranar solo wato Muhammad da Alhaji Salisu da iyalan gidan Alhaji Salisu suka kasance cikin farinci da walwala jin cewar ta sanadiyarsu Addinimu ya samu ƙaruwa. Wanda shikuwa Daniyel ranar Lahadi mai zuwane auransa, kuma baisan bidirin da akeyiba itama titi bata saniba.
Chapter 31 · 0% Book details