← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 67

Sashe 40

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.....Da gudu ta bar gidan bata tsaya sauraron kiran da Kadija ke mata ba har tana cin karo da mamar Kadijan zata shigo ɗakin bata ko bi ta kan ta ba ta kwasa da gudu sai gida. Ta na shiga gida ta tarar da Innah a gurin da ta barta, da sauri ta faɗa jikin innar ta na kuka ta na toshe bakinta. Cikin tsorata da halinda Nana ta shigo gidan Innah ta ce "Nana me ke faruwa? Waye ya taɓaki? Me a ka miki? Cikin kuka Nana ta ce "Innah wallhi walhi yaya ya dawo kuma kuma kuma! Sai ta kasa ƙarasawa ta sake fashewa da wani kukan. Cikin jin haushen abubda take cewa Innah ta ce "Saboda ya dawo shine kika shigo min gida da kuka kamar wacce a ka daka? To saime idan ya dawo, ai dama ni nasan babu inda yaje yana cikin garinnan, kuma in sha Allah sai Allah ya saka mana akan abinda ya sa aka ai kata mana. Cikin rashin sanin abunyi Nana ke kuka tana tsoran sanar wa da Innah abunda taji kuma kar taje abun ya ɓata mata rai! Sai kawai ta ce "Wannan sojan ne ya zo ya kamashi, wai saboda ya dawone yasa aka sakemu. Innah ta ce "To wai dan ƙundun ubansa me ya ha ɗashi da arne? Ina ruwansa da marasa sallah da har zaije ya jawo mana irrin wannan azabar? Nana ta ce "Yanzu dai Innah zanje nemansa Kadija ta ce min tasan unguwarsu harma gidan sojan, saboda haka zamuje tare kinji? "To walhi idan kikasa ƙafa kika bar gidannan da niyar zuwa neman Abduljabaru to ina tabbatar miki cewar bazaki dawo ki sameni a gidannan ba, zan tattara kayana na barmuku gida na shiga duniya ƙila a cikin duniyar na samu waɗanda zasu iya zama dani, dama ai nasan ba gidana bane gidan ubanku ne saboda hk zan bar muku gidan. Da sauri Nana ta rugomo Innah ta na kuka tana bata haƙuri a kan cewar ta fasa zuwa, "Pls Innah ki daina irin wannan zancen bai da ceba samm! Cewar Nana ta na kuka. Innah ta tashi ta bar gurin izuwa ɗakinta tana tunano ma haifin su Nana ɗin. Ganin haka yasa itama Nana bin bayanta ta na kuka, ai kuwa ta na shiga sai ga kiran Dr. Tana ɗagawa ya ce "Ina wa je! Nana ta ce "Innah Dr ne yazo wai yana wa je? Innah ta ce "Tashi kije amma karki daɗe, kuma ban yarda da zuwa ko ina ba. Dr kuwa yau dai ya zo da ƙarfin sa domin baiyana abunda ke cikin zuciyarsa a gurin hasken rayuwarsa.

*GIDAN SOJA*

Addu'a suka duƙufa yi dukkansu domin Allah ya kuɓutar dasu daga hannun wannan ƙaton arnan, ko wa ya manta da komai sai addu'a, wasu kuma suna karatun qur'ani. Muhammad da sauran ƴan uwan nasa wanda suma kaɗan daga cikin ƴan cikin ƙauyan Katungu ne da suka musulunta shine fa Daniyel ɗin ya haɗa dasu, sannan yaje ƙauyan ya sanar wa da iyayensu cewar ai dama idan ka ƙarɓi musulimci kuɗi a ke yi da mutum, saboda haka Solo yaje yayi kuɗi da yaransu. Hakanne yasa suka ƙara ƙiyayyar Addinin Musulunci, wanda har wasu da ɗan dama sun fara nuna buƙatarsu ta shiga addinin saboda yawan zuwan da Muhammad ɗin keyi cikin ƙauyan Katungun, amma yanzu duk sun ƙara jin sun tsani addinin da ma mutanan cikin ta. Hakanne yasa suka fara kashe duk wani ko wata Musulmi da ya shiga yankin nasu. Yanzu dai cikin ƙauyan Katungu babu dama wani musulmi ya shiga.

Muhammad, Umar, Usman, Salis, Hajiya Babba, Laɗifa, AJ. Sune a cikin ɗakin rai bakwai(7) kuma dukkansu musulmai. Ko wa ƙoƙarin karanto duk addu'ar da tazo bakinsa ya keyi, banda Laɗifa wacce tun da ta shiga jikin mahaifin ta take ta kuka har yanzu, Hajiya Babba ma kam izuwa yanzu ta saddaƙar domin bata manta abunda ya ce mata ba, ga kuma ƙarar tashin motocin su da sukaji alamar sun tafi. *(Tofa!)*

Gudu sukeyi sosai wanda yasa suka isa cikin garin Bokon da wuri, dubada yanda jiniyar motocin nasu ke tashi a dukkan hanyar da suka biyo, kowani mai abun ha wa ƙoƙari yake ya basu hanya kar a halakashi. Abun da ya ɗaure wa kowa kai ku wa shine...suna shigowa unguwar da yake ɗin suka ga al'umma a tsaye a bakin gidan, ga kuma hayaƙi da ke tashi. Ko da suka ƙarasa sai sukayi gamo da abun mamaki. Gidan wani ɗan kasuwa ne ya kama da wuta hakan yasa ya laso na kusa dashi, shima ya kamo na kusa dashi, wanda kuma gidan Comandar Daniyel ne a tsakiyar su. Ko kafin ƴan agajin suzo har kowani gida ya gama cinye wa tass. Ganin sojoji yasa sauran al'ummar dake tsaye a gurin suna kallo kowa ya ɗau na kare. Cikin tashin hankali Elixa ta fara rusa ihu har ta manta da ita ɗin wacece, ihu ta kayi tana faɗin irin dukiyar da ta ajiye a cikin gidan, su kansu sojojin mamakin wannan abun sukeyi, domin ai ba wannan gidan bane ya ka ma ta a ce ya ƙone. Shi kuwa Comandar tsabar ruɗewa bai san lokacin da ya tun kari wutar ba, duda cewar wutar ta gama cinye komai amma har yanzu tanada zafi.

Kamo shi a keyi yana ƙwacewa ana ruƙoshi yana shiga. Da sauri ya ya tsaya cak yana wani tunani. Waya ya ciro ya kira ɗaya daga cikin sojojin da ya bari a wancen gidan, ai kuwa tana shiga suka ɗaga. Da sauri ya tambaye su cewar sun ƙona gidan ne? Cikin tabbatar da cika umarnin su sukace "Yess sir. Ai da ƙar fi Daniyel ya ce "Nooooooo a kashe wutar yanzu-yanzu kafin ta cinye gidan?. Cikin rawar baki suka cce "Ai muna saka wutar muka bar gidan domin kar a kamamu. Ta ke Daniyel ya sulale agurin a sume ya na sakin wayar tasa. Elixa kuwa sai ihu takeyi tana kiran sunan mijin nata. Da sauri sojojin suka saka Ogan nasu a mota suka kama hanyar asibiti, shi kuwa Samuel zafin bulet ya hanashi gane a wani hali suke ciki ne yanzu. Suna cikin tafiyane wayar dake cikin motar tayi ƙara a lamar kira daga Captain. Wato Captain ɗin dukka sojojin Benue sts, domin shi dama Comandar ne na iya barikin da yake.

Da sauri na hannun damansa ya ɗaga. Cikin umarni aka buƙaci Daniyel a cikin garin Benue sts yanzu-yanzu. Ai kuwa bai tsaya jin me zai ce masaba ya kashe wayar. Cikin sauri sojan ya sanarwa da Elixa abunda ke faruwa. Cikin tashin hankali ta ce "An ƙona wancan gidanne? "Sojan ya ce ""eh an ƙona. Ai ta ke ta sake sakin wani sabon kukan, sai yanzu taga wawtarsu na sawa a ƙona gidan. Sojan ya ce "Yanzu fa dole saide muje offece ɗin Captain idan kuma ba haka a kwai matsala. Da sauri Elixa ta kalli mijin nata cikin jin haushin shawarar da ya basu ta ɗauki ruwa mai sanyi ta watsa masa, ai kuwa ya saki wata ajiyar zuciya yana far kawa da da wani ihuu! "No Pls don't se Yes Please Elixa don't . Cikin ruɗewa ya fara faɗin (ƙaryane karkice min gaskene dan Allah Elixa karkice hakane)

Cikin tashin hankali ta ce "Pls dan Allah ka nutsu kaji halin da muke ciki. Nan fa Daniyel ya rikice, ganin haka yasa Elixa sanar masa da umarnin Coptaing. Chk ya tsaya da kukan yana kallon dreban nasa, sai kuma ya kai kallonsa izuwa hanyar da suke bi, ta ke cikinsa ya bada wani sauti. Bai ƙara cewa komaiba har suka shiga cikin Makurdi. Saboda tabbatarwa Elixa ta ce da dreban yabi ta ƙofar gidan nasu sugani. Ai kuwa suna shiga unguwar suka tarar da ƙofar gidan cike damutane, ga ƴan kwana-kwana har sun isa gurin sun fara aikinsu, sannan kuma kamar motar sojoji suka hango a gurin harda police, nan fa hankalinsu ya ƙara tashi. Ta ke Elixa ta shiga tunanin idan Sarah tana cikin gidan fa! Shikuwa Daniyel gabansa ne ya shiga faɗuwa yana tinanin Allah dai yasa dukkansu kowa ya ƙone, domin kuwa idan har ba hakaba to tasa ta ƙare, lokacin da ya hango motar police da sojoji kuwa take yasa suka juya da mutarsu suka koma hanyar da zata sadasu da office ɗin Captain.

*SARAH POV*

Da gudu ta fita ta ƙaramar ƙofar gidan kasan cewar dama tasaba bi ta gurin idan zata fita, kuma duk gidan babu wanda yasan tana da makullin ƙofar. Gidan su Usha ta nufa babu ko taƙalmi a ƙafarta, dukda cewar tsakanin gidan su Usha ɗin da gidansu a kwai ta zara hakan baisa ta hau abin hawaba. Sai da tayi tafiya sosai kafin ta isa gidan. Mai gadin gidan na ganin ta a cikin wannan halin ya buɗe mata get yana mai cewa sannu. Bata ko tsaya bi ta kansa ba ta shiga gidan da gudu. Tana shiga palorn gidan sai ga mamar Usha ɗin wato Titi cikin shigar ta zata fita unguwa. Da gudu ta faɗa jikinta tana kuka tana nuna mata hanyar waje. Jin kukan ta ne yasa Usha dake ɗakinsa shima ya gama shiryawa kenan da alamar dai tare zasu fita. Da gudu-gudu ya sauƙo yana ƙarasowa gurin yana mai jawo fuskar Sarah ya ce "Menene? Me a ka miki? Itama Titi cikin tsoron kodai wani abune ya samu ƴan gidan nasu ta ce "Sarah meke faruwa ne? Ki nutsu kiyi magana mn? Da sauri Usha ya ɗau ko ruwa ya bata, ai kuwa take ta sha kusan rabi, wanda dama tana buƙatar ruwan. Sai a lokacin suka kula da yanayin ta, tayi baƙi ta rame ta koma kamar wata ƴar almajira.
Chapter 40 · 0% Book details