← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 67

Sashe 55

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan ba abun kunya ba ne Salis, domin aure na ce muku nayi ba zina na aikataba, wannan ma kawai ba abin farin ciki bane ace mahaifiyar ku tayi aure kuma harda c"...."Ya isa haka Momy ya isa ya isa bana so bana so? "Yanzu auran AJ shine abun alfahi a gurinki? Abin farincik? Shin Momy ko dai kin manta da waye AJ ne? Yaro ne fa ɗan ƙarami, na girmeshi sosai ma kuwa, amma kije ki aureshi? Wahy! wahy! Momy mai yasa zaki aikata mana haka? Shin kin manta da cewar kinada yara a gabankine? Ya ƙarasa yana sake sakin wani kukan. Laɗifa ta ce "Wannan tsinanan yaron ai ko nu zan gyarmeshi wallahi, amma wai Momy har kike iya cewa kin aureshi?

Cikin sanyi rai da a'lamar kuka a muryarta ta ce "Shin Salis lokacin da na ce muku zanyi aure kukaƙi saurarata a wannan lokacin ba kwa tunanin komai? Shin a wannan lokacin ba kuyi tunanin halin da zan shigaba? Har kuka nake yi ina roƙonƙu akan ku barni nayi aure amma ko nayi niya zaku ɓata? Ni kuma na kai adadin da bazan iya jurewa ba shine nayi aure, shin da ba aure nayi bafa!? Hajiya ta faɗa kan kujerar dake bayanta tana sake fashewa da kuka. Kallon mahaifiyar tasu yayi sai kuma ya kalli Daddy wanda ya zuba musu Ido sai ya sunkuyar da kai yana furta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Yana kaiwa nan ya tashi da niyar barin gurin.

Itama laɗifa miƙewa tayi zata bi bayan sa amma Daddy ya tsayar dasu. "Ku dawo ku zauna? Kamar bazasu zauna ba haka suka dawo kowa ya zauna rai a ɓace.

Muhammad ya ce "Salis?

"Na'am". Ya amsa.

"LaÉ—ifa?

"Na'am Daddy? Itama ta amsa kamar bakinta na ciwo.

"Duk wanan abin kune kuka jawo, domin kuwa mahaifiyarku ta ce zatayi aure amma kunce bazaku yardaba shin wace hujja kuke da ita na hanata yin wani auran? Sanan shi yaron da ta aura ɗin yayi ƙaramine kokuma dai yaya? Idan har yayi ƙaramine to mai ya hana kubarta ta auri babba? Addininmu bai hana auran da tayi ba, hasalima taraya sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne! Saboda haka dan Allah inaso kozo muhaɗu mu rufawa junanmu a'siri, dan Allah Salis da Laɗifa kudawo cikin hankalinku, ita kanta sai yanzu take da tasanin yin auran, kuma tayi ƙoƙari zama babu miji harna tsawon shekaru masu yawo, ya kamata mu ɗaya hannu mu godewa Allah da yasa aure ne ya samar da wannan cikin.

Salis ya ce "Nagane Daddy kuma na fahimta na gamsu, amma kuma Daddy naji ka ce harda ci ci....sai kuma ya kasa faɗa yana jin ɗacin abin da zaifaɗa ɗin. "Eh harda ƙaruwa na ciki, amma kusa hakan a ranku cewar Allah yayi sai tayi koda bada AJ ɗin bane, saboda haka kuyi amfanin da tawakalin da a kasan musulmi dashi, ku ɗauka cewar haka Allah yaso. "Amin Daddy amin. Salus ya miƙe ya nufi gurin Hajiya.

"Ɗago ta yayi daga sunkuyan da take sai ya rungumeta yana sakin kuka itama haka. Laɗifa na ganin haka ta miƙe ta bar palon cikin kuka tana zagin AJ. "Kiyi haƙuri Hajiya naga ne cewar duk laifinmune, munyi kuskure kiya fe mana mun tauye miki hakinki da Allah ya halarta miki. Jin haka yasa Hajiya Babba ta ƙara rungumo yaron nata tana kuka ta kasa cewa komai sai ɗan dukan bayansa da takeyi. Sarha da Samuel suma kuka sukeyi ganin yanda suke kuka, take wani irin imani ya shigesu ganin yanda suka warware matsalolinsu cikin sauƙi da min dokokin addininsu. Sarah ta kalli Samuel sai ta miƙe tsaye shima ya bita.

*HOSPITAL (ASBITI)*

Bayan wani lokaci Innah ta farka, aikuwa ta samesu a tsaye a kanta dukkanninsu cikin tashin hankali. Da sauri AJ yazo kusa da ita yana kiran sunanta "Innah? Dan Allah kiyi magana yanzu muna sonki?

"Abduljabaru?
"Na'am Innah ina jinki? Kimin magana dan Allah?

"I'na Salisu?

"Innah bayanan" ya bata amsa yana matsowa

"Abdul baka ɗaukeni a matsayin komaiba, idan ka ɗaukeni da daraja bazan maka magana acikin mutane amma kayi banza daniba...yaronnan ya taimaka mana nida Nana lokacin da ka tafi kabarmu, amma yanzu na fito na samu kuna faɗa dashi har na maka magana amma Abdul kayi banza dani...to ni dai bazan maka bakiba, abin da zance maka shine Allah ya shiyamin kai yasa ka daina wannan halin naka na taurin kai, sannan Nana ta sanarmin cewar yace yana sonta kuma na amince ko bayan raina Salis shine mijinta, kai kuma kaje kayi abin da zakayi domin kafi ƙarfina, kodan kayi kuɗine to, sannan yanzu ka gama zama maƙaryaci yanzu idan nace maiya haɗa ka da Salisu bazaka sanar dani gaskiyaba kuma nasa"..."A'a Innah wallahi na shiryu na daina komai, sanan shima Salis ɗin bansan lokacin da hakan ya faruba, ki daina cewa dan nayi kuɗine walhin na shiryu . Inaah ta ce "To shikenan Allah ya muku albarka, ka dinga rage zuciya Abdul, sannan ka rage son kuɗi da yawa Abdul, domin wani lokaci ko ka samu kuɗin idan ka rasa wani abun naka zakaji dama Allah bai baka wannan kuɗin ba ya barka da wannan abin da ka rasa.

"Dan Allah Innah ki daina faɗin haka banaso jikina na mini wani iri idan kina faɗin haka? Cewar Nana tana durƙusuwa kusa da Innah. Suna cikin haka Dr ya shigo.

A ranar a ka sallamesu Dr ya ƙara jamusu kunne akan a daina ɓata mata rai. Ai kuwa suna dawowa AJ ya ce zai ƙarasa kwashe komai da sukeso na gidannan zaikai sabon gidansu domin daga yau bazasu ƙara kwana a gidan ba. Ita dai Innah bata ce komai ba, haka suka shigar da ita ɗakinta suka kwantar da ita, suka fara fitar da kayan da zasu amfana i zuwa cikin mota. Bayan ya tafi ita kuma ta shiga gyaran gidan. Bayan ta gama ta shigo ɗakin Innah tana cewa "Innah karfa kiyi barci kinga magariba tayi? Jin kamar har ta fara barcinne yasa ta ƙara cewa "Innah!!!!!! Ki tashi!? Nam ma taji shiru, Sai taje harkusa da ita ta ɗagota tana cewa "Kinsan barcin yamma babu kyu amma yanzu-yanzu har kin fara? "Cikin ɗan barcin da ya ɗauke ta ta ce "Nana barni na ɗan kishingiɗa ko zanji barcin nan ya tafi? "A'a fa Innah ai kinsan ba kyu. Haka dai dole saida Innah ta miƙe.

A cikin daran AJ ya gama kaiwa koma nasu, gobe saide kawai su tare a sabon gidan su. A cikin daran Nana ta tambayi AJ abin da Salis ya masa, amma ya sanar mata da cewar babu komai kawai dai yayi tunanin ko zai ɓata mata rayuwane. Badan ta yardaba tayi shiru, shima ya tambayeta tsahon yaushe suke tare? Ta ce "Tin kafin yayi tafiya zuwa Niger. Yayi mamaki sosai amma ya ce "Kuma kina sonsa? Ta ce "Ai shi yana sona" AJ yayi dariya yana tausayin Nana domin yasan idan har Hajiya taji wannan zancen bazata yarda Salis ya auri Nana ba, ko shi Salis ɗin idan yaji bazai auretaba. A ranar a Restaurant sukaje suka sayo abinci, yauma kowa kazarsa da bam ga kayan sha, Nana kam warewa tayi ta zaɓi duk abin da takeso ta sayowa Innah ma nata. Sunyi siyayya sosai kafin suka kamo hanyar gida.

Hira sukayi a daran sosai har Innah tana basu labarin auran iyayensu wato auran mamarsu da babansu, sunyi dariya sosai. Sunci nama sunci abinci sunsha komai dake gurin anaci ana dariya ita dai Innah komai baya mata daÉ—i. Inna ta kalli AJ ta ce "Abdul yanzu gaba É—aya ka daina zuwa gidan kawunka kwata-kwata mai yasa? ÆŠan
Mama-dama ma Nana tana É—anzuwa.

Aj ya ce "Ai Innah kinsan halinsu idan mutum yaje gidan sai kowa ya dinga kawo maka wani ƙablu da ba'adinsa, amma yanzu zan je gobe insha Allah kafin mu tafi! "To Allah dai yasa, kasan shi zuminci yanada daɗi.

Nana ta ce "Aini Innah tin ranar da na karanta miki wannan littafi har kikayi kuka to tinda ga ranar na ƙara gyar mama zuminci. "Innah ta ce "Eh wannan littafin da kika karanta mini a kwanakin baya ko?, ni har yanzu baki bani labarin yanda littafin ya kasanceba. Nana ta ce "To ai haryanzu ban gama karantawa ba, ina cikin karantawa ne a ka kamamuba kuma bayan mun dawo sai banga wayarba, dama Kadija ce ta turamin itama wai yanzu bata dashi.

Innah ta ce "Kai naso jin yanda zata kasance ko idan ƙanin mahaifin nata ya gano cewar ƴar gidan ƙaninsa ce ya zaiyi? AJ ya ce "Ya sunan littafin? Da kuma sunan marubuciyar? Da sauri Nana ta ce "Sunann littafin *UWATA CE SILA.* Marubucin kuma na mijine sunansa S REZA. Dan Allah yaya ka nemomin Pls kaji? Kafin yayi magana Innah ta ce "Walhi marubucin yayi labin cikin hikima da basira, idan har ka karanta littafin to zaka riƙe zuminci da kyu. AJ ya ce "Ikon Allah! Ai kuwa zan nemeshi kodan na ƙaru. Nana ta ce "A kwai wani mai suna Allaji muɗi acikin littafin wallhi mutuminnan da zan ganshi a fili saina zabga masa mari domin mugune, harda mai sunana Nana. Innah ta ce "Ni kuma uwar yarinyar da kuma wannan shegen Uncle ɗin mai koya mata karatunne sukafi ɓata min rai walhi!, ace kina matsayin uwa amma kiyi sakaci da ƴarki akan wani banzan karatun boko. AJ ya kwashe da dariya ganin yanda inna take ta zabga masifa da fushi har hawaye sun fara taruwa a idonta. Ya ce "Innah!!! littafine fa ba gaskebane har kike kuka? Ya ƙara sa yana tashi izuwa ɗakinsa. Nana ta ce "Yaya a'a wallahi true life store ne wannan domin a farkon labarin ma an faɗa.

AJ ya ce "To zan nemo muku saida safe, amma kice Innah ta daina kuka. Ya fita ya barsu suna cigaba da labarin littafin ita da Nana. Shikuma ya fita yana mamakin jin cewar wai labarin na gaskene. Cikin dare Innah ta ke ta faman tari harsaida tasha maganin da Dr ya bata.
Chapter 55 · 0% Book details