Sashe 63
Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka kullum AJ zai kirata amma bazata É—aga ba, zai tura mata message zata karanta amma no amsa. Kullum kuma zaizo gidan domin ganinta amma abun ya fi Æ™arfin sa, a gida kuwa kullum Safarau da Kadija sai sunyi rikici a kansa, Nana har ta fara gajiya da abun da sukeyi, hakanne yasa taje gidan kawu ta sanar masa shi kuma ya kira AJ yace "Idan yanada wacce yakeso ya fitar yayi aure idan kuma babu to ya shirya da Æ´ar uwarsa Safarau. AJ yace yanada wacce yakeso, Kawu ya ce "To gobe za'a zo maganar auran Nana sai kaima ka fitar a saka ranar gaba É—aya. Hakane yasa AJ saida ya sa Salis a cikin lamarin domin baisan ya zaiyi Fatima ta dawo garesa. Salis ya bashi shawara wacce tasa ya yarda da ita É—ari bisa É—ari, kuma yaje yayi amfani da shawar kuma tayi masa aiki yanda yakeso. A washe gari Muhammad da Shek Kabir wanda yazo domin zuwa neman auran Salis É—in da kuma a bokinsa Malam suka tafi gidan kawu. A ranar a kasa ranar auran Salis da Nana wata shida sai Abduljabaru da Fatima zara suna wata shida. Daga nan a ka wuce gidan su Hadiza, farko ma haifin Hadiza yaso yaÆ™i yarda jin cewar É—an gidan Comanda Daniyel ne, domin bazai manta irin cin mutuncin da yakewa É—ansa ba, amma ganin shek Kabir awajan yasa ya amshi abun hannun bibbiyu. Suma dai wata shida a ka saka. A washe gari ne kuma Titi tazo da bayanin halinda su Comanda Daniyel da Eliza suke ci. Dama Muhammad ya naimi indan a ka kai shari'ar tasu amma an rufe duk wata hanya da zaka iya gane komai game da labarin, hakanne yasa ya haÆ™ura domin dai yasan dole yayan nasa ya karÉ“i hukunci domin yaci amanar aikinsa, shi kuwa yafi duk wani guri domin ya sanar dasu cewar ya yafe masa amma ba Æ™ofa, sai kawai yaci gaba da masa addu'a. Bayan ta gama basu labarin komai ne sai kowa dake cikin palon ya fara kuka domin tausaya masu. Zara kuwa harda ihuu tana cewa ita sai taga Momy. Muhammad ya ce Yanzu suna inaa? Ta ce "Suna gidana nace suzo muje gidanka wai a'a bazasu iyaba yaransuma da kuma riÆ™e sun gode! HAJIYA BABBA ita kanta da take mugun jin haushi su saida ta zubar da Æ™walla, sanann tana sake godewa Allah da yasa ita Tata gaddara mai sauÆ™uce. Muhammad ya ce "No Titi zomuj"..."Na bar Titi na koma Halimatus Sadiya! Ta faÉ—a tana fashewa da kuka. Mijinama ya Æ™arbi kallamar shahada bayan sanar masa da labarinmu, jin irin halin kirkin da kayi yasa shima yace zai koma addinin Musulunci, shima Usha ya koma ADDININMU. Tana kaiwa nan Muhammad ya rungumota yana kuka yana mata addu'a haÉ—i da saka mata albarka. Ya ce "Sadiya zomuje gidan naki? Ya faÉ—a yana ji kamar yau zai fara ganin É—an uwan nasa. Hajiya da Zara da Ibrahim sukace zasu bisu, amma Muhammad ya ce "Dukkansu su zauna yanzu zasu dawo tare da su. Haka kuwa a kayi suka zauna cikin tunani har Sadiya da Muhammad suka fita.....ðŸ“
*Tofa! ko dai Comanda ya karɓi hukuncin sojojine, to Salis da Nana dai abu yazo, ina fan's ɗin AJ? Fatima tana gasa masa aya a hannu* 🥰
*Comments ɗinku shine ƙwarin guiwata*
*S REZA âœï¸*
*ADM*
*S REZA...âœï¸*
*First Class writer's asso...*
*PAGE4ï¸âƒ£8ï¸âƒ£*
........ Lokacin da suka isa gidan suka tarar da Usha da Mahaifinsa tsaye a harabar gidan cikin shigar wasu sabbin jallabiyoyi farare haɗe da hulunansu. Wani sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar Muhammad ya sake miƙa gidiyarsa ga Allah buwayi gagara misali mai aiwatar da komai cikin hikimarsa. Yana isa gurin ya ce "Salamu'alaikum? Ya faɗa yana sakin fara'a da murmushi duk a lokaci ɗaya! "Wa'alaikum salam warahamatulla wabarakatuhu". Bayan sun gama gaisawane mahaifin Usha wanda ya samu sabon sunan Musulunci Abubakar Sadiq ya ce "Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda ya haɗamu da mutumin kirki irinka! Tabbas lokacin da Sadiya ta bani labarin ku da kuma abinda ya faru da kai sai naji gaba ɗaya halaiyarka sun bani sha'awa, shine ta ce min wai ai haka halaiyar duk wani musulmin kwarai take mutuƙar zaiyi koyi da ɗabi'un ma aiki Sallallahu alaihi Wasallama. To ina jin haka sai na je gurin wani malami na masa bayani akan ina son shiga musulunci. Muhammad kam farinciki kamar yayi tsalle.
Daga haka suka shiga cikin gidan yana son yin tozali da yayan nasa. Zaune yake ya miƙe ƙafafunsa daga shi sai gajeran wando da senglet fara kansa babu hula ya kafe guri ɗaya da kallo kamar mai tuto wasu abubuwan. Da sauri Muhammd ya ƙarasa kusa dashi yana kiran sunan sa. "Yaya Daniel? Yaya! Yaya!!! Ganin ya kasa juyawa ya kallesane yasa Abukar cewa "Bazai iya maganaba muma munyi dashi amma daga kallon guri ɗaya sai zubar da hawaye. A lokacin ne Muhammad ya kai kallonsa ga ƙafafunsa sai yaga ɗaya ta kumfura sosai ɗayar kuma ta shanye, ya kalli hannayansa suma haka suke, ga kansa da yayi ƙato wuya kuma ya sirance. Cikin damuwa Muhammd ya ce "Mai ya faru dashi haka? Ban gane ba ina Eliza? Yana rufe baki sai gata tafito riƙe da cufi a hannu tana juya abunda ke cikin kofin da cokali.
Da sauri ya karaso gurin da take ya ce "Mai ya faru da yayanna? Eliza ta fashe da kuka itama kanta a birkice take, kamar ba itace wannan ma'abociyar kwalliyarnanba. Cikin kuka ta ce "Mutanan Ƙauyan ku ne( wato mutanan KATUNGU) Sune sukazo har gida suka ɗauki wandonsa guda ɗaya, suka ciri gashin kansa shima ziri ɗaya, to tun daga ranar ya fara rashin lafiya duk inda zamuje sai a ce bazza a iya karya a sirin ba, wai a she ƴan uwanan wannan mutanan da ya rufeku tarene suka masa a siri. Muhammad ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!. "Faɗamin abunda ya faru tun rabuwarku da mu?
Elixa ta fara cewa "Ya kai wata uku a ƙulle batare da kowa yabi ta kansa ba, bayan zuwan Captain ɗinsu sai ya naimi zama dashi, bayan an karanto laifukansa wanda ya yi a lokacin da ya samu ƙarin girma. Hatta ƙananan sujojin da suke ƙarƙashin sa suma kuka sukeyi dashi. Sannan bayan ku da ya ƙulle a she ya sa an kashe wasu da yawa musulmai sojoji idan an kawosu aiki ƙarƙashin sa, babban amininsa wanda suke aikata aikin tare shine ya sanar da cewar ya kashe a ƙalla sojoji kusan takwas ba tare da laifin komai ba kawai dan sun kasance Musulmai. Da farko ya fara yin musu amma ganin hujjojin da aminin nasa ya kawone yasa ya yarda. Ana cikin wannan sai a ka sake sakowa batun ku a kan ya kulkeku har sama da shekaru a shirin,kuma daga ƙarshe ya rufeku a ciki ya saka muku wuta. To bayan tabbatar da laifinne kuma a take a ka cere musu kayan jikinsu a ka fara hukuntasu da hukunci irin nasu na sojoji. Bayan kwana bakwai a ka fara bin komai da ya mallaka na gidan soja a ka kwace, sannan gidan da yasakawa wuta shima a kace sai an biya domin ba nasa bane. Sannan bayan an gama biya kuma za'a harbesu a cikin barikin sojojin dake cikin gari. Wannan shine hukuncin da za'a masa.
Bayan haka suka bamu wata biyu a kan mu biya tarar da a ka cimu, kuma kuɗaɗene masu yawa wanda gaba ɗaya nidashi bamuda koda rabunsu. Daga nan muka wuce gidan Abbana tare da sojoji guda biyu wanda duk inda zamuje suna tare damu har wata ukunnan su cika. A nan muka tattara komai da mukamsllaka amma ko rabin abunda a keso bai kaiba. Mun shiga tashin hankali sosai , muka naimi auro a gurin babanna amma yace baida shi, daga ƙarshe ya ce ko dai Daniyel ya bar masa gida kokuma mu tafi tare. A haka muka cinye wata guda babu komai sai wahala.
Cikin rashin tunaninmu da kuma naiman mufita sai muka tafi garin Katungu domin sayar da gidanku dake can. Alokacin da mukajene a she dama suma naimansa sukaye, a ranar da mukaje bamu kai ga hutawaba suka cika gidan suna zage-zage da cewa sai sun É—au fansa. Babu wanda ya hanasu suka ciri gashin kansa da wandon jikinsa sukace sai yaga abunda zai sameshi. Ganin haka yasa muka baro garin cikin jigatuwa da azabar tafiya. kuma abunda zai baka mamaki komai dake faruwa a gaban waÉ—annan sijojinne, amma babu ruwansu.
Daga nan mukaje gidan wata aminiyata, itama kwana ɗaya ta koremu, to a lokacin ne kuma muka rasa ina zamu dosa. Sai yace muje gidan Titi amma nace a'a kar muje. Dele muka koma gidan babana wanda da gyar ya amshemu a karo na biyu. A nan gidan muka cika wata biyu da kwana tara. A wannan lokacin ne kuma ciwonsa ya zama abun mamaki, domin Bama iya barci kullum abun sai ƙaruwa yakeyi. Hakanne yasa babana ya koremu. A nanne yake tambayata Sarah da Samuel nace suna gidanka.
A ta ƙaice dai su kansu sojojin da sukaga halinda yakeciki sukace har sai ya warke kafin ya karɓi hukunci kuma ko sisi basu taimaka mana dashiba. Hakanne yasa mukazo gidan Titi. Elixa ta ƙara sa tana fashewa da wani irin kuka.
Kowa ya tausaya masa, Muhammad kam kuka yakeyi yana so ya kamo ɗan uwan nasa amma yana tsoran karya taɓo ciwon nasa ya famashi. Muhammad ya ce asbiti za'a kaishi yanzunnan" Elixa ta ce "Ba ciwon asbiti bane dmon munje sunce basu san me ke damunsa ba. Muhammad ya ce "Zamu tafi dashi gida idan yaso zan kira Usman na tambayeshe waye yayi wannan a sirin, yanzuma dan banzo da wayana bane. Haka dai Muhammd da Sadiq da Usha wanda ya koma Auwal suka fara ƙoƙarin ɗaukar Daniyel amma sai sukaji kamar dutse suka ɗauka, haka sukayi iya yinsu amma sun kasa ɗagoshi daga gasa. Shi kuwa baya iya magana sai hawaye da ke wanke masa idanu alamun dai yana jin jiki. Haka dole Muhammd ya koma gida domin kuwa yau zaije KATUNGU.