← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 67

Sashe 7

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokaci d'aya haushin abun da Zainab d'in tamasa da kuma abun da ya tarar d'in suka had'e masa yanzu, yanufi gurin da suka jona wayar, yana zuwa ya cire wayar daga cikin abun speaker d'in, baiyi wat-wataba ya buga wayar da 'kasa.

Ita kuwa Maryam jin an katsemata yasa ta juyo da niyar zagin qawar tata, a tinaninta itace ta kashe. Ai kuwa tana juyowa sukayi ido hud'u da shi, kafin kace me ya d'auke ta damari, had'i da bin kawayen nata. Sukuwa basubi ta kan jakokinsu ba da ta'kalmin su, ita daiyar ma harda gyalenta da wayarta. Haka suka fita da gudu, shikuwa ganinn sun gudune yasa ya dawo gurin Maryam, itama ta nufi d'akin ta da gudu tana kiran sunann Mommy.

Dai-dai ta turo 'kofar zata rufe shima ya iso d'akin, kafin ta tura ya rigata, ya turo, hakane yasa ta fad'a a tsakiyar d'akin. Nann ya cire hular kansa,. Sannan ya zare wayar caja dake d'akin ya shiga lamta mata, tana ihuuu yana zabga Mata, saida ya mata shegen duka kafin ya ce "Bade ke mai taurin kaiba muje zuwa ina dai-dai da ke... tsabar kin raina mutane kizo har gida kina kunna mana wa'ka!? Ya kara d'aga wayar ya labtamata, har saida Maryam ta daina kuka tsabar azaba.

*AJ POV*

Sarah waye ya baki wannan kud'in!? Yafad'a yana 'kura mata ido?

Sarha ta ce "please 'kar'ba in kuma bakaso tom na koma dasu?. AJ ya kar'ba ya 'kirga yaga dubu d'ari dai-dai, kallonta yayi ya ce "To amma yanzu yazaa..." Zamuyi waya kar Daddy ya dawo yaga bananan. Haka ta sake rungumarshi sanna ta tafi, ta barshi tsaye yana kallon ta. Shima cikin kasala ya kama hanyar gida.....📝

*
*PAGE* 👉6️⃣

............ A.J. Duk yanda yakai da son kud'i yaukan yaji ya tsorata da wannan kud'in, shi babban tashin hankalin sama shine... kar Daddy ya kama Sahra ita kuma tace shine yake turata. Haka ya shiga gida jiki babu 'kwari. Ko sallama baiyiba ya shiga gidan nasu yana tinanin mafita, Nana ce kad'ai a tsakiyar gidan tana cin abinci, hakanne yasa ta tsaya tana kallon yanayin yayan nata. "Yaya Lafiya kuwa kake?. Shikuwa A.J baima san tanayiba. Ganin bai bata amsa ta ce "Yaya kiran sallar isha fa a keyi kuma naga kashigo gida? Cikin hanzari ya dawo daga tinanin na sa ya ce "Sorry na mantane yanzu zanje nayi. Tana kallosa ya bargidan da alama dai wani abun na damun sa.

*SALIS POV*

Kallon 'kanwar tasa ya keyi cikin soda ƙauna, tinda suke tare da ita basa ɓoyewa junann su komai domin kuwa ko saurayine yazo gurinta tofa saita sanar da shi haka shima, dukdade shi baitaɓa cewa yana sonwata yarinyar ba. Akaro na farko kenann yakejin bazai iya sanar da ita abun da ke ransaba, saninn halinta na kushe zaɓin wani.

Cikin zuciyar sa ya shiga tinann abun da yafaru yanzu minti kaɗan da suka huce. Tsaye yake a 'kofar gidan su AJ yana jiran yaga yaro ya aikeshi ya kira masa AJ, kasan cewar yakira wayar AJ ɗin bata shiga. Yana tsaye ya ga yaro yazo shiga gidan, nann take ya sanar da yaron cewar in ya shiga yace ana neman AJ. Bayan kamar minti 2 yaron yazo ya ce wai bayanann amma ga ƙanwarsa wai zataga kowaye in yazo sai a faɗa masa. Salis ya ce "ok. Sannan ya kira yaron ya masa ihisani. Cikin gidan kuwa Innah ce ta ceda Nana taje ta dubo kowaye, domin kuwa sunsan A.J da abokai kuma duk yaran masu kuɗi.

Hakanne yasa ta saka hijab ta nufo ƙofar gidan. Leƙowa tayi ta hango baƙar mota a fake a ƙofar gidan, gakuma mutum a jingine a jikin motar, hakanne yasa ta nufi gurin sa. Tana zuwa tayi sallama haɗi da gaishisa. Salis da yake danna waya, ko kallonta baiyiba ya ce "Idan A.J yazo kice masa Salis ne yazo kuma kuce yasameni a gid... Maganar tasa ce ta maƙale a bakin sa sanadiyar tozali da fuskar Nana.

Cikin rikicea ya ce "am am am kikace baya gida ko? Nana ta ce " Eh baya gida amma yanzu zai dawo.

Ai take Salis yayi mutuwar tsaye jin wata sassaiyar muryarda tamasa magana da ita. Ya ce "To kice Salis ne yazo neman sa, Kuma kice yazo gida yanzu.

Nana ta ce "to zan fad'a masa, tana faɗa ta juya ta nufi gida cikin takunta na yan mata masu natsuwa. Salis kuwa neman fad'uwa ya keyi ganinn yanda take tafiya kamar zata karye, haka ya bar ƙofargidan cikin begen Nana.

Sauke ajiyar zuciya yayi bayan ya dawo daga tinanin.

LaÉ—ifa ta ce "bro lfy kuwa tin É—azu kazo Kanata tinani kuma kayi shiru?

Salis ya ce "sis ina maganar da hajiya Babba tamana É—azu?

LaÉ—ifa ta ce "Maganar aure ko maganar yaronnan abokin ka É—an talakawannan?

Salis kuwa cikin ranshi ya ce "Allah ya sa ban faÉ—a mataba da wallhi bazata goyi bayana ba. Afili kuwa ya ce " maganar aure... Na yarda zanyi domin kuwa nasamu wacce na keso. Cikin mamaki LaÉ—ifa ta ce "Yanzu-yanzu daga kaje gidansu A.J ka dawo kace min kasamu matar aure? Salis ya ce "Yes haka Allah yake abun sa. LaÉ—ifa ta ce "Tofa!! Lallai koma wacece ta iya kamu, tabaÉ—a had'i da yin dariya sannan ta ce "ya sunann ta? Salis ya ce " ban saniba, bata faÉ—a min ba.

LaÉ—ifa ta ce "To yanzu dai muje mu sanarwa da hajiya Babba, kaga itama saita dena maganar aurannan nata ko ya kace? Salis ya ce hakane tashi muje?. Haka suka jera suna tafiya LaÉ—ifa na tsokanar sa, wai wata yarinyar tayi WUFF da shi a cikin lokaci kaÉ—an.

*ABDALH POV*

Cikin tsananin ɓacin rai ya bargidan ya nufi gidan sa wanda ke unguwar hotoro ɗan marke, yau ransa in yayi dubu to duk sunɓaci, baisan yazaiyi da Maryam ba, a'ce wai ƙanwarsa da suke uwa ɗaya uba ɗaya itace keyin rawa, rawa da waƙar ƴan bidi'a!!?. Yanufi gidansa da niyar bazai dawo ba sai gobe domin a'san yanda za'a yi da Maryam, kawai aure za'a Mata. Wata zuciyar ta faɗa masa, ai kuwa ya aminta da hakan.

Maryam kuwa bayan Abdalh ya fi ta, ta yunƙura da niyar tashi amma Ina, take ta sake rusa ihuuu, hakanne yasa nura da tin shigowar yayan nasu yagudu,. ganinn yanda fuskarsa ta ɓaci. Dukda nura bashida ƙarfi haka ya taimaka mata ta miƙe tsaye ,ya kwantar da ita a kangado. Abin dariya amma ba damaryi, haka ya gintse dariyarsa ganinn yanda takeyi kamar wacce a ka ɗaye fatar jikin ta, ga ihuu da takeyi. Ganinn kamar nura nason yin dariyane yasa cikin kuka ta ce "Wallhi nura in kasake naji dariyarka saina kusan karkaryaka.

Shikuwa nura jin yanda tayi maganar cikin kuka da rakici ne yasa dariyarsa kufcewa, aikuwa ya saki dariyar, haɗi da sakin ta ta faɗa kangadon da ƙarfi. Aiku mai neman kukane aka jefeshi da kashin a waki, nann take kuka ya dawo sabo, tadin buɗe baki tanayi, shikuwa nura yabar ɗakin yana dariya.

*ZAINAB VOP*

Dariya takeyi wacce rabon da tayi irin ta harta manta. Kallon Isa tayi ta cigaba da bashi labari. "To bayan ya tafine mukayi wa'azi sauran abokan nasa harda wani kafeni da ido, Nikuwa ko ta kansu bambiba.

ISA ya kwashe da dariya sannan ya ce "Amma fa kin burgeni Wallhi, wani abuma saigobe in munje kusa da gidansa gabatar da walimar da zamuyi, nifa Allah har na matso naji wannan sabuwar wa'kar da kikace zakiyi mai taken bud'ad'd'iyar wasi'ka.

Zainab ta ce "Yanzuma zan je na ƙarasa aikinta, ai i'na sane da Al'kawarin da na ɗaukarwa mlm. Isa ya ce "Ɗazu Aliyu yazo wai ya kira number ki baki ɗaga ba? Zainab ta ce " Oo!! Allah sarki ban sanar dashi batun zuwana walimar bane, Kuma kasan idan i'na kan aiki bana ɗaka waya, Allah dai yasa baije gurin mlm ba?

ISA ya ce "Nima agurin mlm ɗin na ganshi, kuma nasan maganar ce ta kawoshi, kuma zakigani mlm zai miki mgn. ISA ya cigaba da cewa "To Zainab in kina sonsa kawai kiyarda ayi auran mana tindade shi yace ko yaushe kika shirya?. Zainab ta miƙe ta bargurin haɗi da cewa Yaya zamuyi mgn anjima yanzu inada aiki.

*LAÆŠIFA SALIS. POV*

Salis ya ce "No Sistar karmu sanarwa da hajiya tukunna, saboda ban samu mun yi magana da yarinyar ba, kibari nann da kwana biyu lokacin mun shirya da ita. Lad'ifa ta kwashe da dariya sosai kamar zata faÉ—i sannan ta ce "Kai bro karfa kodai kaima irin mazannanne masu tsoran Mata?

Salis ya ce "Dama a kwai mazan da suke tsoran Mata!?

"Hh mana ga É—aya ma a gabana.

"Haba yarinya aini jarumin mazane, ke bama niba duk mai irin sunan Salis to yanmata ma shakkarsa sukeyi.

LaÉ—ifa ta ce "Tom zade mugani

.Haka suka bari sai ya shawo kan yarinyar. ( Wanda ya kasance ranar ne A.J yaje gurin Hajiya)

*A.J POV*

Bayan ya dawo daga sallar isha ne ya shigo gida, cikin kwarin gyiwa domin kuwa zuciyar sa ta bashi tabbacin kawai yaci kuɗin domin Sarah bazata tona masa asiri ba. Kallon Nana yayi ya ce "NANA goba zan baki wayata iyah kuma zansiyo mata ƙarama, amma fa bance ki dinga tara number samari a waya ba, kuma kullum sai na Kar'bi wayar naduba, kin yarda?

Da sauri ta barcin abincin da sukeyi tare da yayan nata ta ce "Yaya wallhi na yarda, ni daga number ka sai number Innah sai kuma number kadija ƙawata shikenan. AJ ya buɗe baki zaiyi magana yaji wayarsa na ƙara, yana dubawa yaga number Hajiya wacce ta bashi akan zata kirashi, da sauri ya ɗaga yana cewa hello Hajiya?. "AJ hajiya Babba ta Kira sunann sa ta cikin wayar.

"Na'am"

Hajiya ta ce "Kazo gida misalin qarfe goma na safe, kuma banason Africa time?.

"Angama Hajiya in Sha Allah zanzo. Amma hajiya kituro Salis sai mutafi tare da shi?

Da sauri Hajiya ta ce "no banason yasan da zuwanka, Kuma karka sanarmasa da cewa kazo kuma duk aikin da na baka karka nuna masa komai kaide yardarka kawai nake buƙata.
Chapter 7 · 0% Book details