Sashe 49
Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ATM ɗinsa ya ɗauka ya fito ya kalli Innah da Nana ya ce "Lokacin da mukaje tonon zinaren gol ɗinnan ko? Innah ta ce "Ina jinka? Ya ce "mun samo fa sosai amma da yake ogan namu mugu ne sai ya ce wai muje zai nememu. Kumafa masana abun sunce idan zai bamu sai kowa ya mallaki gida da mota hardama na jari? Innah ta ce "To ai sai kuyi haƙuri indai rabonkune zai nemeku tunda ya ce zai nemeku ɗin. AJ ya ce "To Innah Allah yasa dai da gaske ya ke? Kuma ana bani nawa zamu bar unguwar nan zan siya mana ƙaton gida mukoma. Innah ta ce "Au wato dai bazaka daina wannan shegen son kuɗin naka bako? Abduljabaru ina guje maka ranar da kuɗi zasu jefaka a damuwa. Nana ta ce "Haba mana inna wannan ai hakƙinsane kuma ai ya sha wahala a baya kinga yanzu ai sai jin daɗi. Ta ƙarasa tana faɗawa a kan innar. Itama innar tayi dariya ta na cewa "To amma dan Allah Abduljabaru ka sake kula da mutuncin ka da kuma namu, domin a dundiya babu abu mai wahalar samu kamar mutunci yana zubewa shikenan, idan baka samu wannan kuɗin ba ka koma aikin ka na gidan bredin nann dan Allah karka sake jawo mana abun magana.
AJ ya taɓa ATM Ɗinsa dake jikin sa a zuciyarsa ya ce "Innah kenan ai yanzu saide ma ni na samo dareba ya dinga tuƙani. Afili kuma ya ce "Ok Innah, yanzuma gidan bredin zanje domin susan na dawo. Har zai fita sai kuma ya dawo ya ce "Yauwa Innah da ma akwai sauran kuɗin da ogan namu ya bani lokacin da zamu tafi, yanzu zanje na sayo waya da layi idan naga ya rage to zan zo da ɗan abunda yasamu, kar sai na kawo ki tsareni kina cewa a ina na samo kuɗi. Inna ta ce "To a dawo lafiya amma dai karka daɗe kaga dai ba lafiya gareka ba? Haka ya bar gidan cikeda jin komai yazo masa cikin sauƙi.
Yana fita ya tare mai mashin ya je bank ya ciro kuɗi masu yawa, ya je ya sayo waya ƙirar samsung. Ya siya layi ya tsaya bin layi domin yin welcome bak.
*SALIS POV*
Suna dawowa daga siyan kayan da su Usman zasu tafi dasu, yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya ya sa hula ya nufi gidan su Nana. Tafiya ya keyi yana addu'a Allah dai yasa suna lafiya kuma sun dawo gida. Da mamaki ya ga ƙofar gidan a buɗe sai ya tsaya yana jiran ko zaiga yaro. Yana tsaye a gurin bai ga kowa ba sai kawai ya koma cikin motar yana jiran ko Allah zai kawo wani. Kamar daga sama yaganta tana tafiyarta irin ta kamammun matanan, tafiya takeyi kamar bazatayiba, babu a lamar sauri a cikin yanayinta kumu da alamar a hakan sauri takeyi. Ganin zata shiga gidan batare da ta kula da motar tasa bane yasa ya yi saurin fitowa daga motar ya ce "Nana?
Sauri takeyi ta shiga guda domin ta ɗan daɗe a gidan su Kadija, taje sunsha hira kuma kadijar ta sheda mata cewar tana son AJ, itama tayi murna domin tasan halin kadijar tanada kamun kai gashi bata tara samari. Sauri take ta sanarwa da Innah wannan maganar domin tasan Innah zatayi farinciki sosai, sauri take ba ta ko kula da motar dake kusa da gidan nasuba sai jin Muryar da bazata taɓa mantawa da itaba ta shiga cikin kunnuwanta. Tsayawa tayi ba tare da ta juwoba. Sai da taji ya ƙara cewa "Nana?.
Ƙara sa gabanta yayi ya ce "Nana ina kika shiga kwana biyu nazo bana samunku? Kallon sa tayi cikin ido sai kuma ta sun kuyar da kanta ƙasa tana jin wani tausayinsa ganinn yanda yayi da fuskarsa. Ta ce "Na'am ina uni?
Salis ya ce "No bawannan na tambayekiba. Ina kika shiga? Nana ta ce "Bari nayi magana da Innah sai ka shigo, tana faɗa ta bata tsaya jin mai zaice ba ta wuff ta shige gidan tana jin wani sanyi a rannta na ganin sa cikin ƙoshin lafiya.
Da mamaki Innah ta ce "Allah sarki yaron kirki Salisu ko? Ya ce "Eh Innah fatan dai kuna lafiya?
Innah ta ce "Lafiya lau muke, ai sai muka nemeka bamu gankaba muna ta addu'ar Allah yasa dai ba wani abun suka maka ba, domin nasan basuda imani kasan fa duk wani arne to babu wani imani a zuciyarsa.
Salis ya ce "Ai nima ku nake ta tausayi kar ko sun kaiku wani gurine domin na koma gurin ban samekuba na dawo gida kuma ba kwanan.
Innah ta ce "Ai kaide yaro Allah ne yayi muna da sauran rayuwa a gaba. Nan inna ta kwashe komai ta sanar war Salis har abinda AJ ya sanar musu na cewar yarinyar mai gidan yake turawa ta sato masa kudi shine ya kamata ita kuma ta nuna gidansu shikuma Abduljabaru baya nan yatafi Niger shida uban gidansa shinefa yasa a ka tafi damu.
Salis ya yi shiru yana tunani , kenan Sarah AJ ya ke turawa! to dama a kan haka Daniyel ya kama su Innha! kenan abunda yasa AJ yaje gidan Daniyel kenann. Salis ya ce "Ok to yanzu ina AJ ɗin yake? Innah ta ce "Wai me yasa bazaku na kiransa da sunan da iyayensa suka yanka masa na sunanaba sai wani AJ to me AJ ɗin take nufi? Wata ƙilama sunan wani ƙaton kafirin ne kamar dai shi wanda ya kullemu ɗin, ni bana son naji ana cewa aj, ga suna mai sauƙin faɗa nann amma sai kun wani bawa kai wahala. Salis da Nana sukayi dariya ya ce "To ai Innah aj ɗin ya na nufin Abduljabaru ne, anyi hakanne domin sauƙin faɗa. Inni ta taɓe baki ta ce ku dai kuka sani. Innah ta ce "Ina ɗaya yaron da kuke zuwa tare dashi gurinmu a gidan ƴan sanda? Salis ya ce "Ok Allah sarki nima ai ban san saba dama a unguwar nann yake. Innah ta ce "Allah sarki yanada kirki. Salis ya ƙara cewa "Innah ina AJ ɗin yake? Ta ce "Allah sarki ya je ya sanar da gidan bredin da yake aiki cewar ya dawo, ko zasu sake ɗaukarsa, kasan yaxu na masa faɗa a kan shigewa yaran masu kuɗinnan, domin gujewa jin mutuncin al'umma.
Salis ya ce "Ban ganeba! Inace Hajiya ta ɗauke shi aki! To ko yace bazaiyi bane? To amma ai ɗazu tazo gidannan kuma tace zata bashi wani abun to me ya faru kenan? Afili ya ce "Ok to Innah idan ya dawo ace nazo ban ganshiba kuma zan bawa Nana numbar na sai ta bashi. Innah ta ce "To zata sanar masa a gaida gida. Ta faɗa ganin ya miƙe zai tafi. Ya zaro kuɗi ya ajiye wa Innah ya ce "Gashi wannan babu yawa? Innah ta dinga godiya tana saka masa albark.
Bayan ya fito ya tsaya ya jin gina a jikin motar sa yana tunanin zantukan Innah. Yaushe AJ yaje Niger? Dama yasan Sarah? To Hajiya batazo gidan bane! Yana cikin haka saiga Nana ta fito riƙe da wayarta a hannu ta ce "Salamu alaikum? Ya amsa sai ya ce "Wato kinada waya shine ko ki nemeni ko? "ban reƙe numbar ka a kaina bane, kuma waccear wayar ta ɓata.
Ya ce "Ok baki riƙe numbar na ba amma ni na riƙe taki ko?, lallaikam baki ɗaukeni da wani amfani ba ko? Ta yi ƙasa da kai ta ce
"To ai kaine ka tafi baka sake dawowa ba nima ai ban...sai tayi shiru ta kasa ƙarasawa ya ce "Umhum ina jinki? Ta ce "To ban riƙe numbar ka ba.
Ya ce to yanzu zan baki tawa sai ki riƙe kuma yanzu.
Ta ce "To. Take ya saka mata Numbar sa yayi seveng ya kira saiga numbar nan ta baiyana ya ce "Kema karɓi kimin seve da kanki?
Ta karɓa wayar ta yi seve da Nana. Ya duba ya gani ya ce "Ni haka nayi wa nurbarki? Duba kigani? Ya bata ta duba taga yasa my heart. Ta ce "Nagani ya ce "Me nasa? Ta ce "Ai ba sai na faɗa ba? Ya ce "Ni kuma sai kin faɗa? Ta ce "To my heart. Ta rufe ido a lamar kunya. ya ce "Yawwa haka zaki dinga kirana? Nan dai suka sha hira irin ta masoya sosai kafin ya mata sallama ya tafi. Takai minty ashirin a gurin tana jin daɗin zantukan da yamata kafin ta shiga gida. Bayan ya tafi AJ ya dawo ɗauke da kayan abinci masu yawa da kayan shayi, harda nama. Bayan ya zaunane Innah ta sanar masa da cewar wannan abokin nasa yazo wanda ya tai makemu a gidan ƴan sanda kuma harda kuɗi ya bamu? AJ ya ce "Allah sarki to ina ya ke? Nana ta ce "Ya bani numbar idan ka dawo a baka? Ya ce "To bari wayata tayi chaji zan ƙarba .
Salis kuwa bai je gidaba saida ya tsaya ya sayowa Sarah da Samuel wa ya ganin duk kansu basudawaya sannan yayi salllar magariba da isha kafin ya nufo unguwarsu. Koda ya iso gida bai samu damar sun zauna da Hajiya Babba ba sai kawai ya ba Samuel tasa wayar ita kuma Sarah saida safe idan zasu tafi Katungu. Ai kuwa Samuel yayi murna sosai ganin babbar wayar da ya bashi.
Muhammad ne a ɗakinsa na sama daga shi sai matar tasa bayan ya gama sanar da ita abinda malam ya ce masa game da auransu. Hajiya Babba ta ce "Ƙaryane addinin musulunci ba haka ya ce ba. Da mamaki Muhammad ya ce
"To me kike nufi?
Ta ce "A tsarin Addinimu sai an É—aura wani auran kafin zamammu ya halarta.
Muhammad ya ce "A'a Addinimu wato addinin Musulunci ya ce "Idan har bakiyi wani auranba to kawai zamucigaba da zamammu ne na ma'aurata, idan kuma kinyi wani auran to zaki zaɓa ko ni ko wanda kika aura ɗin.
"A'a ni gaskiya ban yarda da wannan malamin ba, ai koda banyi aureba dolene a sake É—aura wani auran gudun gujewa wani abun.
Da mamaki Muhammd ya ke kallonta ya ce "Aisha ko dai kinyi aurene bayan bananann? Ya tambayeta cike da kokonto a ransa.