← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 67

Sashe 43

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Karna ƙara jin wannan maganar ta auran ka da Zainab da kuma shi Isa da Maryam ɗin, kuma ka tashi ka je ka ba Daddynku haƙuri yanzu nann? Momy na faɗa ta miƙe zata bar gurin Abdalh yayi saurin cewa..."Momy ina sonta kuma ita nakeson aura, shin hakan bai dace bane? Cikin tsananin mamaki ta ce "Eh bai daceba, kuma karka sake min wannan maganar, kema kuma karna sake jin kiyi magana da shi yaron. Momy ta faɗa tana nuna Maryam cikin ɓacin rai. Da sauri Maryam ta gyaɗa kai tana jin cewar ai ku wa ba zata saɓu ba.

Cikin ƙarfin hali Abdalha ya ce "To Momy a kam me? Ya ci gaba da cewa..."Haba Momy karkema ki zama karmar Daddy mana, kecefa kike ƙaramin ƙaurin gyiwa akan abunda muke aikatawa, amma yanzu kema kina so kiyi hani da abunda Allah bai hanaba. Dan Allah Momy ki tayani shawo kan Daddy ya gane cewar badon ɓacin ransa zanyi ba. Momy ta kalli Abdalha taga hawaye sun wanke masa fuska ta kawar da kai ta ce "Abdalha duk abunda zaka aikata mutuƙar babu yardar iyayenka to wannan abun ba zai taɓa albarkaba, kuma kaima kasan da haka, amma yanzu abinda na keso da kai shine..."Kaje ka samu amincewar daddynku idan har ya yarda to nima na amince.

Abdalha ya ɗaga kai ya kalli Momy ya ce "To amma Momy kema ki tayani masa bayani mana ko zai sauƙo da hanzari? Da sauri Momy ta ce "A'a yanzu idan ba sokake dukkanmu ran kowa ya ɓaciba to ka je da kanka. Abdalha ya ce to Momy na gode sosai kuma zan dage da addu'a domin Daddy ya yarda. Momy ta katseshi da cewar "Ita yarinyar ta yarda zata aureka ne? Kuma iyayenta sun amince? Abdalha ya sauke wata a jiyar zuciya ya ce "itama mahaifinta ne kawai matsalar, amma mamarta ta yarda. Saide kuma.... Sai yayi shiru yana sosa ƙeya. Momy ta ce "Uhum sai de kuma me? Abdalha ya ce "Momy har yanzu fa ban ban sa sa nar mata ba.

Momy ta ce "Ban gane baka sanar mata ba? Kafin Abdalha ya yi magana sai jin dariyar Maryam sukayi. Dariya ta keyi sosai ka kace sabuwar kamu ce. Ta ce "Momy Yaya fa yana nufin bai sanarwa da Zainab É—in cewar yana sontaba.

Sadiya ma abun ya bata dariya amma ta shanye kayarta a cikin ta. Galala Momy ta ke bin Abdalha da kallo ta ce "Da gaske? Ya harari Maryam ya ce "Umm, amma ai tasan ina sonta kuma itama haka dama kawai kune nakeso kuyarda. Momy ta ce "Allah dai ya kyuta. Tana faÉ—a tabar musu palon itama Maryam ta tashi da gudu ta koma É—aki. Abdalha ya saki dariya yana kamo hannun auta Nura suka nufi É—akin Daddy.

Haka dai Abdalh ya ci gaba da shawo kan Daddy amma Daddy ya ce "Mutuƙar shine zai masa aure to bazai aura masa ƴar gidan Malam Adamu ba. Ɓangare ɗaya kuma har zuwa yanzu bai sanar da Zainab cewar yana sontaba, amma dai yana nuna mata alama kuma itama tana gane wa. Sai a kayi Sa'a itama ta na sonsa, saide kuma ya makara domin yanzu haka lokacin auranta matsowa ya keyi. Abdalha kuwa shi ya ma manta da cewar an kusa auran Zainab, burinsa ma hsifinsa ya yarda sannan ya tunkareta. Yanzu haka auran Zainab ya rage wata guda da kwana huɗu, amma har yanzu babu wani canji a gurin Daddy. Abdalha kuwa yanzu hira sukeyi da Zainab ta waya Sosai, amma dai bai furta mata kalmar soba. Haka suma Sadiya da Nusaiba auranmsu saura wata ɗaya da kwanaki. (Wannan kenann)

*BENUE*. *ASIBITI*

Cikin aminci Allah jikin marasa lafiya yayi sauƙi. Yau kwanansu shida a asibitin kuma yaune za'a sallamesu. Dama dukkansu jikinsu yayi sauƙi Hajiya Babba ce dai tafisu shan wahala, sai kuma Laɗifa itama da ta samu buguwa a ƙafarta. A.J kuwa lokacin da ya farfaɗo sunan Innah ya fara kira yana mai sakin wani sabon kuka, amma sai yayi ido biyu da Sarah a bakin gadonsa tana sakar nasa murmushi. Tin baya sake mata hardai ya fara bata haƙuri domin kuwa kunyarta ya keji, kullum idan sun zauna sai yata bata haƙuri ita kuma ta ce ta haƙura ai dama bai mata komai ba. Cikin kwana biyu har suka sake sakewa da juna, Sarah kuwa duk lokacin da ta ganta a gaban AJ ɗinta sai wani sanyin daɗi ya mamaye ta. Tana son AJ sosai sonda bata san asalinsa ba, tanada tarin tambayoyi da take son masa amma tsabar farin cikin da take ciki na ganin sa cikin ƙoshin lafiya yasa duk ta tattara ta ajiye a gefe guda. Titi da yayanta Muhammad kuwa kuka suka sha sosai tana bashi haƙuri akan abunda ya faru, shima yace babu komai. Salis ma ya samu sauƙi so yake a sallamesu yaje ga masoyiyarsa, laɗifa kam ganin babu wanda yaji ciwo sai ita sai kawai ta ƙara lanƙwaɓewa sai zuba shaƙwaɓa takeyi, Ga kuma haushin yanda taga Sarah na mannewa AJ kamar ta sanshi, sannan ga ɓakin cikin rashin Samuel ɗinta, ko yanzu yana wani hali harbin da a kamasa!. Umar da Usman ma duk sun dawo haiyacin su. Cikin sauri Dr ya shigo ɗakinda suke tare da wasu manyan sojoji, suka yiwa Titi da Muhammad tambayoyi game da Daniyel da kuma abunda ya faru. Ai kuwa Titi ta kwashe komai ta sanar musu. Dr ya basu sallama sannan a ka haɗasu da masu kula dasu harna tsahon lokaci, kuma suka tabbatar musu da cewar za'a buƙaci ganin su a kowani lokaci. Dr ya kamo hannun Salis ya ce "To Allah ya ƙara lafiya , saide a dinga kula da Hajiya domin na kula tana cikin damuwa, kuma idan wani abu ya faru za'a iya nemana. Salis ya saka masa numbar sa sannan sukayi sallama.

Anfito za'a tafi AJ ya ce shi abarshi ya tafi gida domin kuwa har yanzu a tsorace yake. Yasan meye aure kuma yasan meye mutuwa kuma ya gane cewar yanzu idan bai rabudasu Hajiya Babba ba to tabbas a kwai matsala, wata zuciyar kuma tana tuno masa da miliyan hamsin É—insa.

Salis ya ce "No kazo muje gida idan kayi wanka kaci abinci ka huta sai na rakaka? Sai a lokacin komai ya dawowa Hajiya Babba. Ai kuwa cikin sauri ta ce "A'a ai tunda kaji yace gida zaije to ai kawai abarshi ya tafi, domin ko ya biyomu bazai samu nutsuwa ba, kawai ya je, Allah ya kiyaye hanya. Hajiya ta ƙara cikin rawar murya kamar mara gaskiya. Laɗifa ma ta ce "To dama me zaije ya mana a gida bayan suma sunada nasu gidan, kawai ya tafi abunsa. Ta faɗa tana hararansa. Sarah da Usha da Titi dai basu san me a ke cewa ba amma sun lura da cewar AJ ne keson tafiya gidan su. Muhammad ma ya sa baki a kan yazo amma Hajiya Babba ta ce sam bazaije ba, abun ya bawa Salis maku. Ya ce "Wai Hajiya ko kin manta da cewar AJ dreban kine?

Cikin sauri ta ce "Eh na sani yanzu na bashi hutu harya warware. Kafin Salis ya sake magana Sarah ta ce "Pls My AJ karka ƙara tafiya ka barni dan Allah Pls kazo mu tafi. Take Hajiya Babba ta kalli AJ shima ya kalleta, sai kuma ya tuno da dokokin auransu, ita kuma gabantane ya faɗi jin kamar Sarah ta san shi. Laɗifa ce ta ƙwace hannun AJ daga na Sarah ta na cewa "Rabu dashi ya tafi umma ta gai da Aish. Cikin dabara Hajiya Babba ta yiwa AJ magana da ido alamar ya tafi zasuyi magana ta waya.

Haka kuwa a kayi badan Sarah ta soba suka nufi gidan Hajiya Babba baki É—ayansu. Kowa yayi wanka sannan Muhammad da su Umar suka je shagon aski a ka gyara musu fuskoki aka dawo gida aka fara hirar bayan saduwa amma banda Hajiya Babba.

Hajiya Babba ɗakinta ta shiga ta rufe da maƙulli sannan ta fara zuwa da dawo a cikin ɗakin cikin neman mafita. Afili ta ce "Na shiga uku ni Aisha wannan wani irin masifa ne ke nufoni, yanzu dai a zahirin gaskiya inada aure kuma gashi tsohon mijina ya dawo, to yanzu a ƙaidar Addinimu ko da nasa AJ Ya sakeni to ai dole sai an ƙara ɗaura wani aura. Wata zuciyar ta ce "To kawai ki sanar masa da cewar kinyi aure amma mijin ya mutu sai kawai a ɗaura muku wani auran. Ajiyar zuciya tayi sai kuma ta ce "To Salis da Laɗifa fa ai sunsan banyi aureba, kuma idan suka sani a kwai matsala. Cikin tashin hankali Hajiya Babba ta fashe da wani sabon kuka tana ɗoraj hannu a kai tsabar rashin ma fita.
Muhammad kuwa ganin Hajiya Babba mata gurinne ya kalli Salis ya ce "Ina Aisha? Kafin yayi magana Titi ta ce "Solomon Pls".... Kafin ta ƙarasa Salis ya ce "Pls Anty Titi not Solomon is Muhammad. Ya faɗa cikin wasa ai kuwa dukkansu suka fashe da dariya, Titi ta ce "Ok Oga Salis naji Muhammad. Titi tayi gyara murya ta ce "Wai Hajiya ita aisha ɗin tunda solom or sorry Muhammad ya tafi bata sake yin wani auran bane? Ko dama Addinin naku baya yarda idan mijin mutum ya mutu yayi wani auran? Gaban Muhammad ne ya yanƙe ya faɗi, domin kuwa tambayar da ya keson ya yiwa Salis da laɗifa kenan amma ya rasa ta ina zai fara....📝

*TOFA! ANA WATA SAI GA WATA*

*BY S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*

*S REZA...✍️*

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Chapter 43 · 0% Book details