← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 67

Sashe 41

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alokacin Titi ta ƙara shiga tashin hankali. Usha kuwa ya jawota jikinsa yana kwantar mata da hankali. Sai da ta ɗan samu nutsuwa sannan ta ce "Anty Titi kinsan Solomon? Zumbur Titi ta miƙe tana nuna Sarah cikin tashin hankali ta ce "Me ya faru? Sarah ta ce "Yana raye bai mutu b"...Ai kafin ta rufe baki Titi ta ruƙota jikinta tana neman ƙaryata ta ce "Me kikesone kicemin? Ta ke Sarah ta kwashe dukan abunda ya faru ta sanar wa da Titi da Usha. Cikin tashin hankali Titi ta ce "Solomon bai mutuba? Yana gidan ku? No ƙaryane wannan ban yarda ba. Cikin mamaki Usha ya ce "Dama bayan ke da Daddy kuna da wani ɗan u'wa ne? Da sauri Titi ta ce "Yes mu ukune amma ɗayan ya mutu, wanda shine mafi hankali da tausayi a cikinmu, duk lokacin da na tuno da Solomon sai nayi kuka, idan na tuna da abunda ya faru a tsakanin na da shi kullum sai nayi kuka, yanzu gashi ya mutu "No bai mutuba sai de ko yanzu Daddy ya kashe su, amma idan kina son ki ga ɗan uwanki kizo muje gida walhi yana can kuma Daddy zai kashe su. Ai da sauri Titi da Usha suka bi ta a baya, mota suka ɗau ka suka nufi gidan cikin tashin hankali, wanda shidai Usha abun ma mamaki yake bashi, domin har yanzu bai gano komai ba.

Koda suka isa gidan suna zuwa sojojin da suka saka wutar suna barin gurin, ai da sauri Titi ta kira ƴan kwana-kwana, shi kuma Usha ya nufi police ɗin yan sanda, su kuma police jin cewar gidan Comanda ne yasa suka kai zan cen sama, ai kuwa kafin ka ce me, sai ga motocin ƴan sanda haɗi da na sojoji, suna zuwa suka tarar da motar ƴan kwana-kwana har sun iso sun fara aiki. Titi ta tabbatar musu da cewar a kwai mutane a cikin gidan, hakanne yasa suka fara aikin cikin sauri, yayinda wasu daga ciki kuma suka shiga cikin gidan. Wutar sosai ta ke ci, hakanne yasa wanda suka shiga ɗin suka kasa gane ko wacce hanya da zasubi domin shiga gidan, kana ganin wutar kasan sakawa a kayi dubada yanda ko ina keci. Abun mamaki an duba ko ina na gidan babu ko wa, kowani loko da saƙo anduba babu wani ɗan adam hakanne yasa suka fito suna sanarwa da Titi, ai kuwa ta ke Sarah ta sake kwatanta musu inda ɗakin yake. Ai kuwa cikin ikon Allah suka ga ɗakin, suka ɗauki wani abu mai kama da zare wanda da irinsa suke buɗe ƙofa.

Saida suka sha wahala sosai kafin ƙofar ta buɗu. Ai kuwa saiga bayin Allah a yashe a gurin, wuta ta kusa cinye saman ɗakin wasu daga ciki sun suma, wasu kuma sun fita a haiyacinsu, har wuta ta fara faɗowa daga sama a kansu. Da sauri a ka fara fita dasu cikin sauri. Suna zuwa ƴan sanda suka kwashesu a ka sakasu a motoci a ka nufi asbiti da su...📝

*Muje dai zuwa*

*S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*

*S REZA ✍️*

*First Class writer's asso...*

*PAGE3️⃣2️⃣*

.....Da sauri a ka ƙarɓesu a asbiti Titi ta ce "Usha da Sarah su zauna a gurin su Salis ita kuma tananan zuwa yanzu. Tinda ta fita bata dawo ba, sai lokacin Usha ya ce da Sarha ta shiga toilet ɗin asibitin tayi wanka, ita ku wa sai kallon fuskar AJ takeyi wanda idunsa ya kumbura ga kuma bakinsa shema kumbure tsabar duka, batasan lokacin da wasu diraran hawaye suka biyo kuncintaba. Usha ne ya sake yin magana a karo na uku, sannan ta kalleshi ta ce "Wannan shine AJ Daddy ne yasa a ka masa hk. Tana faɗa tabar gurin cikin kuka ta nufi toilet ɗin shi kuwa Usha yabi ɗan yaron da a kace shine AJ da kallo. A fili ya ce "To shi kuma AJ ɗin me ya kawo shi gidan da har za'a haɗa da shi, sannan yana mamaki ganinsa ƙaramin yaro. Ɗakin da su Sarah suke a ciki ne a ka kwantar da Salis da laɗifa da AJ. Sai kuma ɗaya ɗakin a ka kwantar da Muhammad da Hajiya Babba wacce duk tafisu jigatu wa domin ita wuta ta faɗo mata daga sama. Sai Umar sai Usman.

Hannun yayan nata ta kamo a cikin na ta, sannan ta ɗora a fuskarta tana rusar kuka tana cewa "Pld Solo ka tashi walhi ina buƙatar ka a rayuwata Pls And pls, kuka takeyi sosai wanda kana gani sai ka tausaya mata tsabar yanda ta fita a haiyacinta, tana cewa "Dama ashe kana raye, dama baka mutuba? PLs Solo. Amma ina baima san tana yiba. Likitane ya shigo ɗakin yana mai bata haƙuri a kan ta daina kuka anjima kaɗan zai farka babu abunda ya samesa, da kyar dai Titi ta bar ɗakin. Da kudu-kudu ta shiga motarta ta bar asibitin tana tafiya tana kuka har ta isa gurinda zataje.

*DANIYEL POV*

Suna isowa yasa aka wuce da Samuel asbiti domin har yanzu kuka yakeyi yana kiran zafi zafi. Cikin tsoro ya tura ƙofar office ɗin ya shiga, yana shiga ya tarar da manyan Sojoji a zaune a gurin ko wa fuskarnan a murtuƙe, kasa zama yayi sai bin kowa da kallo ya keyi. Caraf idonsa ya sauƙa a kan Titi wacce ke zubar da hawaye tsabar rikici. Ɗaya daga cikin sojojin ne ya umarce sa da ya zauna, ai kuwa da sauri ya zauna yana ci gaba da kallon ƙanwar tasa cikin mamakin me ya kawota nan gurin. Wani ya kalli Titi ya ce "Mai-maita abinda kikace a kan ɗan uwanki? Ai kuwa cikin kuka ta fara zaiyano komai da tasani akan ƙulle ɗan uwansu da yayi, sannan ta ɗora da wutar da yace a saka a gidann, sannan ta ce "She kara kusan ashirin kenan yana kulle wai dan saboda kawai ya koma yin Sallah, kuma bama shi kaɗan ya kulle ba mutum uku, sannan kuma ya kamo family ɗinsa suma ya haɗa a gurin zai ƙone. Titi ta ƙara sa tana fashewa da wani sabon kukan. Kowa dake gurin suka zubawa Daniyel ido cikin tsan-tsar mamaki, da yake a cikin gurin harda Musulmai. Wani ya ce da Daniyel "Kaji abinda a ka ce shin hakane ko ba haka bane? Ya ce "No No is my brother"..."Na ce hakane ko ba haka ba ne? Cewar sojan cikin ɓacin rai wanda shima musulmi ne kuma a gaba dashi ya ke?. Ganin yaƙi yin maga ɗayane yasa Captain ɗin cewa ya cire rigar jikin sa, ta ke ya cireta ya ajiye.

Captain ya ce "A tafi dashi kafin oga ya zo( Wato shugaban sojojin gaba ɗaya) haka a ka tafi dashi ya na sanar musu da cewar ƙaryane shi daii bai yi komai ba. Captain ya ce da Titi ta koma asbiti idan har oga yazo za'a nemeta daga ita har ɗan uwan nasu, haka ta amsa cike da jin daɗin za'ayi adalci.

*ABDALHA POV*

Kallon su tayi tana son tabbatar da abunda Isa ya tsara mata ta ce "To Abdalha kasan da cewar ba kaine ka saceta ba to menene yasa kace kaine? Abdalha ya ce "Momy idan nafito na ce bani bane nasan babu wanda zai yarda dani shine yasa kawai na ɗauki laifin. "Yanzu dai ai tafito ko? Ya ce "Eh Momy "To masha Allah tundade yanzu ta dawo kuma cikin ƙoshin lfy ko? Isa Abdalha suka haɗa baki ƙurin cewa Lfy lau ta dawo. Momy ta ce "To yanzu bari na kira Abbanku sai ka masa bayani domin har yanzu fushi ya keyi da kai sosai. Tin daga nesa Shek Kabir kabuga ya fara ce wa "Duk naji bayanin da kukeyi kuma ka sani idan ma kayi hakane da wata manufa to ina dai-dai da kai, kuma ka ce da wannan yaron dake kusa da kai ya tashi ya bar min gida bana son ganin sa. Cikin mamaki suka kalli gurin da Daddy ke sauƙowa rai a mugun ɓace. Abdalha ya kalli Isa shima Isa ya kalleshi sai Abdalha ya dawo da kallonsa izuwa gurin Daddy. Ya buɗe baki zaiyi magana saiga Sadiya da Nusaiba da Maryam duk sun fito daga ɗakunan su dalilin jin Daddy na faɗa. Basu kula da baƙon dake tare da Abdalha ba saida suka nemi guri zasu zauna idon Nusaiba ya sauƙa a kan Isa da ya kafesu da idu. Ai da wani irin tsalle Nusaiba ta meƙe tana mai kare jikinta kasan cewar kayan barci ne a jikin ta. Itama Sadiya ta miƙe a kunyace ta bar palon. Ita kuwa Maryam guri ta samu ta gyra zama ko a jikinta. Kallon da Abdalha ya watsa mata ne yasa ta saki wani siririn tsaki ta kawar da kanta daga kallonsa.

Kawar da kansa yayi daga kallon ta ya dawo da kallonsa zuwa ga Daddy ya ce "Pls Daddy kayi haƙuri tundade ai yanzu yarinyar sa tadawo kaga ai komai ya wuce. Daddy ya ce "Komai ya wuce amma ya barmin gida domin nan gidan ba gidan ƴan bidi'a bane, idan kuma kanaso daga kai harshi ranku ya ɓaci to? Da sauri Momy ta ce "Tirr da irin wannan halyyar taka, idan har haka sunna ta koyar da kai to tabbas ba sunna kakeyi ba. Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana koran baƙo daga gidan sa? Shin yana gaba da kowa? Koda mutum ba musulmi bane yana kywatata zamantakewar su, kuma muma haka ya koyar damu, dan Allah kayi aiki da iliminka ka ganar da jama'a gaskiyar da kuke ɓoyewa? Daddy ya ce " Bakisan waye Adamu bane shiyasa kike cewa shi ɗin mlm ne . Da sauri Momy ta ce "Kenan a kwai wani abu a tsakanin ku bayan babbancin aƙida? Daddy bai tsaya saurarontaba ya bar palon cikin ɓacin rai. Momy ta baiwa Isa haƙuri sannan ta musu wa'azi mai ratsa zuciya, sannan Isa ya bar gidan cike da tunanin to meye tsakanin Mlm da Daddy. Ita kuwa Maryam duk abunda a keyi tana zaune a gurin tana jin komai dama ita kaɗai ce ta fita Zakka a gidan, domin babu ruwanta da wannan faɗan nasu, sannan ta kafe Isa da ido duk ta hanashi sakewa a gidan har saida ya fita.
Chapter 41 · 0% Book details