← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 67

Sashe 35

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tin kafin ta buɗe ido komai ke dawo mata kaman dai mafarki, hakanne ya sa ta farka ɗauke da addu'ar ta shi daga barci *(Subuhana rabbiyal lazi a'ha ya'na ba'a dama a'mata na wa i'laihim nishur)* Ta na buɗe ido ta sauke shi a kan babban maƙiyinta, wanda a faɗin duniya shine mutum na ɗaya da ya shiga rayuwarta ya keson tauwatsar mata rayuwa, rintse idon ta sakeyi ta na sake tunano komai da ya faru. Tabbas ta tuno komai kuma ta yarda da cewa ba mafarki ta keyi ba. "Ƙwatsam ta ji sauƙar muryarsa a kunnuwanta "San'nu kina lfy? Ya jiki? Babu abun da ke damunki ki. Dr Musa ma ya ɗora da cewa "San'nu me ke damunki yanzu? Cikin dauriya da jajircewa ta ce "Gida na keson zuwa yanzu. Ta faɗa ta na haɗe fuska. Abdalha ya ce "Gida ba yauba sai kin samu lfy. Shima ya faɗa ya na haɗe fuska.

Da sauri ta kai kallonta zuwa gurin da ya ke, ai kuwa suka haɗa fuska cikin ido, yayinda ko wa ya ɗaure fuskar sa kai ka ce ba shine ya gama mata sannu ba. Sun kai minti uku a haka kowa yana kallon juna kuma fuskoki a haɗe babu mai murmushi. Dr Musa da Aisha kuwa sai kallon ikon Allah sukeyi ganin wani irin sabon lamari, wai yau Abdalha Kabir kabuga ne ta re da Zainab Ambato a zaune a guri ɗaya, kuma da a lama wani babban lamari ne a tare da su. Domin shi Dr Musa baisan ta ya ya Zainab tazo hannun Abdalha, ko dai dama soyayya sukeyi a tsakanin su ne, sai kawai ya ɗauki rumut ɗin tv ya kamo wani tasha da suka gabatar da wani abu da ya ɗaure masa kai. Ganin dai har yanzu kallon juna sukeyi ka ka ce faɗa zasuyi tsabar ƙyayar da ke tsakanin su. Dr Musa ne ya ce "Eh kawai ki bari ki ƙara samun lafiya sai kawai ki tafi gida kinji? Ya ƙara maganar ya na kallon saura lokaci kaɗan a fara mai-maita abunda ya keso gani.

Cikin sauri dukkansu suka kawar da kansu yayinda Zainab ta sa ki wani siririn tsaki wanda babu wanda ya ji sai shi Abdalh da ya ga bakinta. Abdalha ya ce "Dr Musa karka damu na gama magana bazata je ko ina ba. Ya na faɗa ya miƙe tsaye zai fita. Yayinda itama Zainab ɗin ta fara ƙoƙarin ta shi daga kan gadon batare da ta yiwa kowa magana ba. Ganin haka yasa shima da wo wa ya na kallon ta. Ta ce "Dr na gode sosai zan tafi nasan yanzu ana nemana a gid"... Ai kafin ta ƙarasa ta ji ana nuna hoton Abdalha a tv ɗin da Dr Musa ya kunna tun ɗazu, a kan ya sace wannan shahararriyar mawaƙyar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, wacce kowa ya santa da suna Zainab Ambato. Sannan kuma yanzu gashi mahaifinta mai suna Malam Adam, wanda shima babban malami ne wanda ya yi suna a faɗin duniya gaba ɗaya, ya kai ƙararr ɗan gidan Shek Kabir kabuga wato Abdalha Kabir kabuga, ya miƙashi kotu a kan zargin sa ce masa yarinya.

Kallon tibin da ke ɗauke da hoton Abdalha da Zainab ɗin ta yi, sai kuma rubutu da ke nuni da ranar da za'a shiga kotun. Cikin tsananin mamaki ta kalli Abdalha shima ya kalleta kafin ta kalli Dr Musa wanda shima ya ke son ƙarin bayani domin kuwa abun ya ɗaure ma sa kai sosai....📝

*Barkan mu da ranar Juma'a🕋 Allah ya amshi ibadunmu. Amin ya Allah*

*Labari na tafiya dai-dai kuwa?*
[10/21 22:05] Aliyu Makko: *ADDININMU*

*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*

*PAGE2️⃣8️⃣*

.........Dr Musa ya meƙe tsaye da ga kujerar da ya ke zaune ya ce "Jiya muna kallo nida Madam naga wannan sanarwar shine abun ya bani mamaki kuma na ce sai na tambaye ku domin kaina ya ƙulle walahi, shin da gaske ne kai ne ka sace ta? Ya ƙara sa maganar ya na kallon cikin idon Abdalh wanda shi kuma ya ke kallon Zainab wacce har idonta ya cika da ruwan hawaye. Cikin kuka da ya kuffce ma ta ta ce "Ba shi ba ne ya sa ceni, ha salima saboda shi a ka sake ni, amma ni ban san dalilinsa na yin hakan ba! "Babu wa ni dalili na wa kawai na yi ne domin Allah da ku ma wanke kaina a idon duniya domin ko wa na tunanin ni ne na sace ki. Dr Musa ya ce "Shek kabuga ni fa ban gane me kuke ce wa ba fa, dan Allah kusanar min da komai, amma to idan ba kai ba ne to su wa ye? Nan ta ke Abdalh ya kwashe komai ya sanar wa da Dr Musa, sannan ya ɗora da abunda ya faru lokacin da ya je gidan su yarinyar da mahaifinsa ya tura sa domin su ga juna. Da sauri Dr Musa da Zainab da Aisha suka kalleshi jin abun da ya ce. "To su yaran da su ka sace ta me ta musu?Cewar Dr Musa cikin mamakin lamarin?

"Wai sabo da waƙar da ta yi ta buɗaɗdiyar wasiƙa. "To suɗin ƴan gidan uban waye da har zasu mata wannan jan aikin!... Kai kuma ka barsu suka tafi baka sa police sun ka ma suba?

Cikin kukan da ya fara fin ƙarfin ta ta ce "Dan Allah inaso na tafi gida ni ɗaya, domin nasan me zan ce wa malam ya fahimce ni, kuma kaima zaka fita da ga zargin da al'umma su ke ma ka, amma dai ni ka ɗai zan je gi da kuma yanzu. Ta ƙara sa ta na fashewa da wa ni sabon kukan. Abdalha ya ce "No tare zamu tafi domin nasan abun da zanyi ko mai ya yi dai-dai kamar yanda na ce a baya. Zainab dai bata yarda ba har sai da Dr Musa _yasa_ baki kafin ta yarda zasu tafi da Abdalha amma sai da daddare domin idon gudun idon mutane. Haka suka yanke akan zasu tafi ɗin.

Ɓan garan gidan su Abdalha ku wa kaman yanda ya amsa musu cewar shine ya sa ce Zainab haka ko wa ya hau ya zauna daram, harda Momy wacce izuwa yanzu basu gama shirya wa da mai gidan nata ba tun abun da ya faru a kan Abdalh wancan lokacin. Suna zaune kamar yanda suka sa ba duk bayan sallar magariba ranar juma'a domin gabatar da karatun littatafan addini da Momy ke ƙara koya musu a duk yan macin ranar. Cikin sauri har yana ƙoƙarin zame wa ya shigo gidan cikin tsan-tsar ɓacin ran abun da ke tafe da shi ɗin, tin kafin ya ƙara so ya fara ce wa "Ina kike ke mai ɗaure wa wannan yaron ginɗi! Yanzu me hakan ya haifar wannan wani irin abun kunya wannan yaron ya ɗauko mana, yanzu a ke sanar min da cewar wai Abdalh ya je gidan Shek gurin yarin yar da na turashi wai yarinyar ta ce bazata auresa ba, saboda abun da ya aikata. Yanzu kuma gashi wai wannan malamin ƙar yar ne wai ya kai Abdalh kotu akan sai ya fito masa da yarinya. Yanzu dan Allah wannan wani irin abun kunya ya ronnan ya je ya kwaso min, a ce wai ni Kabiru gabuga ne ɗana zai je neman aure wa ni gidan amma a faɗin aibunsa! Shek Kabir kabuga ya ƙarasa maganar ya na mai nuna Momy kamar ita ce Abdalha ɗin.

Cikin tsan-tsar tashin hankali Momy ta ce "Kotu fa ka ce Malama? Ta faɗa ta na miƙewa tsaye. Cikin mamaki Maryam ke kallon Daddy jin wai yarinyar ta ce bata son Abdalh. Ita dai ta san Nana ta na son Abdalh sosai, kuma tasan irin addu'ar da takeyi a kan ta samu Abdalha amma yanzu a ce wai yarinyar ta ce ba ta son sa! Kai saide ko an zuga ta kokuma dai a kai wani abun a ƙasa bayan haka. Ta na cikin tunani ta ji Daddy na faɗin. Ni dai Walhi ba zan je kotu na tsaya ni da wannan banzan dattijon ba, bansan komai ba sabo da haka shi da ya je ya taro abun sa shi ne zai jagoranci kayarsa, ha ka kawai yaro lokaci ɗaya ya zo ya zama wani iri, to wallhi xan mutuƙar saɓa masa in dai a kan ƴan bidi'ar nanne, bana sonsu bana ƙaunar ganinsu bare wai har na je na haɗu dasu a kan na sace musu yarinya. To idan na je na ce musu me? Na ce musu dan Allah suyi haƙuri? Ha ka dai Daddy ya dinga sarfa masifa ta idan ya shiga ba ta nan ya ke fitaba, ƙarshe dai ya ƙare da kiran Abdalh amma no amsar, hakanne ya sa ransa ƙara ɓaci, domin yaso Abdalh ya zo ya sanar da shi gidan uban wa ya kai musu yarin ya domin shi dai Daddy bai yarda cewar ya sa ce ta ba, kawai ya masa haka ne domin ransa ya ɓaci. Ɓacin ran Daddy yau kam ya ɓaci, nan Momy ta ke sanar ma sa da cewar ai yau kwana biyu kenan ma Abdalha baizo gida ba.

Ita dai Maryam ta shi ta yi ta bar gurin izuwa É—akinta domin kiran Nana, dan ida kam ba ta yarda cewar Nana ce da kanta ta ce bata son Abdllah ba. Ai kuwa ta na shiga kira ya shigo wayar ta, sunan kamal ne ya baiya na a kan wayar, (kamal wanda Abdalh ya raba su tun da É—aÉ—e wa, a she basu rabubu) "Sorry Man mu na palor muna ka ratu ne wayar kuma ta na É—akina. Kamal É—in ya ce "Ok ba damuwa, amma dai yau zaki zo ko?

"Yes yau ina so zaka rakani wa ni guri, amma fa ni zanzo na sameka.
Chapter 35 · 0% Book details