← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 67

Sashe 26

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko sallama baiyiba ya ƙarasa gurin tsabar a rikice yake ya ce "Ina kuka kaimin Innah ta da Nana Pls? Yayi maganar ne baisan cewar abunda yafito daga bakinsa ba kenann yaci gaba da cewa...Dan Allah ku fito min dasu sune kaɗai gareni pls dan Allah kuyi mgn Walhi zan iya shiga wani hali, idan laifi nayi muku a kaina zaku sauƙe basuba. Kamar haɗin baki yana kaiwa aya duk samarin gurin suka watse suka barshi babu wanda ya tamka masa sai wani guda ɗaya wanda daga gani kasan yafi kowa jin haushin Aj ɗin ya ce "Kai amma Walhi kama raina mana wayo, watoma mune ɓarayin da zamu sace maka u'wa ko? To me suke dashi da har zamu sacesu, kaje can gurin da ka aikata satar ka kanemesu amma ba nann ba. Kasan cewar sunji wai-wai AJ ɗin sata yiyi daga bakin duniya. Saurayin na gama faɗar haka ya bar gurin cikeda jin haushin AJ ɗin.

Shiru yayi yana tauna maganar yaron ta ƙarshe wai sata! sata! sata! Haka yaketa mai-maita sunan sata ko zai tuno lokacin da yayita amma ya kasa ya ce "Nine nayi sata!? To a ina! Kuma yaushe! ƙaryane walhi ƙaryane ni ban taɓa sataba saide wani amma baniba. Ya ɗaga kai domin tambayar gayan amma ko alamarsa bai hangoba, ya juya izuwa hagunsa sai yaga yara suna klonsa kamar wani mahaukaci. Tabbas sai yanzu yasan cewar ashe abokima wani ɓangarene da zai dinga taimaka maka a rayuwa, shi baida abokai duk yaci mutuncin su, ya koresu wai abota ƴaƴan talakawa a tare batada amfani. Chak ya tsaya bayan ya tuno da abokinsa Kamal, Wanda babu irin cimutuncin da bai masaba amma kamal ɗin yaƙi haƙura domin yana zuwa nemansa kokuma yaje su haɗu a gidan bredin da yake aiki a da. Da sauri yatashi domin nufar gidan su kamal ɗin amma ya ji ankira sunansa AJ.

Chak ya tsaya yana juyowa fuskarsa duk ajiƙeda hawaye, idonsa yayi ja duk ya fita a haiyacinsa. Kadija ce ƙawar Nana wacce itama ta samu labarin abun daga bakin ƴan unguwar domin kuwa kowa yaji lokacin da sojojin suka shigo unguwar kuma suka tafi da su Nana ɗin. "Sojojine sukazo suka tafi da Innah da Nana yau kwana huɗu kenan basu dawo ba kuma bamusan inane suka kaisuba. Ya manta da cewar yarinyar ta ce masa basu san me su Nana sukayiba amma tsabar ruɗewa ya ce "Sojoji! mai sukayi, ya faɗa yana ruƙo hannun kadijar kamar itace zata sanar masa da komai. Ta sake cewa Walhi abunda na sani kenan. Tafaɗa cikin rawar murya domin riƙon da ya mata. Kafin aj yayi magana wani saurayi da yasan AJ tare da Sarah ne ya ce...

"Wannan sojan baban wannan arniyar budurwarka ɗain ne yazo ya tafi dasu harda duka da zagin duk wani musilmi dake duniya bama iya kan ƴan unguwaba kuma harda yarinyar a kazo da alamar dai itace ta nuna musu gidan naku, kuma sunzo basu gankaba shene sukayi ram da tsohuwar Allah da batasa hawaba bare sauƙa...sau rayin ya ƙare da cewar damade ba ciki kamataba domin naga itama sai kuka takeyi da alamar dai itama an ɗan samota kafin su fito, kasan fa sojoji basuda tausayi harta ƴaƴan suma tafka sukeyi bare ƴaƴan wasu.

AJ ya saki hannun Kadija wanda shi baima san ya riƙetaba, afili ya ce "Soja Sarah baban ta kenan ya kamata ita kuma ta zo nunani. dalla-dalla zuciyarsa ta faiyace masa komai shikuma baisan cewar a fili yake faɗaba, acikin minty ɗaya zuciyar sa ta sanar masa da duk abunda ya faru, kuma yasan hakanne. Rasa wani irin tunani zai farayi daga ciki domin kuwa yasan yakamata yayi tunani amma ya kasa, sai kawai ya miƙe ya nufi gidan su Sarah cikin dakiyar zuciya, yana tafiya yana tuno irin wahalar dasu Innah suka sha a hannun wannan baƙin kafirin da kowa yayi shedarsa wajan cin mutuncin Addinin Musulunci koda kuwa babu dalili bare kuma a ce akwai dalil. Yana tafiya hawaye na wanke masa ido na tausayin su Innah da Nana.

*ABDALHA POV*

Da sauri Abdalha ya dawo da kallonsa izuwa gurin samarin dake cikin gidan ya ce "Me kuka ai kata mata? Yayi tambayar cikin rikicewa, kafin su bashi amsa yayi gurin da take kwance kamar macacciya ya ɗago fuskarta yaga idonta a rufe, sai kawai ya ɗauketa izuwa matarsa, bai ko ƙara kallon samarinba, ɗaya daga cikin samarinne ya ce "Mlm Walhi taci albarkacinka badan hakaba da daga yau idan akace ta ƙara zagin malamammu a ciki waƙa bazata ƙaraba shegiya kuma har yanzu zamuci gaba da bibiyarta shege ka fasa mara kunyar banza ƴar tasha kawai. ɗaya daga cikin kuma yana ganawa cikin ihuu!. Abdalha baiko bi takansa ba ya hanyar barin gidan. Kasancewar yanzu nemanta akeyi kuma ko ina hotontane ke yawo sai kawai ya kaita gidan likitan sa domin sirri. Tun kafin ya isa gidan ya kira likitan ya sanar dashi cewar yazo gida idan baya gida yanada emergency, likitan ya sanar masa da cewar yana gida yau domin madam ɗinsa bata jin daɗi. Haka kuwa a kayi ABDALLAH ya huce da Zainab gidan likitan nasa.

Shine ya ƙara ɗaukarta har cikin gidan bayan likitan ya taimaka masa, likitan mai suna Musa bai ganetaba domin kuwa yanda ta fita a haiyacinta ga kuma rama da tayi sosai, nan take yace da Abdalha zai fara mata al'lura kafin yaje asibiti yadawo zai ɗauko kayan ƙwaji, nan ya tafi yabar Abdalh zaune kusa da ita yana ƙura mata ido cikin tausayi.

*ZAINAB VOP*

Tinda aka zuba mata wani abu a fuska bata farkaba sai cikin dare. Ihu takeyi tana tambayar a ina take domin kuwa ɗakin yayi duhu. A haka ta kwana a cikin ɗakin babu wanda ya kulata. Washe gari ma sai misalin ƙarfe tara na safe kafin ta ga wasu samari guda huɗu, kowanensu ya rufe fuskarsa da baƙin ƙyelle. Tambayarsu ta farayi cikin kuka domin kuwa harga Allah ta tsorata. "Suwaye ku? Me naimuku Pls Dan Allah karku cutar dani pls? Babban cikinsune ya ce "Tambayarmu ma kikeyi cewar me kike mana ko? To kafin muci ubanki bari mu fara nuna miki dalilin kawoki nan da mukayi shegiya mai kamar ubbanta, masu ƙaryar addini masu son rarraba kawunan musilman gaskiya. Yana kaiwa nann ya zaro wayarsa daga aljihu ya kunna mata waƙarta da tayi mai sunan buɗaɗɗiyar wasiƙa. Babu wanda ya sake yin magana harsaida waƙar ta ƙare har ƙarshe, kafin ya sake dawowa da ita akaro na biyu. Waƙar ta farayi kenan ya kashe ya kalleta ya ce "Daga yau bazaki ƙara yin wata waƙa irin wannan ba, kin zagi malamammu kinci mutuncinsu hakanne yasa mukace sai mun hukuntaki domin kisan cewar malamai ba mutanan banza bane.

Sannan ya ce "Zamu kunna miki waƙar ki dinga fassarata domin kuwa wani guri a har-harɗe tayi maganar. Take Saiyada ta haɗiyi wani yahu maƙot, tayi dauriyar cewar..."Walhi bada kowa nakeba kuma ni nayi waƙarne domin Allah. Saide kawai wani guri da nayi gargaɗi akan wasu, kuma nasan sunji kuma su..."Wani mari taji mai sauƙar ungulu daga gefenta, wanda yasa jinta tsayawa na ɗan daƙiƙu kaɗan, bataji ƙarar wani marin da aka ƙara mataba sai dai taji zafinsa sannan ga kuma bakunansu dake motsi wanda ke nuni da cewar wannan karan dukkansune suke mgn amma batajin me ceke cewa.

Tana kallonsu sai nunata da hannu sukeyi alamar dai zasu iya ai kata mata komai a wannan lokacin. Tana haka taji an ƙara mata mari, kafin ta ɗago ta gane waye anyi boll da ita, sake kamo kanta a kayi aka ɗago buskarta ido cikin ido yake mata mgn alamar gargadi dai, yanayi yana nuna mata hannu wanda ko kaɗan batajii abun da ya ce ba. Tunani takeyi shin abun da tace ne ya ɓata musu rai haka da suke mata wannan dukan. Yana gamawa ya ƙara mata mari aɓarin da aka mata na farko.

Hakanne yasa taji wani abu shuuu ya huce ta kunnanta ta faɗi agurin ta fashe da kuka. Cikin mamaki taji yana cewa "tsabar raini ki kalli idonmu kice wai wani guri ne kikayi gargaɗi ga wasu! wato malaman mune wasu ko? sai kinsan kinyi da malamanmu mahaukaciya babu wanda zaisan ina kike har gaba da abada dan ubanki, dama nifa na tsaneki walhi ban samu damar ɓatar dake bane tun da sai yanzu, yana kaiwa nann ya barta agurin suka tafi. Haka Zainab taci gaba da zama a gurin har yammma kafin aka zomata da abinci ɗan kaɗan babu ruwa. Bayan nan bata sake ganin suba sai washe gari, wato dai kwananta biyu a gurin.

Yauma da safe sukazo kamar ranar farko, suka tarar da abincin da suka kawo mata ko kallonsa batayiba. Babban ya ce "Good Saiyada haka mukeso kar kici abinci kinji? Ya faɗa yana sakin dariya. Kallonsu takeyi cikin wata murya tace "Dan Allah ku barni na tafi gida me kukeso dani kusanar min idan kuɗine zan baku Walhi zan baku koda kuwa nawa kikeso....sannan dan Allah waye yasa ku kumin wannan zalunci? Duk tayi maganar ne babu ko haɗiyar yawu. Ya ce "Ubanki ne ya turomu! Ji kake tass tass tass har sau uku yaci gaba da cewa..."Ke yanzu har kin kai a ce wani ya turomu gurinki! Mune muka turo kannmu, kuma bari kiji ko uban ki wannan mai kama da aljanunnan baida kuɗin da zai bamu bareke ƴar maula. Yana kaiwa ya ƙara mata mari yayi boll da ita, suka fita suka bar mata ɗakin. Tayi kuka har ta godewa Allah kafin ta tsagaita da kukan ta shiga nazari akan Abdalh ne zaisa a mata wannan aikin tabbas shine.

Washe garima haka wanda yayi dai-dai da kwananta uku kenan a gidan. Yauma saida taci uban duka kafin suka jawota zuwa parlon gidan ɗaya daga ciki wanda ba shine oganba ya ce "Munaso kibar wannan aƙidar taku daga yau ki dawo tamu ta gaskiya wato sunna, kuma kiyi mn alƙawarin bazaki koma waccar taku ɗinba koda kin koma gida, kuma kin daina aikata duk wani bidi'a da ubanki ya koya miki?
Chapter 26 · 0% Book details