← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 67

Sashe 20

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy ta ce "Abdalha me nake gani? Shin da gaske kaine ka sace ta!? Mommy tayi maganar bakinta na rawa kamar zatayi kuka ba. Cikin zuciyarta ta ce "ya Allah karka nunamin wannan ranar. Maryam kuwa wani irin dariya ta bushe dashi tana cewa "To ai basai an tambayaba, ninasan yaya son Zainab yakeyi kuma bazai iya faɗa mataba shine ya sace ta, ai kuwa abun zaibada citta, kunga kafin ya dawo da ita soyayya tayi nisa. Ta ƙarasa maganar tana mayarwa da Nusaiba wayar sannan ta juya zata koma ɗakinta.

*NANA* *POV*

Cikin mamaki ƴansanda suke kallonta jin yanda tayi maganar cikin ihuuu. Wannan ɗan sanda da ta kira da wannan ihune ya nufo gurinsu cikin ɓacin rai, yana zuwa ya wanke mata fuska da mari, kafin ta ankara ya ƙara mata, wanda yasa Nana faɗawa jikin Innah ta saki wani kuka mai ƙarfi, itama Innah kuka takeyi. Cikin muryarsa da suke tsananin tsoro ya ce "Dan uwarki ko ance miki nann gidan ubankine da zaki dinga magana yanda kikeso, yana maganar yana buɗe gurin da makullin hannusa ya tura ya shiga, ya ɗago Nana daga jikin Innah ya ce "Wato ke mara kunyar ko? Banace karna ƙara jin muryarku anann ba? Duk abunda ya ke cewa inna bataji domin bada Hausa ya keyiba. "Kunci sa'a ku matane amma Walhi da sai kunsan kun shigo nann. Yana kaiwa nann ya turata ta faɗi kafin ya harari Innah yana ficewa daga gurin.

Haka Nana taci kuka har tana ciwonkai, sannan ga yunwar da ta ƙara rikice mata ciki. Haka suka zauna a gurin har, bayan sallar la'asar. Izuwa wannan lokacin kuwa har Nana ta daina kuka tsabar azabar yunwa, ita kuwa Innah kwanciya tayi tana jin kamar kayan cikinta zasu zubo, idonta a kafi tana kallon sama. Suna cikin haka sukaji ana kiran sunan Nana.

"Nana... "Nana... Nana? Dukda cikin rawar baki yake maganar da kuma sauri, amma hakan bai hana Nana gane muryar waye ba. Tana ji amma ta kasa magana jitakeyi kamar tana magana amai ne zai zibo, ita kuwa Innah batasan ma me a ke cikiba. Da sauri Salis ya ce da ɗan sanda ya buɗe masa gurin da sauri, amma police ɗin ya ce "Ai ba haka sukayiba, sunyi a kan kawai zai gansune ya tafi, da sauri Kamal ya ce da ɗan sanda Please dan Allah ka taimaka baka ganin halin da suke cikine? Police ɗin zaiyi magana SALIS ya ƙara zaro kuɗi ya miƙa masa haɗi da cewa Please ya buɗe.

Ai kuwa take ya buɗe musu, Salis ya yi kan Nana yana kiran sunanta, yayinda Kamal kuma yake ɗaga Innah. Ganin suna ƙoƙarin fita dasune yasa police ɗin cewa "Lfy kuwa ban gane ba? "Asibiti zamu kaisu baka ganin yanayin sune? Cewar kamal yana kallon police ɗin. Wani irin zaro ido police ɗin yayi yana cewa "Kai! Kai! Kasan kuwa me kake cewa? To wallhi idan har nabari kuka fita dasu to nabar aikina kenann, yanzu ma lokacin ku ya ƙara kuzo ku fita karku jamin masifa, yana faɗa yana jawo ƙofar zai rufe.

SALIS da Kamal sunyi yin duniya amma ya ce bazasu tafi dasuba, mutanan da sukayi sata, cikin mamaki suka ce "sata!! Police É—in yaga alamar fa suna son jawo masa masifa ne, nan danann ya rufe gurin yana cewa idan baku bar gurin ba kuma za'a haÉ—a daku. Da kyar dai police É—in ya barsu a kan zasu dinga kawo musu abinci, safe rana dare, shima a kan zasu dinga biyan sa. Haka Salis suka yarda, take sukaje suka siyo musu abinci da magani suka kawao musu.

*A.J .HAJIYA BABBA* *POV*

Aruɗe ya kalleta domin kuwa ta tsorata shi, da sauri ya karɓi kayan da take miƙomasa ya juya baya yana sakawa ransa a ɓace. Saida ya gama sosai kafin ya buɗe ƙofar toilet ɗin ya fito yana wani haɗe fuska. Kan abar sallar da yaka tayi shima yaje ya tada sallah ko kallon inda take bayayi. Bayan i idar ne ya ɗaga hannu yana addu'a wanda ni (S REZA bansan me yake roƙaba)

Bayan ya idar da addu'ar ne ya kalli Hajiya Babba cikin haÉ—e fuska ya ce "ina wayata?

Hajiya Babba ta tasu tazo har gabansa sannan ta ce "Good morning angona, da fatan ka tashi lfy.tana faɗa tana ƙoƙarin zama a kusa dashi.

Cikin sauri ya miƙe tsaye haɗi da cewa "Please dan Allah kibani waya wallhi Innah ta zan kira ban saba kwana ba tare da suna kusa daniba, Please dan Allah kiyi haƙuri karki ce wannan ma yana cikin kwangilar mu Please? Aj ya ƙarasa Maganar kamar zai sa kuka.

Hajiya Babba kuwa wannan abun da yayi sai yamata kyu, domin kuwa tana son ganin namiji na shaƙwaɓa, abun burgeta ya keyi. Cikin kwantar da muryar, kamar wata budurwa kai ka rantse da Allah cewa ba itace ta haifi laɗifa da Salis ba ta ce "Haba mijina acikin wannan asubar zaka kirasu ai sai kasa suyi tunanin ko ba lafiyaba, kabari zuwa safiya sai ku gaisa kafin mu tafi, Please yanzu kaje ka huta nasan a gajiye kake, Please, ta ƙarasa tana kawar da hannusa da ya miƙo mata tin ɗazu a kan ta bashi wayar.

Tabbas da alamar dai AJ bai gane me hajiya take nufi da cewar kafin su tafiba, shi yayi tunanin ko kafin su tafi gidane. Hakanne yasa ya kasa cewa komai domin kuwa kewar su Nana ce ke damunsa, gakuma sabon al'amari da yakeji a tare dashi yanzu tsakanin sa da Hajiya Babba.

Anann kan daddumar ya kwanta yana tunanin abuwa masu yawa wanda zaiyi idan ya gama cinye wannan kuɗin. Sai gani yayi itama tazo kusa dashi ta kwanta tana haɗe fuskokinsu, ai da sauri ya miƙe zaiyi magana ta ce "A cikin sharuɗanmu babu raba shin fiɗa mutuƙar zamu kwanta tare.

AJ ya ce "Amma ai baki faÉ—a hakaba, kuma ai yanzu ba barci zanyiba, kawai zan hutane. Ya faÉ—a yana tuno suman da yayi É—azu. Ta ce "Ai na faÉ—a maka cewar zamu kwana duk lokacin da naso, sannan kuma ai koda ba barci zakayi ai ni matar kace ADDINIMU bai haramtaba, ladama fa zaka samu.

Ya ce "Walhi kaina kemin ciwo. Ta ce "Aiya sorry muje mu kwanta babu abunda zai faru. Haka yana ji yana kallo ta É—iorashi a kan gado sannan itama ta hau ta ja musu bargo, suka faÉ—a barci mai daÉ—i irin na miji da mata. AJ gaba É—aya a takure yake domin kuwa duk ta manne a jikinsa, shikuwa duk sai yaji ya kasa cigaba da barcin.

Misalin ƙarfe bakwai da wasu ƴan mintina yaji alamar tana ƙoƙarin tashi, sai ya rufe idon sa domin karta gane cewa baiyi bacceba. Tashi tayi tana sauƙe idan ta a kan fuskarsa sai taga ya ƙara mata kyu. Miƙewa tayi ta saka hijab sannan ta fita. Bayan kamar minti goma ta dawo lokacin shikuma yayi dube-dubensa ko zaiga ina ta ajiye wayar sa amma ya rasa. Tana shiga saiga ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin reƙeda tire na abincin su. Bayan sunci ne Hajiya Babba tace ya shirya da huri zasu tafi. Haka AJ bai ƙara mata zancen wayarsaba ya shirya cikin shigar wasu sabbin kaya da tabashi. Fita ta sakeyi ta kira Salis ta sanar dashi cewar wani aiki ya kamata saboda haka bazata dawo yauba, ya kula da laɗifa tare zasu zauna da AJ amma bazasu huce sati ɗaya ko biyuba, tana jin yana tambayar ina AJ amma ta kashe wayar damin kuwa batason komai ya shiga tsakanin ta da angonta.

Haka suka fito daga cikin hotel É—in suka shiga motar da sukazo da ita sukaje gidan malamin da ya É—aura musu auran suka ajiye motar. Cikin mamaki AJ ya ce "Bada motar zamujeba?

"Cikin basarwa ta ce "Ina zamuje da motar?

"Shima cikin ƙosawa ya ce "Gida mana ko a motar haya zamu tafi?

"Sai a lokacin Hajiya Babba ta tuna da cewar a shefa bata sanar dashi da maganar tafiyar bafa. Juyowa tayi da kyu ta kalleshi sannan ta ce "Ƙasar zamu bari amma ba nisa zamuyi muna cikin Africa ina so mu samu Kamar sati biyu ne kafin mudawo kaga lokacin mun ci amarci sosai kaima idonda ya buɗe.

Cikin mamaki da rashin tsammani AJ ya ce "Tafiya waje sati biy!! Ina bazan iyaba, tayaya zanyi sati biyu batare da naga Innah ta da Nana ba, no ai babu wannan tsarin a cikin sharuɗanmu? Kuma koda da wannan bazan iyaba, Ni no no no, ya ƙarasa yana kirkiza mata kai haɗida jadabaya kamar zai ruga da gudu.

Hajiya Babba tayi shiru!!! Sai zuwa wani lokaci ta kalleshi cikin murmushi ta ce "Shekara É—ayane kwangilar mu ko? Aj ya É—aga mata kai alamar eh.

Hajiya Babba ta ce "To idan har ka yarda muka bar wannan ƙasar har mukayi sati biyu to idan mun dawo gida, wata biyar zamuyi shikenan kaci kuɗinka miliyoyin hamsin. Ina jiranka yanzu, idan kuma baka yardaba to muje gida muyi shekara ɗaya ɗin. Ta ƙarasa tana sakar masa murmushi!!!!....??

PAGE* 1️⃣7️⃣

........*A.J* Shuru yayi yana kallon Hajiya Babba kafin ya buɗe baki ya ce "Kina nufin idan munyi sati ɗaya shikenan saura wata biyar? "Eh saura wata biyar amma fa shima da sharaɗi? A.J ya ce "Wani sharaɗi kuma bayan wanda nake ciki? Hajiya Babba ta kalleshi da kyu kafin ta matso kusa dashi kamar zata shiga jikinsa ta ce "Sharaɗin guda ɗaya ne kawai idan har zaka yarda? Taci gaba da cewa... Banaso kayi waya da kowa har sai mun dawo, abun nufi shine bazaka kira kowaba har mu dawo, kuma..."Bata ƙaraba ya ce "Na yarda. Cikin mamaki take kallon sa kafin ta ce "kayarda? Ya ce "Yes na amince, amma inaso zanyi waya da Nana yanzu? Hajiya Babba ta ce "Badamuwa. Haka ya shiga kiran numbar Nana amma bata shiga, sai ya kira number Innah itama dai bata shiga.
Chapter 20 · 0% Book details