← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 67

Sashe 50

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsoro da fargaba da rawar baƙi ta fara cewa "No a'a kawai fa dai ni kawai naga hakan shine dai-dai, kuma ma idan baka yarda daniba kaje ka tambayi su Salis sunema suka hana n"...

"Ok Tom kwata kiyi barci ya isa na gane idan mun dawo daga Katungu gobe zamuyi magana. Hajiya Babba wacce kamar jira takeyi sai kawai ta kwata tana jan bargo har fuskarta. Muhammad ya gyra mata kwanciya ya gir-giza kai ya fita.

Eliza kuwa koda ta dawo asbitiin aka sanar mata da cewar Samuel ya gudu, sai kawai ta hau zagin kowa dake asibitin , da gyra aka rarrashinta ta haƙura amma ta ce anemo mata ɗanta. Tunani takeyi akan ta barsu a gidan su Solomon ne ko dai taje ta kwaso kayanta domin kuwa tanada tabbacin can suka tafi. Wata zuciyar ta ce "idan kika barsu kuma suka koma yin Sallha fa? Wata ta ce "Ta ɗaukosu ta kaisu gidan babanta, a haka dai ta yanke a kan gobe zataje gidan ta karɓo yaranta.

Washegari dukkansu ƴan gidan suka tattara izuwa ƙauyansu wato Katungu, garinda Salis da Laɗifa basu taɓa zuwaba domin gudun abinda zaije ya dawo. Suma kansu su Samuel ɗin sau biyu suka taɓa zuwa, Titi da Usha ma dai bawani zuwa sukeba. Titi da Usha da da Samuel da Laɗifa a mota ɗaya, yayinda Usha ne ke jan su, Titi kuma na gaba, Laɗifa da Samuel na baya. Hajiya Babba da Muhammad da Usman suma suna mota ɗaya. Sai Salis da Sarah da Umar suma a mota ɗaya.

AJ kuwa suna zaune bayan sun gama karyawa sai jin sallama sukayi, bayan aJ ya fitane yaga wata dalleliyar mota a waje, ƙirar corola. Wani sanyin daɗi yaji yana mai hamdala a zuciyarsa, dama tun ɗazu tunanin da ya keyi kenan. Bayan mutumin ya shiga ne suka gaisa da Innah yayi kamar yanda Hajiya Babba ta ce masa, ya mallakawa AJ gida da mota harda wasu kuɗadan, ya ciro takardun gidan ya miƙawa Innah sannan ya miƙawa AJ makullin motar....📝

*Kunsan ranar Lahadi bana typing amm gashi yau na muku*

*Anya masu karatu wannan sirrin zai ɓoyj* ?

*To kunjifa a adddinin su Hajiya Babba sai an ɗaura wani auran ko a wani addinin ta ke ohooo🤗*

*Comments ɗinku shine ƙwarin guiwata*

*By S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*

*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*

*PAGE3️⃣8️⃣*
.... Innah da Nana harma da AJ duk bakunannsu sunƙi rufuwa tsabar farin ciki da abun alherin da ya samesu, Innah ta kamo ƴan jikokinta guda biyu ta rungumosu tana saka musu albarka kamar ba gobe. Kallon kuɗin da mutum ya ajiye musu a cewar sa wai AJ ɗin ya kama wata sana'ar. Nana ta ce "Shekinan yaya yanzu babumu ba zama a wannan gidan. Ta faɗa tana jin wani sanyin daɗi na ratsa zuciyarta. Innah ta ce "Kai amma gaskiya wannan ogan naka ɗan arziƙine Allah ya saka masa da albarka. Dukkansu suka amsa da amin sannan AJ ya kwaso wannnan kuɗin ya ƙirga su naira dubu ɗari biyu ne dai-dai. Innah ta ce "To Abdauljabaru kaga dai yanda Allah yayi damu cikin lokaci ƙan-ƙani sai ka sake nutsuwa domin kaima yanzu Allah ya baka naka, kuma ba ruwanka da surutu domin kasan halin wannan zamanin namu ana jinka da ɗan abun harziƙi sai kaga ana neman halakaka. "AJ ya ce "Haba Innah a naira dubu ɗari biyun za'a wani damu dani, to walhi a wani gidan ma wannan shine kuɗin abincisu na rana ɗaya. Innah ta rafko salamulai tana tafa hannaye a lamar mamaki. Haka dai tai masa faɗa sosai kafin ta ce masa ba yanzu zasu koma gidan ba sai ya fara sana'a tukunna, AJ da yake son a gobe subar unguwar ya ce "No no no ai kawai tattarwa zamuyi gobe-gobe mubar wanga unguwa, sannan ya ce yanzuma zasu tafi da Nana domin ganin gidan. Innah ta ce "A wani unguwa gidan ya ke? "Innah ai ba a kusa muke ba can wajan gidan kwamna nefa. "Har kusa da gidan kwamna, to ai naga gurin yayi nisa, to amma Allah dai ya kyuta. Haka Nana da AJ sukayi wanka suka shirya izuwa sabon gidansu. A'jinkin takardun gidan ya duba yaga sunan unguwar da gidan harda Numbar gidan. Gidane ɗan dai-dai mai ɗauke da ɗakuna shida, sai toilet a kowani ɗaki kicin guda ɗaya palon biyu babba da ƙarami, sai filin gidan mai ɗan girma sai gurin da motoci kamar huɗu zasu faka. Gidan yayi asalin haɗuwa, da a lama dai sabon gidane domin babu komai a ciki. Haka suka dawo cike da shawƙin gidan. A ranar kuma suka ƙara fita da Nana domin siyan wasu kayan su fara kaiwa gidan batare da Innah ta saniba.

Dubu ɗari biyun da Hajiya Babba ta basu ya haɗa da sauran kuɗin da Hajiya babbar ta bashi tun kafin su tafi Cemeron ya haɗa suka shiga kasuwa da sabuwar motarsa. Duk gurin da yaga wanda ya sani sai ya sauƙe glas ɗin motar ya ɗaga musu hannu, masu mamaki sunayi masu tambayar junansu nayi. Burin AJ kenan a ce yau ya mallaki gida da mota ga kuma kudaɗe masu yawa, burinsa ya ganshi a cikin mota wacce kowa ya ganta sai ya ƙara kalla. Yana cikin tafiya wata zuciyar ta ce masa "Yanzu meme burinka na gaba? Yayi shiru yana tunani sai kawai yaji wata zuciyar ta ce "Sarah ce burinka na gaba, ta maka hallacci ta soka da zuciya ɗaya. Afili ya ce "No ƙaryane ba gaskiya bane ba zai taɓa faruwaba Addininmu ba ɗayaba.

*HANYAR KATUNGU*

Salis ya kalli Sarah wacce gaba É—aya tayi nisa a cikin tunanin da takeyi, izuwa yanzu ta haÉ—a komai da zai tabbatar da cewar AJ aure sukayi da Hajiya Babba. To amma yaushe kuma a ina? Batasan hawaye na mata zirya afuskartaba tana jin wani sabon son AJ É—in na shigarta, ita koma me zaiyi tana sonsa, tana haka har saida taji Salis ya kira sunanta. "Sarah! Sarah!.

Da sauri ta goge idon ta ta amsa da "Yes Bro?

Sai ya ciro wayar da ya sayo mata ya miƙa mata ba tare da yace mata komai ba, amma yana lura da ita ta gefen ido. Hanunta tasa ta karɓa tana kallonsa, domin jin ƙarin bayani. "Wayar ki ce idan muka dawo kije kiyi welcome bak.

Taji daɗin kyutar har cikin zuciyarta, amma a fili sai ta kasa nuna masa cewar taji taɗin sai kawai bata ce komai ba ta ajiye wayar a kan cinyarta ta ci gaba da kallon waje. "Sarah inason muyi magana da ke akan saurayinki, kuma banaso kimin ƙarya? Lokaci ɗaya ta ɗaga kai ta kalleshi sai kuma ta gyara zamanta da kyu tana kallonsa yana tuƙinsa kamar ba shine yayi maganar ba. "AJ saurayinki ne, ni kuma a bokinane to saboda haka inaso na miki tambaya akansa? Ya sake yin maganar yana cigaba da tuƙinsa.

"AJ abokinka ne? Itama ta tambayeshi tana kallon kyawawan i danunsa da ya zubasu a kan ƙwaltar da suka tafiya?

"Eh abokinane sannan kuma yayanane.

"Yayanka kamar ya?

Sai kuma ya waske ya ce "AJ yana turaki ki É—aukarwa Daddy kuÉ—i ki kai masa ko?

Da sauri ta sake kallonsa ta ce "Eh amma waye ya sanar maka?

Ya ce "Bani labarin haɗuwarku da rabuwarku? Sarah ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ai bamu rabuba har yanzu muna tare, amma naji Laɗifa ta ce min wai ya taɓa yin aiki a gidan ku ko?

"Eh yayi aiki amma fa aikin bai kwana ko ɗaya ba sukayi tafiya da Hajiya, to bayan ya dawo n... Sai kuma Salis yayi shiru yana tunani ya ce "Innah ta ce yaje Niger baya gida a ka kamasu, kuma lokacin yayi dai-dai da tafiyan da sukayi tare da Hajiya, kuma shi baima san ko tare suka dawoba. Ya ce "Lokacin da Daddy ya kamaki AJ yana gari? Itama ta shiga tunanin ranar rabuwarsu da AJ ta ƙarshe. Idan bata mantaba ranar har kuɗi ya bata bayan sun dawo daga club, kuma a washe garin ranar ne a ka kamata, kuma dama ya ce mata zai tafi ba laillai ta sake ganin sa ba. A yanzu kam Sarah ta gama yarda da cewar AJ aure sukayi da Hajiya Babba auranma na kuɗi.

"Ya ce min zaiyi tafiya ne, bayan haka ban sake ganin saba sai da yazo gidanmu. Nan Sarah ta bashi labarin haɗuwarsu da AJ har zuwa ranar da suka rabu. Salis ya ce "AJ yanada kirki matsala sa ɗaya shine son kuɗi, amma banda wannan gayan ya iya zama da mutane ga sakin fuska ga iya mu'a'mula da mutane, amma a kan kuɗi zai iya yin komai indai ba zai taɓa mutuncinsaba to amma ya akai yake turaki satar kuɗi!?

Sarah tayi shiru tana tunanin kodai a addininsu idan mutum ya aure mamar a bokinsa ba wani abu bane! Ko kuma Salis ɗin bai sani bane, to ko dai ta sanar masa! Haka dai ta keta saƙe-saƙe, shi kuma Salis sai yabon halin AJ yakeyi, tawani gefen kuma yana haɗawa da Nana. Kamar ta tambayeshi sauran abu guda biyun da ta riƙe a hirarr su AJ da Hajiya Babba amma tana tsoro. To me ma zan tabaya bayan komai ya baiyana kansa.

Ɓangaren su Samuel da laɗifa kuwa sukam soyayya suke zubawa babu kunyar kowa, domin izuwa yanzu Samuel ya zubar da makaman yaƙinsa yana son laɗifa ta shiga daga cikin zuciyarsa tukunna. Hajiya Babba kuwa dukda irin damuwoyin dake cunkushe a zuciyarta hakan bai hana sarkin ɓarayin duniya barci yayi wuff da itaba. Tafiyar a'wa ɗaya da wasu ƴan mutuna sukayi sai gasu a bakin titin da zai sadasu da cikin ƙwayan katunku.

Babu laifi yanzu ƙauyan sun samu burji har cikin gari. Usman da Umar da Muhammad tun daga nan suka fafa kalle-kalke domin kuwa garin ya koma musu kamar ba shiba. Titi ce da yake ita tazo tin bayan samun wannan burjin sai ta dinga nuna musu hanya har suka shigo cikin garin. A tsarin dokar garin Katungu duk wani musulmi idan ya sake ya shiga cikin garinnan tofa ya zama gawa, tun labarin da ya riskesu na cewar Solomon ya mayar da yaransu masu yin Sallah kuma an kashesu.
Chapter 50 · 0% Book details