← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 67

Sashe 19

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AJ kuwa yanajin ta har ta fara sallah yayi sauri ya shiga toilet, domin kuwa duk hankalin sa na kanta, yana kallo tanata murmushi. Yana shiga ya tsaya yana Kallon jikinsa daga sama har ƙasa kafin ya ce "Na shiga uku ni AJ!! Ina kuma sankuɗina ya kaini! dama haka a keji idan anyi aure? To meyasa wasu mazan suke cewa daɗi a keji!? Nidai wallhi matarnan kasheni tasoyi, idan ya tuno irin wahalar da yasha, domin kuwa abarsa har wani zafi take masa, tin tana iya tsayawa har ta lanƙwashe. Ya ce "kai wallhi bazan iya da wannan abunba, ni wallhi sai najima na tsani aure indai haka a keji mutum ya kusa mutuwa, amma fa da farko yaji daɗi. Take ya tuno da ranar da sukaje clup da Sarah ranar da yakusa keta mata haddi. Afili ya ce. Kenan itama da nayi haka zanji wannan a zabar!? "Allah sarki Sarah ko yanzu tana wani hali na rashini!? gashi ko kiranta banyiba...ooo!! Allah sarki innah ta da Nana, kwana guda ban jikuba, ku kwantar da hankalin ku na kusa yin kuɗi, duk zaku huta, gida zan siya mana babba wanda komai sainasaka mana.

Haka dai yayi wankan tsarki kafin yayi a laula, sai kuma ya rasa kayan da zaisa, domin kuwa tsirara ya shiga toilet ɗin kuma gashi ba komai a toilet ɗin. Haka ya keta bin jikinsa da kallo, kafin ya buɗe baki ya ce "Amiƙomin kayana. Hajiya Babba dake zaune ta idar da Sallah tana jiran fitiwarsa. Ai kuwa ta saki dariya jin abunda yace. Tashi tayi ta ɗauki sabbin kayan da ta siyo musu jiya shida ita, domin kuwa ta shirya da safe zasu bar ƙasar. Ɗauka tayi ta nufi toilet ɗin, baiji tafiyartaba sai ji yayi an buɗe ƙofar an shigo.

*ABDALHA POV*

Shek Kabir kabuga ya ce "Maryam wato kin rainamu ko? Kina son mayar damu mutanan banza a idon al'ummar ko? Muna hani da ai kata bidi'a amma a dinga samunsa a gidanmu, me kike tunanin za'a ɗaukemu!? To daga yau kaman yanda yayanku ya ce...babu ke ba zuwa ko nann da bakin get, sannan wayar ma ai dama shine ya siya muku, to bani wayar? Ya miƙa mata hannu babu a lamar wasa, ai kuwa ta bashi har izuwa lokacin kuka takeyi. Sannan ya kalli Sadiya da Nusaiba ya ce "idan har naga wayar wata a hannuta to kuma waya ta haramta a hannuku. Yana kaiwa nann ya miƙe yabar ƙurin cikin ɓacin rai.

Yana fita Maryam ta faɗa cinyar Mommy tana kuka. Mommy ta tureta haɗi da cewa "Ai maganin wacce bata jin maganar uwarta, ai saida na ce karkije tunda yayanku baya so, amma kikace sai kinje. Abdalha ya miƙe ya kalli sauran ƙanyan nashi ya ce "Kunji abunda Daddy ya ce ba saina ƙara muku wani ƙarin bayaniba. Bai jira cewarsu ba yabar palorn Mommy na binsa da harara.

Yana fita Maryam ta sake fashewa da kuka tana cewa "Wannan ai san kaine me ya hana a karɓe wayoyin su Sadiya idan ba ni kaɗai a ka tsanab..."Kafin ta ƙarasa Mommy ta bige mata baki haɗi da cewa "Mune muka tsaneki ɗin?

Nusaiba harda Nura suka kwashe da dariya suna barin ƙurin , yayinda Sadiya ta zauna tana mata faɗa da kuma sanar da ita illar aikata bidi'a, dukda tasan Maryam ɗin tafita sanin komai abinda ya shafi addinmu, domin kuwa duk gidan bayan Daddy da Abdalha. To tafi kowa ilimi harda Mommy kuwa, saide Mommy ta faɗa mata saninn littafin addini wanda itama tayi amma ba kamar Momy ɗinba, domin kuwa har yanzu suna ɗaukar karatun litattafai a gurin Mommy ɗin, wanda sukeyi kowani dare, ranar asabar da Lahadi kuma harda rana, kasan cewar ba su kaɗai take koyarwar ba harda wasu daga cikin matan unguwar su. Ita kuma Maryam tana koyar da matan aure da ƴan mata karatun Alkur'ani mai girma kullum da daddare. Cikin ɓacin rai ta ce da yayar tata "Ya isa haka mlm saidinawa masu jiran ganin an min wani abu suyi dariya, to wallhi duk baƙin cikinku dani saide ku barni amma wallhi nida Zainab sai mun zama ƙawaye, kuma ku zuba ido kugani, abu kamar mutum yana gidan kaso. Taja wani dogon tsakiii mtsiiii sannan ta bar gurin. Mommy da yayar tata Sadiya suka bita da kallon mamaki.

Abdalha kuwa yana fita ya tararr da Daddy na jiransa a waje, take ya sanar dashi cewar yaje masallacin da shek É—in yakeyin wa'azi duk ranar juma'a da yamma kafin ayi sallar magariba. Akan yaje yayi shi zaiyi tafiya zuwa Zariya sai kwana biyu zasu dawo. "Ok Abbalha ya masa sannan ya masa fatan dawowa lfy.

*ZAINAB. VOP*

Mama ce tare da Aisha da kuma Isa da malam tareda halifiyar Zainab ɗin da kuma namijin halifan nata. Mama ce ta ce "Mlm ku sake kiran numbar nata. "Mama wallhi numbar bata shiga kingani? Isa ya faɗa yana nunawa mama wayar. Malam ya ce "kumata uzuri baku saniba ko ta tsaya yin wani abunne. Hakanne yasa duk suka tsaya a wajan suna jiran ta. Wasa-wasa har ƙarfe shida da rabi, babu Zainab babu dalilinta. Nann fa hankalin su ya tashi. Gefe ɗaya kuma ga masoyanta mazauna unguwar au ( wato waɗanda suke unguwa ɗaya da ita) suna jiran dawowarta, domin kuwa sunji daɗin waƙar da ta sake ɗin. Hakafa har aka idar da sallar isha.

Take Isa ya shiga tunanin abunda ta ce masa ɗazu. Ai kuwa cikin yarda da abunda zuciyarsa ta ɗarsa masa ya ɗauko wayar sa, dama a recording take, take ya ce "Mlm inada tabbacin Abdalha Kabir kabuga ne ya sa ceta, kokuma ya sa aka kamata, kode ɗaya daga cikin su, domin kuwa tace ya turo ƙanwarsa ɗazu. Ai kuwa ya kunna musu yanda sukayi da ita.ai kuwa take suka yarda, amma Mama ta ce "Isa karkaje kayi abunda bakada tabbaci a kai, kaga baka da tabbacin abunda kake son ai katawa.

Take Isa ya fita bai tsaya ya saurari mama ba. Yana fita ya tararr da masoyan nata a ƙofar gidan su sai ɗaga hotunan Shehu nannsu haɗi da na Zainab ɗin, sannan sun kunna sabuwar waƙar sunayi domin kuwa har wasu sun riƙe waƙar. Baiyi wata-wata ba ya sanar musu da cewar Abdalh Kabir kabuga ya sace Zainab dalilin waƙar da tayi. Aikuwa nann take suka fara zaginsa, domin kuwa maganganun da tayi a cikin waƙar tamkar dashi takeyi, dama kowa yasan takun saƙar dake tsakanin su. Ai kuwa cikin daran labari ya bazu ko ina akan Abdllah Kabir kabuga ya sace Zainab saboda waƙar buɗɗiyar wasiƙa.haka dai duk inda ka shiga, dama abune na sanannun mutane, ɓangaren sada zuminta talabijin zancen a kayi.

Yayinda rikici ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyi guda biyun, garin kono ko ina zancen akayi, wasu na cewa ai dama batada kunya, meyasa zata zageshi a cikin waƙarta, ai ƙwara haka. Yayinda wasu suke cewa ai dama ita bata taɓa masa martaniba shikuwa indai zaiyi wa'azi saiya saka da ita, to mezaisa dan tamasa ɗaya ya tsargu. Rikici dai mara dalili da tushe, abunda yaƙara raba kan sauran ɗan abunda ya rage daga ƙungiyoyi guda biyon. Wasu mazauna kabuga yan ƙungiyar Zainab ɗin suka haɗa kai domin zuwa gidan Shek Kabir kabuga ƙwato Zainab...✍️.📝
PAGE* 1️⃣6️⃣

.......Haka samari majiya ƙarfi ƴan ƙungiyar Zainab suka doshi gidan Shek Kabir kabuga, bakajin komai sai zage-zage da ikkirarin cewar sai an fito musu da Saiyadar su kokuma kowa yaji a jikinsa. Ɓangaran Isa kuwa, gaba ɗaya hankalin sa ya tashi, tun yana kiran numbar ta tana shiga har yakoma kira yaji ance tana kashe, nan fa ya shiga kiran duk wani babba da yake a ƙungiyar tasu, dama manyan malamansu yana sanar dasu cewar Abdalha Kabir kabuga ya sace Zainab saboda waƙar buɗɗiyar wasiƙa, kowa hankalinsa ya tashi, haka dai kowa ya kasance cikin mamakin lamarin har zuwa washegari.

*ABDALHA POV*

Yana barin gurin Daddy ya koma gidansa ya shirya ya tafi gurin da zai gabatar da wa'azin. Haka ya gabatar da wa'azi sosai wanda yasa al'ummar dake gurin kowa ya jinjina masa domin kuwa wa'azin a kan iyaye matane yanda suke sakaci da yaransu, harda mazan ma. Yayinda wasu daga ciki suke mamakin sa ganin komai idan zaiyi irinna mahsifinsa ya keyi harta muryar su, idan kana sauraron karatun su, bazaka taɓa babbace muryar Shek Kabir kabuga da kuma ta ɗansa Abdalha Kabir kabuga ba. Saide ko idan kana kallonsu. Kaman dai yanda yasaba yauma bayan ya gama wa'azin saida yayi tsokaci a kan ƴan waccer ƙungiyar, musammamma waƙar da sukayi ɗazu, domin kuwa tsaf yaji waƙar har ƙarshenta. Saida ya caccakesu sosai kafin ya yi addu'a ya rufe karatun.

Gidan su ya nufo daniyar zuwa suyi magana da mommy. Kaman yanda yayi tsakanin, hakane kuwa ya faru, domin kuwa yazo ya samu Sadiya ce ke koyawamatan da Maryam ke koyawa karatu. Cikin faÉ—a ya ce "Ina Maryam?

"Wallhi yaya anyi-anyi tazo ta koya musu karatu amma tace wai bazatayi ba.

Abdllah ya ce "Ina take? Yayi maganar cikin tsananin ɓacin rai.

"Tana cikin ɗakinta ko abinci taƙici, ko fitowama taƙiyi. Cewar Sadiya tana kallon yanayin yayan nasu. Da sauri Abdllah yayi ɗakin Maryam cikin zafin rai!. Ya kai hannu zai buɗe ɗakin yaji Nusaiba ta kwalla masa wani uban kira har bakinta narawa, ita kanta Maryam da take cikin ɗaki tana karatu saida ta tsorata domin kuwa da ƙarfi takira sunan nasa. "Yaya Abdalha!!!!!!!!!.

"Cak ya tsaya cikin ruɗewa domin kuwa yasan babu lafiya, itama Mommy da take ɗaki tana koyawa Nura karatu saida ta fito. Hakama Sadiya da ita da ɗalinbanta saida suka tsorata. "Da sauri ta ƙaraso gurin da yayan nata yake hannunta na rawa ta nuna masa abin da tagani yanzu ana yayatawa.

Karɓa yayi yana dubawa, dai-dai mommy da Maryam duk sun iso gurin. Suma kallon wayar sukeyi suna duba abinda ke cikin wayar. A kiɗime Mommy ta kalli Abdalha wanda ya kafama wayar ido yana kallo. Tabbas bazaka gane halin da yake cikiba, domin kuwa babu alamar yaji tsoro ko mamaki, ko firgici.
Chapter 19 · 0% Book details