← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 67

Sashe 53

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Karki sa ke kice zaki fara ai kata kuskuren zubar da ɗan sunna, Idan har haka ta faru to walhi zakiyi mamaki. Wannan yaron walhi sai kin haifeshi domin da ubansa kuma kike zancen kar su Salis su sani to tayaya zaki raini cikin a gidan da suke? Kuma ya zama dole a sanar da uban ya ron. Cikin sauri da tsoro ido ta ce "To dan Allah ka ɗauki cikin a matsayin naka sai kawai muce bayan dawowarka muka samu, idan na ai'hu sai mu riƙe yaron ba tare da kowa ya saniba, Pls dan Allah kamin wannan alfarmar dan darajar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama. Hajiya ta ƙarasa ta na kamo ƙaffun Muhammad. "Dan Allah kamin rai ka rufamin a sari walhi kunya zanji bazan iya kallon Salis da Laɗifa na ce na auri yaronnan har ya min cikiba, dan darajar Allah ka taimakamin? Ta na kuka kanta a sun kuye a ƙasa tana na damar wannan auran da tayi, wanda take jinsa tamkar a ce ciki shige ta je tayi. Ganin Muhammad ya yi shirune ya sa ta ƙara cewar "Dan Allah ko a zubar da cikin ko kuma mu karɓi yaron a matsayin namu? Dan Allah ka zaɓi ɗaya, walhi nayi na da ma, na tuba....📝

*Tofa! Muhammad sarkin tausayi da yafiya, shin wanne kuke ganin zai zaɓa a cikin alfarmar da Matarsa ta nema?*

*GA AJ GA SALIS*

*Comments É—inku shine abun alfaharina*

*S REZA....*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*

*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*

*PAGE4️⃣0️⃣🔕*
....."Shin Aisha i'na hankalin ki da tunanin ki suka ta fi? Wannan abun da kika ai kata ba haramun ba ne, Addininmu bai yi hani ba amma gaba ɗaya kin hana kan ki sukuni haba Aisha!? "Eh na san ba haramun ba ne, am'ma wallhi na kwam'maci da na ai kata haramun ɗin da wann! "Subhana lillahi! A'uzu billahi! Aisha ba ki da hankali ne? Kinsan mai kike faɗa kuwa? Ko kinyi hauka ne? "Ban yi haukaba am'ma na tabbatar zan yi hauka idan har Salis da Laɗifa suka samu wannan labarin. Hajiya Babba ta ƙara sa ta na sake fashewa da wani sabon kukan. Muhammad ya na so ya rarrashinta amma ya rasa mai zai ce ma ta sai kawai ya fita da ga ɗakin cikin damuwa. Ya na jin yan da take ihun kiran sunan sa am'ma ya fita da ga ɗakin.

Kuka take yi sosai kai ka rantse da Allah dukanta a ke yi. "AJ ka cuceni ka tuna min asiri ci ki! Ni ni ni Aisha ɗauke da cikin abokin ɗana? Allah ka sa na mutu kafin ganinn ranar tonun wannan asirin! Muhammad da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin ya shigo cikin ɗakin cikin wa ni sabon salon tashin hankalin ya ce...

"Ya zama dole uban cikin da ke jikin ki ya san da wannan zancen, sannan dole yaranki suma susan da wannan abun arziƙin, bazan bi ye miki ki sake ai kata wa ni kuskuren ba, wanda kika yi a bayama ya isa haka, ki gode wa Allah ba cikin shege ba ne, walhi i'na ta ya ki murna da Allah ya tsareki da ga aikata alfasha. "Sannan ki sa ni wannan kukan da saɓon da ki ke yi ba shine ma futa ba. Ya na faɗa ya ƙara barin ɗakin jin a lamar da wowar su Sarah.

*AJ POV*

Idon sa a kan su ya fito da ga motar ta sa ya na bin Salis da wani irin kallon tsoron kar abin da zuciyarsa ta aiyana masa ya tabbata. Salis da Nana da suka ji ƙarar dukan mutar da AJ ɗin ya yi ne ya dawo da su daga duniyar soyayar da saku ta fi. Suna ganin AJ Salis ya saki murmishi ya na kallon fitowarsa da ga cikin motar da ya ke mamakin ganin sa cikin sabuwar mota. Ita ko Nana kunya ta ji domin ba ta so ya ganta a halin da ya same su ba.

"Lafiya Malam? Mai ya kawo ka gidan mu? Kuma gurin ƙanwata? AJ ya faɗa ya na haɗe fuska tamkar bai san wa ye Salis ba. Ci ke da mamaki Nana da Salis suke kallon sa ganin babu a lamar wasa a fuskarsa. Cikin tsawa ya ce da Nana "Ɓace min a nan kafin na fasa miki baki yanzu! Ai kafin ya ƙara sa har ta shige gida cikin kuka. Ya dawo da kallonsa izuwa ga Salis wanda ya yi mutuwar tsaye ya na kallon ikon Allah. "AJ Ka na cikin haiyacinka ku"..."Salis ka bar ƙofar gidannan yanzu Please? Ya faɗa ya na ƙoƙarin kawar da abun da ya zo masa zuciya.

"Wani abu ya faru ne da Hajiya ta zo gidannan? Ko dai Laɗifa ta zo ta ce wani abu a kan soyayyar mu da Nana? Salis ya yi wannnan tambayar ne domin yasan Hajiya Babba ta ce zata zo gidan su AJ. Kuma yasan Laɗifa ce ka ɗai tasan ya na son Nana. Cikin sauri AJ ya ka tsaye shi da ce wa "Ka yi haƙuri Nana ta na da Miji dan Allah kar ka ƙara zuwa ƙofar gidannan. Cikin tsananin ɓacin rai shima Salis ya ce "Ƙarya kakeyi AJ walhi Nana ta wa ce babu wanda ya isa ya rabamu da ita!

Cikin fitar haiyaci AJ ya kamo kwalar rigar Salis ya ce "Kai ɗin banza wa ye kai Nana ba sa'ar ka bace, kuma walhi sai ka bar mana ƙofar gida wawa kawai. Ganin da gaske AJ ya ke yi yasa Salis shima kamo rigarsa ya fara turashi. A na cikin ha ka Nana da Innah su ka fito. Dai-dai AJ ya sa ƙarfi ya ture Salis, ai kuwa ya yi baya-baya sai ya faɗa jikin motarsa. Da ƙarfi Innah ta ce "Abduljabaru"...."Abduljabaru"? Amma AJ ko kallonta bai yi ba. Ganin ha ka ya sa Innah ta je ta kamo hannun Salis ta na jansa cikin gidan. Da sauri AJ ya sha gabanta ya na ce wa "Walhi ba zai shiga gidannan ba, kawai ya bar an'guwar nan ga ba ɗaya. Cikin kuka Innah ta ce "Yanzu Abdul ban isa da kai ba kenan ko? Yanzu bazan maka magana ka ji ba ko? AJ ya kawar da kai gefe ya ce "Innah wai Nana ya keso kuma babu aure a tsakaninsu domin ita ɗin ba sa'ar sa ba ce, kai ga ba ɗaya ma an mata miji. "To ƙarya ka ke yi , sai na bashi ita, kai ɗin banza, Abdul ka ba ni hanya? Amma ko gizau AJ baiyi ba.

Cak Nana ta tsaya da kukanta ta na kallon AJ wanda ya ke ta zuba kamar ya zauce. "Babu aure tsakanin mu! An min miji! Wannan maganar ita ce Salis da Nana ke ta nazari. Ganin mutane har sun fara taruwa ne ya sa "Innah fashewa da kuka ta na dukan AJ wanda gaba É—aya ya fita a haiyacinsa. Shi dai kawai ba ya son ganin salin a gabansa tsabar kunya da tsoro .

Ganin ha ka ya sa Salis cire hannunsa da ga na Innah ya na kallon Nana da itama shi ta ke kallo. Kallonta ya ke yi har ya buɗe motarsa ya shiga ya ta da ta ya bar an'guwar ci ke da ɓacin rai da tunani. Ganin ya tafi ya sa Nana sakin wani kuka ta na jin ta rabu da Salis kenan har a bada, AJ ya rabata da masoyinta na gaskiya. Da sauri AJ ya yi kan Innah da sauri ganin ta sume a gurin tammkar ba numfashi. "Innah! "Innah! Ha ka ya ke ta kiranta amma ko motsin ba ta yi. Da sauri ya ɗauke ta izuwa cikin motarsa, itama Nana ta bi yo bayan sa cikin ihun kiran sunan Innah har suka bar an'guwar.

Da sauri a ka karɓesu da umarnin Dr Lurwan wanda fituwarsa kenan da ga cikin asibitin zai tafi gida. Sun ɗauki a ƙalla a'wa guda kafin Dr ya fito ya na kallonsu da zuba masa Ido. "Dr Innar mu ta na lafiya dai ko? Dr ya ce "Ku biyoni? Ba musu suka rufa masa baya zuciyoyinsu na dukan tara-tara. "Dr ya kalli Nana ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na jin tsoron abunda zai fito da ga bakinsa a kan innar ta su. "Kin manta bayanin da na miki a kan ciwonta a wancan lokacin ne? Nana ta kalli AJ shima ya kalleta. "Dr ta sanar da ni, amma yanzu dai ai ta na lafiya ko? Dr ya ce "zuciyarta ta ƙara samun matsala fi ye da na baya saboda haka dole sai"...."Ya isa haka Dr idan kuɗi ne ko nawa ka ke so za'a baka Please dan Allah karka ce komai. AJ ya katse shi cikin tashin hankali. Ganin kamar baza su fahimci shine ba ne ya sa ya ce "To shikenan karka damu za'a kula da komai. Ha ka suka fito daga gunsa jiki a sanyaye.

"Laɗifa" Laɗifa" Salis ke zabga ma ta kira tun kafin ya buɗe palon, ka na kallon sa kasan ya na cikin tashin hankali mara musaltuwa. Laɗifa da Samuel da Sarah da Muhammad su na zaune a palon suka ji wannan kiran na Salis. Ya na shigo wa palon ya ɗauketa da wa ni mari, kafin ta yi magana ya ƙara ma ta. Daddy Muhammad da Samuel su ka yi saurin ta shi su na kamo shi ganin ya na shirin ƙara ma ta wani marin. Cikin ihu da zafin rai ya ke magana "Mai ya kaiki gidan su AJ? Mai kika je kika ce ma sa a kaina? Wato saboda ke Allah ya yi mara kunya shine ki ke tunanin kowa ma haka ya ke? To Nana na keso kuma sai na aureta ko ki na so ko bakya so. Da ga cikin ɗaki Momy ta ji kamar a na faɗa-faɗa a cikin gidan, cikin rashin sanin abunyi ta miƙe ta na nufar palon domin jin muryar Salis.
Chapter 53 · 0% Book details