← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 67

Sashe 21

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nann take hankalin sa ya ɗan tashi domin kuwa yasan Nana bata barin waya babu chaji, saida takira yakai sau goma amma dai bata shiga. Har ya haƙura sai ya kira number Sarah, itama dai ga numbar ta shiga amma no amsar, haka ya dage da kira amma dai duk ɗaya, sai kawai ya rubuta ɗan ƙaramin text message ya tura mata sannan ya miƙawa Hajiya Babba wayarta kafin suka fara tafiya. Basu samu damar tafiya a ranarba dalilin babu jirgin da zaitashi, sai zuwa gobe. Ai kuwa washegari haka suka tashi da sassafe bayan ansha amarci, suna zuwa basu daɗba jirginsu yabar Nigeria izuwa ƙasar *MOROCCO*.

Ɓangaren su Salis kuwa, da ƙyar sukaci sa'a police ɗin nan ya amince zasu dinga kawo wa su Innah abinci sau uku a rana, hakanma saida sukayi ciniki da police ɗin, domin kuwa yace idan har a ka kamashi to wallahi korarsa za'a yi. Haka dai har su Innah sukayi kwana huɗu a cikin sell ɗin nan amm Daddy baibi ta kansu ba. Salis da Kamal kuwa kullum sai sunje, dukda basa wani samun damar yin magana dasu, domin kuwa police ɗin yace idan a ka gansu to da matsala. Ananne Salis ya tambaye police ɗin a kan waye ya kawosu police station Kuma a kan meye?

Nan police ɗin ya sanar dashi komai game da Daddy, wato ya ce "Comomda Deniel ne ya kawo..."Ai bai ƙarasaba Salis ya miƙe tsaye ya ce "What!! Daniel? Shima police ɗin cikin mamaki ya ce "Yes Kasan shine? Salis bai tsaya amsa masa tambayar ba ya bar cikin police station ɗin cikin sauri kamar zai faɗi. Shikuwa ɗan sandan ganin irin razanar da Salis yayine yasa yayi tunanin kodai Salis ɗin yasan Daniel ɗinne!?.

*GIDAN SOJA*

Yau kana huɗu kenann da kullesu Samuel wanda yayi dai-dai da kulle su Innah da Nana a cikin sell. Har kawo wannan lokacin Daddy bai ƙara zuwa police station ba, sannan bai ƙarabi ta kansu Samuel da Sarah ba. Yanda ya shirya a ransa shine...kwanakin da ya basu na cika zai ɗau hukunci a kansu. Su kuwa Innah da Nana ya barsune a kan har lokacin da shegen yaron zai dawo, idan kuwa bai dawoba, to tabbas kamar yanda ya ce abaya saide su mutu a haka. Har yamatsu yayi ido biyu da wannan A.J ɗin, domin kuwa tun kafin ya ganshi har ya tsaneshi.

Samuel kuwa sun gama shiryawa da shi da Laɗifa da kuma Umar a kan zasu kawo kuɗin gobe. Bayan haka kuma sun shirya a kan Samuel ɗin zai gudu daga gidan bayan komai yayi dai-dai. Ɓangaren Sarah kuwa acikin wannan kwana huɗu tarame sosai kuma kullum sai sun kira number A.J amma har yanzu bata shiga. Tayi kuka har ta godewa Allah. Samuel kuwa yanzu mugun tausayin ta yakeji, domin kuwa yasan halin Daddy tsaffff zai zaneta a kan kuɗinsa. Kaman yanda yace sau biyu za'a ɗinga basu a binci a kullum, tabbas hakanne, idan kuwa an kawo Samuel zaice Sarah tace itama tace yaci. Haka dai zasu zauna suci don dole. Wannan ɗan zaman da sukayi har sunyi shaƙuwa sosai wanda da basuyi ba....

Ko wannan su yanzu tausayin É—an uwansa ya keyi, yayinda Samuel yake shirya yanda zai gudu da ita batare da Daddy ya saniba. kallon ta yayi cikin yaransu na tibi ya ce "Sarah yanzu idan wannan kwana shidan ya ciki AJ É—in bai zoba ya zakiyi?

Cikin kuka da yazama mata aiki ta kwanta a jikin yayan nata ta ce "I don't no! ban saniba, amma inaji a jikina cewa AJ zai dawo gareni, domin kuwa yana sona.

Samuel ya ce "Sister saura kwana biyu fa? kina tunanin zaizo a cikin kwana biyu?

"Ban saniba! Ta baɗa tana kifa kanta a kan ƙafarsa tana fashewa da wani irin kuka mai cin rai!. Tabbas Sarah tana son AJ sosai, domin kuwa ita har yanzu zuciyarta bata yarda a kan cewar kuɗi yayi ya guduba, amma wani ɓangaren daga zuriyar ta tana sanar mata irin son kuɗin AJ ɗin, tabbas tasan aj sosai, tasan halalin sa na san kuɗi, domin yana faɗa mata cewar...

"Sarah duk wani abu da zai kawo min kuɗaɗe to tabbas zanyishi mutuƙar ADDINIMU bai hanaba, inason naga nayi kuɗi sosai kodan na taimakawa Innah ta da ƙanwata da kuma matar da zan aura da kuma ƴaƴana. Sannan zan iya yin komai wajan kare mutuncin family na, zan zamar musu bango a rayuwarsu, bazan barsu suyi kukan rashinaba koda kuwa zan ƙarar da rayuwata a kan hakan.

Da sauri Sarah ta tashi tsaye bayan ta dawo daga tunanin ta ce "No no no AJ bai guduba, bazai iya guduwa yabar family ɗinsaba, a kwai abun da ke faruwa, AJ baisan an kulle su Innah ba da ya sani zaizo koda kuwa Daddy zai yanka shi. Ta ƙarasa da cewa akwai abunda ke faruwa!. Samuel ya kamota yana kuka yana mata sorry. Amma yaƙi sanar da ita cewar harda ita zasu gudu, domin yasan bazata yardaba. Haka dai ya rarrasheta har yayi sa'a tayi shiru tana bai cigaba da tuno magan-ganun Aj akan kuɗi da kuma family ɗin sa.

*LAÆŠIFA. UMAR. POV*

Kallonta yayi ya ce "Gaskiya ni bazan iya zuwa gidannan ba, domin kuwa mutumin yasanni, kuma ya tsani musulmai sosai, bai ƙaunar addinin Muslunci koda kuwa a gurin kasuwacine bare har wata mu'amala ta haɗashi dasu. Cikin jin haushe da kuma ganin tsoron Umar ɗin Laɗifa ta ce "Kaide wallhi anyi raƙon na miji a gurinnan, gaka dai namiji iya namiji amma sai shege tsoro. Umar ya ce "Aini da kika gani inada kiyaye lafiyata harta ƙanwata Hadiza a bokiyar faɗarki to itama tsoranta nakeyi domin kuwa wallhi yarinyar tamkar mai aljannun, tasha faɗa da maza kuma tayi nasara a kansu, shiyasa ake tsoranta daga maza har mata, kema dande baki santa bane da har kika biye mata.

Laɗifa ta ce "Au dama aljannun gareta!? Ta ƙarasa tana zaro ido.

"Eh tanada su masu shegen ƙarfi ma kuwa. Ya faɗa yana dariya.

LaÉ—ifa ta ce "Kaga yanzu dai faÉ—a min gidan su Samuel É—in da kuma sunan Daddy É—insu ni zankai tinda kai matsoraci ne. Ta faÉ—a tana kawar da wancen zancen da sukeyi.

Umar ya zaro ido waje ya ce "Kece zaki kai kuÉ—in!? Bakiji abun da nace ba?

Ta ce "Please faÉ—a min bana son wasa? Tafa da alamar da gaske take.

Umar ya fara address É—in gidan sannan ya ce "Sunan sa Comamdar Daniel!

Cikin rikicewa da nuna alamar mamaki ta ce "What!? me ma kace Daniyal ko wane!?

Shima Umar meƙewa yayi cikin mamaki ya ce "Eh Daniel na ce kin san shine!?

Cikin tashin hankali Laɗifa ta ce "Umar zan kiraka bari naje gida Please, zan nemeka anjima. Bata tsaya taji mai zeceba ta bar shi agurin baki a sake yana binta da kallon mamaki. A fili ya ce "Ninasan bazata iya zuwa gidan wannan ƙaton arnan ba, domin kuwa kowa yasan ƙiyayar sada musulmai a garin nan, ƙwafa yayi yana ɗan taɓa baki irin ko a jikin sa kafin shima ya bargurin cikin jin haushen ta barshi da hawa keke.

*ABDALHA. POV*

Kafin Maryam ta rufo 'kofar d'akin nata har Abdalha ya kamota, kan kace me ya ɗaga hannu ya zabga mata mari, cikin ɓacin rai da jin haushin abunda ta ce ya ce "Ni abokin wasan kine da har zaki kalli idanuwa kice wai sonta nakeyi!? Ya faɗa yana ƙara ɗaga hannu da niyar ƙara mata wani marin, sai sukaga mai gadin gidansu ya shigo har palorn gidan cikin kiɗimewa abunda bai taɓa yiba.

Ganin haka yasa Abdalha ya mayar da kallonsa izuwa gurin mai gadin. Ya buɗe baki da niyar fara yiwa mai gaɗin faɗa a kan shigowa gidanne domin kuwa sun hanashi shigowa, koma me zaiyi ya tsaya daga waje. Mai gadi cikin rawar baki yace "Ranka shidaɗe, ga wasu samari nan sunzo sai bub-buga ƙofar gida sukeyi suna kiran sunan ka suna zagi wai a fito musu da Zainab.

Cikin tashin hankali Mommy ta ce "Ai kagani abunda nake gudu kenann, me ya kaika sace ta!! Shinma wai saceta ɗinne zaisa ta daina waƙoƙin kodai mai!? Mommy ta fara faɗa tamkar zata ari baki. Maryam da Sadiya da kuma Nusaiba da Nura, sai kuka sukeyi, domin kuwa izuwa yanzu suna jiyo ƙarar dukan get d'in gidan. Su kuwa ƴan matan da sukazo ɗaukar katu, jin abundake faruwa ne yasa, suma suka fara ihuuu, domin kuwa ƙarar dukan git ɗin da ƙarfi sukeyi.

Abdalha kuwa hankalin sa ya tashi ganin irin kukan da Mommy da kuma sauran ƙanƴan nasa sukeyi, sannan kuma ga magan-ganun da mommy ɗin keyi. Shi gaba ɗaya ma abun ya ɗaure masa kai, bai masan ta ina zai faraba. Afili ya ce "Tabbas wasu suna bibiyata!! Take ya ɗauki waya ya kira police station ya sanar dasu abunda ke faruwa a gidan su. Suna jikin haka saiga kiran Shek Kabir kabuga, kallon wayan Abdalha yayi wanda shi tsabar ruɗewama har ya manta bai kirashiba. Ya ɗagawa Shek Kabir kabuga ya ce "Abdalha ina ka kai musu yarinya!? Shin dama abun da kake shiryawa a kanta kenan!? Shek yayi maganar cikin ɓacin rai domin kuwa yanzu ya fara ganin saƙonnin da kuma kira akan samari sunje gidan sa. Nann aka fara kiransa har saida ya kashe waccar wayar tasa.

Shiru Abdalha yayi yana mai jin kansa na sara masa. Azuciyarsa ya ce me ke shirin faruwa ne! Harda Daddy. Yana cikin wannan tunani yaji muryar daddy na cewa "Abdulhi bada kai nake bayaniba!? jin aldalha baiyi magana bane yasa Daddy cewa Abdullah..."Kit yaji an kashe wayar. Daddy yabi wayar da kallo yana mamaki, kenann da gaske Abdalha ne ya saceta!?.
Chapter 21 · 0% Book details