← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 67

Sashe 65

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɓangaren su Daniyel kuwa ƙafa sai ci gaba takeyi da kumbura daga ƙarshe ma sai yan keta a kayi. Mahaifin Momy Elixa kuwa da kansa yazo ya tafi da ƴarsa a kan zaman su ya ƙare. Haka badan tasoba ta tafi tabar mijin nata dake cikin mawuyacin ciwo. Saidai kuma tana zuwa gidan uban nata taji bazata iya zamaba saboda takura da matar ubanta da dangi suke mata, kasancewar anji labarin yaranta sun koma yin Sallah. Kasancewar mahaifinta babban Pastor ne sai yace dole taje ta dawo da yaran dangin su, ita kuwa ganin yanzu yaranta sun koma rayuwar farinciki da kwanciyar hankali ga annuri dake tashi a fuskokinsu ne yasa ta ce sam bata san da wannan zancen ba. Hakanne ya jawo mata suka a gurin ubanta da matar ubanta domin suna jin cewar itace tasa suka bar addidinsu.

Lokacin da Ibrahim yazo gida Sadiya ta sanar masa da cewar mahaifinta yazo ya tafi da ita. Ai kuwa har gidan yaje ya dawo da ita sannan ya musu gargaɗi da cewar su fita a harkarsu. Alokacin da pastor yaga Ibrahim saida gabansa ya faɗi ganin yanda ya cika masa fuska, lokaci ɗaya yaron ya masa wani baƙe-baƙe sai kace ba Samuel ɗinsaba.hakanne yasa ya kasa cewa komai har ya bar gidan.

Muhammad ya kira Salis da Ibrahim ya zaunar dasu a kan batun aiki. Ya sanar musu da cewar kafin a ɗaura auransu ya kamata a ce dukkansu sun fara aiki. Ibrahim ya shida masa cewar ai shi takardunsa sun ƙone a wancen gidan nasu. Shi kuma Salis ya ce "Dama shi yana ɗan zuwa saidai ba sosai ba. Muhammad ya sanar masa da cewar kar yaji komai za'a samar masa wata takardae. Ibarahim ya ce "No Daddy takardun sunanan domin gaba ɗaya mommy ta kwashesu lokacin da zamu bar gidan. Cikin ikon Allah kuwa yaje ya tambayi Momy ta kwaso masa harda nata da na Daniyel, Zara kuwa dama ita bata kammala Secondry school ɗinta ba. Take Daddy ya ce da Salis a je campaign su na Abuja a ma Ibrahim intabiyu idan yaci a bashi opiece. Ai kuwa takardunsa sunyi kyu domin kuwa yanada ƙoƙari. Haka a ka masa intabiyu kamar yanda a kewa kowa kuma yaci. Daddy ya mallaka masa gida a habujan domin a can zai zauna da matarsa, sannan Daddy ya ƙara siyan wani gidan ya ce na su Daniyel ne, idan ya warke zasu koma can. Ibrahim ya share hawaye ya ce "Ka manta da cewar a kwai hukuncin kisa a kansa koda ya warke? Kawai kabar siyan gidan Momy kuma zamu zauna tare a gidana, yanzu babban burina shine ace Daddy ya karɓi kalmar shahada kafin su kasheshi. Daddy da Salis suka amsa da amin in sha Allah zai karɓba.

*BAYAN WATA BIYU*

Zaune yake kamar yanda ya saba a koda yaushe ya ƙurawa waje ɗaya ido yana sauraron maganar da matarsa take masa a kan cewar gobe ne auran Samuel da Sarah dukda kuwa yasan da zancen. Tana maganar ne badan tasan zai amsa mata ba amman dai tasan yana jinta. Da mamaki taga ya gyaɗa mata kai yana son yin maga amma ya kasa. Tana cikin haka Salis da Zara da Ibrahim da Laɗifa da Muhammd da Hajiya Babba riƙe da Hajara da ta fara wayo suka shigo ɗakin suka zauna suna kallonsa. Burinsu shine Daniyel ya furta kalamar shahada kafin ranar Lahadi, domin kuwa sojojine sukazo har gida a kan cewar ko ya warke ko bai warkeba ranar za'a yanke masa hukumcin. Zancen ya bazu a ko'ina har gida rainiyo da jaridu, domin kuwa babu wanda baisan Commanda Daniyel ba a lokacin sa. Babu yanda basuyi dashiba amma ya kasa magana sai kallonsu ya keyi, yau sama da kwana goma kenan suna so ya furta koda kalmar shahada ce amma ya kasa cewa kimai. Ibrahim yaje ya ɗauko takarda da biro wai ya rubuta kalmar shahadar amma ya kasa ɗaga hannayansa ma bare a je ga rubutun. Zara da Momy sai kuka sukeyi. Zara ta kalli mommy ta ce "Pls Momy kema ki dawo Addininmu addinda shine na gaskiya Please! Momy ta gir-giza kai alamar bazata iyaba babanta zai kasheta. Babu yanda busuyi da itaba amma ina Eliza ta ce "bazata iya barin addininsu ba.

Haka dai suka bar gidan cikin tausayin halinda suke ciki. Washe gari da safe a ka ɗaura auran Salis da Nana sai Ibrahim da Hadiza sai Abduljabaru da Fatima Zara. Ɗaurin auran ya samu halarta mutane sosai, duk wani maaikacin dake aiki a ƙarƙashin su Salis to saida ya halarci taron, haka shima AJ mai mutane kala-kala. Shima Ibrahim haka ta ɓangaren abokansa musulmai dama wanda basuba sun halarta. Amarya Hadiza tasha kwalliya kamar ba itace wannan ballagazar ba, ta natsu tayi kyu cikin kayanta na amare. Gefe guda kuma ga angonta fuskarsa cike da annuri da kuma damuwa duk a tare da fuskar tasa.

Kasancewar ranar juma'a a ka ɗaura auran kuma ranar Lahadi ne Daniyel zai karɓi hukunci irin na sojoji, hakanne yasa a kace sai ranar juma'a ta sama kowace amarya zata tare a gidanta, Auran dai kawai a ka ɗaura. Ɓangaren Laɗifa kuwa sai a ranar tayi ido huɗu da Hadiza ai kuwa kallo ɗaya ta mata ta ganeta, cikin wani tsananin mamaki take Binta da kallo domin ko shekka babu itace wannan mara kunyar yarinyar kuma ballagaza. Ita kuwa Hadiza tana haɗa ido da ita ta ga kamar ta ganeta, domin kuwa ita har ga Allah ta manta da ita, domin kuwa ita batasan adadin mutanen da tayi faɗa ko zage-zage dasuba. Hakanne yasa laɗifa shiga wani hali tana neman Umar akan mai yasa bai sanar mata da cewar ƙanwarsa ce yarinyar da Ibrahim zai auraba har saida a ka ɗaura auran ta sani. Abunka da wanda bai san komaiba sai yaudaran ƴan mata da ya sabayi a baya, bai duba irin halin da take ciki ba a wannan lokacin kawai ya furta mata kalmar da tun safiyar yau yake ta bitarta kafin ya fito daga gida, ya aiyanawa kansa cewar ko kasheshi zatayi saidai tayi amma sai ya sanar da ita.

"Tasss" Kakeji ta ɗauke shi da wani gigicacan mari tana nunashi da hannu cikin huci da ɓacinrai..."Baka da hakalune harni zaka kalla kace kana sona saboda na sakar maka fuska ko? To Wallhi idan na sake ganin ka a gidannan saina sa an ɓatar da kai wawa ɗan matsiyata. Tana kaiwa nan ta koma ciki ta barshi a gurin riƙe da kunci yana kallonta har ta shige gida. Murmushi yayi ya ce "Zan iya jure komai a kanki domin kuwa ina sonki!.

Ɓangaren Salis kuwa a daran ranar da a ka ɗaura auranne ya saci jiki ya nufi gidan su Nana ganin AJ baya gidan yana tare da su Abdalh da sauran abokansu. Gidan ba mai gadi sai ya sauƙo ya buɗe get da kansa ya shiga gidan, guri ya samu yayi paking sannan ya nufi ciki harda haɗawa da gudu, kasancewar ba'a gidan a ke bikin ba sai bai ga mutaneba sai kawai ya nufi palon domin kuwa ba baƙonsa bane gidan. Yana tura ƙofar palon zai shi sai kuwa yaji sauƙar flet a kan hancinsa, kafin ya ankara saiga gorarr ruwa ceke da ruwa shima a kan goshinsa. Ai da sauri ya saki ƙofar ya koma da baya yana riƙe hancinsa.

Safara'u da Kadija kuwa da suke faɗa basuma san da shigowar Salis ɗin ba, ita kuwa Nana a kan idonta abun ya faru, domin lokacin da Safara'u ta jefo plet ɗin Kadija kuma ta sun kuya sai tabi flet ɗin da kallo. Da sauri tabi bayan Salis ɗin. Ai kuwa ta sameshi a bayan ƙofar har hancin yayi ja, ga kuma jini yana zuba. Abun sai yayi kamar abin dariya, amma sai ta dake tana masa sannu. Da gyar ya ce "Kuna kiwon mahauka a gidanku ne dama shine baki sanar min ba? Wannan karan kam sakin dariyar tayi tana ce wa "A'a ba mahaumkata bane. Cikin zafin ciwo ya kalleta ya ce "Au ke abunma dariya ya baki ko? Ta ƙunshe dariyar ta ce "A'a to ma wai kai me ya kawo ka gidan nan a wannan lokacin? Tana maganar tana ɗauko gorarr ruwan tana zuba masa a fuskarsa yana wanke jininn. Sai da suka gama wankewa ya bata amsa da cewar "Rabon hancina ya fashene ya kawoni.

Ya faɗa yana matsowa kusa da ita riƙe da hancin da yayi jaaa. Ta ce "Please za"...."Shiiiiiiii. ya katse ta yana ɗoro hannusa a kan bakinta. Ganin yanda ya matso dafda itane yasa jikinta fara rawa tana neman hanyar arcewa. Salis ya matso da bakinsa kusa da nata saura kaɗan ya haɗe sai sukaji an daki ƙofar da sauri wanda yasa duk saida suka tsorata. Da ƙarfi ta tureshi ta buɗe palon ta shiga a kunyace. Lokacin kuwa Kadija da Safarau sun bawa hammata iska sosai, domin kuwa mai rabun batanan. Da mamaki Salis yake kallonsu ganin yanda suka lalata tufafin jikinsu, wata har jinine a bakinta wata kuma a hancinta. Ga kuma palon shima an faffasa abubuwa. Gaba ɗaya kallonsa sukeyi domin kuwa babu wacce bata sanshiba. Ya tambayi ba'asin abinda ke faruwa. Suna cikin tsara masa saiga AJ ya shigo gidan.

Cikin ɓacin rai ya ce dukkansu su tattara a darannan subar masa gida. Nana ta ce "No yaya zunzo taya amarya kwana nef"..."Amaryar banza! Ya faɗa ransa a ɓace. Ai kafin kace cass har sun bar palon suna hararar juna. Saida ya rakasu har waje kafin ya rufe gidan ya dawo, yana jin yanda Safara'u ke cewa zata ɗauko kayanta amma bai ko bi ta kantaba. Yana shiga palon idonsa ya sauƙa a kan hancin Salis. Dariya AJ yayi wacce rabonda yayi dariya a gaban Salis har ya manta domin kuwa har yanzu kunyarsa ya keji. "To oga zamu rufe gida? Salis ya ce "Nima a nan zan kwana" Nana ta waro ido waje ta ce "No a'a wallhi ba ruwana. AJ ya ce "To kawai ka ɗauki amaryar mana katafi da ita ba sai kamin tashin kunya ba. Salis ya ce "Tom nidai koma me zakuce Allah bazan tafi da fashenshen hanci ba. Ƙarshe delo a gidan ya kwana...📝 ( *Muhaɗu a gurin harbe Daniyel)*

*Comments É—inku shine abun alfaharina*
Chapter 65 · 0% Book details