← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 67

Sashe 64

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda yaje gida ya tararr har lokaci Zara tana kuka. Ya kwantar musu da hankali batare da ya sanar dasu komaiba. A ranar ya tafi Katungu shida Salis koda yaje garin ya tambayi Umar da Usman zancen waye yayi wannan asirin sai suka sanar masa da cewar ai rabansu da cikin garin Katungu har sun manta domin dukkansu jiya suka iso garin daga cikin Benue sun haɗa ƙafa sun gina babban shago. Su kansu sun shiga tashin hankali da mamaki jin abunda ya faru, domin su tun wa'azin da Muhammd ya musu a kan yafiya sukace sun yafe masa. Nan fa gaba ɗaya su ukun suka shiga tambayar a salin abunda yafaru da kuma waye yayi a sirin amma duk garin kowa yace bai saniba, tamkar dai abun haɗin baki. Haka dai har dare babu wanda yace komai daga musulman harma wanda basu karɓi Musuluncin ba. Haka suka dawo gida batare da sanin abunyiba.

Acikin gari kuwa Salis da Muhammd suna fita Zara da Ibrahim suka shiga É—aya daga cikin motocin gidan suka nufi gidan Sadiya, lokacin Hajiya Babba tana ciki tana fama da rikicin Hajara. Lokacin da suka ga halin da mahaifin nasu ke ciki sai kowa daga cikinsu ya fara kuka, Elixa ta haÉ—asu gaba É—aya ta rungume tana kuka. Shiko Commda sai kallon guri guda yakeyi amma yana jin duk abunda suke cewa. Suna gidan har su Muhammd suka dawo, shima yasan dole zasu
zo sai yasa bai ce komai ba. Lokacin Sallha nayi ya umarcesu da sutashi suje suyi. Haka Elixa taji abun wani babbaraƙwai babu daɗin ji wai "Ibrahim ku tashi kuje kuyi Sallah. Kasan cewar da English yayi maganar sai ta hau mamaki ganin duk sun tashi. Bata iya cewa komai ba, domin kuwa sai taga gaba ɗaya ma halaiyarsu ta canza ba kamar daba.

A gidan Zara da Ibarahim suka kwana suna taya mahaifiyar tasu jinya. Wasa-wasa abu ya rincaɓe, domin kuwa kullum ciwon nasa ƙaruwa yakeyi ga kuma har yanzu babu labarin wanda yayi a sirin, sannan duk lokacin da zasuyi yunƙurin ɗagashi bazasu iyaba. Haka dai yaci gaba da zama a gidan Sadiya sai dai Ibrahim da Zara suzo duba shi. Shima AJ da Nana sunzo sau ɗaya, hakama mutanan Kano duk sunzo, sannan Muhammad yasa a na masa sauƙar alqur'ani. Wannan kenan!

*BAYAN WATA HUÆŠU*

kwana huɗu ya rage bikin Zainab da Abdalha da kuma Maryam da Isa, sai kuma Aliyu da wata daga cikin danginsu da yasamo kamar yanda malam Adamu ya ce masa, ai kuwa shine ya masa komai na sadaki. Mutanan Benue Makurdi ne a kan hanyarsu ta zuwa bikin. Jirgi suka hau dukkansu, Muhammd da matarsa Hajiya Babba domin kuwa tun tana kammala arba'in a ka ɗaura musu wani auran, sai Salis da Ibrahim da Laɗifa da Fatima zara da shi kansa AJ ɗin. A cikin wannan wata huɗun ya kama business sosai kuma Allah ya saka masa albarka, Hajara da Nana kuwa sunsan cewar AJ yana ji dasu , ita kuwa Zara har yanzu taƙi sakar masa fuska domin har yanzu basu zauna sunyi doguwar maganaba. Ita kuwa Laɗifa yanzu ba ruwanta da kowa a gidan daga ɗaki sai kuka sai gobe ciwo jibi lafiya. Kullum Hajara tana gurin zara domin wani irin so da takewa yarinyar, kodan jinin AJ ce, ko kuma dan ta na kama da shine.

Sosai sukayi murnar ganinsu, angwaye da amarema sai murna sukeyi domin kuwa dama su a je jira a matsayin abokan angwaye da ƙwayan amare. Ɓangaren Nana kuwa jin Abdalh zayi aure yasa ta sami Maryam ta faɗa mata gaskiyar abun da yafaru lokacin da Abdalha yazo gidansu, cewar mamartace ta zugata a kan taci masa mutunci, amma yanzu dan Allah ta bashi haƙuri ya dawo tana sonsa. Maryam ta mata wani irin kallon alamar baki da hankali. Haka Nana taje gida ta fara ma mahaifiyarta rashin kunya, mahaifinta kuwa yaje har gida ya ba Shek Kabir kabuga haƙuri .

Ranar juma'a a ka ɗaura auran Abdalha Shek Kabir kabuga da a maryarsa ZAINAB Adamu Ambato. Da kuma Isa Adamu da Maryam Shek Kabir kabuga a kan sadaki Naira dubu ɗari-ɗari. Masha Allah! Alhamdulillh! Haƙiƙa wannnan auran da a kayi ya ƙara haɗe kan al'ummar Musulmai da dama, domin kuwa dama sune jagororin al'umma kuma sun haɗe kansu. Al'umma takotaina sai kiran sunan ango da amarya akeyi. A ranar da yamma a ka gabatar da wa'azi sosai game da haɗin kan al'ummar musulmai. A washe gari suma abokan ango su Salis da Ibrahim da AJ suka haɗa ƴar walima ta angwaye da amare. Sosai aka ci a kasha a kayi ƙasidu da wa'azi masu Ratsa zucoyoyin al'umma. A ranar a ka raka kowa gurin amaryarsa bayan nasihoyi da iyayen nasu suka musu.

Da sallama Abdalha ya shigo cikin ɗakin nata yana kallonta ita kaɗai a tsakiyar kado kanta rufe da farin mayafi, tsayawa yayi yana kallonta yana sakin murmushi yana jin cewar yau Allah ya cika masa burinsa bayan doguwar kwa-kwar mayar da a kasha. Abdalha kenan tun daga ƙofar gida ya sallami a bokan nasa a kan cewar yanzu tazama tashi shi kaɗai babu wanda zai kallar masa ita, murmushi ya keyi yana tuno irin tsiyar da suke masa.

Bayan sun gabatar da Sallah raka'a biyu kaman yanda shari'a ta zarta, sai kuma kowa yayi shiru yana tunanin abunyi. Haka ya kamo kanta ya fara jero addu'o'in neman zam lafiya a tsakaninsu, ya ɗau lokaci yanayi tana sauraronsa tana jin yanda Muryar tasa take tasiri a zuciyarta. Bayan ya kammala itama ta riƙo kansa ta fara tata addu'ar, sosai itama tayi, kafin Abdalha ya ce "To yanzu Malama nine zan miki tambayoyinne kodai kece zakimin domin naga fa kamar sai kin sake koyar dani. Murmushi tayi ta sunkuyar da kai domin kuwa yau kunyarsa ta keji sosai. A cikin wannan daran Abdalha ya angonce da amaryar sa.

Washe gari Su Muhammd suka tattara nasu ya nasu suka koma batare da sunyi sallama da angwaye ba. Sosai Abdalh da Zainab suke zaman lafiya da gyrmama juna da kuma baiwa kowa damar yin zaɓinsa. Sannan Zainab ta ajiye yin ƙasidu, amma tana rubutawa ta bayar a je a rera, kamar yanda Abdalha ya ce idan zata fita koda ina zataje to sai tasa liƙaf, itama hakan ya mata sosai. Soyyaya sukeyi mai tsafta wacce kowasu ma'aurata suke burin yin irinta.
Wannan kenan!

*BENUE MKD*

Sosai Muhammd da iyalan gidan sa suke shirin auran yaransu da ke gabatosu. Umar ne tsaye a gaban Salis da Ibarahim yana sanar dasu cewar yana son Laɗifa amma yana ganin kamar tafi ƙarfin sa, shiyasa yakeso su taimaka su sanar mata. Salis yayi dariya ya ce "Yanzu tsabar rashin kunya ina matsayin sirikinka amma nine zanje naima maka izini ko?. Haka dai suka ce kawai ya cire tsiro ai mace bata fin ƙarfin Namiji. Haka ya shiyar ya nufin gidan domin sanar mata da sirrin zuciyarsa. Wanka yaci sosai cikin manyan kaya ya shiga gidan ya zauna a harabar gidan ba tare da sanin su Salis ba ya tura mai gadi ya kira masa ita. Yana zaune a gurin ya hangota ta nufo gurin idanunta karr a kan ganin ki waye yazo har gida nemanta. Lokaci ɗaya Umar yaji tsoron ya dawo, cikinsa ya ɗuri ruwa sai yakejin kamar ya ruga a guje, lokaci ɗaya cikin sa ya bada guuuuu! Daidai lokacin da ta ƙaraso gurin ....📝

*Congratulations Zainab And Abdalha*

*To fa! Umar ko da rabon shan mari😂*

*Comments É—inku shine abun alfaharina*

*S REZA ✍️*

*ADM*

*S REZA ✍️*

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

*PAGE4️⃣9️⃣*

........Tana zuwa Umar ya miƙe tsaye gaban sa na cigaba da faɗuwa. "Umar kaine kake kirana? Tayi tambayar da ɗan mamaki. "Am am umm dama dama na zone a kan. Umar ya kasa magana tsabar cika masa ido da Laɗifa tayi.Ita a tunaninta yazo a kan maganar abokinsa ne, hakan ya sa ta kalleshi cikin wata raunanniyar murya ta ce "Umar kafi kowa sanin irin sonda nakewa Ibrahim domin da kai a ka dinga shiga da fita har na samu na kuɓutar dashi daga shirrin Mahaifinsa, amm ya rasa da abbun da zai sakamin sai auran wata shigiya yar matsiyata, har yana iya ksllon idona yace ita yakeso. Tana maganar tana kuka hawaye na wanke mata fuska. Umar ya sauke a jiyar zuciya jin irin zagin da takewa ƙanwarsa, sannan kuma shi ba wannan zancen ne ya kawoshiba a zuciyarsa ya ke cewa wato batama san cewar Hadiza ce yarinyar da Ibrahim ɗin yakesoba, a fili kuma sai yaji tausayinta ganin tana kuka. "Ki yi haƙuri Laɗifa matar mutum ƙabarinsa in sha Allah kema Allah zai kawo miki miji daidai da ke kawai ki share ki kalli gabanki. "Da sauri ta kalleshi ta ce "Anya kasan so kuwa? Kasan yaya mutum keji idan wanda yakeso ya ce baya sonsa ko kuma wanda keso baisan yanayi ba? A cikin zuciyarsa ya ce "Ai kuwa nine nasan haka.Laɗifa taci gaba da cewa "Ina jira ya auro koma wacece dan uwarrata da kanta zata gudu gidan iyayenta.

Duk yanda Umar ya kai ga son sanar da ita sai ya kasa cewa komai sai ma haƙuri da yake bata, a haka ya bar gidan cike da jin haushin kansa. Bayan ya fita daga gidan ya fara dukan kasan yana kiran kansa da lusari mara wayo mai tsoron Mata. Ita kuwa Laɗifa gaba ɗaya ma haushin kowa ta ke ji a gidan, barinma Hajiya Babba da ƴarta Hajara. Tunda a ka haifi yarinyar bata taɓa mata wasaba bare a je ga ɗaukarta, kowa na gidan yasan da haka amma Daddy Muhammd ya ce a rabu da ita domin kuwa yana tausaya mata. Shi kansa Daddy ɗin yaso ya haɗa auran Salis da Zara ne da kuma Ibrahim ɗin da Laɗifa, amma abun ya zama ba hakaba shine yasa yake tausayin ƴar tasa. ( Wannan kenann!)
Chapter 64 · 0% Book details